BABI NA SHA BIYU

2.1K 131 2
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
                      *12*

Ta ce " A haba dai Meena kema kinsan haka ba zai yuwu ba, sai dai ki kawo wayar ki in yi masa da naki."

Murmushi Meena taja ta ce

" To ai ga wayar nan kusa da ke ki yi masa, nidai burina Allah ya sa ya zo, don shima satin sama ne bikin sa."

Wani mummunan faduwar gaba ya zuyarci Ameesha lokaci guda, tare da wani irin sarawa da kanta ya yi, ji taji kamar Meena ta watsa mata ruwan zafi

" Da gaske auren sa ya kusa? "

Tayi tambayar hankali a dan tashe.

Mamaki ya kama Meena ganin yadda ta tashi hankalin ta lokaci daya, tabbas tasan wacece Ameesha ta kuma san halinta tsaf, a wannan karon ma akwai tunanin da take a kan Ameesha da Dr dan fullo.

Saurin kawar da tunanin ta yi tace
"  Allah kuwa lokacin da ake maganar a asbiti kina ina? "

Da sauri ta wayan ce   don kar Meena ta gane ta ce

"  Oh!  Wallahi kam na manta, Allah ya sanya Alhairi."

" To ai yanzu na tuna maki don haka sai ki shirya masa abin gudummawa."

Tsaki kawai Meesha ta ja tare da gyara kwanciya,bayan ta tura masa text din, zuciyar ta na wani irin zafi da maganar da Meena ta fada mata, har tana mamakin kanta na jin faduwar gaba da taji maganar auren sa.

Haka akayi ta shagalin bikin, anyi lafiya kuma an tashi lafiya, Meena gidan su Ameesha aka kaita bangaren da Yaya Abdul ya gina, ya yin da ita kuma matar Yaya Jaheed take gidan da ya gina a sabuwar gwandu, Dr dan fullo ya yi kokari wajen halartan bikin.

Tun kafin a gama bikin Ameesha ke Fama da wani zazzafan jiwon kai, da zazzabi daurewa ta tayi har aka gama bikin, Yau dai abin yana nema ya yi yawa don har ta kai ga ta kwanta jikinta ko ina rawa yake hakoran ta sai haduwa suke da juna.

Hajiya Halima ce ta haura saman Ameesha, ganin har rana tayi sosai bata fito ba gashi suna da school, don haka sai ta ce bari ta leka ta ga ko lafiya

" Inna Lillahi wa Inna ilaihin Raju'un!  Shine abin da ta fada tare da saurin karasawa bakin gadon da take kwance.

" Auta lafiya meke damunki? "

Da kyar ta iya faɗin

" Zazzabi"

Hankali tashe ta dauki wayar Ameesha dake kusa da ita ta soma kiran layin Yaya Abdul.

Minti uku kacal sai gashi sun iso tare da Meena, suma hankalin su ya tashi  da ganin jikin Ameesha

"Kira Dr don jikin nata sam babu dadi."

" Ummi asbiti ya kamata muje fa, kalli yadda ta ke? "
" Eh ina ga zuwa asbitin zai fi."

" Gaskiya kam Ummi."

"  Je ka fitar da mota, bari mu fito da ita. "

Ita dai Ameesha bata ma San abin da su ke yi ba, don yadda take jin jikin nata.

Ummi da Meena suka taimaka mata har zuwa wajen mota.

*******************************

Asmad ne zaune shi da abokan su, suna ta tsara yadda bakin zai kasance, shi dai shiru ya masu ko ta tafasa a sauke bai ce ba, tunanin sa na kan Ameesha wacce yau kusan kwana uku bai ganta ba.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now