KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.8K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 40

292 25 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 40*

*FREE BOOK*

Shiru parlorn ya ɗauka Aisha na riƙe da Hidayat har lokacin ta ɗaura kanta bisa cinyar ta tana shafawa, Allah kaɗai ya san me ke tafiya cikin ran Raed don gabaɗaya be taɓa sanin menene ainihin ciwo a zuciya ba seda yaga irin kalar kukan da Hidayat take yi, gabaɗaya he wasn't his self yana riƙe da Junior da ya fara rikici, hamza na zaune gefen Abba da yayi shiru kawai amma shi kaɗai ya san me ke tafiya a zuciyarshi.

Daadida ma na zaune gefenta buzayen nan ne namijin yana riƙe da Hajiya da take ta so ta fisge, gyaran murya mahaifin Rashida yayi yace
"Toh Alhamdulillah aka ce komai yayi farko zae yi ƙarshe, sannan duk nisan jifa ƙasa zata dawo, abubuwa da dama sun faru wadda kawunanmu duka suka kasance cikin duhu Dulum tunda ga wacce aka tabbatar da mutuwar ta zaune a gabanmu, sannan ga hajiya dake wasu maganganu kaman wacce ta samu taɓuwar kwakwalwa, na tabbatar kowa a nan yana son sanin me ya faru? Taya abubuwa suka kasance a haka? Yaya kowannenku yayi rayuwa?"

Shiru ya ɗan yi kan ya cigaba
"Aisha! An auro ki an raboki da iyaye da en uwanki aka tsallake gari ya gari aka kawo ki har garin Kano, aka kuma damka amanarki hannun Hajiya Balaraba, ta karɓa hannu bibbiyu wadda seda kowa yayi sha'awar zamanku ake yiwa Usman dacen samun maatan kwarai kwatsam se kuma abubuwa suka juye, shin me ya faru?"

Ba tare da ta kalli hajiya balaraba ba tace hawayenta ya kasa tsayuwa
"Kaman yadda duk kuka sani sunana Aisha haifaffiyar garin mambila na jahar Taraba, na taso nayi rayuwa da iyaye na kaɗai ba tare da wani ilimi akan zama da kishiya ko kishi ba, ko da aka kawo ni garin Kano wallahi da zuciya ɗaya na shiga gidan yaya balaraba, a yadda ta karɓeni ta riƙe ni kaman ƙanwarta kowa se yayi sha'awar zaman mu, da ita zamana lafiya amma da mijina gashinan.... Mun Rayu cikin wannan aure da daaɗi ba daaɗi, dukda son juna da muke, matsalar da muka fara fuskanta shine a duk sadda ranar kwana na ya zagayo jini ne ze balle min baze tafi ba har se ya bar wurina ya koma wurin balaraba, tun bamu damuwa har abun ya zo ya fara damun mu saboda ina neman shekara da aure babu abunda ya taɓa shiga tsakaninmu.

Da farko iyayena na so samu da matsalar, don damuwar har ta saka ni fara rama Dukda Alhj be taɓa nuna damuwa ba yana hakuri yana kuma Adu'a nima yana kokarin kwantar min da hankali da cewa lafiya ta ƙalau Dukda kankatar shekaruna na san ba lafiya ba, ranan muna zaune da Yaya balaraba se take tambaya ta..

"Ni kam Aisha lafiyanki kuwa? Kwanan nan fa se rama kike tayi ko de mun kusa jin kukan jinjiri ne kike ɓoye min?"

Nayi murmushi nace
"wani irin kukan jinjiri bayan abunda ya dame mu ya damemu"

Tace
"ban gane ba?"

Nan na faɗa mata duk abunda ke faruwa, ban san kowa a Kano ba, bani da ƙawa bayan mahaifiyata a lokacin kuma sede ziyara, basu da waya a gida bare in faɗa mata damuwata ta waya, na ɗauki dukkanin yarda da amana na baiwa yaya balaraba, tashin hankalin da ta shiga a sadda taji wannan labari ko Alhj se haka, tayi ta damuwa tana maimaita maganan bayan kwana biyu ta nemi mu je wurin wani malami ya duba matsalar kilan mutanen ɓoye ne.

Ban yi mata musu ba na tambayi Alhj, ze nuna rashin amincewa na saka mishi rikici don a ganina ba shine a cikin matsalar ba, Allah kaɗai ya san irin azabar ciwon mara da nake sha a duk bayan kwana biyu, haka ya kyale mu muka tafi malamin nan ya tabbatarmin da matsalar sheɗanu ne ga abunda za'a kawo a fara jinya.

Seda nayi jinyar wata ɗaya zuwa biyu kan jinin ya fara ɗaukewa, a sannan hankalina ya fara kwanciya don ko ze zo bayan kwana biyun baya ciwo kaman baya, a sadda na fara murnan samun sauƙi a sannan Alhj ya ƙaurace min, baya cin abincina, baya kwana ɗakina magana wannan in ze Haɗa mu sede ya faɗawa yaya ta faɗa min, ita na samu da wannan matsalar ma ina kuka nake gayamata ga abunda ke faruwa tsakanina da Alhj, da kanta ta ajiye mu don yi mana sulhu buɗan bakinshi se cewa yayi na zama ƙazamiya komai nawa yana wari shiyasa baya son zama kusa dani da mu'amalantata don ko abincina kyama yake bashi.

Nayi kuka sossai na shiga damuwa, se in yi wanka sau biyar a rana, nayi ta yawon tambayar Yaya ko tana jin wari jikina se tace ita kam bata ji komai ba, a lokacin Hamza na ƙarami sossai dashi nake yini nake kwana yana debe min kewa gabaɗaya na barwa Yaya Alhj ina me cigaba da Adu'ar samun sauƙi wurin ubangiji ina kuma yin maganin wannan malami da yaya ta kaini wurinshi.

A taƙaice wannan matsala seda ta kaimu kusan watanni takwas, matar abokin Alhaji ita ce mace na biyu da take kaman ƙawa a gareni a Kano ta girme mini don zata yi sa'a da balaraba hakan yasa bana iya buɗe mata cikina gabaɗaya, har na je gida na dawo babu wadda ya san ina cikin damuwa saboda ganin irin farin cikin ganina da su Mama suka yi yasa na kasa faɗa musu matsala ta kar na saka su cikin damuwa.

Bayan na dawo ne na kai mata ziyarar wani ɓari da tayi, nan take tambaya ta ni kam shiru ba ciki ba labari? har ga Allah ban so fitar mata da sirrin aurena ba sede abun na damuna, nan na bata labarin komai, bani da maraba da naani a gidan Alhj Usman, don komai na hamza a wurina yake, haka girki daga nawa har na Yaya ni nake yi ita ta kwana da miji.

Salati ta saki ta fara yi min faɗa akan kishiya ko ya take ka ji tsoronta, ban hanaki zama da kishiyarki lafiya kuma da zuciya ɗaya ba sede fa ki kiyaye ki zama me lura da hange, ni ba son raba zaman lafiyanku nake ba sede akwai Ayar tambaya me girma akan Hajiya Balaraba.

Tashin farko na nuna mata ban yarda ba, don har ga Allah duk wadda ze zagi ko ya kushe yaya har raina haushinshi nake ji, duk yadda ta so fahimtar dani na kasa fahimta se ta koma ta bayan fage, mahaifinta malami ne ta mishi bayanin komai ya neme ya ganni, roko na ta dinga yi akan kar na faɗawa Yaya haka ban faɗa mata ba na fita muka je.

Adu'o'i da tofi ya bani da wasu magunguna akan in na fara sati biyu kar in fita ko ina, hayaƙi kuma in yi tayi a ɗakina, sossai ruwan da ya bani na sha ya taimaka mini, inda na dawo gida nake magungunan, kaman kuwa an toshe min baki ban fadawa yayar ba se bayan da na gama maganin ranan da rana muna zaune a babban parlor se ga Alhj.

Da sauri na tashi zan shige ɗaki don kusan haka zaman namu yake a sannan yayi saurin cewa
"Aisha! Ina zaki daga shigowa ta?"

Daga ni har yaya da mamaki muka tsaya muna Kallonshi.

Yace
"kawo min ruwa pls"

Na wuce kitchen na Haɗo mishi ruwa na kawo ya karɓa yayi godiya yana me kallona, zan tafi yasa na zauna hira suke da yaya ya kan sako ni ciki Dukda shakkar amsa shi da nake ji don ban manta wahalar da na sha a watannin daga gareshi ba, ko hanya muka Haɗa bani da maraba da kashi a wurinshi.

A ranar a tare muka ci abincin rana da yamma ya fita damu shopping, yana ta kokarin janyo ni jiki yayinda yaya take nan shiru kaman ruwa ya cinye ta.

Bayan mun dawo a lokacin ma bayan isha'i se gani nayi Alhaji yayi ɗaki na, da lallami yasa na saki jiki yayi ta min rantsuwar be san meyasa yayi min abunda yayi ba, tsakanin miji da mata se Allah, se a ranar Allah ya nufi tabbatuwar aurenmu bayan kusan shekara biyu.

Washegari da Yaya ta fahimta se ta ɗauke min wuta, gashi Alhj se riritani yake yana lallaɓani, in na mata magana se ta share ni na sameta har ɗaki nake tambayar ta lafiya? Tace
"ban san me kika daukeni ba Aisha! Ni kam a matsayin ƙanwa na dauke ki ashe har zaki iya tsallakeni ki je wurin wata neman taimako? Yanzu kin bata aikin malaminmu na farko kuma ya ce akwai matsala don aljanun da ya raba ki dasu na farko zasu iya dawowa"

Na tsorata nayi ta bata hakuri tace ba ruwanta sede mu koma wurin malamin, duk a zatona hajiya Adama(matar abokin Alhj) ita ta gayamata.

Haka muka sake komawa wurinshi ya bani wasu magungunan, zamana da yaya babu matsala amma Alhj yau lafiya gobe babu, na sha wahala sossai nayi ta rashin lafiya don sau kusan biyar ina yin ɓari, bani da sirrin da yaya bata sani ba tsakanina da miji na, kwarai naji tsoron Allah na ji tsoron munafukin mutum me fuska biyu, don na bata yarda ta ci amana ta, tana da baiwar lafuzza wadda ko baka so idan ta kanainayeka se ta ji cikinka da salon munafurcinta.

Mun je kasashe kusan biyar ganin likita akan yawan ɓarina sede ba chanji, wani cikin da nayi Seda ya shiga wata na bakwai nayi nakuda me matukar wuya na kusan sati, na fita hayyacina gabaɗaya saboda wahala a lokacin muna a Saudia, da taimakon Allah wani malami kuma likita ya taimaka mana inda na haifi kadangare, iya tsoro mun tsorata nan ya kwantar mana da hankali ya tabbatar mana aikin asiri ne akwai Mahaifinshi ze taimaka mana.

Mutumin nan ya taimake mu tsawon wata shidda nayi jinya kan na dawo garau, tun yaya na mita har ta gaji ta kyale mu a Tunaninta zama kawai muke ko jinya nake ta hanani zaman lafiya, bamu baro Saudi ba seda na samu cikin hidayat na wata uku.

Ko da muka dawo wurin Adama naje muka kara komawa wurin mahaifinta nan yayi ta min nasiha yace kuma in kiyaye kishiya ta shima kuma ze cigaba da bani taimako, anan na fara jin tsoron Yaya don tabbas na yarda fuska biyu gareta.

Da ta fahimci hakan se ta fara nuna min ainihin halin ta a fili, munafurci da kirsa babu wadda ban gani ba wurin yaya, wani lokacin Alhj ya yarda wani lokacin kuma Allah ya taimake ni, duk burina akan cikina ne, nayi alkawarin bashi kariya da raina da numfashina, babu abunda zata bani inci tayi yin duniya ta gaji ta kyaleni, cikina na wata takwas wani rana ina kwance bayan nayi walaha se bacci ya ɗan sureni.

Mummunan Mafarki nayi macizai na fito min daga jikin gini zasu marasa kyaun gani, bakunansu na zubar da bakin jini kuma suna kiran sunana cikin muryar amsa kuwwa, a firgice na farka se muka Haɗa idanu da yaya da sauri tace

"Aisha!"

Nace
"Na'am yaushe kika shigo?"

Wannan magana shine na karshe da nayi da wani a gidan Alhj, a take naji na tsani environment ɗin da gidan na tsani garin Kano gabaɗayanta, kaman tunzura ni ake ana turani akan in bar garin, da hijab a jikina jakana kawai na ɗauka na rataya na fice ba tare da na sake ko waiwaye ba.

Tasha na iso ina ji na ba lafiya ba, kaman me maƙuwa haka nake ganin kaina bana gane duk wani magana da ake a gefena ko a kusa dani, da taimakon Allah na ambaci Taraba a tashar nan suka gane inda nake son zuwa kenan aka ce min rana yayi motocin jalingo sun tafi sede Gombe, haka na biya na Gombe.

Kusan tafiyar awa takwas ta kawo mu Gombe Dukda tarin gajiya, yunwa da ƙishir ruwa da nake ji haka na sake neman tasha ba tare da na damu ba na biya kuɗi aka sake dauka ta zuwa Taraba(jalingo) nan ma wata tashar na nema na samu motar da za shi gembu, kafafuna sun kumbura sumtum in banda sunan garinmu ban yiwa kowa magana ba tun fitowa ta don kaman bebiya na zama duniyar tayi min shiru babu abunda nake so illa in yi nisa da Kano.

Kwana nayi a hanya don ban isa gidanmu ba se wurin karfe goman washegari, jiri nake gani sbd yunwa ga tsohon ciki da kyar na iya na kawo kaina gida, amma se yaya Buba ya ƙi amsata bakin ciki da ciwon da nake ciki ya hanani iya furta ko wacce kalma don ko nace zan furta ɗin ma bani da tabbacin magana me anfani ne ze fito daga bakina don kwakwalwata ya riga ya juye gabaɗaya bana jin nice karan kaina.

Yana wullo ni na samu na kare cikina, na mike ban tsaya ba don nan ɗin ma ji nayi na tsani kowa, na mike na naushi hanya nayi tafiyar kafa na kusan awa uku zuwa huɗu don bana gani da kyau kafafuna basu iya daukana, ashe na bar gari ma gabaɗaya na fara shiga tsaunuka, anan na faɗi.

Na farka na tsinci kaina a wani gida cikin wasu mutane, da kyar na iya buɗe idanuna cike da son fahimtar nan ɗin ina ne, se na fahimci kaman gida ne na masu zaman kansu ko na haya, don wasu na zaune suna karta, wasu na shaye shaye, wasu na
Cacar baki, wasu na wanki suna jin wakokin da daga ka ji zaka san ba na mutanen arziki bane, babu abunda babu a tsakar gidan en daudu, mata da maza.

"Kin ganta nan riba biyu, ga na ɗan ciki ga na jikinta.. A nawa zaki saye ta?"

Matar da tayi kama da tsohuwar kilaki tace
"amma ai kaman bata da cikakken lafiya gaskiya Ba zan baka ya wuce dubu ɗari uku ba"

Yace
"kai Asabe! Kin san Allah duk gembu ba zan sama miki irin macen da kike so me kyau da diri kaman wannan ba, ina me rantse miki tana haihuwa shikenan zaki fara Moran ta yadda ya dace"

Ina kwance kaman mutum mutumi ana ciniki na, daga karshe dubu dari biyar ta bashi, ta sa aka kama ni aka kaini wani ɗaki ina rungume da jakana da be bar jikina ba.

Abinci aka kawo min saboda irin yunwar da nake ji jikina na rawa ainun na hau ci hannu baka hannu ƙwarya na gama na sha ruwa se bacci, ba zan tashi ba se idan lokacin sallah yayi wannan kam Allah be mantar dani ba zan tashi na gabatar na sake komawa bacci, bana tashi se yunwa.

Idan suka hana ni baccin kuma to haka zan kwana in yini ina maganganu wadda suke alakantawa da hauka, don zan yi kuka, in yi dariya duka ni kaɗai.

Seda nayi sati uku wannan gida ba tare da na san a ma wani gari bane, wata rana tsakar dare wuta ya tashi a gidan.....

#Vote
#share
#comment




                 🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

6.1K 233 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
593K 62.8K 25
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...
57.3K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...
45.1K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...