SANGARTA COMPLETE

Galing kay ZulayheartRano89

120K 6.6K 88

labarin soyayya da ban tausayi Higit pa

part 1
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA DAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
ASHIRIN DA SHIDA
ASHIRIN DA BAKWAI
ASHIRIN DA TAKWAS
ASHIRIN DA TARA
TALATIN 30
TALATIN DA DAYA
TALATIN DA BIYU
TALATIN DA UKU
TALATIN DA HUDU
TALATIN DA BIYAR
TALATIN DA SHIDA
TALATIN DA BAKWAI
TALATIN DA TARA
TALATIN DA TARA
ARBA'IN
ARBA'IN DA BIYU
ARBA'IN DA UKU
ARBA'IN DA HUDU
ARBA'IN DA BIYAR
ARBA'IN DA SHIDA
ARBA'IN DA BAKWAI
ARBA'IN DA TAKWAS
ARBA'IN DA TARA
HAMSIN
Complete

ARBA'IN DA DAYA

2.3K 123 1
Galing kay ZulayheartRano89

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

*Wow gaskiya ina godiya sosai masoya, bani da bakin da zan iya kwatanta farin ciki da nake ciki, sai dai nace Allah ya saka da mafificin Alhairi, ina alfahari da ku😍😍*

'''Khadija S Muhammad
         &
Badeeyar Adam (beauty queen) hakika ku ɗin na daban ne, babu abin da zance akan ku, sai Allah ya saka maku da Alhairin sa ya bar mana zumunci har karshen rayuwa. (Aneesa tana gaisuwa lol)'''

_*Sorry sister SHAMSHIYA SALIS wallahi na yi missing contact naki, na yi ta jira ko zan ga maganar ki na ji shiru, amma jiya nasa mu Number insha Allah zaki ganni yau*_
       
 
                  *41*
Ya yi kusan minti biyar a zaune, rungume da Ameesha wacce ke ta sakin ajiyar zuciya, kallonta ya yi cikin tausayawa ya kaima goshinta sumba, tabbas ya jinjina mata don sosai ta yi kokarin amsan lalurar sa, bai so tun yanzu ya nuna mata haka ba so ya yi sai ta ɗan kwana biyu amma sam a daren jiya kasa control ɗin kansa ya yi, gyara mata zama a jikinsa ya yi yana faɗin

"Allah ya maki albarka Maryerm hakika kin cika yar halas."  Jin Dr ya yi sama da ita yasa ta kuma rintse ido don bata son su yi ido hudu, bai zame ko ina da ita ba sai toilet inda ya haɗa mata ruwa masu dan karen zafi, Ameesha batai aune ba sai jinta ta yi cikin wannan ruwan, ai da karfi ta saki k'ara saboda yadda ta ji shigar ruwan jikinta, sam Dr bai damu ba sai ma ci gaba da buɗe mata kafa yadda ruwan zai shiga da kyau yake yi, tun tana mugun jin zafi har ta soma jin dadin sa.

Sai da ya sanya ta cikin ruwan zafi sau uku, sannan ya barta.

"Heartbeat ki yi wankan tsarki ina zuwa." Dr ya yi maganar yana fita.

"To." Ameesha ta amsa idonta a rufe don taki yadda su hada ido.

Fita ya yi ya cire zanen gado ya canza wani, sannan ya koma toilet ya ɗauko Ameesha akan gado ya yi mata masauki, fita falo ya yi bai wani jima ba ya dawo hannunsa dauke da cup din shayi.

"A'a wai har kin kwanta?"

"Dr bacci nake ji."

"Ok tashi ki sha tea sai ki sha magani kin ji ko?"

"To." Ta amsa tana tashi zaune.

"A'a wai lafiya kuwa, shi idon yau an daina buɗe shi ne?" Yana maganar ne yana mik'a mata cup.

Turo baki ta yi cikin shagwaɓa, bata ce komai ba haka ya shiga bata tea a baki ido na rufe kamar makauniya, bata wani sha da yawa ba ta ce ta koshi, magani ya balla ya bata yana shafa mata gadon baya ya ji ta saki gyatsa, babu jimawa bacci ya yi gaba da ita. Gyara mata kwanciya ya yi ya rufe ta da blanket, kafin ya nufi toilet ya tsarkake jikinsa, lokacin karfe uku na dare sallaya ya shimfida ya shiga nunawa Allah farin cikin sa tare da gode ma Allah da ya ba shi Ameesha matsayin mata, yana mai addu'a da babban murya Allah yasa kwallonsa ya shiga raga.

Ya daɗe zaune yana addu'oi kafin ya kwanta rungume da ita a jikinsa, bacci mai dadi ya ɗauke shi, yadda jikin Ameesha ke kadawa ne ya farkar da shi a gigice a lokacin  karfe shida an dade da isar da asbah, kallon ta ya yi a dimauce jikinta babu inda baya rawa  haƙora ta sai haduwa suke da juna, saboda zafin zazzaɓi, magani ya ballo ya bata da kyar ta iya hadiyewa, sannan ya goge mata jiki da ruwan sanyi da towel, sosai zafin jikin ya ragu har bacci ya dauketa, sai lokacin ya samu nutsuwa har ya yi sallar asuba.

Bai koma bacci ba sai zama da ya yi yana jiran ya ga tashin ta,  yana ta zaune har ya soma gyangyadi bai sannan lokacin da wani nannauyan bacci ya dauke shi ba, sun sha bacci inda Ameesha ta soma farkawa karfe tara, yanzu kam jikin da sauki sai dai jinta take fayau da ita kamar iska zai dauketa. Shiga toilet ta yi tare da haɗa ruwa, sai da ta kuma zama cikin sa ta yi wanka hadi da alwala, har zuwa lokacin Dr bai farka ba sallah ta yi, sannan ta tsantsara kwalliya cikin wata jar atamfa dikin riga da siket, sosai kayan suka amshi jikinta, feshe ko ina na jikinta ta yi da daddaɗar turarenta mai sanyin kamshi ta yi, har ta zauna sai kawai ta tashi ta nufi bedroom ɗinta, don tasan Dr ba barinta zai yi ba.

Tana shiga ta haye gado tare da jan blanket, wayarta ta ɗauko ta yi dailling Number Meena, ringing biyu Meena ta dauka

"Hello Meesha amarya ya garin?"

"Lafiya lau wallahi, shi ne tunda ku ka aje Ni babu wanda ya kuma lekowa?"

"Ki bari kawai k'awata, wallahi ko jiya naso zuwa sai Ya Abdul ya hanani."

"Shi yasa nake fushi, ai na gane ashe duk kun koda na bar gidan ne ku huta."

"Haba Meesha wani irin magana ce wannan, karki manta amarya ki ke dole a bar ku ku sha soyayya, anata dirzan amarci."

"Kai Meena wa ye ya faɗa maki? Ko kin manta Dr ustaz ne?"

"Ummh raba ni da yari auran sarki, kin ga yanzu ma awo zan tafi kika tsayar dani, Ummi ta ce in daina bari sai rana ta take kafin in tafi."

"Masu maza bari na barki, don bacci nake ji sai anjima, amma Please yaushe zaki zo?"

"Don Allah ki barni da maganar zuwan nan, inda yayanki ya barni cikin satin sama zan shigo."

"Satin sama?" Ameesha ta tambaya cikin sauri.

"Eh!

"Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama. Bayan sun gama hira bacci ya dauki Ameesha duk da yunwar da take ji.

Cikin bedroom ɗin Dr farkawa ya yi tare da mika bakinsa dauke da addu'a, kara bude ido ya yi ganin babu Ameesha, murmushi ya saki a zuciyarsa yasan guduwa ta yi, tashi tsaye ya yi yana tafiya har wani layi yake domin yunwa yake ji.

Kai tsaye bedroom ɗinta ya shiga, kwance ya hangota ta rufe da bargo, girgiza kai ya yi ya fita, ɓangaren Aneesa ya yi zaune a falo ya sameta tana aikin latsa waya.

Ko dubansa bata yi ba, sai ma ci gaba da abin da take ta yi

"My Anee baki ganni ba ne?"

"Ina kallonka me zan yi ma?" Ta ba shi amsa cikin ko in kula.

"Ko arzikin gaisuwa ba zan samu ba?"

"Kamar baka ko ya min ba."

"Ok kawo min break."

"Break wani irin break kuma?" Ta mai tambayar cike da rainin hankali.

"Kina nufin baki yi break ba? Kuma ai a kwanakin nan da zamu yi ke ya kamata ki rika yi mana abinci."

Wani irin tashi tsaye ta yi tana hankada masa harara "Lallai Dr Asmad sannu, wato kai ka je ka kwana da mace, sai ni da yake shashasha ce sai na yi maku girki ku tashi ku ci ko? To wallahi baki isa ba, ba a haifi matar da zan bauta wa haka ba, can ka je kasa ta yi ma girki." Da zallar masifa take maganar.

Girgiza kai Dr ya yi domin gaba daya maganar Aneesa ta gama daga masa hankali, yarinya karama kamar Aneesa ke faɗa masa magana yadda ta ga dama, Allah ya taimaketa ba ya da agenda ta duka mace wallahi da sai ta gane kurenta, kada kai ya yi kawai ya mike cikin ɓacin rai ya dubeta

"Kina nufi bazaki girka ba ko?"

"Eh! Ta faɗa da babban murya.

"Gud." Shi ne abin da ya faɗa ya bar mata falon.

Mtsss ta rakashi da dogon tsaki.

Nutsuwarsa ya tattaro lokacin da ya shiga bedroom din Ameesha, ganin ta buɗe ido yasa shi sakin murmushi cikin sauri ya k'arasa inda take ya na faɗin

"Cutie har kin tashi?"

"Eh" ta ba shi amsa fuskarta ɗauke da murmushi.

"Ok bari na yi wanka shaf-shaf in nemo mana abin da za mu ci, nasan kina tare da yunwa ko sorry."

"To." Ta amsa tana sauka.

A tare suka shiga bedroom nasa, ganin ya shiga toilet yasa ta fita, kai tsaye hanyar kicin ta yi, sai da ta haɗa duk abin da take buk'ata ta sannan ta soma aikin ta cikin gwarewa, nan da nan kamshi ya cika kicin ɗin break ta haɗa  masu lafiyayye. Bata son abincin siya sam, da tasan haka da tuni ta gama haɗa masu.

A nutse take aikinta saura kadan ta kammala, sam bata ji motsin shigowar sa ba sai ji ta yi an rungumota ta baya, sosai ta tsorata har ta bude baki zata zuba ihu ya yi saurin rufe mata baki yana faɗin

"Cutie shi ne ki ka taho kicin kina aiki alhalin baki da lafiya kuma na ce maki zan fita in sayo mana me yasa?"

"Sorry beby wallahi gani na yi duk wannan kame kamen ba zai kaimu ba, kuma gashi time ya yi nisa yanzu fa sha daya ake nema." Ta yi maganar tana shigewa jikinsa.

Shafa kanta ya yi tare da bata sumba a kumatu ya ce

"Kar ki damu cutie na baki uzuri, amma daga yau sai kin yi sati kafin ki fara girki."

"Yawwa na gode beby, bari na kwashe wancan dankalin kar ya kone."

"No! Zauna anan ya yi maganar yana zaunarta a kan kujera." Da kansa ya kwashe dankalin  ya gyara kicin ɗin. Ameesha na zaune tana kallonsa har ya gama, taimaka masa ta yi da ɗaukar food plaks din, a kan dining suka shirya komai.

Dr da kansa ya rika bata a baki har ta koshi, haka Ameesha itama ta rika ba Dr a baki har ya koshi, sun ci sun koshi cikin zallar soyayya da k'aunar juna, wata irin nutsuwa ce ke saukarwa Dr a duk lokacin da yaga Meesha cikin farin ciki, ko bayan sun kammala yin break da kan sa ya kai kayan kicin, Ameesha ta taimaka suka gyara komai suka san ya shi ma'ajinsu sannan suka bar kicin ɗin.

"Kin ga bari na fita yanzu bazan daɗe ba."

"Ina zaka je beby?"

"Zan je asbiti kuma zan biya gidan Nenne."

"A dawo lafiya Allah ya tsare hanya."

"Amin cutie Ina godiya da addu'a."

Har wajen motar ta taraka shi, sai da taga fitar da kafin ta koma ciki, kwanciya ta yi akan kujera.

Dr kam yana fita asbiti ya soma zuwa, cikin sauri sauri ya gama duba wanda suke kwance, domin ba aiki ya zo ba bayan ya gama ne suka shiga motarsa shi da Hafiz lokacin karfe sha biyu da kusan rabi, suna tafe suna tattauna yadda bikin Hafiz din zai kasance har suka isa gidan Bobbo. A parking space ya faka motar suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama.

Nenne dake fitowa daga kicin ta amsa tana faɗin

"A'a ku kuma daga ina haka?"

"Daga asbiti." Suka bata amsa.

Zama suka yi akan kujera suna gaidata. Cikin sakin fuska ta amsa tana tambayarsa Ameesha da Aneesa.

"Duk suna lafiya." Ya bata amsa.

"Madallah! A rika hakuri dai da zaman tare, domin in aka rasa hakuri matsala tana yawan faruwa."

"In sha Allah Nenne za'a rika hakurin." Asmad ya bata tabbaci, suna dai zaune a gidan har ɗaya da mintina, sannan Hafiz ya masa sallama don yana da wasu aiki da zai yi, raka shi ya yi kafin ya koma cikin gidan don yana da magana da Nenne, don haka ko da ya koma ciki zama ya yi a kasa kusa da kafafunta, murmushi ta yi don tasan da magana wai gawa ta rike mai wanka, ya yi minti uku kafin ya dubi Nenne wacce ke zaune ya ce

"Ummh." Sai kuma ya yi.

"Asmad akwai magana a bakin ka, faɗa min domin ni ce mahaifiyar ka nafi kowa sanin halin ka."

"Ehmm! Dama cewa zan yi inda an yi abinci a gidan nan, a rika kai mana har Ameesha ta yi sati guda ta amshi girki." Ya karasa maganar yana sosa kai.

Tsira masa ido ta yi kamar mai son gano wani abu, sai zuwa can ta ce

"Ita Aneesa aikin me take yi?"

"Ehmm Ummh! Dama bata da lafiya ne, ba zata iya yin wani girki ba." Dr ya shirgo karya.

Duk a zaton Nenne ciki ne da Aneesa. Don haka cikin murna ta ce

"Masha Allah! Na yi farin ciki, gaskiya bai kamata kam ta shiga kicin ba musamman kila ba mai son kamshin abinci bane, ka riƙa lallaɓata Allah ya inganta, an ri ga da an kammala abincin bari nasa Larai ta haɗa maku kawai, da yamma direba zai kawo na dare."  Nenne ta yi maganar tana mik'ewa don zuwa kicin.

"Hmmmm! DR ya sauke a jiyar zuciya kawai, shi dai ba maganar cikin Aneesa ba ce matsalar sa, tunda ta amince zata basu abincin shi kenan.

Ipagpatuloy ang Pagbabasa

Magugustuhan mo rin

5.7K 143 22
It's classification day for Riley. he is finally 18 but when he gets his results things turn for the worst quickly when he has to stay with his broth...
55.2K 1.2K 26
.. a story, of a girl who has a condition that could change her life for the greater good. Loni has a medical condition that stopped her from develop...
14.8K 1.4K 17
" ඇයි අයියෙ ඔයා කොයි වෙලෙත් මාව සුදු අරලිය මලකට සමාන කරන්නෙ.." මං අයියගෙ මූන දිහා බලන් අහනකොට එයා මගෙ ඇස් දෙක දිහා බැලුවා.. මගෙ අයියගෙ මූනෙ ඇඳිලා තිබ...
18.2K 45 22
This is the second instalment to my 3 Part series of Books about a Young Blonde Teen Girl who suddenly starts to loose control of her bladder and bow...