KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 46
Page 47

Page 45

366 21 1
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 45*

*FREE BOOK*

"Har yanzu da sauran ku a sanin rayuwa Kausar... Kai Yusuf har ka isa kayi claiming right akan yaran nan? Anya akwai zuciya a kirjinka? Ka manta yadda ka dinga dukana kana azabtar dani da yunwa duk don kawai saboda kar su zo duniya? Ka manta duk wannan? Ka manta yadda ka ɗaga Usman ka buga kanshi da pillar wadda ya zama ajalinshi? Kana Tunanin wannan rayuwa da kake ciki shine kaɗai alhakin ran Usman? Yusuf wallahi wallahi da za'a bani izinin kashe mutum kwara ɗaya rak a duniya babu wadda zan zaɓa in halaka se kai, ka sani baka ga komai ba... A da nayi niyyan in ɗau fansar Usman da hannuwa na sede a yanzu na fasa wannan kuduri, kar ka yi tunanin saboda Abba ne ko su Aisha a'a, don babu ruwan Allah da wani yaci albarkacin wani a ranan gobe, ranar da uwa zata guji ƴarta, ƴa ta guji uwarta dangi su guji dangin su.. Abunda duk ka aikata shi kaɗai kai kaɗai zaka girbe abunka.. Aisha!!"

Ta kira Aisha dake cikin mota, saukowa yarinyar tayi ta tako ta zo kusa da Hidayat tace
"mommy ga ni!"

Inda Yusuf yake bata kalla ba, wasu irin hawaye masu ciwo ne ke fitar mishi, se a yanzu yake jin wani irin ƙaunar yaran da son su na shiganshi, kallon Aisha yake yana fata ko sau ɗaya ne ta kalleshi ta kira shi da suna 'Abba' abunda da a baya idan sun kira shi da hakan ji yake kaman sun jingina shi da mutuwa, Kallonshi hidayat tayi ta kalleta tace

"Aisha ga Abbanki na magana..!"

Aisha bata juya ba tace
"Mommy ni shi ba Abba na bane, ga daddynmu nan..!"

Ta Nuna Raed, rarrafowa Yusuf yayi yana shirin kai hannu Jikin Aishan don riƙeta wani irin ihu ta saki tana tsugunawa ta boye kanta cikin kafafunta

"No! Please don't touch, karka taɓa ni Mommy kice kar ya taɓa ni mugu ne! Ze kasheni yadda ya kashe yaya Usman... Mommy don Allah mu tafi kar ya dake ki ba zan iya shigar miki kaman ya Usman ba...!"
Gabaɗaya ta ruɗe, da sauri Raed ya ɗaga ta yana calming nata.

Yusuf kife kanshi yayi a ƙasar wurin yana kuka sossai, hidayat tace cikin muryarta dake rawa sossai
"ka gani ko? Yusuf ruwa cikin cokali ya ishi me hankali ya sha yayi wanka! A yanzu da nake da komai cikin harda duniya wato kuɗi ina da daman da zan sa a daureka ko a kasheka ba tare da kowa yace komai ba amma ba zan yi hakan ba! Ka zauna kayi tunanin laifukanka da hukuncin ubangiji kilan ka rage wasu abu daga cikin manyan zunubanka..."

Juyawa tayi tana kallon Abba tace
"Abba ni ma mutum ce kaman kowa, ina da zuciya a kirjina Abba sun min abunda ko kuɗi nake takawa basu cancanci taimakona ba, amma ba zan iya barin su hakanan ba! Abba ka basu wani abu su sake gina rayuwa albarkacin Abbana"

Daga haka ta juya ta koma mota tana share hawayenta, duk da kallo suka bita har ta koma, sossai umma da Yusuf ke kuka lallai rayuwa, haka Mahaifinta ya rubuta cheque ya ba umma, duk suka koma mota wannan karon kam Aisha motar Raed ta shiga suka bar arean, Maami bata ce komai ba saboda ta san idan Yusuf me hankali ne kalaman Hidayat gareshi shagube ne, idan ya fahimta yayi aiki dashi ya yiwa kanshi idan kuma be yi ba duk kanshi aka ce 'A word is enough for the wise'

Seda suka sauke Ummi gida kan suka koma asibiti, jikin Buba dae gashi ga yanayin shi, se dare duk suka watse..

Har suka koma gida mood ɗinta be dawo daidai ba Dukda yadda yake ta comforting ɗinta, bayan sun yi wanka suka kwanta nan ne ya mata ainihin rarrashin da ya kamata suka yi bacci hankali kwance..

Washegari aka kira shi wani meeting na Kano pillars Kaduna, kwana biyu ze yi don ze shiga Abuja sannan ya dawo, ya so tafiya da ita amma ta ƙi.

Gidan Abbanta ta koma, Laure ta nemi Maami da ta bata wasu kudade ta shiga kasuwa don sun riga sun zama kaman dangi babu wani kunya ko nauyi tsakaninsu, aiko ta bata dayawa ba tare da ta tambayeta me zata yi dasu ba.

Sayayya taje ta yi sossai ta fara gyaran hidayat, tun tana kunya har ta sake tana kwasan ilimi wurin Laure, har Maami bata take ta sha, kwana uku kaɗai suka yi gyaran ciki da waje seda hidayat ta sauya, a ranar da ze dawo da safe ummi ta zo ta ɗauke ta suka tafi saloon suka wanke kai daga nan suka je gidan kunshi inda aka zuba mata kunshi ja da baki wadda yayi mugun amsar ta, rabon ta da kunshi tun sunan Junior shima ba wani me kyau bane chan.

Ta fito a Amaryar ta se shining take, azahar a gidanta ya mata Baaba Laure na ta tsokanarta ko a jikinta, Maami dae se dariya bata ce musu komai ba.

Ita da ummi da Rashida suka raka ta gidanta, suka yi en goge goge tunda ba datti yayi ba suka Haɗa mishi abinci, tuwon semo miyan kubewa da yaji naman rago tayi, rashida tayi rice da vegetable sauce se chicken kebab, ummi kuwa zobo ta hada se ta ɗan taya su da ayyukan suka shirya dining dab magrib...

Sallama suka mata dama da motan Rashida suka taho, rashidan ta sauke Ummi kan ta wuce gida.

Bayan sallahn magrib ta shirya cikin Atampha riga da skirt da ya zauna ya fitar da shape ɗinta sossai, isha tayi kan tayi light make up ta ɗaura dankwalinta ɗas.

Kallon kanta take tana murmushi lallai rayuwa wani abu ne me cike da darasi iri iri, a da ina ta san wani wankan jiran miji amma ji ta a yanzu rayuwa babu zagi, ba firgici, ba duka, ba yunwa ba rashin sutura, babu ya zan yi yau da rashin lafiyana da na yarana, rayuwa ta sauya mata zuwa kololuwar daraja cikin dangin ta da jin daaɗi.

Sam bata ji shigowarshi ba sbd nisa da tayi cikin Tunanin se ganin mutum tayi tsaye bayan ta mirror, tsorota tayi zata kurma ihu yayi hanzarin zagaye ta ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana dariya.

"Matsoraciya ni ne fa!"
Ajiyar zuciya me karfi ta sauke se ta sauke hannunshi tana tura baki a shagwabe tace
"shine ka tsorata ni..!"

Yace
"Toh kin ɓace a Tunanin da ban san na menene ba har fa sallama nayi baki amsa ba"

Juyowa tayi tana zagaye hannunta a kwankwasonshi ta ɗaga kai tana kallon shi sbd tsawo da ya ɗara ta tace
"bani da wani tunani se naka paapi..! I missed you sossai"

A goshi yayi mata peck yana fadada murmushinshi yace
"missed you more baby gurl"

Kan tayi wani magana ya riƙe bakinta cikin nashi, da kyar ta dakatar dashi duk suna sauke numfashi tace
"mu je kayi wanka ka ci abinci"

Kallon lips ɗinta kaɗai yake a shagwaɓe..

Dariya take mishi ganin abunda yake yi kaman wadda ta hana shi wani abinci me daaɗi, ƙara rungumota yayi ya sake fara kissing ɗinta yana murmuring
"bari nayi maganin me mini dariya..."

Janyewa tayi tana sake dariya, yana jefa mata rikitaccen kallon yace
"Baby gurl I can't stop myself from kissing your lips...cause you are the reason why I turned so romantic"

Jan shi tayi zuwa toilet tana blushing,
"ni de ba ruwana! yi wanka abinci na jiranka"

Yace
"bazaki taya ni ba?"

Kafaɗa ta make tace
"so kake in ɓata wankan da ko nayi kyau baka kai ga cewa ba?"

Wara idanu yayi ze yi magana tayi saurin rufe toilet ɗin tana dariya.

Ɗakin shi ta koma ta ɗauko mai kananun kaya da armless abubuwan da yafi sakawa, ta feshe su da turarukan shi kan ta kai mai ɗakinta ta sauka ƙasa gabaɗaya ta zauna.

Saukowanshi yasa ta ɗaga kai tana Kallonshi suka sakarwa juna murmushi, a nan tsakar parlorn ta shirya mai abinci don ita bata cika son zaman dining ba ko don bata saba chan bane oho, tana zuba abincin yana bin hannayenta da kallo seda ta gama kan ya riko hannayen yace

"hannunki yayi kyau sossai baby gurl I love this..."
Yayi maganan yana bin zanen lallen da yatsanshi wadda ke tada mata tsikar jiki, yace
"zaki dinga yi min? Ban taɓa sanin suna da kyau haka ba"

Kai ta gyaɗa tace
"amma fa in mun koma Paris da wuya a samu wurin yi"

Yace
"and ur dressing ban san haka kayan Hausawa ke da kyau ba, u look so breathtaking die hard I love you..!"

Murmushi kawai ta saki tace
"ga wani abincin Hausawan ma I know bazaka iya tuna Last da ka ci ba I cooked it myself I promise you will love it"

Yaukin kubewan yake kallo yana ɓata fuska, da kanta ta wanke hannu ta ke yankan tuwon tana bashi, ba karya yayi daaɗi sossai da kuma ya cinye Leda biyu se yaji ya koshi fiye da yadda yake koshi da abinciccikan turawa, zobo ta bashi ya sha yana lumshe idanu yace
"amma fa Daadida na cuta na, bata taɓa min tayin irin abubuwan ba when ever I visited her"

Yayi maganan yana tura baki, dariya take yi tana cewa se ta faɗa mata santi ya saka yana mata sharri kilan da ta bashi ya ƙi ci ne...yana ce mata yanzu ma ya baro ta asibiti se Wayanshi ya katse shi.

Picking yayi da "hello!"
Da sauri ya miƙe tsaye yana cewa
"What???"

*****

Tun da Hidayat suka Barsu anan sun jima sossai zaune suna Tunanin abubuwan da suka aikata a rayuwa, barinma umma da Yusuf in suka tuna abunda suka aikata se su ji kaman su kashe kawunansu, basu taɓa sanin rayuwa zata juye musu haka ba.

Se yanzu Allah ya ɗaura mishi tsananin ƙaunan yaranshi sede kuma sun riga sun mishi nisa babu yadda ya iya, da kyar ya iya maida kanshi gida ya rufe kanshi a ɗakin matarshi da ta gudu ta Barsu bayan ta gama dasu.

Hannunshi da yake ji kaman ana yagalgalawa don ciwo yake kallo yana maimaita kalaman Hidayat, yayi karatu ya san me hannunka me sanda yake nufi, shin me anfanin rayuwarshi a yanzu? Yayiwa Allah laifuka masu yawan gaske, yana neman sassauci wadda tuba yayi kaɗan, Allah ya riga ya yanke dukkanin hukuncin laifukan shi shin ze zauna ya cigaba da ganin iftila'i kala kala ko ze nemawa kanshi sassauci wurin karɓar hukuncin da ta dace?

Kwana yayi be runtsa ba, da sassafe ya miƙe ya fice daga gidan ba tare da yacewa kowa komai ba.

Ko da ya isa inda za shi seda yayi jiran awa biyu kan aka buɗe, ya miƙe ya shiga.

"Don Allah alkali nake nema?"

Mutumin ya kalleshi yace
"ko lafiya kake nemanshi?"

Yace
"abu me matukar muhimmanci ne ya kawo ni"

Yace
"ka ɗan yi hakuri yanzu zaka ga ya shigo"

Zama ya sake yi minti minti se su Haɗa idanu da secretary ɗin be damu ba, illa kawai zuciyarshi da baya jin daaɗin ta ko kaɗan.

Chan se ga alkalin ya iso bayan wani ɗan lokaci yayi umarni da a shigar da Yusuf, bayan ya shiga ya zauna suka gaisa ya tambayeshi me ke tafe dashi?

"Na kawo kaina ne a yanke min hukuncin laifukana bisa tsarin shari'ar musulunci ko zan samu rabauta ranar gobe, nayi abubuwa masu yawa wadda bana Tunanin a yanzu in na mutu zan ji ko da kamshin aljanna ne... Ka taimakeni yallaɓai"

Girgiza kai alkalin yake yi kwarai Allah na son Yusuf da tuba da har yayi wannan tunani
"ko zan so sanin menene ka aikata haka?"

Cikin kuka yace
"na aikata zina da matan da ba zan iya kirgawa ba, abu mafi girma da na aikata shine kisan kai! Na kashe ɗana na cikina da hannayena saboda ya karewa mahaifiyarshi dukan kawo wuƙa da nake mata!!"

Salati alkalin nan ya saki ya sake sakewa, a hankali Yusuf ya dinga bashi tarihin rayuwarshi da Hidayat har karshe, Seda alkalin nan ya zub da hawaye, shiru ya kasa magana.

"Ka zalunce wannan baiwar Allah, ka cutar da rayuwarta, lallai lallai kan kowani hukunci da za'a yanke maka ka fara neman yafiyanta, Allah kan yafe laifin dake tsakanin shi da bawa amma baya yafe laifin tsakanin mutum da mutum wannan tsakaninku ne"

Yace
"a yanzu babu inda zan iya ganin hidayat in nemi yafiyar ta, ina so a sadda za'a yanke min hukunci in yi video sakona ya isa zuwa gareta watakila bayan raina zata yafe min, ina kuma so labari na ya zama izina ga mutane, a lokacin da ka samu dama kayi aiki me kyau da ita kan ta kubce maka wallahi wallahi tsakani da Allah na fara son hidayat sede ganin bata da galihu bata da gata sheɗan yayi nasara a kaina na cutar da ita na san babu wadda take dashi a duniya da ze kwantar mata enci na manta Allahn da yayini me kuɗi da dangi itama shine yayi ta..."

Ajiye shi aka yi, bayan dogon zama tsakanin manyan malamai aka yanke mishi hukuncin bulala na laifin zina se kisa ta hanyar rataya bisa kisan Usman da yayi, yayi kuka sossai a sadda ya ji hukuncin wadda aka bashi kwana biyu ya gyara tsakanin shi da Allah ya tuba iya yadda ze iya kan kwana biyu ya cika😭😭

             DIDDIGAR ƘAYA
        (Mai wuyar Tsincewa)

Gureenjo🥰😍

Paid book
300

Tsokaci/Dandano

Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.

"Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!"

Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
"Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.."
Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace
"ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!"

Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.

Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe

"Ammi! Baba Alhj basa ƙauna ta Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwana na be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!"
Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar?

Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin?

"Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina"

Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa

"Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..."

Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta...

"Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba se a wannan karo, baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..."
Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa.

Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna kan ya miƙe a zuciye kaman kububuwa ya fice....

"Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?"
Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta.

Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi.

"Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki"
Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka.

Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta...

***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa?

Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa)
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank

Karku sake a baku labari.


                🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

1.6M 97.8K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
425K 23.7K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
12.3K 568 13
Love, romance, destiny, paid
82.9K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...