KOWA YA GA ZABUWA...

Por Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... Mais

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 37

323 23 0
Por Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 37*

*FREE BOOK*

Wasa kawai take da yatsun hannunta tana alwalar kuda wadda babu ruwa, motar ta ɗauki shiru banda sanyin Ac da fitinannen kamshin shi babu abunda ke tashi, yadda yake tuƙi kaman ba ze tafi ba tunda ya ɗauko ta yasa ta ɗan ɗago ta saci Kallonshi.

Da suke Gaisawa da Ummi kaman ranshi ba'a ɓace ba amma kallo ɗaya ta mishi taji bata so ta sake Kallonshi cikin wannan ɓacin ran ko ba Sanadiyarta ba bare sanadin ta, a hankali tace

"Paaapi!"
Be amsa ba Dukda muryar da tayi anfani dashi ɗin ba karamin shigarshi yayi ba, Raurau tayi da idanu muryarta na rawa tace

"am so sorry....! Na san ban kyauta ba amma..."
Kukan da yake son kubce mata ne yasa tayi shiru, kaman ze share ta sede ba ze iya ba, parking yayi gefen titi ya zuki iska ya fesar a lokaci ɗaya ya sanya hannu ya yaye hijab ɗin jikinta ya cire kan ya mirginota zuwa cikin jikinshi ya rungume.

Dukkansu idanu suka lumshe suna jin kewa, soyayya da kuma tausayin juna.

Hawayenta ne yake diga mishi har cikin fatar kirjinshi, ƙara sanyata yayi jikinshi cikin taushin murya ya ɗago haɓarta yace
"shhhh! Baby gurl you cried enough today pls don't start again now..."

Hannunta ta ɗaura bisa rigar shi ta kara riƙe shi jin yadda yake sake mannata da jikinshi cikin salo.
"My fatherrr....!"

"Shhhh baby don't say anything about him, ba laifinshi bane now u know who that evi...."
Da sauri ta saka tattausan hannunta ta rufe lips ɗinshi.

"Duk munin halayyar iyaye babu inda aka mana umarni da mu ci mutuncinsu ko mu zage su, Paapi I love you and bana son fushin ubangiji ya hau kanka saboda Baba Buba, pls find a place in ur heart and forgive him ɗan Adam ajizi ne..."

Kallon mamaki yake jifan ta dashi yace
"after all he have done to you? And my aunt? I mean ur mother?"

Kai ta gyaɗa tace
"Besides ni na yafe mishi, please forget the past and focus on the future..! Kaga ba don shi ba kila we will end up as cousins not lovers, ba don shi ba kila da baka min taimakon da ze sa in ji duk duniya babu wadda bana so ko kuda ya taɓa ba kaman kai... Maybe I wouldn't have given birth to Usman, Aisha and Junior you! Ka ga every disappointment is always a blessing..! Had it been be maka abunda ya maka ba da pastor polycap be ɗauke ka ka zama the greatest footballer of our Era ba..."

Yadda ta kare maganan da wink yasa ya saki wani malalacin murmushi, lip ɗinshi ya kai yayi pecking idanunta da ta lumshe, ya dawo yayi na hagu kan yayi kissing nose tip ɗinta daga karshe ya dira a lips ɗinta.

Seda ya gaji don kanshi ya gyara mata kwanciya yana saka hannunshi na hagu ya tallabo chin ɗinta yana shafawa a hankali yace
"Baby gurl you are a blessing indeed! I love you"

Tace
"nima haka yayana!"
Fuska ya ɓata yana turo lips yace
"what?? What's nima haka again? I said I love you"

Dariya tayi har hakwaranta na fita tace
"love you more..!"

Kiran Wayanshi ne ya katse shi, a hankali ya saka hannu ya ɗauko ba tare da ya raba ta da jikinshi ba ya manna a kunne, mintuna biyu ya sauke ya kalleta yace

"ur dad regain his consciousness and yana so ya ganki please die hard don't cry again for my sake..! Allah baki ji yadda na shigo Nigeria da rashin daaɗin zuciya ba when ever Tunanin kin yi kuka ko kina kai yayi crossing mind ɗina, and please don't ever go out again without my consent I was totally upset ɗazun nan!"

Lakace mishi kumatu tayi har dimple ɗinshi ya Luɓa suka yi dariya a tare tace
"I won't in shaa Allah, am sorry"

Kai ya gyaɗa kan ya taimaka mata ta koma mazauninta seda suka saka hijab a tare kan ya tada motar suka yi tsadaddiyar Asibitin da dama chan aka saba kai Alhaji Usman kuma anan suka kawo Baba Buba.

****

Da kwatancen Daadida suka iso Amenity room ɗin na VVIP wadda bashi da maraba da gida sbd haɗuwa da tsaruwarshi, hannunsu riƙe cikin na juna yayi knocking kan ya tura ita kuma tayi sallama..

"Hidayat!!!"

Muryoyi biyu suka yi kiranta wadda ya sakata tsayawa chakkkkk kaman an dasa ta, da sauri ta kalli wadda ya kirata na biyun ta maida kanta ga na farkon wadda shine mahaifinta ta kara maida idanunta ga na biyun muryarta na rawa tace

"Ya Hamza???? Me kake yi anan? Dama ka san wannan??"
Ta Nuna Alhj Usman don har yanzu bata san da wani suna zata iya kiranshi ba.

Yace
"Hidayat..! Wannan ai mahaifina ne, me kike yi anan? Dama kece hidayat da yake ta kira tun farfaɗowarshi?"

Hajiya tace
"kai! Kai!! Kai ni fa kun kulle min kai... Kowa hidayat hidayat hidayat! Daga mijina har ɗana? Ke wai wacece ke ne nikam? What's the meaning of whole this??"

Alhj Usman yace
"Hidayat jini na ce! Hidayat ƴata ce ta cikina! Hidayat ɗiyarmu ce ni da AISHA! ita ce ribar soyayyar mu.."

Duuuuummmm haka Hajiya da Hamza suka yi, shi kam tsabar kaduwa ne, hidayat da yake hauka da mutuwar so har yanzu yana kan kallon likita sbd aman jini da be dena ba da damuwa ita ce yanzu ake cewa uban su ɗaya? Kenan ko ba Raed sun haramtawa juna ko menene? Kwarai yana iya tuna ya taɓa jin sunan Aisha chan chan baya matsayin matar Mahaifinshi... Da sauri ya kalli hajiya da ta zabga wani ashariya tace

"Wallahi baze yiwu ba! Alhaji me ki....ka..ke nufi? Wace Aishar??? A ina ka samo ta bare har ka san wannan me kama da sadaka yallar ɗiyar ta ce?"

Daga hidayat, Raed har Daadida sede wannan ya kalli wannan suna rarraba idanu tsakanin hamza, Hajiya da kuma Alhaji.

Murmushi yayi yace
"kwarai da aniya wannan jinin Aisha ce da baki so gani ba a duniya Hajiya Balaraba, hamza! Hakuri zan baka ina kuma baka tabbacin cewa bad deeds ɗin mahaifiyarka ne Allah ya ramawa baiwar Allah ta hanyar jarabtarka da matukar soyayyar ƴar uwarka jini ɗaya, ita mahaifiyarka na faɗi tashi wurin ganin ka tsira yayinda a baya tayi faɗi tashi wurin ganin ta raba auren sunna ta raba uwa, uba da ƴar su sede dayake Allah ba azzalumin bawansa ba Kaine ka wahala Sanadiyarta don ko ba komai da a gabana hidayat ta tashi da baka mata wannan son mutuwar ba..."

Dishi Dishi hamza ya fara gani, ya kalli hajiya ya kalli Abban shi se kuma ya kalli hidayat, idanunshi ya sauka bisa hannayensu dake sarkafe cikin na juna da Raed, runtse idanu yayi wasu zazafan hawaye suka zubo.

Hidayat hajiya ta zubawa idanu jin kalaman da Abbanta yake faɗa game da ita, kenan itace silar komai? Kenan ita ce ta raba ta da farin ciki da jin daaɗi na rayuwar wannan duniya?

Shigowar likita ne yasa duk suka kalli kofa, yace
"ya kamata ku barshi ya huta hakanan duk abunda Zaku tattauna ku bari gobe da safe jininshi ya hau har ya wuce misali.."

Daadida tace
"hakane Dr, yanzu zamu tafi in shaa Allah zamu hakura da jin koma menene seda safe"

Hamza mikewa yayi da niyar fita se ya yanke jiki ya faɗi, Hajiya ta kurma ihu tayi kanshi tana cewa
"Hidayat ce! Wallahi Hidayat ce! Duk itace, ita ce fa wallahi itace...!"

Yadda take maimaita kalma ɗaya zaka yi tunanin akwai matsala a kwakwalwanta, Dr kiran nurses yayi aka ɗauki hamza zuwa wani room ɗin don dama shima ba'a sallame shi a asibitin ba yana kan medication ne.

Hannu hajiya ta sa a kai ta kurma ihu tana nuna hidayat tana cigaba da faɗin duk ita ce wallahi duk ita ce ta rusa mata gida..

Raed dae bayanshi ya maida hidayat yana mata wani irin disgusting look, gangan Alhj Usman suka koma ya ɗan duka ya gaida shi, ya amsa cikin kulawa yana murmushi.

Daadida tace
"Sannu da jiki Alhj Allah yasa kaffara ce"

Ya amsa da
"Ameen mama na gode! Amma don Allah kan ku wuce ku duba yaya Buba tare muka zo yana next room"

Shiru Raed yayi Daadida ta fara share hawaye tace
"Allah sarki! Duk abunda yayi maka baka duba ba ka nufe shi da alkhairi? Allah ya saka ya sa a mizani mun gode... Raed ka gani ko? Ka ga irin zuciyar mutanen kirki? Shi fa salwantar mai da iyali yayi a lokacin be ma sa ran sake ganinsu ba hakan be hana shi taimakon shi ba se kai da ya haifa ya kawo duniya zaka Gaza yafe mai laifukanshi gareka..!"

Hannunshi dake cikin nata ta ɗan matse ya kalleta da idanunshi da suka rine da ido ta mishi alamar please! Ya kalli Daadida yace

"na yafe mishi already albarkacin macen kirki Hidayat..! Kiyi hakuri yanzu zan je na duba shi"
Rungume su duka tayi tana kuka en jikokinta da bata da Kamarsu a duniya.

A hankali Raed ya saki hannunta ya kama na Daadida ya ja suka fito yana yiwa hidayat kallon be careful Dukda hajiya tayi gaba already tana kaɗa zani sbd birkicewar da tayi har lokacin bata dawo daidai ba.

A hankali hidayat ta taka gaban gadon ta ja kujera ta zauna tana kaucewa kallon da Alhj Usman ke mata, muryarta na kakkarwa tace

"Saan..nu Ab....ba "

Lumshe idanunshi yayi yana jin sanyi na ratsa shi, tunda ya farfado se yanzu yake jin wani abu na farin ciki na shiga cikin zuciya da ruhinshi, dukda yayi babban rashi sede ya gode Allah da ya bar mishi hidayat ɗin ma.

"Sannu princess!"
Se ta kalleshi jin sunan da ya kirata dashi, a tare suka sakarwa juna murmushi.

Yace
"princess yau zaki zauna da Abba ko? I want to spend the night listening to ur stories Ina so every single thing na rayuwar da kika yi kar ya wuce ni..! I've missed a lot bana so in sake missing ko da second ne na rayuwarki.."

Murmushi me tafe da ciwo tayi tace
"Abba gwara kayi bacci ka huta in Allah ya kaimu gobe se in baka labarin don in har na baka yanzu bazaka iya bacci ba"

Shiru yayi na mintuna kan yace
"mahaifiyarki mutumiyar kirki ce, har Abada zan cigaba da kewar macen arziki mar'atussaliha irin ta..!"

Murmushi kawai tayi a hankali yake bata labarin wacece mahaifiyarta se ta fahimci a halayyar su kaɗan ne kawai suka sha bambam amma kusan duka halayyar su iri ɗaya ne, yadda yake murmushi me ciwo zaka san kwarai ya so mahaifiyarta kuma yayi kewar ta.

****

Kusan a tare da Daadida suka shiga ɗakin sede shi daga bakin kofa ya ja ya tsaya yana kallon Baba Buba, yadda ya zama bazaka taɓa cewa shine Buban chan ba, Buba me son tarin abin duniya, Buba marar mutunci duk ya kwanjame baki a karkace, rabin jikinshi a mokaɗe.

"Buba!"
Daadida ta kira sunanshi da tarin mamaki don bata taɓa zaton jikin ya kai haka ba.

"Buba baka samun kulawa ne? Baka cin abinci ne? Innalillahi wainna ilahi rajiun"
Ta faɗa hawaye na zubo mata, lokaci ɗaya shima ya fara zub da hawaye me ciwo idanunshi na kan Raed dake tsaye daga bakin kofa ya kau da kai sbd hana hawayen idanunshi zuba.

Ko yayi magana ba ji za'a yi ba in ya nace kuma shi yake shan azabar ciwon.

Hannu kawai ya sa ya kama na Daadida yana zub da hawaye.

Raed da kafafunshi suka gaza ɗaukan shi ya juya ze fita se Buba yayi karfin hali fusgo sunanshi..

"Muhammad!"

Chak ya tsaya se ya juyo yana kallon shi.

Baki a karkace cikin taune harshe yake maimaita
"ka yafe min don Allah! Ka yafemin!"
Yana kuka sossai.

Da sauri Raed ya zo ya riƙe hannunshi Ɗayan yana zub da hawaye yace
"Na yafe maka baba, ka dena kukan nan ka samu lafiya ka ji?"

Yace
"ni kaɗai na san azabar da nake ciki Muhammad! Ni da lafiya kuma har Abada, na zalunceku na raba abunda Allah yafi so Wato zumunci na cuci kaina na cuci rayuwata...."

Tarin da ya fara me yawa ne yasa Raed danna red button se ga Dr da nurses.

Dr yace
"am sorry please wani irin Nutrition kuka ɗaura shi a kai? His condition is very bad am sorry to say!"

Yace
"ban gane ba? Is it about the paralyze or something else?"

Dr yace
"I don't really know me aka bashi we are not sure but rabin hanjinshi ya ruɓa, a hoton da muka yi ya nuna mana an yi aiki an yanke sede ba'a yi replacing ba so he keep suffering yanzu dole se mun sake aiki! Please karku bashi ko ruwa ne har nan da 5 days muga yadda aikin ze kasance"

"innalillahi wainna ilahi rajiun!!"

Daadida ta faɗi tana dafe baki, tace
"duk yaushe aka yi haka Buba? Ina kudaden da nake aika maka na abinci da magani? Me hakan ke nufi Buba? Innalillahi wainna ilahi rajiun"

Raed ɗauke idanu yayi yana maida hawayen ciki, yace
"I think we are leaving to another country"

Dr yace
"duk abu ɗaya ne sir, muna da duk wani kayan aikin da zaka same shi a kasashen waje haka likitocin mu zasu yi mishi aiki fiye da na Kasar waje kwanciyar hankalinku muke bukata da nashi, in shaa Allah ze samu lafiya sede yanzu yana jin jiki"

Kai suka gyaɗa Raed dae was not convinced, asibitin kam ya amsa sunanshi sede hankalinshi be kwanta ba.

Babu wadda ake bari ya kwana, wuraren karfe ɗaya Hidayat ta zo ta duba baba Buba itama Seda tayi kwalla, lallai kaji tsoron rayuwa. Yanzu wannan alhaki dake dawainiya da wannan bawan Allah in tace bata yafe mai Bama ai ba zuciya a kirjinta itama kaman shi a baya.

Haka suka bar asibitin cikin alhini me girma, Raed bayan ya sauke su gidanshi ya wuce duk se ta damu don kallo ɗaya zaka mishi ka san ganin Baba Buba ya taɓa shi ko min lalacewar uba ubane tabbas.

#Vote
#share
#comment


                  🖤Gureenjo🖤

Continuar a ler

Também vai Gostar

6.2K 234 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
10.1K 686 15
Dannar kirji... Gajeren labari mai dauke da darussa kala kala na wata uwargidah da akaiwa abokiyar zama(amarya)😻💕..NA MRS JH AND MSS XOXO
421K 23.6K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
45.1K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...