part 13

827 33 0
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Bissimillahir rahmanirraheem


                   *60-65*

Jikin Mama yai sanyi ta rungumeta ita ma ta fara hawaye sannan ta ce "wai Hajiya mai ya ke faruwa dan Allah? ya kamata ki mun bayani kin zauna kinata kuka, dan Allah Hajiya ki mun bayani ga shi dai na sameku lafiya waye to a gadon ba lafiya?"

Nuna mata kawai tai da hannu da sauri ta riketa suka karasa bakin gadon salati tai ta sanar da ubangiji ganin Arfan kwance kamar gawa magashiyan yana jan numfashi da kyar.

Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un! lafiya  Hajiya? Mai kuma ya same shi haka? Kuka ta kuma rushewa da shi dan bata san ta ina zata farai mata bayani ba.

Alhaji nai ya ce "ba wata matsala ba ce Hajiya zazzabi nai mai zafi ya kamashi shi nai ta ke ta kuka na rarrasheta amma ta daga hankalinta."

"Haba Hajiya bai kamata ki daga hankalinki har haka ba, kiyi hakuri kiyi shiru haka dan Allah sai ki kara daga mana hankali, ai alhamdulillah tun da ke kin warke shi ma ya warke." Kukan ta hadiye ganin Alhaji ya samo mata mafita, sai watso tambayar data gigita shi kansa Daddy "yanzu ina ita Umman yaran da Alhaji da Maryam din?"

Wata sarkewa yai dan muguwar kunya ce ta kamashi, ganin sun mata shiru ta ce "ko sun tafi nai?" da kyar Momy ta daga mata kai ta nai mi waje ta zauna Daddy ya ce "a'a Hajiya ta shi zaki nasa driver ya maida ki tun da yana nan.

Saboda yanzu kin ga kin baro Nafeesat ita kadai sai masu jinya kuma tana bukatar kulawarki sosai a halin yanzu daure muje."

Baza ta iya musu da shi ba saboda sirikinta nai akwai kunya tsakaninsu "ba matsala Alhaji Allah ya ba shi lafiya idan na dubata zuwa dare zan dawo naga jikin nasa."

"A'a ki zauna dan Allah nima zan yi kokari nazo na ganku bakwa bukatar komai dai ko?" "A a wallahi akwai komai mungode Allah ya saka da alkhairi" ya fito yasa driver ya maida ta.

Nafeesa ta gaza nutsuwa saboda sam tunanin kanwarta ta ke da mijinta tun da Mama ta fita ta kasa sukuni, Allah kadai yasan abun da ke damunta ba abun da ta ke so irin ganinsu amma bata san ta tambayi Mama tayi laifi.

Daddy nai ya karasa dakin, sun samu sun shawo kan matsalar hawan jini nai yai mugun kamashi wanda Allah nai ya takaita bai kamu da paralyse ba.

Daddy nai ya kira Umma "Hajiya inaso miyi magana da ke tun da cikin nan karami nai, kuma a kansa Alhaji ya ke neman shi ga wani hali hasali nayi tunani tarin abun kunya ya yiwa wannan cikin yawa.

Duk da har ga Allah banso haka ba amma dole ce, mai zai hana a zubar da cikin kowa ma ya huta ita ma yarinyar ta samu nutsuwa, wallahi Hajiya nayi alkawari tun da Allah bai haramta mun auren ta ba zan aureta."

DAN ISKAN NAMIJIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora