KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

21.7K 1.4K 47

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 47

Page 46

404 17 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 46*

*FREE BOOK*

*Aunty Safeeya kin ɗaure ni da jijiyoyin jikina, babu yadda na iya na bazama wattpad🤧🤧🤧In shaa Allah final page ze sauƙa gobe*

Duk me ɗaukan duniya matabbata tabbas ya ɓata ɓat ba tare da sanin mecece duniyar karan kanta ba, Hausawa kan ce duniya budurwar wawa, kwarai duk wadda ya bi ruɗin duniya ya ɓata lahirarsa yana cikin tsaka mai wuya domin tabbas duniya ƙaryace, rayuwarta taƙaitacciya ce lahira kuwa ita ce daahir, a kusan lokaci ɗaya Baba Buba da Yusuf sun tafi gidan gaskiya.

Sun tafi ne ta hanya mabanbanta inda tsananin tausayin da jama'a suka nunawa Yusuf da labarin shi yasa dayawa suka mishi Adu'ar samun rabauta ciki har da Hidayat, ta roki Allah ya yafe mishi ita kam ta yafe, ta roki ubangiji ya sanyaya makwancinshi albarkacin tuba na gaskiya da yayi.

Yayinda Buba ya tafi cikin mawuyacin halin ƙishi da yunwa, ya tafi yana me kukan abubuwan da ya aikata ba tare da ya san makomanshi ba, dukkanin su an kaisu Gidajen su na gaskiya inda Zaka girbi abunda ka shuka. Allah ya sa mu fi karfin zuƙatanmu.

BAYAN WATA GUDA

Kwance yake hannunsa cikin nata, kanshi na a kan kirjinta hannunta ɗaya na cikin gashinsa da ya taru yayi baƙi siɗik yayi kyau, a tausashe tace

"Paapi!"

"Uhmm my love menene?"

"Yaushe ne zamu koma? Kaga an buɗe school ba nawa kaɗai ba har da yara ko mun dawo kenan?"

Dariya yayi ya ɗago yana shafa lips ɗinta yace
"Ina jin daaɗin zaman mu anan saboda ke kaɗai nake gani 24/7, bani da matsalar komai bani da Tunanin kowa da komai, ni yanzu maraya ne ina bukatar kulawarki amma in mun koma zaki manta dani ki ke shareni shiyasa bana so mu koma"

Murmushi sossai tayi tace
"Allah ya kula da maraicinka mijina, nayi maka alkawarin kulawa ta har abada, ko da yara, karatu da kuma aiki, dukda kasancewata me uwa da uba ka zamar mini mijin marainiya to me yasa zan kasa kulawa da kai?"

Peck yayi mata a lip yace
"in shaa Allah next week zamu koma I wanted to tell you tun jiya ma just carried away da maganan zuwa gembu ɗin nan"

Tace
"yeah hakane, but please muna kan magananmu ko?"

"Ba na ƙi shawararki bane, but bana son ɗibo yaran nan in kawo su su hana Daadida kwanciyar hankali, you know at her age tana bukatar natsuwa"

Shagwaɓe fuska tayi tace
"su huɗu ne fa kwata kwata suke gida, Maami ta ce a bata ɗaya, sannan su Baaba Laure zasu koma da ɗaya, biyun su zauna wurin Daadida I am very sure na wurin Baaba Laure da Maami baza'a samu matsala ba, su kuma na wurin Daadidan suna shakkarta don bata yi musu wasa, sannan ga ka nan akwai kuma security ba ta yadda zasu fita bare su yi wani abu marar kyau, su kuma na Gidajen mazajensu da suke fama se ka basu jari... Please kannenka ne Kaine matsayin uba yanzu a garesu karka duba halayen iyayensu mata, baka san ta inda Allah ze rama maka alkhairin ka garesu ba"

Ajiyar zuciya ya sauke kan ya miƙe zaune yana janyo ta itama ta zauna tana gyara towel ɗin jikinta
"since you insisted babu yadda za'a yi madame"

Rungume shi tayi tana murmushi, Daadida Tayi maganan ya ƙi shine ta Haɗata da shi, dira yayi daga kan gadon ya saɓeta suka yi toilet, ta sakale hannayenta a kafaɗansa suna hiransu.

Bayan sun fito suka shirya juna suka fice zuwa gidan su hajiyar hamza da suka yi alkawari, hannunsu cikin na juna suka shiga ɗakin yana zaune ganganta, zainab na riƙe da hajiyar yana bata abinci.

Rabi ke shiga rabi na zuba, in ka ganta kaman irin me ciwon paralyze sede ba paralyze ɗin bane ta lalace gabaɗaya banda miyau babu abunda take dilalarwa ga rashin hankalin, sossai hamza da Zainab suke kula da ita bayan me aiki da take dashi sede Dukda haka tana fuskantar tsangwama da kyara daga wasu cikin dangin ta musamman waenda suke cikin gidan.

Ita kanta zuwa yanzu ta gaji da rayuwar, bata iya bacci Sam saboda razani da firgici, abinci wannan baya iya shiga cikinta, babu hankali ta rasa komai banda wannan ɗa da Allah ya ba ta to me ya saura mata a duniya? Tana kan girban abunda ta shuka mutuwa take fata Dukda tana cikin matsanancin tsoron abunda zata tarar sede rayuwar kuma ta isheta ta gundureta cikin wannan hali, ashe in Allah ya baka lafiya ka gode masa...

Gaisawa suka yi, Hidayat ke tambayar
"ya hamza ya me jiki?"

Yace
"ga ta nan Dae jiya e yau, amma Alhamdulillah"

Tace
"Allah ubangiji ya bata lafiya"

Suka amsa da Ameen, Raed yace cikin hausarsa da har yanzu ba wai nuna tayi ba
"ya kamata ku Haɗa da Islamic, karka ce bazaku nemi magani ba kuyi ta zama haka..."

"And please rokon Allah ayi ta sadaka da neman yafiya, Allah ya bata lafiya me anfani"

Godiya hamza ya musu, dukda su kan haɗu sossai barin ma lokacin rasuwarnan sede har yanzu baya iya yin doguwar magana da Hidayat sede Raed, su kan jima suna hira ita kuma hidayat ita ke saka shi cikin magananta wadda haka dole ze amsa Dukda irin kunyarta da har yanzu yake dawainiya dashi.

Kayan amfani suka ajiye musu irin su madara,milo da dae sauransu, hidayat na cewa zainab tayi fushi bata taɓa zuwa gidanta ba sede su haɗu Wurin Abba, da wannan Hirar suka musu rakiya zuwa mota suka tafi.

Wani madaidaicin gida suka yi parking, suka sauko a tare suka shiga da sallama, umma ce ta fito tana musu maraba sanye da hijab har ƙasa.

Madaidaicin parlorn ta yi musu iso suka shiga suka zauna, ruwa taje ta kawo musu tare da zama ƙasa hidayat tace
"A'a umma, don Allah zauna saman kujera babu yadda za'a yi muna zaune sama ke kuma kina zaune ƙasa"

Tace
"hidayat barni kin ji, don Allah ina me kara rokon afuwarki da gafararki wallahi nayi nadama, nadama me girma ki yafemin..."

Kuka ne ya ci karfinta, tun rasuwar Yusuf wani irin nadama ya shigesu kwarai abun ya girgiza su, maganganun hidayat sun musu tsayuwar ƙawara a zuƙatansu yadda suka hana su ko da kwakwaran motsi ba tare da sun tuno makomarsu ba, hidayat me rama cuta da alkhairi bayan kwana uku da rasuwar ta kasa hakuri ta koma garesu albarkacin Abba, gida ta fara saya musu cikin unguwar mutunci da kudadenta wadda ta samu lokacin da Abbanta yayi mata walima, ta nemawa su Surayya islamiyya ta ɗinka musu uniforms suka fara zuwa, fahariyya da rana tana zuwa learning center tana koyon ɗinki, yayinda khausar ke koyon abinciccuka Albarkacin wannan hidayat da basu taɓa dauka da muhimmanci ba a rayuwarsu se gashi ashe ita ce rufin asirinsu.

Ta sayi katon freezer umma na sayar da kayan sanyi daga cikin gida, Raed shi ya cika musu store da kayan abinci, ya kuma basu shawaran adana kuɗin da Abba ya basu zuwa gaba, Sossai Abba da Maami suka musu nasiha da tunatar dasu girman uwa wadda a yanzu suke yiwa umma biyayya yadda ya dace Dukda tun farko laifinta ne da bata ɗaura su a hanya madaidaiciya ba.

Abinci ta musu tayi suka ce a koshe suke ɗan hira suka yi, hidayat ta bata form da ta yankarwa Surayya na diploma da wasu kudade suka yi mata sallama suka fice.

Daga nan gidan Abba suka yi, sun ɗan jima a chan suna kwasar hayaniyar ƴaƴansu kan suka wuce gidan Daadida daga nan se Airport a pjet ɗinshi suka ɗaga se Taraba state daga nan chopper suka hau zuwa gembu, Sossai iyalan Buba suka basu tausayi ko rasuwar ta waya Daadida ta gayamusu basu iya zuwa ba saboda babu halin zuwan, suna wani irin rayuwa cikin tsananin yunwa da talauci.

Ko zama Raed be yi ba ya bawa su Badi'ah 100,100k akan su koma gidajen iyayensu su yi sana'a don gidan Buba sayarwa za'ayi a raba gado don baya so abar Buban da wani nauyi bayan wadda ya tafi dashi, inda ya saka en matan Haɗa kayayyakin su in kaga fuskanshi babu ko ɗigon fara'a, hakan yasa jiki na rawa suka fara.

Ya sa aka kira mishi na gidanjen mazaje suka zo, faɗa sossai ya musu akan kar su kwantar da hankali su zauna lafiya ai duniya ce suna ganin karshen iyayensu yadda ya kare, dukda harshenshi yayi musu kaifi sede sun ɗauki nasiharshi, suma duk jari ya basu kuma ya karbi layukan mazajensu.

Daga nan abunda za'a yi duk aka yi aka raba gadon wadda shi kam be iya karɓa ba se hidayat ce ta karɓa, tusa en matan yayi suka wuce dare dare suka sauka a Kano.

A gidan Daadida kannenshin suka kwana, da safe ya je ya sake ja musu federal warning, malama mace suka nema wadda ze ke yiwa su biyun lesson da karatun addini a gida.

Ya ɗauki biyun suka yi gidan Abba, ya samu su Laure har sun fito da shirin tafiya garin su, sun shirya cikin yaduka masu tsada ga jerin Motoci guda biyar da zasu tafi dashi cike da dumbin arziki, tuni Abba ya je har Nijar ya cika alkawarinshi cikin maradi ya samar musu fantsamemen gida me haɗe da gidan gona, dabbobi har na waje akwai tunda dae Gamji ya ce burinshi kiwo.

Raed yayi alkawarin gina company a maradin wadda yake so ake sarrafa duk wasu kalar nau'in albarkar kowacce dabba, inda yace a hannun gamjin ze bar komai.

Kaman wasa ya basu kanwarshi ɗaya suka wuce, an riga an zama en uwa da kyar aka Rabu kaman kar a rabun, Ya ajiyewa Maami ɗaya.

Daga nan gidansu ummi yaje Sam hidayat bata sani ba ya saya musu wani gida a nan cikin unguwar su, kusa ma sossai da su, ya samawa babanta aiki me tsoka tunda dama da karatunshi, kannenta duk ya sauya musu makaranta a sadda suke mishi godiya yace
"babu godiya a tsakaninmu ummi, a lokacin da Bama tare da Hidayat kin tsaya mata kin so ta saboda Allah, kin bata shoulder to cry kin kwatar mata ƴancinta wurin masu zaluntar ta, komai nayi miki wallahi yayi kaɗan, Allah kawai ze saka miki ina ma kowa ze samu ƙawa ko aboki irin ki a duniya? Zuciyarki me kyau ce Allah ya baki abokin zama na gari"

Godiya tayi mishi kwarai, ka kasance me aikata alkhairi karka damu da Tunanin me zaka samu bayan hakan saboda gashinan, bata taɓa Tunanin arzikinsu na tafe sanadiyar hidayat ba, ta so ta da zuciya ɗaya kuma Allah ya dubi lamarin su, sune cikin unguwar girma cikin manyan masu kuɗi, mahaifinta ya daina hawa machine se mota wadda Abba guda uku ya ajiye musu a gidan.

Yana da kujerar Makka da shi da mahaifiyarta daga hidayat to me ya saura musu kuma?

Kaman yadda Suka tsayar sati na zagayo wa suka tarkata suka koma Paris, basu yi sati ba ya fara processing musu transfer To Riyadh saboda Saudi sun saye shi, ze koma Al-nasar club tare da famous ɗan wasan nan Cristiano Ronaldo.

Tsaye take tana gama kimtsa kayan na Norah tana jin abunda take faɗa a gefe ɗaya.

"Shine se da dare zasu shirya miki taron? Bana son fitan daren nan fa Norah"

Shagwaɓe fuska tayi tace
"Mommy in shaa Allah ba zan kai goma a waje ba I promise, mata ne kuma class mates dina ne kawai, they didn't knew that gobe ne zamu wuce da sun yi da rana ne wallahi"

Ita da hankalinta be so ba, haka tace ta shirya ta je amma driver ze jira ya dawo da ita..

Da gudu taje ta shirya Dukda riga da wando ne sede decent, Rigan ya sauka zuwa gwiwa and akwai na ciki long sleeve tayi light makeup ta yafa jersey scarf ɗinta da ya zauna bisa gashin kanta.

Fita tayi tana sallamar mahaifinta, fitowa hidayat tayi daga kitchen tana miƙa mishi  mug ɗin coffee ɗinshi tace
"Dad is getting lazy these days abubuwa sun maka yawa baka fa ɗaukar karatun ka"

Yace
"I swear! Ke de bari, but in shaa Allah the moment we settle a Saudi zan baki mamaki bcs I promise ke ce malamata har in sauke"

Murmushi tayi zata yi magana se Wayanshi yayi ringing, dubawa yayi ya ɗaga mintuna biyu ya sauke yana jan tsaki yace
"it's Jacob wai saƙo ze bani kuma ba ze iya zuwa ba"

Tace a shagwaɓe
"shine ze fitar min da miji cikin daren nan?? Is it that important? Na ga baka da yawan friend cikin club members dinku"

Yace
"yeah, form ne na leaving da na yi singing the coach wasn't around and bana so in yi dare shine na bar musu akan in ya dawo ayi photocopying bayan ya sa nashi hannun su kawo min, daga karshe dae suka ba the most unserious person mtseww"

Dariya kawai tayi tace
"and you have to collect it bcs k san 6am ba ze same mu Paris ba"

Yana mikewa yace
"oh yes! Zo ki rakani baby gurl"

Kallon jikinta tayi don ta san shi fita a haka a wurinshi normal ne daga shi se three quarter da armless, ita kam wando ne jikinta da wani shiffon orange short shirt wadda motsi tayi se ya ɗan nuna fari sol ɗin cikinta.

Mikewa yayi ya je ya dauko mata After dress me kauri ta saka da kanshi ya yafa mata gyalen ya riƙe hannunta suka fice, yaran suna dakunansu sun ma kwanta don akwai su da baccin wuri barin ma yau da duk seda kowa yayi aiki duk sun gaji.

Ko da suka isa hotel ɗin tsaye tayi daga jikin mota tana jiran shi, ya san irin ɗakunan en ball barin ma turawa baza'a rasa ƴan mata ko kayan maye ba shi kam ba ze iya barinta shiga ba, tana nan tsaye ta ga wasu teenagers zasu wuce dukkansu sanye da short gowns different colors and design gashin kansu duk waje da idanu take bin su tana mamakin yaran turawa, kaman an ce mata kalla da kyau ta hangi wata kaman Norah a cikinsu...

Bin bayansu tayi tana sake Kallon ta da kyau, babu tantama idanunta Norah suke gane mata.

Ƙara sauri tayi ganin sun shiga cikin hotel club ɗin, ko da shigarta en matan sun fara rawa yayinda Norah ke rakube tana ta kakkare jikinta kawai se ji tayi an fisgo hannunta, zata yi magana Hidayat ta daka mata mummunar tsawa
"shut up ko in tsinka miki mari.... Norah yaushe kika yi girman zuwa Night club? Ashe kin zama maƙaryaciya ban sani ba?"

Zata yi magana hidayat ta gwabe mata baki saboda haushi da ya kusa kashe ta ita zata yi fooling ta taho night club? Allah kaɗai ya san me yaran turawan nan suka koyamata.

Zuwan Raed ne ya katse su ganin shigan jikin Norah da kuma yadda ran Hidayat ke ɓace ya san akwai matsala, kafadan Norah ya riƙe yake cewa
"are you OK? Me yasa take kuka?"

Ya jefawa Hidayat maganan yana sake kallon bakinta da har ya ɗan yi jini.

            DIDDIGAR ƘAYA
(Mai wuyar Tsincewa)

Gureenjo🥰😍

Paid book
300

Tsokaci/Dandano

Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.

"Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!"

Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
"Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.."
Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace
"ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!"

Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.

Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe

"Ammi! Baba Alhj basa ƙauna ta Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwana na be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!"
Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar?

Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin?

"Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina"

Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa

"Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..."

Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta...

"Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba se a wannan karo, baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..."
Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa.

Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna kan ya miƙe a zuciye kaman kububuwa ya fice....

"Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?"
Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta.

Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi.

"Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki"
Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka.

Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta...

***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa?

Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa)
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

442 134 20
[TAG-LISH] MOONSTONE SERIES #1 "Welcome to my humble abode," Xyve. 𝐆𝐞𝐧𝐫𝐞: Fantasy/Mystery-Thriller/Romance/Action Start: September 15, 2021 End...
27K 1.3K 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace m...
112K 7.9K 38
Tace "ke ni kin isheni, kin saka ni a duhu, me kike nufi da waďannan zantukan? Nace "kin sha faďa mini yadda mace ke gane tana ďauke da ciki da ya...
163K 10.1K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...