part 12

814 41 3
                                    

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Bissimillahir rahmanirraheem

                  *55-60*

Yana budewa Alhaji Ghali ne ya dawo a lokacin da bai taba tunani ba dan ya dawo da wuri sosai, yaga alamun rashin gaskiya daga gareshi karara amma bai kawo komai ba ya wuce ciki.

Ya fara leka dakunan kasan amma bai ga kowa ba, yaje bakin dakin ta har ya tura ko mai kuma ya tuna sai ya fasa ya wuce dakin su ya cire kayansa.

Sai da gabansa yai muguwar faduwa dan sunyi da wajewa ba wanda zai kara cin amanar kowa tsakaninsu, shi ya sa ya ke taka tsantsan yasan lokacin da ya ke kawo mazansa.

"Haba Alhaji wannan wane irin abu ne? wato zargina kake shi ya sa kake leka dakuna? to ka manta ai baka hau sama ba sai kai azama ka hau ka duba ko na boye wani a can."

"Haba Baby mai yasa kake haka dan Allah! kawai dan na laika dakuna ba wani abu bane, na kwana biyu ban duba  ba ne shi ya sa kuma sai na tuna ka hanani ganin yarinyar nan shi ne kawai nafi two weeks ban ga gilmawarta ba.

Wani tukukin kishi ne ya tasowa Baby Chakwai "eh lallai ka ce kana kewar ta kawai to sai ka je ai ka ganta ina ga hakan zai fi ma" fuuu ya wuce.

Da gudu ya bishi yana lallashi da lallabawa sannan ya dawo suka tsunduma duniyar masha'arsu wadda basa gajiya da ita.

Kwana uku a tsakani Alhaji Ghali na kewar Nauwara dan yana masifar sha'awarta a yanzu amma bai san ta ina zai fara ba da safe ya shirya yai wajen malaminsa.

Ya sanar masa bukatarsa yai binkice kawai ya gyada kai dan tabbas yasan yai wa Baby Chakwai aiki mai zafi akan sa amma zai ba shi dama shi ma dan ya dan dama.

Ya gyara zama "abun da zai faru shi ne zan baka wani magani wanda zaka din ga barbada masa a duk lokacin daka bukaci zuwa wajen ta shi kuma zai zube yai ta bacci har sai ka tashe shi."

Yaji dadi yai farin ciki sosai ya zube masa kudade masu yawa ya taho yana murna da farin ciki.

Bokan nasu ne ya sheke da dariya dan ba'a kira shi Malam ba, "mahaukatan banza da wofi duk kan ku wajena kuke zuwa kowa bai san kowa na zuwa ba, kuma ina nan ina gwara kan ku dan ta kusa kare muku asirin ku ya kusa tonuwa.

Saboda haka gwara na tarkata ya nawa ya nawa na gudu kafin ta kwabe asirina ya tonu, hhhhhh! na samu abun da na samu kuma na dau fansa burina ya cika, gwara na bar nan naje nai sabuwar rayuwa dan na zama hamshakin mai kudi yanzu."

Nan ya dinga wasu surutai yana karanta dalasimai sai ga wani narkeken aljani ya bayyana ya sheke da dariya mai tsanani, "hhhhhh! ya kai aljanu dan mulmuli inaso ka tarwatsa komai burina ya cika a yanzu.

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now