KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 21

265 22 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 21*

*FREE BOOK*

"In shaa Allah we will all be happy again..!"
Da kyar ta iya faɗan hakan tana share fuskanta tare da ƙin Kallonshi.

Be fahimci me take nufi da we will da tace ba hakan yasa ya miƙe tsaye yana me ci gaba da kallonta ya kai babban yatsanshi ya sosa giranshi kan ya juya ya fice kawai.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tare da bin bayanshi da kallo har ya fita, mikewa tayi taje toilet ta wanke fuskanta Tare da fitowa ta sauka kasa ta ɗauko junior wurin Miss Mary, ta dawo ta karasa Haɗa musu table ɗin duk fuskanta ba wani fara'a tana jin hayaniyar su daga wani room kuma na gidan dake daura da na Dad ɗin nasu bata De leka ba ta koma ɗaki tare da shayar da Junior tana Tunanin mafita, ta yadda zata shiga rayuwarshi a hankali ta samu ta karkato da hankalinshi zuwa bautar Allah ɗaya.

Har dare yaran basu dawo sun dame ta ba, ko da Aisha ta shigo ce mata tayi Daddy ne ya hana su zuwa kar su takura ta she need a space, murmushi kawai tayi ta shirya yarinyar ta kwanta.

Norah ma ta shigo ta mata good night ta kalleta tace
"Norah hope u prayed?"

Kai Norah ta gyaɗa mata tace
"we prayed with Aisha in my room"

Murmushi tayi tace
"ok kiyi adu'a kan ki kwanta"

Tace
"good night miss hidayat!"

Ta juya ta fice.

Kwanan Father biyar ya tafi duk yadda ya so ya sa Raed sallamar Hidayat kin amincewa yayi, dama kuma su abunda basu iya ba takurawa yara Dukda hidayat ta fahimci sarai baya kaunar ta sede tana mishi uzuri don ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar Raed ɗin kuma ta san duk me ƙin ta a bayan umma ne.

Ta kan yi waya da ya hamza akai akai don shi da gaske yake son ta yake kuma yana so ya aureta anytime soon.

Sanadiyar shakuwarsu da Farrah kuwa shine rashin lafiya da tayi, hidayat ta kula da ita sossai wadda ya kawo kusanci tsakaninsu har yarinyar ta fara son ta, ta kuma fahimci daga miss hidayat har Aisha basu da wani nakasu kawai dae dama kishin Aisha take.

Zaune yake a parlor yana aiki a system ɗinshi yayinda yaran suke tare da Hidayat a ɗaki a irin wannan lokaci ne take musu tarihin annabawa, sanin yana parlor yasa ta fara first move ɗinta cikin danne fargabar da ya cika mata ciki tace
"mu yi tarihin nan a parlor"

Aiko da gudu suka fito itama ta fito, kallo ɗaya ya musu dukansu ya maida idanunshi kan abunda yake yi suka samu wuri suka zauna tare da saka ta a tsakiya.

Ba tare da ta kalleshi ba ta fara musu da
"yanzu bari mu fara yin tambayoyi akan darasin mu na baya, wa ze gaya min annabawa nawa Allah ya ambaci sunansu a Qur'ani?"

Dukkansu uku suka ɗaga hannu ta nuna Farrah.
Da sauri yarinyar tace
"25"

Hidayat tace "Attakbir"
Suka ce "Allahu Akbar"

"To wa ze kira min sunayensu ɗaya bayan ɗaya?"

Norah ta ɗaga hannu ta mike ta fara lissafo su daga kan Annabi Adam (As) har zuwa kan Annabi Muhammad (SAW) zuwa lokacin hankalin Raed ya fara yowa kansu.

Alama he started getting Interest akan abunda suke yi, tace
"to a Tarihin wa muka tsaya ma?"

Suka ɗaga hannu ta nuna Aisha.
"Annabi Nuhu(As) inda yayi katoton jirgi saboda tseratar da kanshi da mutanenshi tare da dabbobi daga ruwan ɗufana"

Itama takbir tasa aka mata, daga nan ta cigaba musu da tarihin cikin muryarta me sanyin daaɗi, gabaɗaya hankalinshi ya Mika musu yana jin tarihin kuma yana mamaki don be taɓa ji ba, tana yi har ta zo inda ɗan Annabi Nuhu (As) ya ƙi shiga jirgin yace ze hau saman tsauni ruwa baze same shi ba amma daga karshe shima ya mutu don yana daga cikin taɓaɓɓu.

"Wani darasi kuka koya cikin wannan Tarihi?"

Nora ta ɗaga hannu tace
"Ba zaka ɓoyewa Allah ko ka guje mishi ba in de har ya tashi kama ka da laifukanka"

Takbir ta sa aka mata tare da Satan Kallonshi se suka Haɗa idanu, fuskewa yayi ya maida kanshi kan system ya cigaba da aikinshi da ya ma manta me yake yi.

Wa'azin Bin othman ta kunna musu a iPad ɗin ta inda yake magana akan sallah.

Inda ya ɗauko ta da zafinta yake cewa
"Allah madaukakin sarki cikin Suratul Maryam aya ta 59 yana cewa 'se waensu en baya suka zo a bayansu suka tozarta sallah kuma suka bi sha'awowinsu. To da sannu a hankali za'a jefa su cikin gayyah"
Allah SWT ya kuma cewa 'sede wanda ya tuba, kuma yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai' shima cikin Suratul Maryam aya 60."

Babban Sahabin nan ibn Abbas Allah ya qara masa yarda yace "ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba a'a kawai sun kasance sun jinkirta yinta ne akan lokacin ta"
Kunga kenan da wannan fassarar ta ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai waenda suke jinkirta sallah akan lokacinta wato basu yinta se lokacin da suka ga dama wannan aya akan su take, waenda suke wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wanchan ayan ba tana magana ne akan kafirai bane a'a tana magana ne akan waenda suke ikirarin su musulmai ne!
Saed ibnul musayyib imamat-tabi'ina Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wanchan Ayar sai yace
"sune waenda basu yin sallar azahar har se lokacin la'asar, basa yin la'asar har se lokacin magrib basa yin magrib har se lokacin isha kuma ku sani duk wadda ya mutu yana a cikin wanna hali be tuba ba lallai alkawarin Allah a tattare dashi ita ce wutar gayyah!
Wato wani Kwari ne a cikin wutar Jahannama wadda yake da zurfi mai nisa  kuma zasu dinga cin wani mummunan abinci me wari da ɗaci da uquba"

Lokacin magrib da yayi ne ya sakata tsayar da Wa'azin tana me satar kallon shi, tsikar jikinshi tayi wani irin tashi idanunshi sun sauya, saboda yadda bin Othman ɗin ke Wa'azin dole In kana cikin masu aikata irin laifin hankalinka ya tashi.

Jin tana cewa yaran suje su yi Sallah ya saka shi ajiye system ɗin shima ya miƙe ya nufi ɗakin shi don yin sallar.

Da kallo ta bishi har ya shige, he's so soft and gentle sannan zama da yayi da su Philip ya hana shi tabuka komai a addininshi wadda ba laifin kowa bane laifin Mahaifinshi ne, kuskuren shi shine da ya girma ya mallaki hankali me yasa be nema sani da kanshi ba? Allah ba ze karɓi hujja akan Babanshi ba sede a karan kanshi.

Tana fata ya sauya a hankali.

Yana shiga yayi alwala ya zo ya gabatar da sallar bayan ya idar ya zauna se ya rasa Adu'ar da ze yi, be san ta yadda ake tuban ba cikin wani irin ciwo da zafin zuciya ya ɗaura fuskanshi bisa tafukan hannunshi hawaye masu zafi suka gangaro mishi.

Wasa wasa kullum tare dashi ake jin tarihin annabawa da kuma wa'azuzzuka, wani Wa'azin mufti menk da yayi akan girman uwa da kuma muhimmancin yi mata Adu'a idan ta rasu yasa ya kasa rike hawayen shi wadda a idanun Hidayat suka ganganro da sauri ta kauda kanta itama idanunta na cika da hawaye.

Ita karan kanta in ta ji irin Wa'azin nan se tayi kuka, mahaifiyarta mutuwa tayi sede bata san ta yadda ta same ta ba har ta faɗa hannun Abba, bata taɓa Tunanin ta hanya me kyau aka sameta ba Dukda yadda Abba ke yabon halayyar mahaifiyarta kan rasuwar ta.. Tambayoyi ne Bila adadin a kwakwalwanta sede bata da me amsa mata.

Magananshi ne ya katse mata Tunanin da ta tafi.
"Miss hidayat! Ya ake Tuba?"

Ta kalleshi da kyakyawan idanunta da suka cika da hawaye murmushi na wanzuwa a fuskanta tace
"sharudan tuba guda uku ne, na farko yin nadama bisa abubuwan da ka gabatar na zunubanka.na biyu ɗaura niyyar cewa bazaka sake aikata irin waenan laifukan ba nan gaba a cikin rayuwar ka, abu na uku shine ka dena aikata aikin saɓon nan take ko da ka kasance kana chuɗanya da ita"

Kai yake gyaɗawa cikin fahimta tace
"idan da hali ka yawaita ambaton Allah in shaa Allah ze yafe maka duk wani zunubanka"

A hankali yace
"thank you! I want to learn from you"

Da sauri ta kalleshi shima kallonta yake alamun tabbaci, ya sake cewa
"ki faɗi ko nawa ne zan biya ina so na koyi abubuwan da kike koyawa yaran nan! I want to pray for my mom"

Wani irin daaɗi ne ya rufe ta cikin murmushi da har yake nuna hakwaranta tace
"bana son ko Naira daga gareka, zan yi saboda Allah.. Nima ba kwararriya ba ce koyo nake har yanzu"

Ze yi magana wayanta ta ɗauki ƙara Aisha dake rike dashi tace
"laaa Daddy hamza ne"

Karɓar wayar tayi Dukda yadda take jin kaifin idanunshi kanta hakan be hana ta ɗauka ba tace
"nayi fushi fa!"

Daga ɓangaren shi yace
"Afuwan gimbiya ai in kika yi fushi da ni se in kashe kaina...!"

Dariya sossai tayi kaman gaske, yace
"kina Tunanin wasa ne ko hmm, yanzu ma kasa hakura nayi da kewar ki dake addabata na taso na zo har Paris"

Wara idanunta tayi tace
"Da gaske don Allah?"

Yace
"sa wasa"

Tana dariya ta mike ta shige ɗaki suna me cigaba da wayan inda ya tabbatar mata da gaske yana Paris yanzu fa rabon da ya ganta yayi 3months, kuma ita yake son kallo da yamman nan, da kyar ta yarda zasu fita da yaran gabaɗaya.

Shiryawa tayi cikin doguwar Abaya black and red ta sa red shoe, tare da riƙe handbag red ta fito tace
"gurls who's in for outing"

Ihu duka suka yi kan suka miƙe da gudu kowa yaje ya fara shiri don ta koya musu saka mayafi duk nata ta babbasu tace su ke rufe kansu in zasu fita.

Tunda ta shige ya jingina da kujera tare da lumshe idanunshi, yana jinsu suna hayaniyarsu har suka fito ta kalleshi tace
"Daddy mun fita"

A zuciyarshi ya maimaita wani daddy mun fita, kwafa yayi yace
"in zaki fita ki tafi ke kaɗai don't involve my children"

Da sauri duk suka kalleshi daga yadda yayi magana zaka san ranshi a mugun bace yake, a sanyaye ta sake hannun Farrah dake cikin nata har zuciyarta maganan be mata daaɗi ba se kace wacce zata je yin aikin zunubi?

Kau da kanta tayi daga Kallonshi tace
"ok Farrah, Norah u should sit at home"

Ta kama hannun Aisha tana rike da Junior suka nufi gangarawa se Farrah ta saka kuka, Norah na Kallonshi da puppy face tace
"Daddy pls, we want to go also na san Miss hidayat zata kula damu kuma bazata bari mu yi dare ba, look at how she's upset ga Farrah na kuka"

Yatsunshi masu kyau da tsari ya cusa cikin gashin kanshi tare da hautsinawa yana me fitar da iska, fuskanta kaɗai da ya nuna rashin jin daaɗi yake gani a idanunshi yana jin wani irin sabon damuwa na bijiro mishi.
Murya chan kasa yace

"follow them bfr they leaves!"
Da gudu suka ganganra ya koma jagwab ya jingina da kujera cikin tsananin mamakin abunda ya faru a yanzu, be taɓa jin hakan ba duk yadda ya so ya saka shi a mizanin hankali ya auna yaga dalilin jin haushin shi be gani ba.

Har magrib yayi yana zaune doing nothing a wurin banda tunane tunane daga baya ya mike yaje yayi sallah, da laptop ɗinshi yayi searching karatuttukan malamai inda ya zaɓi na Sheik minshawi don ya fi mishi natsuwa ya saka yana saurare Dukda ba iyawa yayi ba sede ya samu natsuwa me yawa daga sauraran Alqur'anin.

Awa guda chur ya kwashe a wurin yana ta searching wa'azuzzuka yana downloading, bayan ya gama ya tashi yayi isha daidai lokacin ya ji hayaniyar shigowansu.

Dakinshi su Norah suka yo suna nuna mishi shopping da Daddy hamza yayi musu, kallon kayan kaɗai ɓata mishi rai yake gyaɗa kai kawai yayi yace suje su ajiye a ɗakin su suka juya suka fice.

Mikewa yayi ya fito ya samu wuri ya zauna yana kallon cook ɗinshi dake jera mishi abinci a bisa dining sede ba taste ɗin abincin cook ɗin yake so ba, taste ɗin abincin da ta bashi a sadda bashi da lafiya yake kwaɗayin sake ji.

Junior ne dake Tatata ya fara fitowa yana ganinshi ya fara miƙa mai hannu yana dariya, mikewa yayi yaje ya ɗauko shi yana cilla shi sama yaron na ta dariya, fitowa tayi da nufin kama junior don Aisha ce ta bar kofan buɗe har ya fito turus tayi saboda kusa faɗa mishi da tayi da sauri ta ja baya tana me kau da kanta.

Gyaran murya yayi yana me kallon fuskanta yace
"I'm sorry for earlier"

Ɗan Kallonshi tayi ta ga still ita yake kallo cikin sanyin muryanta tace
"ya wuce ai"

Kai ya gyaɗa yace
"in da gaske ya wuce i want to start my lessons now"

Kai ta gyaɗa ta koma ɗaki ta ɗauko iPad ɗinta ta fito zaune ta same shi ya ɗaura junior kan kafanshi yana mishi wasa, a ƙasa ta zauna tare da tankwashe kafafu shima kasa ya komo yayi irin zaman da tayi, ɗan muskutawa tayi ta kalleshi ya ɗaga mata gira alamun what?

Kau da kai tayi tace
"daga ina zamu fara?"

Yace yana buɗe system ɗinshi
"we have to go for Qur'an and Islamic books shopping it's embarrassing bamu da ko guda a gidan"

Kai ta gyaɗa cikin yarda da abunda yace.

Ya sake cewa
"See ni fa apart from these three surah ban iya komai ba kuma"

Dariya ne ya kama ta jin yadda yake maganan da iyakar gaskiyar shi ko kunya baya ji murmushi tayi har haƙorinta ya bayyana, tace
"zaka koya ne a hankali maybe u r a fast learner"

"Uhmm to Allah yasa kar in baki kunya in ganki gobe da bulala"
Sossai ta saka dariya ashe ya iya cracking jokes, shi kuwa he was lost da ganin dariyar a fuskanta hakan yasa ya cigaba da kallon ta yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata.

Haɗa idanu suka yi tayi saurin hadiye dariyar tana muskutawa, bismillah tayi shima yayi ta fara mishi daga Suratul adiyat.

Masha Allah muryanshi har tada mata tsikar jiki yake duk da yadda yake cracking na en koyo sede yana da murya me tsananin daaɗi da ratsa zuciya, aya biyar din duka suka yi.

Bayan sun gama yayi mata godiya murmushi kawai tayi tana gujewa eye contact ɗinshi duk jikinta amsawa yake a duk sadda suka Haɗa idanu.

"The girls basu yi having dinner ba kar su yi bacci"

Ta girgiza kai tace
"they slept already dama sun ci a waje"

Kai ya gyaɗa, mikewa tayi zata ɗauki Junior da yayi bacci a kafafunshi ya ɗan sosa kai yace
"am starving"

Kallonshi tayi ta kalli dining area tace
"in kawo maka abincin nan ne?"

Girgiza kai yayi yace
"i don't like that, please wani abu zaki min me sauƙi if possible"

Yadda yayi da murya alamun roko ne ya so bata dariya se ta danne kayan ta tana mamakinshi Dukda kasancewar shi me kuɗi kuma oganta baya abu da gadara, ze iya bata umarni kawai ta cika amma ji yadda yake rokon ta.

Kitchen ta nufa shi kuma ya zauna ya cigaba da koyon ayoyinshi Qur'ani na ratsa zuciya da ruhinshi be san akwai wata natsuwa ta musamman daga cikin Qur'ani ba se yanzu.

Duba time yake yana da training gobe a stadium ɗinsu it's getting late, call ne ya shigo mishi ya duba yaga Kimorah shi har ya mance da ita ma, ɗagawa yayi yace
"hey!"

Nan ta fara Mishi shagwaban wai ya manta da ita daga tayi tafiya, a natse yake amsa mata kaman yadda tsarin shi yake cikin tsararriyar muryarshi dake kashe ta da son shi da kuma kishin shi.

"Kinga bana son rigima, I have a training to attend as early as possible nd it's getting late we talk tomorrow"

Daidai lokacin hidayat ta dawo riƙe da karamin tray, a kanshi bowl ne gefe tissue da spoon se ruwa me rangwamen sanyi.

A gabanshi ta ajiye tana sauraran irin kalaman da Kimorah ke mishi sbd wayan a handsfree yake, haka kawai ta tsinci kanta da jin haushi ranta yayi baƙi nan take da ta rasa dalili, ba tare da ta kalleshi ba ta ɗauki junior ta juya tayi ɗakinta, lumshe idanunshi yayi sbd kamshin ta da ta bar mai me kashe jiki ya ware su bisa kanta har ta rufo kofan ba tare da ya san me kimorahn ke cewa ba.

Daga karshe sallama suka yi ya janyo abincin ya fara ci, shi ɗan kwallo ne yana da ci sossai sbd training da suke yi yana saurin burning colories a jikinsu, da ɗan yawa tayi dankalin na turawa da ta sarrafa shi da kifi yaji kayan haɗi ga persely da yayi garnishing abincin kamshin kaɗai ze tsinka maka miyau, tas ya Cinye abincin ya sha ruwa kan ya mike ya kai tray ɗin kitchen ya dawo ya kashe komai ya wuce room ɗinshi duk abunda yake yin nan kuma yana sake biya karatun shi a ranshi.

#like
#share
#comment

                    🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

11.5K 1.5K 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da b...
425K 23.7K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
1.6M 97.8K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
57.6K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...