5-6&7-8

2.5K 86 1
                                    

[10/3, 4:59 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*

               *NA*

*FAREEDA ABDULLAHI*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Assalamualaikum warahmatullah ina Mika godiya ta ga dukkan masoyana ako Ina suke a fadin duniya Ina Mika godiya ta ga dukkan masoyana Dan Allah kudena Bina private Kuna in turo muku da novel abubuwa sunmun yawa indai nai posting dinsa kanema a group Dan Allah banhana Bina private mu gaisaba Amma ko kace na turo ma bazan turoba gsky Dan Banda lokaci*

            5-6

Tsayawa tai kamar gunki chan wata kawarsu ta dafata nauwara lafiya figigit ta farfado lafiya wlh kinzo kenen nazo naganki ke kadai a tsaye Ina kawarki ta shiga ciki yanzun Nan nima wani sako zan karba yanzu zan shigo ok sai kin shigo tawuce da sauri ta fito da kudin maimuna taraba biyu tadau dubu hamsin takara a nata wlh Bata Isa nabata dubu dariba ita taimun wahalar gwara nakaiwa malam hamsin din yayi mun aiki na mallake alhaji ghali ya manta da wata maimuna mtsww Taja tsaki ta wuce ciki ranta a jagule

Tana shiga ta hango su maimuna da sauran kawayensu dama maimuna mazari ce harta Fara chashewa mtsww me wannan tafini sai dai hasken fatar Amma nafita komai na duniya kyau da komai sai dai bakar fatar Kuma bakina me kyaune bana shafe shafe Amma tunda Fara yakeso zanje nasiyo mai anjima na Fara sawa idanma nono ne zan siyo na nonon tunda nafita duwawu tanata sake sake ta karasa wajen tajawo maimuna gefe kawata gashi yace nabashi mtswww wallahi bakida hankali nauwara wannan uban kudin mezanyi dasu bakisan shiba saboda shegen kwadayi ki karbo Masa kudi yau ma tabbatar baki da hankali

Sanme kudin naki har yakai daga ganin namiji yabaki kudi ki karba sai kinje ko danyan kan Kaine ya yankaki eh naji idan bakyaso kigayamun base kin tsaya yimun dogon sharhiba har kowa yaji lefina Dan na karbi Abu a hannun mijina cike da mamaki ta kalleta mijinki eh insha Allah Dan mungama magana abun yabawa maimuna mamaki tasan ita yace yanaso Taki kulashi Dan bemataba baya cikin iron mazajen datake so Bata da burin auren kudi Amma Wai kiri kiri mijinta ko kunyar idonta Bata jiba dama da gaske itake kwace Mata samari kenan Kamal ma Dan tasan talakane shiyasa dama Ana gaya Mata Bata taba yarda ba seyau ko ajikinta Allah ya Sanya alheri yasa yin na Allah ne indai wannan rayuwarce gaki gata Nan

Indai auren kudine kiyi shi ko guda dayane ki gwada Zaki Sha mamaki kodai harkin Fara bakin ciki da hassada ta sheke da dariya allah ya sawake nauwara nai Miki bakin ciki ko hassada ko Wanda bansaniba bana fatan hassada tashiga tsakanina dashi Allah yasa damu za ai ta juya ta Fara tafiya ungo kudinki a a banaso inje gida ince Ina nasamo nabar Miki keda kayan mijinki ki hada ki rike kyaje kiyi bayani a naku gidan cike da murna tace kinwa kanki Ni gaba takaini sun Kara yawa yau akwai wadaka zamuci kaji nida umma take fada aranta

Lawanne ya jawo ummi ya Bata Mari lafiyayyu guda uku Dan uwarki nizakiwa hauka nizaki gwadawa cin Kai a gida keda ko a kitabul fantsara Babu sunanki mekika sani na cinkai harda za a kawowa yarana Kaya ki jefa musu kayansu ki nadawa Yara duka badai kishi kike ba to ko haukacewa Zaki saina auro Laila wallahi kinsan bana magana biyu ke Baki Isa ba Koda uwata da ubana zasu dawo duniya basu isa Susa nafasa auren Laila ba bare wata ke banza Kuma wallahi kigama haukan ba saki tsakaninmu aurena dake mutu ka raba danke kadaice Zaki iya jure halin Zama dani ko kinki kokinso baki Isa ki wani Abu akan wannan auren ba ya hankadata ciki tanata kuka ga duka ga tsinka jaka dama ya Saba agaban yayanta ma dukanta yake

Yaushe kika Zama Yar iska me kika sani a iskanci kiduba kitabul fantsara suna nane a shafin farko Dan haka dawasa Kika kara korar duk Wanda yazo wajena kema sai jikinki yagaya Miki aurenmu ba saki bare yaji Kuma yanzu zanje na karbo kayan sai dai ki mutu Dan sai sunsa wannan kayan sallah ta kusa Dan bakin ciki Zaki mayar musu da kayansu cikin kuka tasa dariya ai wallahi bazawu taba moruwaba Dan gutsi gutsi na yankasu na mayar Mata dakayanta leda har takalman na farka kutumar uba yau zakisan Dan iskane Ni nizakiwa iskanci a gida

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now