KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.8K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46

Page 47

486 21 4
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 47*
LAST PAGE

*FREE BOOK*

"yarinyar nan wai har tayi girman fooling ɗina, ce min fa tayi zata get together ta kuma fita da decent dressing amma yanzu ji dress dake jikinta? Ya Subhanallah"

A sanyaye yace
"calm down die hard baki gani gabaɗaya hankalinta ya tashi? She's just a teenager for goodness sake"

Norah ɗin ya riƙe yana goge mata bakin nata, duk fuskanshi ya bayyana damuwa, Kallonsu ta tsaya yi kerere lallai Raed be ɗauko hanyar tarbiyatar da yaranshi ba, Juyawa kawai tayi ta koma mota ta zauna da kallo ya bita har ta rufo kofar kan ya kamo hannun Norah ya sanyata bayan mota shima ya shiga ya ja suka bar wurin.

Har suka yi nisa babu wadda ya iya magana, chan ya dube ta ganin yadda take fushi ita kaɗai..

"Baby gurl please you need to calm down, ba wani abu me muni kika samu yarinyar nan tana yi ba..."

Katse shi tayi
"ba abu me muni ba ka ce? OK shikenan! Nunamin kawai zaka yi ƴar ka ce baka so in hukunta ta bayan ka san laifin da ta aikata babba ne, taya zata yi irin wannan rayuwa tana ƴar musulma?"

"Ya Subhanallah! Hidayah me ya kawo wannan magana?"

Shiru tayi bata ce komai ba har suka isa gida, duk ta riga su fita ta haura ta shige ɗakinta, ko da suka hauro da Norah kuka take yi

"am sorry dad na Haɗa ku faɗa da mommy I had no idea night club zasu ja ni naje, wlh I dressed like this saboda zuginsu ban taɓa ba, ka tayani ba mommy hakuri duk su suka faɗa min abunda zan faɗa mata ta barni na fita ba zan ƙara ba"

Zaunar da ita yayi shima ya zauna yace
"kin san mommynku is my first cousin sis ko?"
Kai ta gyaɗa ya ce
"yau ko bani da rai she have all the right da zata zauna daku ta hukuntaku idan kun yi ba dae dae ba, sannan karya bashi da kyau kin yi ƙarya saboda ki aikata saɓo in kin mutu me zaki cewa Allah?"

Kuka take yi ta sake cewa
"am sorry"

Yace
"Yafiyar Allah zaki nema sannan ki ba mommynku hakuri idan ta huce, Thank God we are leaving France 2morrow, je ki cire kayan nan ki kwanta ok?"

Kai ta gyaɗa ta miƙe ta nufi ɗakinta, ɗakin hidayat ya kurawa idanu yana nazarin ɓacin ranta a saninshi tana da sanyin hali da ko laifi aka mata cikin natsuwa take hukunci, amma kuma kwarai be ji daaɗin kalmarta na wai ze nuna mata Norah ba ƴarta bace, mikewa shima yayi ya nufi ɗakin shi, tun da ta tare gidanshi basu taɓa raba wurin kwanciya ba se ranar.

Babu wadda yayi baccin kirki a ranar asuba farko ta fita ta fara Haɗa musu break, bayan ta gama ta bi su ta tashesu suka fara yin sallah kan suka yi wanka suka hau shiri, Farrah ta aika ta tada Norah ta dawo, har gari ya ɗan yi shaa kan suka fito suka karya, ko da ya zauna a dining ma
"Good morning"
Kawai tace tare da saka mishi abinci ta tura mishi, kaɗan ya ci ya koma parlor da suka bar komai an dae rufe da Fararen kyalle, suna gamawa suma Paul ya gama fitar da akwatunasu suka bar gidan zuwa Airport anan suka samu Rashida suka yi sallama, har suka sauka Riyadh Motoci kusan biyar suka taryesu babu wadda ya cewa wani komai se yaran ke ta hayaniyar su.

Katuwar Mansion ne, komai gold da fari harta paint ɗin, ba karamin kyau gidan yayi musu ba barin ma cikin gidan babu abunda ba'a saka ba na anfanin gida, ɗakuna biyar ne ƙasa biyar sama, parlor huɗu ga manyan kitchen gidan dae ka san ba karamin kudi ya ci ba a kallo guda kawai in ka mishi.

Dakunan saman ya nunawa Norah nata ya nunawa Aisha da farrah da komai nasu bibbiyu ne nasu, miss Mary da Junior ya nuna mata ɗakin junior ya kuma kwatanta mata nata a ƙasa in tayiwa junior wanka ta sauka, golden door da taga ya nufa saɓanin sauran da suke white yasa ta bishi da kallo..

Be nuna mata ɗakinta ba, bayanshi ta bi janye da karamin loggage ɗinta, parlor ne tsararre me wasu mahaukatan coushines da suka tafi da ita, ɗakin da ta tabbatar nan ya shiga ta buɗe itama ta shiga..

Har ya zauna a wani kujera bayan ya fidda black German suit da ya saka da white shirt ɗinta daga shi se wandon suit ɗin, duk kakkarfar kirarsa a waje, akwatinta ta ajiye bayan sun haɗe idanu ya ɗauke kanshi, kwankwaso ta riƙe seda ta shiga ɗaki jiya ta san maganan da ta faɗa be dace ta faɗeshi ba ko ina za'a je a dawo ita ɗin uwa ce ga yaranshi.

Toilet ɗin ta leƙa ita dae daga ɗakin har toilet ɗin bata ga wani wurin sa kaya ko ajiye kaya ba, gashi so take ta watsa ruwa ba laifi Akwai nisa tsakanin France zuwa Riyadh, direct white ɗinshi ta ɗauka ta shige toilet ɗin ya bita da kallo.

Wanka tayo ta sanya rigar wadda ya sauka zuwa rabin cinyarta hannun yayi mata yawa yadda ya rufe duka hannayenta karamin towel da ta samo bayin take anfani dashi wurin tsane gashin kanta,dab da kujeran ta zauna daga bakin gado tana me cigaba da abunda take yi, kamshin shower gel da tayi anfani dashi da kuma ruwan gashinta da ta watsa mishi ya saka shi ɗagowa a hankali, idanunshi suka fara sauƙa kan ƙafafunta ya fara haurowa har zuwa santala santalan cinyoyinta dake waje, ya Sani hidayat is super hot ta kan fitar dashi hayyacinshi da kallo ɗaya kawai da ze mata, yana kaunar ta kuma be san ya ake yi take turning ɗinshi on a koyaushe baya iya gajiya da ita ba, motsa kafafun nata da yake kallo tayi wadda seda ya saka shi fidda iska daga bakinsa yana kokarin kwarewa da miyaun bakinshi da sauri ya kawar da kai.

Chadak ta miƙe ta nufi gaban window tana gyara labulen da taga ya yaye mata sossai, tsawon ta be kaiwa hakan yasa take Haɗawa da tsalle, be san ya ajiye system ɗin hannunshi ba ya miƙe ya nufe ta yana kara kallonta tana shirin kashe shi da ranshi, daidai lokacin ta juyo tana gyaran wuyan Rigan da bata saka buttons na saman ba ana iya kallon rabin kirjinta, wani kalar runguma taji yayi mata yana sauke numfashi.

A hankali itama ta sanya hannunta ta zagaye zuwa bayanshi da babu komai a tare suka sauke ajiyar zuciya, kan yayi magana tace
"Am sorry paapi"

Lumshe idanunshi yayi seda ya gama shigar da ita jikinshi ya gama jin duminta da yayi missing kan ya ɗago ta yana maida mata gashinta baya a lokaci ɗaya idanunshi na bisa fuskanta yana aika mata da wani rikitaccen kallo yace
"ko na ce zan yi fushi dake I can't baby gurl, when we first started talking I didn't realize you would become this important to me, u are someone I don't want to go a day without talking to, please karki sake furta irin kalaman da kika furta a gareni jiya, Norah da Farrah yaranki ne and you are allowed ki yi musu duk hukuncin da kike so a sadda suka yi laifi just understand faɗa da duka baya gyara yaro"

Idanunta ta Sauƙar daga kanshi itama bata ji daaɗin abunda tayin ba barin ma a gabanshi ta san yaranshi are the most valuable things to him tun a da kuma soyayyar su ba wai ya chanza ba, she should have treated Norah better.

Sake rungumarshi tayi tace
"am so sorry it won't happen again nima ban san sadda raina ya ɓaci haka ba, believe me you are all I got jiya ban iya nayi bacci ba, I realized cewa you are not just my man, you are my home, my rest, my heart and my safest place Kaine komai nawa.."

Murmushi me sauti yayi yana squeezing shirt ɗin nashi dake jikinta buttons ɗin na ballewa ɗaya bayan ɗaya suna zuba ƙasa, yana bin neckline ɗin ta da mahaukatan wet kisses yace within his throat
"then let's grow old together like this baby...! I have gone totally crazy for you.."

Gabaɗaya ya haukace mata kaman yau ya fara sanin ta, in a romantic way ya ɗaga ta zuwa kan gado yana hautsina mata lissafi da duk sauran wata natsuwa da ta saura musu, idanunshi da suka sauya yake bin jikinta da kallo dasu, yayinda ta lumshe idanunta cikin haukar giyar soyayyarsa da yake shayar da ita....

Da kyar muryarshi ya iya furta
"All my life baby.. I haven't seen anyone as beautiful as you by Allah I love you Morethan life..."

****

Bayan shudewar awanni, tsaye take a kitchen tana Haɗa musu abincin dare saboda ya riga ya zama addicted to girkin ta baya iya cin abincin kowa yanzu, abincin hawa kanta yake yi babu yadda ta iya ne kawai take girkawa da siririn gyalen kanta tayi amfani wurin toshe hancin ta, tana Tunanin tana da ciki.

Saboda duk wasu alamu sun bayyana, wannan ne cikinta na huɗu kuma duk cikin da tayi baya babu likitan da ya gayamata ita tayi noticing kayan ta, yawan zafin jiki da take fama dashi da kuma zaɓen abinci yasa ta fara zargin hakan se kuma saurin hasala ga yanzu kuma tashin zuciya.

Fitowa tayi tayi rubutu bisa takarda ta bashi akan ya samo mata kan ta gama abinci, ficewa yayi ko da ya dawo ta gama ta shirya musu a babban parlorn saman, se lokacin Norah ta zo ta tsuguna kanta a ƙasa tace

"am so sorry mommy about yesterday, I won't repeat that again please forgive me..."
Muryarta rawa ya fara alamun zata yi kuka, hidayat bata kula ta ba ta karɓi sakonta wadda shi karan kanshi uban gayyan be san me aka aike shi ya siyo ba, zama yayi be sa musu baki ba.

Abinci tayi serving ɗinshi kan tayiwa sauran yaran ta zuba nata ta fara ci ba tare da ta kula Norah ba se ta ɗan ɗago taga dukkansu huɗu sun yi fuskan tausayi suna kallonta, shi ta kalla shima yayi puppy face duka suka ce

"Sorry mommy don Allah ki dena fushi da Adda Norah"

Ajiyar Zuciya ta sauke kan ta kalli Norah tace
"it's fine, amma karki sake kin ji? It's haram in our Deen"

Kai ta gyaɗa tace
"thank you mom"

Abincin suka ci suka gama Norah, Aisha da farrah suka tattare kwanukan, anan ta barsu suna bitar karatun Qur'aninsu har Junior da yake Alhamdu, toilet ta shiga tana murmushi ta fara gwada PT strip ɗinta se gashi layi biyu ma'ana tana da ciki...

Ribar soyayyarsu da Raed, ɗan da zata fara haifa zuciyarta cike fall da soyayyar ubansa, wanka tayi ta chanza cikin wasu fitinannun hot red kayan bacci ta saka harda red lipstick, ta gyara gashinta se ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka ta fito, Seda ta tabbatar kowa yayi alwala yayi Adu'a ya kwanta kan ta bishi ɗaki da ta riga raka shi.

Ya fito wanka ɗaure da towel, tana shiga ta zare hijabin daga ita se kayan baccin da wani irin kallo ya bita, a take ya sanya lip ɗinshi na ƙasa a baki ya ɗan ciza yana sakin murmushi yace
"kina kashe ni Baby gurl!"

Hannu ya miƙa mata da wani kalar tafiya da ya kasa haƙurin jiranta ya karasa ya haɗe gab din tsakaninsu yace
"me sirrin ne? Son ki kullum kara karuwa yake a raina Die hard da ana gwada so ko da kullum se likitan nan yayi mamakin yadda naki ke linkuwa at each Second a nan"
Ya karashe yana ɗaura hannunta setin zuciyarshi dake bugawa da karfi.

Zajaye hannunta tayi jikinshi se tayi baya kaman me lilo tana murmushi me ɗauke hankali tace
"Daddy...!"

Yace
"yes mommy"

Se ta saki murmushi tace
"are you sure you are ready to be called dad again?"

Yana rolling eyes nashi yace
"am always ready, wait what are you talking about?"

Tana murmushi tace
"am pregnant..!"

Shiru yayi kaman be fahimta ba se kuma ya zaro dukkanin idanunshi waje yace
"Oh my God! Baby you are what???"

Ta sake cewa
"pregnant..!"

Bata rufe baki ba ya ɗaga ta Chadak ya fara zagaye da ita cikin hannunshi daga karshe suka yada zango kan gado, Rigan ta ya yaye ya hau kissing cikin hawayen farin ciki na zubar mishi

"I can't believe baby, I love you Ina sonki ina sonki! You are the story that I never want to end"
Ita ce wannan karon ta karɓi ragamarshi ganin irin susucewa da rikicewa da yayi.

BAYAN SATI BIYU

Zuwa yanzu sun gama settling a Riyadh yara sun fara zuwa Islamic school da suke boko da Arabic hadda ba'a magana Sam basu da wani lokaci, itama ta koma karatun ta a nan university wata hadaddiyar Jaguar (car) ya saya mata da yamma kullun suna fita koyan tuki cike da soyayyar juna, shima kuma ya cigaba da tafiyar da career ɗinshi cikin nasara da natsuwa.

Tsaye take riƙe da waya tana dariyar faɗar Daadida da maaminta tace
"ni kam se masifa kike kinki faɗamin abunda uwat tawa tayi miki da kike ta sollewa"

Tace
"ai gata gabana, duk ta bi ta ɗagawa bawan Allah hankali wai fa hidayat ba'a haihuwa za'a haifeta? Ciki ne da ita ta ce Sam sede a zubar wai abun kunya haihuwa da jikoki nace a'a tattaba kunne"

Sossai hidayat tayi farin cikin jin wannan zance itama zata samu kani ko kanwa, sede ta boye murnan ta ta lallaɓa Daadida akan ta bita a hankali ne ba da faɗa ba.

Da kyar ta jira Raed ya dawo ta fesa mai suka yi ta jin daaɗi.

8YEARS LATER

Tsaye tayi hannu a kwankwaso tana kallonsu
Norah da ta zama matashiyar kyakyawar buduruwa ta hautsina gabaɗaya parlorn wai tana neman Nose percel ɗinta da Junior ya ɓatar, Farrah da Norah kuwa wai suna gwada water gun ɗin Najwa da Maher katti dasu ƴan mata, shi kuwa bawan Allah Nawaf na zaune gaban TV yana kallon avengers yayinda Junior ke cin abinci.

"Lallai ma Yaran nan wai me kuka maida ni? Ji parlorna kaman na mahaukata? Norah, Farrah, Aisha da girman ku?"

Duk natsuwa suka yi don sun san halin mommyn tasu bata musu da wasa kaman Daad, kallonta suke yi sanye da decent suit da mayafi se after dress hannunta rike da brief case.

"Sorry mommy"

Harara ta watsa mishi tace
"Acici ba, ai kai kam idan aka ce yau ba abinci duniya an bonu da kai Junior"

Da sauri Nawaf ya tashi yace
"mommy welcome"

Tace
"zo babana damo sarkin haƙuri"

Rungumeshi tayi shine farkon ɗan da ta haifa da Raed, wadda yake shekara takwas yanzu tana matukar kaunar yaron saboda hakuri da sanyin halinshi kuma sunan mahaifinta sannan Usman ɗinta Raed ya mayar, tana kallon Norah dake final year medicine tace
"Ina yarana?"

Farrah tayi saurin cewa
"suna bacci mommy"

Bayan Usman(Nawaf) da four years ta sake haifan twins Mairamu da Abubakar sunan iyayenshi shiyasa suka musu inkiya da Najwa da Maher.

Tace
" Naji, ku tabbatar kun tattara min parlor tsab kan in shiga in fito in ba haka ba zan ga me Bi na final wasan Daddy"

Da gudu suka hau tattare, ita kam ɗaki ta shige yau Raed yake wasan shi na karshe daga shi ritaya ze yi su koma Nigeria amma zasu bar Junior saboda shine ya ɗau kafan Raed kwallo yake so kaman hauka har yanzu ba'a ce mishi junior zallah se Raed junior, yana makarantar horas da yara en kwallo.

Cikin awa biyu suka fito a haɗe kaman ka sace, hidayat ta saka wani blue palazo se rigar Al nassr Yellow da blue bayan rubuce da sunan jarumin ta,ta kama daidai cikinta da pin ta baya yadda ya zauna mata kaman dama chan haka aka yo shi, jersey scarf blue ta zagaye kanta dashi se wani hill silver, ta riƙe jakanta na kamfanin D&G blue idanunta sanye da sunglasses Sam bata tsufa kyaunta da kyaun halin ta a kullum shi kowa ke yabo, ga iya ɗaukar wanka.

Tana yawan zuwa Nigeria ita kam sbd a chan tayi call to bar Sannan ta kan karɓi case musamman ta je Nigeria shiyasa kowa ke fatan mijinta yayi retire su dawo don za'a ga jajirtacciyar barrister me faɗa akan irin abubuwan da ake yiwa mata a Gidajen mazaje da ma kan hanya.

Yaran kowa ya ci wanka cikin Al nassr jersey da kalolin wankansu, Motoci uku suka yi zuwa babban filin wasan, hidaya na jan nata, Norah ma na jan nata se driver na jan na karshe, a gaba gaba aka jera su har aka fara wasa da zafi zafi.

Yana cin kwallon farko ya ɗago yana kallonta yayi mata alamun zuciya da hannunshi alamun ya sadaukar mata da kwallon, murmushi me kyau tayi ta mishi blowing kiss ya dafe zuciya yana murmushi kan ya cigaba da wasa, haka seda ya sha ball uku yana mata dedicating a haka wasa ya tashi.

Saukowa suka yi filin aka fara hotuna ana taya shi murnar retire, karramawa da ya samu ba'a magana, yana cikin tarihin Kasar Saudia a harkar kwallo na har abada don babu irin nasarar da be samar musu ba, Seda aka kusa tashi se ga Abba, Maami da en biyunta dake da 8yrs suma Zayd da zayyad, da gudu su Maher suka je suka rungumesu suna kira uncles.

Se ga Ummi da ta auri wani ambassador suna zama US ita da yaranta uku biyu mata ɗaya namiji, chan se ga Rashida ma da nata familyn tana auren babban hafsin soja na Nijeriya yaranta biyu.

A take media ta ɗauka
"Love❤️🫶Moh Raed dedicated his final goals and shows her his heart during his last match in history, later she and the children descended from the stands onto the field🥹🫶"
Hotunan su se yawo yake platforms

An sha hotuna an kuma sada zumunci, inda daga karshe suka wuce gida kwana biyu suka kara suka juyo Nijeria aka maida Junior hostel har kuka yayi gidansu na nan kaman na Paris don su kan je vacation.

Mahaifin mamansu ya rasu Allah be yi ze karɓi musulunci ba, Hajiyar Hamza ma ta cika bayan ta shafe shekara bakwai tana fama da lalura karshe har cisgar naman jikinta tayi tayi kan ta tafi inda ake girban abinda aka shuka.

Ko da suka dawo Nijeriya gabaɗaya an chanza tsarin gidansu zuwa wani na daban hadadde, su umma sun zo yi musu murna khausar na auren wani dattijo itace matarshi ta huɗu, se fahariyya dake auren wani police su biyu ne matan nashi se Surayya da ko shekara bata rufa da auren wani ma'aikaci redio suna sana'ar su har abada kuma suna godewa Hidayat suna sanya mata albarka.

Kannen Raed ma duk sun yi aure, waenda suke gidan mazajensu ma be Barsu ba seda ya tabbatar a ko yaushe babu abunda suka nema suka rasa da taimakon sana'o'insu.

Bayan sun natsu ya fara harkar business ɗinshi ka'in da na'in, ita kuma hidayat ta fantsama ta zama topic da kowani namiji azzalumi yake tsoro, sossai ta jajirce wurin zama mace me kamar maza.

Bayan wasu watanni Raed ya gane dangin mahaifiyarshi, mahaifiyarta da kuma yannenta maza biyu se kanwar ta mace ɗaya sun dawo neman Mairamu aka kwatanta musu gidan Raed da taimakon sisters ɗinshi na nan gembu suka isa Kano.

Sossai yayi farin ciki Daadida ta nace sede su zauna tare ba se an sake nemar musu wani gida ba, mazan ya saka su cikin business ɗinshi.

Kwance take a kirjinshi tana bashi labarin wani mutumin da aka yanke mai hukuncin shekara biyar gidan yari da tara me yawa akan irin zaluntar matarshi da yayi cikin azabtar wa.

Yana shafa bayanta yana sauraron ta yana murmushi yace
"in dae da irin ku Hidayah maza ba zasu zalunci mata ba, su kan manta cewa macece ta haifesu ta kuma raine su har suka zama abunda suka zama, a ko yaushe mace abar tausayi da kulawa ce, Allah ya cigaba da dafa miki matata, kwarai ina kaunarki,zuciyarki tsarkakakkiya ce shiyasa Allah be taɓa bari kin taɓe ba, I love you hidayah today and always karki manta da hakan"

Ɗagowa tayi tana shafa hancinshi tace
"A da ban san kaina ba, kai ka tsince ni ka zamar dani mutum wacce kowa ke alfahari da ita, da kowani namiji irin ka ne da mata basu sha wahala ba a duniya you are not just my favorite person you are my everything Muhammad Raed, I cannot breathe when you are not near. I love you"

Ta karashe tana kissing lips ɗinshi, ya juya ta ƙasanshi yace
"wai me sirrin ne?"
Yayi maganan yana dage mata gira da sauri ta rufe idanunta tana dariya sossai...

TAMMAT BI HAMDILLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BANI LADAN ABUNDA KUMA NA YI KUSKURE INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN, ALLAH YA KAWO MU KARSHEN WANNAN LITTAFI GODIYA ME DUMBIN YAWA A GAREKU DAUKACIN MASOYAN KOWA YA GA ZABUWA.....

GODIYA NA MUSSAMMAN ZUWA GAREKU

FAV SIS(HANEEFA MOHD GURIN)
MAMA TANKO SHANONO
AUNTY SAFEEYA
UMMULKHAIRI
MAMAN SADIQ
MAMAN KHALIL
MAMAN ALI
SIS JIDDAH ADAM
AUNTY FARIDA
MOM MUNEEFA
AMEERATUH
SIS AISHA USMAN KUSHERKI
MAMAN AYSHAT
SIS SADIYA UMAR ADAM
SIS KHADIJA QUEEN
SIS FIRDAUS

DA MA WAENDA BAN KIRA SUNA BA KU SANI WALLAHI NA JI DAAƊIN TAFIYAR NAN DAKU KUMA INA MATUKAR GODIYA BISA HAKURI DA KUKA YI DANI.

ALLAH YA HADAMU A DIDDIGAR ƘAYA... 🥰😍❤️

                 🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

10.1K 686 15
Dannar kirji... Gajeren labari mai dauke da darussa kala kala na wata uwargidah da akaiwa abokiyar zama(amarya)😻💕..NA MRS JH AND MSS XOXO
2.3K 88 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...
67.1K 7.4K 58
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta b...
7.2K 254 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin lit...