KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

14.5K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 31

273 23 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 31*

*FREE BOOK*

**Alhamdulillah jiki na da sauƙi, na gode da adu'o'inku Dukda ba wai na warke bane amma dae Alhamdulillah ku cigaba da sakani cikin Adu'o'inku Allah ubangiji ya raba dukkanin bawa da ciwo🤧***

Shanyayyun idanunshin nan ya sakar mata yana kallon yadda take kuka a hankali cikin rashin sanin makama, cikin wata karyayyiyar murya yace

"ya isa haka! Pls stop crying yana damuna wallahi har tsakiyar kirjina nake jin digar kowanni hawaye naki, Idan kina bukatar lokaci to think I can understand..but please karki ce a'a don ban san ta yadda zan fara ba, all I know is that I promise to love you forever and ever.."

Kai ta gyaɗa tana share hawayen da ta kasa tsayarwa tace
"zan yi tunani"

Jikinshi ya bayyana irin sanyin da yayi, sossai yaji rashin daaɗi maybe bata son shine sbd be da komai a addini, maybe bata sonshi ne saboda hamza, maybe bata son shi ne sbd rough past ɗin shi.. Ko ma menene all he knows shine he Is deeply hurt.

The drive was so silent Har suka dawo gida babu wadda ya sake magana a cikinsu, kokarin fighting na feelings da take ji akan abunda tayi yanzun nan take, she doesn't really know what goes over her abunda ta sani kawai shine she's confuse and abun ya zo mata out of blue, bata taɓa experiencing something like that ba so dole ta rasa Tunanin da zata yi.

"Welcome home dad..! Welcome miss hidayat"

Dukda yadda damuwa ya bayyana karara a fuskanshi hakan be hana sakarwa Norah da Aisha murmushi ba yana ɗaukan junior yace
"thank you gurls, ina Farrah?"

Tana kokarin shiga ɗakinta bayan ta amsa musu sama sama taji Aisha na cewa
"she's upset ko abinci bata ci ba tun break!"

Cikin damuwa yace
"what upset her haka?"

"I think she is having a bad day bcs her friends said something about having a mother.."
Norah tayi maganan itama jikinta na sanyi don ta rarrashi Farrahn har ta gaji.

Da sauri Hidayat ta fasa shiga ɗakinta tayi ɗakin Farrahn, a hankali ya tako sede ganin ta shiga yasa ya tsaya yana jin babu daaɗi a ranshi.

Kwance rub da ciki ta samu Farrah tana kuka, da sauri ta ɗago ta tana juyota tace
"oh my baby me ya ɓata miki rai haka?"

Rungume ta Farrah tayi tace a hankali
"am just missing my mom"

Ɗago habarta hidayat tayi tace
"am always here, in shaa Allah zan maye miki gurbin mom naki ahhhh am already hurt tunda har kika zubar da hawaye sbd mahaifiya afterall gani a kusa dake"

Puppy face Farrah tayi tace
"am not moody just bcs of mom, am moody bcs u are also leaving us soon.. Miss hidayat please don't leave us I promise to be a good girl"

Lumshe idanunta hidayat tayi tare da rungumeta tace
"who says am leaving you?"

"U were promising to marry Daddy hamza and duk sadda kika aureshi  I know u will be leaving..! Daddy promised to talk to u but he didn't please if u have to marry then marry dad and be our real mom"
Da mamaki hidayat ke kallon yarinyar baki kaman kanari da zuba zance.

Tace
"wa ya gaya miki saka kunne a zancen wani abu me kyau ne? It's not a good habit kin ji? Don't do that again.. Oya let's go ki ci abinci"

Hannun da ya ɗaura kan handle ɗin ya janye jin ta fuske magana na biyu da yarinyar tayi, Juyawa kawai yayi ya wuce room nashi yana ji Farrah na sake tambayar ta zata iya kiranta mom sbd mama is not for her yayi local, maganan ya so bashi dariya sede baya cikin mood ɗin yi ɗin har ya shige be kula su Norah da suke shiga zancen nasu ba don already sun fito parlor.

Kasan shower ya shiga tare da dafe glass ɗin da ya zagaye standing shower ɗin ya lumshe idanunshi ruwan na zuba daga kanshi zuwa jikinshi, hidayat na so ta hura mishi wuta, he never expected what she did.. Ya jima sossai a haka kan yayi wanka ya fito, a gaban madubin toilet ɗin ya tsaya ya riƙe kwankwaso yana kallon kirar jikinshi da kyaun surarshi.

Lallai Hidayat daban ce a cikin mata, baya tunanin a kab kasashen da suke duniya akwai inda ze shiga be samu masu sonshi ba, ba ɗaya ba ba biyu ba, ko da macen bata kallon ball ta kan yi social media kuma baza'a rasa shi a kullum a yanar gizo ba Dukda shi ba ma'abocin yin bane sede ayi ta buɗe accounts da handle ɗinshi, wadda yake dashi ma sakuna suna mishi yawa don se ya samu thousands of dms a kowanni flat form da yake, but to his biggest surprise hidayat turns him down.

A kasalance ya shirya yayi sallahn magrib da isha tare da kwanciya don ko fita be sake sha'awar yi ba, ko da junior ma ya tashi daga baccin nashi a nan ɗakin ya bashi madara ya sha sossai yayi mishi wanka ya sa mishi pjmas don duk yaran basa rasa kaya a ɗakin shi, anan suka sake komawa kwanciya.

Yadda yaga rana haka yaga dare yana ta juye juye cikin damuwar da Hidayat ta haddasa mishi, kaman yadda be yi bacci ba haka itama bata runtsa ba, sossai take jin ba daaɗi sede bata so tayi gaggawa wa rayuwarta Sam, chance ɗin yanzu ne kaman yadda ya faɗa kuma a duk iya Tunaninta da hangenta auren hamza shine babban kalubale da zata so fuskanta a yanzu sbd matsalolin family ɗinshi yayinda auren Raed kaman wani kofa ne na dawamammiyar natsuwa da kwanciyar hankali don ko ba komai shi kamilalle ne, yaranshi suna sonta haka ma kakarshi na son ta, sede ko ta ina in ta duba Sanannen mutum irin Raed yafi karfinta a ko wani ɓangare ita ba tsaranshi bace, da taga Tunanin babu inda ze kaita se ta mike ta gabatar da alwala ta zo ta hau nafilfili daga karshe tayi istikhara tana me neman zaɓin Allah..

****

Yau aka sallami Abba daga asibiti sbd komai ya dawo normal tafiya ce dae kam har yanzu se a hankali, a parlor suka yada zango gabaɗaya sbd mutanenshi da suke zuwa akai akai ana taya shi murnar samun cikakken lafiya.

Kowa ya shigo zaka san ba karamin mutum bane don harda minista me ci a yanzu da su comissiononi, en majalisu duk dae wadda yake a tare da Abba a da sbd Abban mutum ne me jama'an gaske, hidima ya hana hamza natsuwar duba waya Seda bayan isha suna zaune a babban parlorn da hajiya da Zainab su biyu suke hiran su don Abba ya bace a duniyar tunani yayinda hamza ya fiddo Wayanshi ya fara dubawa.

A Twitter ya fara cin karo da abunda ya kusa zauta shi, clear picture me tsananin kyau da ɗaukar hankali har ze wuce sbd be sheda macen ba se kuma sunan Footballer Raed ya ja hankalinshi ya sake komawa don dubawa.

"Breaking: the girl with the greatest footballer MOH RAED in the last pictures that go viral wasn't actually his wife she's his girlfriend as he is proposing in a best romantic way ever #Sunset at Seine River❤️"

Be taɓa zagin kanshi ba se yau, yayi Adu'a wani ya fito ya shedawa duniya cewa ba matarshi bace sede gashi a lokacin da Adu'ar shin ta karɓu se ta zama wani kifiya da ya zo ya cake shi a zuciya ya hana gudanar numfashin shi, a take wani mummunan tari ya sarƙe shi kuma ya kasa dena kallon background ɗin don ko a hoto zaka san ba karamin ƙawatuwa wurin yayi ba gata ta fito kaman international celebrity gashi yayi wani tsuguno a gabanta dukkanninsu kuma idanunsu na bisa camera.

Da sauri zainab da hajiya suka yi kanshi, zainab na mika mishi ruwa hajiya na sake salati tana sallamewa.

Be sha ruwan ba sakamakon tafin hannunshi da ya saukar daga bakinshi jini na biyowa baya, ihu hajiya ta kurma tana cewa
"na shiga uku! Jini!! Hamza menene? Me ka gani haka? Wayyoooo Allah na! Hamza"

Shine ɗa ɗaya tilo da take dashi a duniya tana son shi fiye da komai da ta mallaka wallahi bazata iya jurar ganinshi cikin wahala ko wani damuwa ba, Inaaa baze taɓa yiwuwa ba.

Zainab ma kuka ta fara, da sauri ya mike yaje ya kuskure bakinshi a washing hand basin dake dining section ya dawo tare da shan ruwa yana zubewa bisa kujera ignoring duk maganganun da su hajiya suke yi na ya tashi su tafi asibiti zainab na me yake damunshi?.

Abba ne fuska cikin damuwa yace
"Son menene? Me ya sameka haka?"

Idanunshi da suka gama rinewa ya buɗe yace
"Abba hajiya ce take son kasheni! Hajiya ta ƙi aminta da na auri Hidayat gashi wani na kokarin kwace ta daga gareni in ma be kwace tan ba zuwa yanzu"

Ya karashe hawaye na zuba mishi.
Zainab dake Kallonshi cikin wani yanayi ta fashe da kuka me karfi tana mikewa se ta dawo ta zauna tana dafe marar ta tare da sakin kara alamun nakuda da sauri shi da hajiya suka yi kanta Dukda halin da yake ciki se ta buge hannunshi da yake shirin taɓa ta tana Kallonshi cikin kuka tace

"enough! Na gaji kuma ya hamza baka taɓa dauka na da muhimmanci a rayuwarka ba a hakan ne kake Tunanin yin adalci tsakanina da zaɓin ranka? Na sani ni aura maka ni aka yi sbd ni nake sonka sede ban cancanci wannan cin fuska daga gareka ba ko ba don albarkacin aure ba ko don albarkacin cikin jikina zaka tausaya min, idan har kai namiji kishin Hidayat ya saka ka cikin kunci da bakin ciki na kuka har ya kai kana tarin jini ni kuma a matsayi na na mace me ciki me kake tunani? Allah ya saukeni lafiya in shaa Allah zan baku space ka aureta don na gaji.."
Kuka take yi sossai wadda ya mugun taɓa mishi zuciya be san yana illata ta haka ba seda yaga bacin ranta na hakika akan abunda yake yi.

Sam taki ya taimaka mata se hajiya ce ta kama ta suka fice, jagwab ya zube bisa kujera yana ɗaura hannu a kai.

Abba ya kira sunanshi cikin kulawa se kawai ya fara hawaye masu yawa..
"Abba na san bana kyautawa! Na kuma san wallahi in na Haɗa wata macen da Hidayat ba zan yi mata adalci ba! Wallahi ko a sadda hidayat ta auri Yusuf halin da na shiga me sauƙi ne akan wannan, Abba zuciyata ta kumbura likita ya tabbatar min da hakan... Ya zan yi in yi adalci? Ya zan yi in rage yadda nake ji akan hidayat? Ya Allah ka ragwanta mini wannan kadararren Son"

Hannu Abba ya sa ya kirashi ya mike yaje ya kwanta a kafaɗar Abban yana me cigaba da zub da hawaye, cikin tsananin tausayinshi Abba yayi ta shafa kanshi yana kwantar mai da hankali, wannan soyayya ko asiri sede haka tabbas Allah ne ya ɗaura mishi shi kuma tashi kaddarar kenan Allah ya ragwanta mishi.

****

Ko da Rashida ta gani washegari Saturday har gida ta zo ta cika hidayat da ihu, tana son jin kwakwab sede hidayat dake cikin damuwa bata bata amsar da ya sakata farin ciki ba, haushi kaman ta daki hidayat sede a sadda taji silly reasons ɗinta tayi shiru kawai tana kallonta bata ce komai ba, daga karshe ma tattarawa tayi ta tafi.

Akwai UcL da zasu buga so suna da training kuma ba anan Paris ba hakan yasa washegari ya Haɗa kayanshi kawai yayi musu sallama sama sama ya bar Paris.

***

Hamza kashe Wayanshi yayi gabaɗaya, bayan Abba ya gama mishi nasiha ya wuce asibiti Dukda hajiya na cikin damuwar jini da taga yana fita a bakin shi hakan be hana ta Mishi faɗan yadda yake yiwa zainab ba, hakuri kawai ya bata.

Zainab ta sauka inda ta haifi ɗa namiji (nace shikenan raba gardama aka samu)
Kuma tun da ta haihun se ta kama kanta sossai akan hamzan hakan ya saka shi cikin sabuwar damuwa sbd itama yana sonta as his first wife, kuma uwar ɗan shi na fari a duniya, she deserves something good daga gareshi..

Satin suna ya zagayo ya saka ma yaron sunan mahaifinta Dukda ta ji daaɗi kwarai sede bata yi zumuɗi kaman yadda ya so ba.

Fushi sossai yake yi da Hidayat hakan yasa yake iya maida hankali akan zainab ɗin, sbd ya gaji da jin silly reasons nata, ta mishi bayani har ta so ta fishi fushi a sadda incidence na Germany ya faru sede yanzu baya tunanin akwai bayanin da ze gamsar dashi Dukda in ya tuna cewa wani dama ya ba Raed na ya cusa kanshi gareta se yaji kaman yayi tsuntsu ya tafi Paris sede a haka yake ta kama kanshi Abba na bashi shawaran yin abunda ya dace.

***

"mom!"
Norah da yanzu itama ta bi bakin Farrah ta kirata for the first time, hakan yasa firgigit ta kalleta.

"Norah!"
Itama ta kirata tana kallon ta, dukda murmushi ta so saki sede hakan be yiwu ba, ta kula har Aisha ma karfi da yaji Farrah ta hanata kiran mama ta koma mom sede dayake bata cikin cikakken natsuwar ta hakan yasa bata taɓa shiga cikin irin zancen dasu ba.

"Mom! Me yake damunki?"
Norah ta sake faɗa tana kallon hidayat ɗin.

"Nothing baby! Kawai stress na karatu ne u know exams is around d corner"

Norah zata sake magana Farrah daga dakin hidayat ta fara kwala mata kira akan Daddy is on the phone tayi gudu, lumshe idanu hidayat tayi zuciyarta ya buga a lokaci guda, sati ɗaya da kwana uku da tafiyan shi basu taɓa waya ba don da taji ya kira zata gudu kuma bata taɓa jin ya tambaye ta a wurin yaran ba, tana cikin damuwa kwarai sbd hamza ma ta kikkirashi tunda taga yadda hoton su ya zama topic a media yaki ɗagawa.

Raed kuma bata sani ba ko fushi yayi ko yana cikin damuwa, kwarai tana feeling guilty don zuciyarta na tuhumarta da rashin adalci wa Raed, ya fi karfin komai a wurinta ba zuciyarta ba har ranta idan yana so ita me iya bashi ce bcs she's indepted to him.

Washegari ta dawo daga exams na farko da wuri, sbd jarrabawa ya hana su yin magana me kyau da Rashida Dukda itama tana nuna har yanzu haushin hidayat ɗin take ji na ƙin accepting proposal na Raed hakan yasa basu zauna sun tattauna da kyau ba.

Aiki take sede rabin hankalinta na chan wani waje, ringing na landline ne ya sakata dawowa Tunaninta ta fito tana goge hannunta da Towel tare da ɗagawa tace
"Hello..!"

#Vote
#share
#comment


                  🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

47.7K 2.9K 48
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
709 65 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...
83.9K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...
15.4K 804 71
'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba...