KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.8K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 38

273 25 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 38*

*FREE BOOK*

Bata iya ta runtsa ba seda ta tabbatar da yayi bacci, ta kashe lokaci sossai tana kwantar mai da hankali a wayan har ta dena jin amsar shi, mikewa tayi ta watso ruwa ta zo tayi nafila tana me rokarwa mahaifinta lafiya tana kuma Rokon Allah yaji kan mahaifiyarta.

Washegari da wuri ta tashi da kanta tayi breakfast ta Haɗawa Abbanta ma breakfast wadda ze ji daaɗin shi, bayan ta gama taje tayi wanka a lokacin su Norah ma sun yi wanka suna tambayar ta ina taje jiya har suka yi bacci bata dawo ba?

Tace musu
"Dad ɗina ne be da lafiya I have to be there through out"

Aisha tace tana so ta ganshi, tace su shirya su je duka tare.

Bayan sun fito ta shiga wurin Daadida suka gaisa kan ta Haɗa mata breakfast ɗinta nan kan dardumanta don bata iya zaman dining wai na yara ne gwiwowinta se su sage, Albarka ta sa mata kan ta miƙe ta fito, tana rufe kofan yana rufo na parlor.

Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, a tare suka sakarwa juna tattausan murmushi, kallonta yake daga sama zuwa ƙasa, sossai tayi kyau cikin Rigan lace da aka mishi ɗinkin manya, ya haɗu karshe ya kuma bi jikinta kasancewarshi milk da emerald green.. Ɗan kunnen kunnenta fashion marar girma ne emerald green se sarkan mamanta na gold dake wuyanta.

Shi kam as usual sanye yake da kananun kaya designers wando da riga black and ash, hannayenshi zube cikin aljihu, a hankali ya ciro su tare da warawa yana kallon idanunta, zare cute eyes ɗinta tayi kan ta make kafaɗa tana kallon kofan daakin Daadida, baki ya taɓe kan ya fara takowa zuwa gareta yana sakin murmushi ganin yadda ta sunne kanta kasa, shi kam ko a jikinshi ya rungumeta suka sauke ajiyar zuciya a tare.

Peck yayi mata a goshi yace
"Good morning Die hard!"

Tana motsa hannunta dake sanye cikin nashi tace
"morning paapi, hope ka tashi lafiya?"

Kai ya gyaɗa yana lumshe idanu sbd kamshinta dake aika mishi da saƙo yadda ya kamata, tace
"mu je kayi breakfast"

Ya kalli hannunta dake riƙe cikin nashi farare sol kyawawa a gyare tsab yace
"u rejected my proposal yanzu hannunki yayi somehow without a ring"

Murmushi tayi tana jan hannun nashi zuwa dining tace
"wani proposal kuma bayan na zama matar aure gabaɗaya, but that ring yana da kyau sossai fa!"

Yace
"I changed it with another one in mun koma zaki gani, baby gurl we are leaving together today right?"

Zata yi magana yaran da suka kalli baban nasu yanzu suka fara gaida shi, Junior har da saukowa ya zo wurinshi, ɗaga shi yayi ya cilla sama suna dariya suka zauna, da kanta tayi serving nashi ta Haɗa mai tea ta tura mishi gabanshi, itama ta zuba nata don already yaran sun yi nisa a ci.

Yana yin loma ɗaya ya lumshe idanu yace
"you cooked?"

Murmushi kawai tayi, yace
"kin san wani abu?"

Ta girgiza kai tana Kallonshi, yace
"from the first time I tasted ur cook taste ɗinshi be ƙara barina na huta ba, I always longed to eat ur cooking u r really a great Cooker! Thank God"

Yadda ya karashe har yana ɗaga hannu sama ne ya sakata sakin dariya, ƙasa ƙasa yake maganan ko yaran ba jin abunda suke faɗa suke ba.

Cigaba da cin abincinta tayi wani sashe na zuciyarta na tuna mata Yusuf, zata gama wahalar yi mishi girki da mutanenshi babu sannu bare na gode, bare kuma a zo maganan yabawa, ta zauna da monster ne kawai as a husband.

Har suka gama ci suka tashi Tabawa ta zo ta tattare babu wadda ya sake magana. Abincin asibiti aka kai motanshi se ga Daadida ta fito a tare suka tarkata duka suka yi asibitin.

Ɗakin da Abba yake suka fara shiga, yana kishingiɗe hannunshi rike da chasbi yana ja, gabanshi wani farin dattijo ne zaune suna magana, shigowansu ya fadada fara'arshi yana musu sannu da zuwa.

Hidayat dake murmushi ta karasa ta ajiye basket ɗin hannunta kan ta duƙa ta gaida dattijon, ya amsa yana kallonta da murmushi ta juya ta gaida Abbanta da suka gama Gaisawa da Raed, shima ya amsa yana tambayar ta gajiyar jiya, murmushi kawai tayi

"masha Allah, duka waennan jikoki nane?"

Daadida na murmushi tace
"wannan da wannan sune yaran wajen Hidayat babban ya rasu, su biyun nan kuma yaran Raed ne mahaifiyarsu ta rasu duk suna wurin Hidaya yanzu!"

Yace
"masha Allah tabarakallah! Ga mata kam sababbi fil a Leda se wadda na zaɓa, kai kam bana yi da kai..."

Yayi maganan yana kallon Junior, se ya koma ya kama hannun Raed yana Kallonshi fuska a kwaɓe, duk dariya suka yi, Norah da Farrah suka gaida shi yayinda Aisha taje ta kama hannunshi tana Kallonshi tace

"Mommy kin ce Abban ki! Wannan kuma ai ba Abbanki bane na gidan umma...ba kin ce ya tafi kenan ba ze dawo ba? Ko in an mutu ana dawowa? Yaya Usman ma ze dawo?"
Duk ta jero tambayoyin tana kallon hidayat.

Rasa amsar bata hidayat tayi se ta kau da kai hawaye na cika mata idanu, kwarai itama tana matukar kewar Usman da Abba sede ta kan musuAdu'a Allah ya gafarta musu yasa sun huta, Abba ne yace

"Aisha da gaske ne duk wadda ya mutu baze dawo ba! Wanchan ma Abbanta ne kin san mommynki princess ce tana  da Abba's dayawa dayawa"
Ya karashe yana shafa kan yarinyar, cikin mamakin yadda hidayat ta sawa ɗan ta na fari suna Usman don ya san bata san shi ba! Har gwara Aisha ma ze iya cewa zata san sunan mahaifiyarta ne.

"Princess wannan ma Abbanki ne, shine babban amini na minister of finance na yanzu"

Dukawa tayi ta kara gaida shi tana murmushi shima ya amsa cikin fara'a yana mata barka da haduwar su da mahaifinta, Abinci ta zuba musu dukkansu biyu don tana ji Abbanta na maganan tun bayan da ya fito sallar asuba yayo nan don tun jiyan be san yana asibiti ba.

Raed da Daadida da kuma yaran suka wuce ɗakin Baba Buba, se bayan fitansu Abbanta yace
"Yayanki hamza ma yana samun sauƙi ɗazu ya bar nan!"

Tace
"Abba bari na kai mishi abinci ko?"

Yace
"eh ya kamata! Don ban ga hajiyar shi ba banda tabbacin ta zo ko bata zo ba, matarshi kuma na jego"

Kai ta gyaɗa kan ta ɗauki basket ɗin ta fice bayan ya gayamata room number, da sallama ta shiga ɗakin yana zaune kan gadon ya zubawa gini idanu, duk ya rame ya lalace kaman ba hamza ba.

Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, ta karasa ta zauna bisa kujera kan tace

"Yaya ina kwana? Ya jiki?"

Kallonta yayi kan yace
"lafiya na gode!"

"Ba dae fushi kake da hukuncin ubangiji ba yaya? Duk abunda fa kaga ya samu bawa muqaddari ne daga Allah kila taka jarabawar kenan, don Allah ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya ko hankalin Abba ma ze kwanta! Yanzu ka fara rayuwa saboda yanzu ne ka fara tara iyali please be yourself for the sake of Allah, Abba and ur little child"

Hawaye masu zafi ne suka zubo mishi yace
"Meyasa se ni za'a hukunta da laifin mahaifiya....."

"Shhhh Astagfirullah! Karka yi saɓo mana yaya! Ka jingine duk wata damuwa a gefe ka sa a zuciyarka ni haramiyarka ce, ko da Raed ko ba Raed babu aure a tsakaninmu ko da mu biyu kaɗai muka rage a aduniya, don Allah ka komawa Allah duk abunda ya sameka harda sakaci wurin neman zaɓin Allah"
Ta karashe a tausashe.

Kai ya gyaɗa mata, jakanta ta buɗe ta fiddo counter ta bashi, ya karɓa yayi mata godiya.. Abinci ta saka mishi tana zaune a gabanshi har ya ci mai yawa, bayan ya sha kunun gyaɗar ya gama yace

"Amma me kike Tunanin hajiya tayiwa mahaifiyarki da zafi haka? Hajiya wasn't herself tun jiya kaman akwai abunda ya taɓa ta, she called asking for some huge amount of money daga account ɗin Abba ban bata ba na dae bata abunda zan iya daga nawa account ɗin, like she was desperate!"
Ya faɗa wondering don abunda ya hana shi bacci kenan Tunanin me hajiya zata yi da makudan kudin da ta ambata tana so.

Hidayat tace
"Ka dena Tunanin duka wannan yaya! Ka fara samun lafiya tukuna ka ji?"

Kai ya gyaɗa, se aka turo kofan da sallama ɗago kai tayi se suka Haɗa idanu da Zainab.

Ganin hamza zaune yana danna counter yasa ta karaso tana kallon hidayat tace
"Hidayat??"

Dariya hidayat Tayi tace
"ya aka yi kika gane ni haka da wuri Auntyna?"

Murmushi zainab tayi tace
"jikina ne kawai ya bani ke ce hidayat! Sannu da zuwa yaushe a gari?"

Hidayat tana karɓar yaron na bayan zainab tace
"Na kwana biyu amma se jiya na haɗu da yayana, masha Allah wannan yaron ai ni yayo yaya hamza kalli kaga don Allah bamu yi kama ba?"

Murmushi yayi ya san so take tayi cheering ɗinshi ya manta komai ya ɗauke ta as sister, shima se ya daure yace
"sossai ma yaro in be ɗauko goggonshi sakike ba wa ze biyo to!"

Dariya suka yi har zainab, hidayat tace
"Aunty zainab kin shiga wurin Abba kuwa?"

Tace
"eh Seda na gaishe shi na shigo nan"

Hidayat tace
"ko bakon ya tafi?"

Tace
"A'a yana nan"

Hidayat ta miƙe rungume da yaron tana duba wayanta tace
"OK, bari na shiga Da Rashida ta gaida shi, ummi ma tace tana hanya"

Bata jira Cewar zainab ba ta fice..

Kallon Hamza Zainab tayi tace
"kaina ya kulle! Yaushe hidayat ta San Abba haka da har zata gayyato mutane gaida shi daga zuwa dubiya itama? Like yadda take maganan kaman akwai sanayya ko wani abu"

Murmushi me ciwo yayi yace
"Hidayat is my half sister zainab, mahaifinmu ɗaya muma se jiya muka sani"

****

Tana fitowa ta isa enterence na ward ɗin ta shigo da Rashida suna hira, ɗakin Abba direct suka yi suna shiga da sallama Abokin Abba yace

"Rashida?"

Wara idanu tayi tace
"Daddy!"
Se ta saka dariya tace

"Daddy dama ka San Abban hidayat?"

Yace
"eh shine best friend ɗina da na kan baku labari baku taɓa zuwa duba shi bane sbd bakwa zaman Nijeria"

Rashida tace
"Daddy and hidayat is my friend mun haɗu a school a Paris, kaga Ikon Allah ko?"

Abba yace
"ai ba'a mamaki da ikon Allah"

Gaishe shi Rashida tayi tana ajiye Ledar hannunta, ya amsa da kulawa yana tambayar ta school... Suna cikin gaisuwa se ga ummi itama ta zo room number hidayat ta faɗa mata ta karaso itama da karamci Abba ya tarbeta suka gaisa sossai har yake cewa shi ya samu lafiya ma yau gida ze karashe wuninshi.

Duk suka yi murmushi, hidayat tace
"Abba bari na karasa dasu su gaida Baba"

Kai ya gyaɗa yace
"na shiga da safe nake jin abunda likita ya faɗa, Allah dae ya bashi lafiya amma kam yana jin jiki"

Amsawa suka yi da Ameen, kan suka fice zuwa ɗakin Baba Buba suna tafiya Hidayat na musu introducing juna.

Da sallama suka shiga, yana kwance as usual cikin jin jiki, Raed na tsaye yana waya amma tunda suka shiga idanunshi ke manne bisa kanta, murmushi kawai ta sakar mai ta kauda kai, yaran na zaune bisa center carpet dake ɗakin sun saka ma Buba idanu suna kallo sbd yadda yake rattabo zantuka, Daadida na zaune bisa kujera.

Gaisawa suka yi da Daadida kan suka gaida Raed suka kuma gaida Baba Buba, yaran suka gaida su.

"Yaran nan kun ji ko? Wai ba zan sha ko ruwa bane har nan da sati biyu, ko kurɓi ɗaya fa... Wallahi yunwa nake ji, kishi nake ji!"
Cikin tausayawa hidayat tace

"Baba saboda lafiyanka ne in shaa Allah komai ze wuce"

Yace
"uhmm ƴan nan yunwa bai da daaɗi, ashe haka nayi ta azabtar da Muhammad da yunwa ban kyauta ba! Ban kyauta ba wallahi"
Duk fa da kyar yake iya fusgo maganan.

Rashida tace
"baba save ur energy yawan maganan nan yana kara rage maka lafiya ne, ka dinga Ambaton Allah in shaa Allah komai ze zo da sauki"

Kallon Daadida yayi yace
"Mama kin ce akwai ƴar Aisha da ta zama matar Raed anan? Waccecce don Allah in nemi yafiyar ta ko zan samu sassauci?"

Hidayat tace
"ni ce baba! Kuma na riga da na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaya"

Hawaye yake zubarwa da miyau yana cewa
"Allah sarki Aisha!"

Yini sur suka yi a asibitin da su Rashida, ummi da Rashida kaman sun shekara da sanin juna, anan take ganin wasu daga cikin en uwanta ta ɓangaren Abba, duk wadda ya zo Abba ze aika a kira ta ko wurin ya hamza ko wurin baba ko chan waje Inde suke zaune ta zo yayi musu introducing juna, ba laifi kuma kowa na maraba da ita cikin farin ciki.

Yamma Lis aka sallami Abba, hamza ma da Hidayat bata barshi ba ta saka shi yayi ta karatun Alqur'ani da azkar jikinshi ya ɗan yi karfi yace sede a sallame shi, shima aka sallame shi.

Duk wadda ze shiga duba Baba Buba se ya zub da hawaye sbd kowa ya shiga se ya faɗa mai yana jin yunwa, Raed ya mai alkawarin kaza da youghurt me sanyi duk randa likita yace ya ci abinci, abun nashi kaman iska yanzu ze yi ta magana anjima in ciwon ya buge shi se nishi, cikin da ya kumbura kaman balon balon likitocin suka yi mishi Mini-surgery suka saka wani roba ta gefen yana zub da ruwan dake taruwa a cikin banda wari babu abunda yake.

Fitowanta kenan tayi sallar magrib ta idar aka fara kiran layin wayanta, dubawa tayi ta Mikawa Hidayat take cewa
"duba min sunan wanene?"

Hidayat tace
"Daadida ai ba suna lamba ce"

Daadida tace
"kayya! Tun fa jiya ake kirana da lamba in na ba wannan farar baturiyar(Norah) se tace layi ne kawai bazan dauka ba in sun gaji swa barni na shaki iska Haba"

Hidayat tayi picking ba tare da tacewa daadida komai ba ta kara a kunnenta...

#Vote
#share
#comment


                  🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

11.5K 1.5K 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da b...
6.2K 234 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
2.5K 85 19
Wani numfashi yasaki mai ƙarfi agigice yajawota tafaɗo kanshi cikin karaji yace nashiga uku indo sa hannu kija zai fita idan kikayi haka . Kamo hannu...
1.7M 95K 87
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...