KOWA YA GA ZABUWA...

Od Gureenjo6763

13.8K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... Více

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 16

239 23 1
Od Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 16*

*FREE BOOK*

***Kun jini shiru, am sorry ear infection ke damuna wlh kuma dae in har ka san ciwon kunne ka san bashi da sauƙi***

Da sauri hidayat ta shiga tana rike hannayenta tace
"it's ok calm down and tell me menene?"

A hankali tayi mata whispering
"blood"

Murmushi hidayat tayi tana girgiza kai, komai fa na yan gata daban ne ita da ta fara period banda ita da ubangiji babu wadda ya sani yanzu ji wannan kwarmaton, fitowa tayi ta cewa miss Mary please ta dubo musu sanitary napkins a dispenser ɗin jikin makarantar.

Kan ta kawo ta koma wurin Norah tace
"it's fine, kowacce mace nayi yanzu girma ne ya kama ki Norah, dole ki dage mu koyi abubuwa dayawa in ba haka ba kina cikin hatsari sbd a musulunci duk wacce ta fara al'ada ta balaga kenan, kuma duk balagagge kaman an buɗe masa sabon file ne babu abunda ze yi na motsi ko magana ba tare da an rubuta ba kuma dashi ake anfani a yi hisabi"

Hawayen ta ta share tace
"am now a woman?"

Dariya hidaya tayi ta gyaɗa mata kai, cikin mintuna talatin ta gama nuna mata yadda zatayi using har ta saka ta fito tana ta aikin sussune kai for the first time da take jin kunyar mutane har haka a rayuwarta don su basa kunyar komai.

Daidai nan babanta ya karaso, a ruɗe yake sbd yadda miss Mary ta kirashi sanye yake da kananun kaya as usual kaman yadda kuka san ɗan ball da kaunar shorts, ko face cap babu a kanshi haka ma be saka face mask ba fuskanshi banda walki babu abunda take sbd reflection na rana ga shi kaman yana anfani da skin care don kyaun fata, yana da skin color me matukar tsada da fusgan hankali.

Da sauri ya karaso ba tare da ya lura da hannun hidayat dake cikin nata ba kai ko ma ya lura su a wurin su ba komai bane ya sanya hannunshi ya kama nasu duka biyu yana kallon Norah from head to toes..

"Baby..! Are you alright? Me ya same ki?"
Ya jefa mata tambayar da ta saka ta dukar da kai kawai, ya sake matse hannayensu yace
"talk to me, kina da wata matsala ne da zan kasa kau dashi? Are you been bullied? Baki son environment ɗin ne? Should we change SC...."

"Daaad" ta kira sunanshi cikin kunya, yace
"yes darling menene?"

Kasa magana tayi se ta kalli hidayat dake tsaye a wurin kaman statue, shima shanyayyun idanunshi ya juya ya watsa mata..

Tun daga sadda Tattausan fatar hannunshi ta sauka bisa nata ta daskare a wurin, wuta ne ya ɗauke mata gabaɗaya ko maganan da suke a wurin ba ji take ba, tsammm haka take jin wani abu na yawo a jikinta wadda bata taɓa ji ba, yaaa salam! Ta faɗi a zuciyarta a sadda taji saukar kaifaffun idanunshi bisa kanta, ji tayi kaman ɗaure ta akai...

Norah ce ta zame hannunta wadda yayi sanadiyar saukar nata ya zame daga nashi hannun, tana kiran sunanta
"Miss hidayat"

Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana  dawowa daidai ta amsa a daburce, be bi ta kanta ba don wani lokacin gani yake kaman ba daidai take ba abu kaɗan ke gigitata..

Daga wurin miss Mary ya ji abunda ke faruwa, se ya juya yana kallon Norah da kaman ta shige ƙasa daga ita har Hidayat ɗin, murmushi yayi yana rungume ta yace
"my Lil girl is now a grown up woman"

Itama murmushin tayi, suka dunguma sukayi gida Norah a motar babanta yayinda hidayat da miss Mary suka tafi a motar da suka zo na gida, sun samu su Aisha sun dawo har ma sun ci abinci, Seda hidayat ta fara taimakawa Farrah da wanka kan ta zo tayiwa Aisha, Norah ta shigo itama tayi wankanta ta zauna wurin hidayat tana sauraran darasussuka akan period wadda ita bata taɓa sani ba..

Hidayat sossai ta tsoratata da hulda da maza, ta nuna mata hadarinshi ba ga lafiyar ta ba har ma ga addininta, kuma sossai Norah ke ɗauka, kiran landline ne ya katse musu Hirar tasu Norah taje ta ɗauka dad ne yace ta kawo mishi Junior..

Ɗaukan shi tayi ta fito ta bar hidayat ɗin da Tunanin sabuwar yanayin da take tsintar kanta a ciki wadda bata taɓa ji ba..

A tsararriyar bedroom ɗinshi ta same su, Aisha na yin homework yayinda Farrah ke yin game a iPad kunnenta headphone ne tana jin wakar da game ɗin ke yi, haushin kasancewar su tare da Aishan take, karbar junior yayi yana mishi wasa yaron na bangala dariya..

Kwarai yake yabawa da tsabtar maman yaran sbd yadda a duk sadda ze ɗauki Junior kamshi na musamman ne ke tashi a jikinshi goyon ta Sam ba kazanta, a hankali ya tuna ranar da aka samu yaron da abunda ya faru, shi dae kwana biyu da suka yi da Hidayat kai tsaye ze iya cewa bata cikin mutane masu fitina ko rashin kunya, to meyasa babansu ze zaɓi wulakantata ta wannan hanya kawai don bata da kowa?

Da fa shima macece hakan za'a yi mishi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wayanshi da ya ɗauki ringing ganin sunan Godfather yasa ya ɗauka facetime ne, hakan yasa wani kasurgumin pastor ya bayyana sanye da kayansu na father, hannunshi rike da Bible kaman yadda bayanshi ke nuna a church yake..

"Hey my son!"

Raed na murmushi yace
"father good af, trust you are doing great?"

Da gudu Norah da Farrah suka zo fuskan wayar tashi suna leke ganin da gaske father ne yasa suka fara mishi surutu
"hello grandpa ka ce zaka zo har yau baka zo ba, we are really mad at you"

Murmushi yake yana cewa
"am so sorry my queen nd my princess, by God grace I will be with you guys in a jiffy, ayyuka ne suka min yawa a nan muna ta bada word of God, mutane na karbar almasihu"

Norah tace
"u r always talking abt this almasihu but Miss hidayat said he is also a Prophet sent by Almighty Allah, bcs Allah doesn't have a wife nor a son"

A take fuskar mutumin ta sauya yace
"who is miss hidayat?"

Farrah tace
"our new nanny from Nigeria grandpa I don't like her"

Raed na kallon Aisha yace
"hey Farrah be nice ok?"

Mikewa tayi ta fice wai tayi zuciya, girgiza kai yayi yana jin amsan da father yake baiwa Norah a lallai lallai se ta amince da faɗar cewa Almasihu is a son of God, ita kuma hankalinta ya fi kama na miss hidayat, daga karshe kyale ta yayi suka maida call ɗin phone call da Raed..

Kai tsaye ya nuna be son sabuwar nanny ɗinsu ze turo wata daga Amsterdam garin da yake a yanzu yana yaɗa addinin kiristanci ta cigaba da kula dasu, Raed be ce komai ba har suka gama wayan ya kashe..

Da Junior ya cigaba da wasa Aisha da Norah na mishi hira jefi jefi kaman daga sama ya jiyo ihun Farrah, da sauri ya miƙe ya nufi waje cikin Tunanin abunda ya same ta, a ɗakin hidayat ya ji kukanta shi da Norah da Aisha ne suka shiga ɗakin..

Tsaye suka ganta tana kuka sossai riƙe da kumatunta yayinda hidayat ke tsaye idanunta duk a waje zuciyarta kuwa banda skipping babu abunda yake..

"Farrah what is it? Me ya same ki?"
Raed ya watsa mata tambayar yana kokarin cire hannunta da ta saka a kumatunta cikin kuka tace

"she hit me"
Tana maganan tana nuna hidayat.

A razane hidayat take kallon yar yarinyar kaman yadda shima yake kallonta cikin ɓacin ran da be san ya bijiro mishi ba, cikin wata kalar murya yace
"how dare you hit my dota?"

A ruɗe tace
"Wallahi wallahi ban taɓa ta ba, taya zan fara dukanta? She came here tace tana son custard na ce mata ina zuwa bara nayi sallar asr da lokacin ke shirin fita se in je in Haɗa mata se kawai gani nayi ta saki ihu tana rike kumatunta but ban taɓa ta..."

"Enough please..!" Ya faɗa har lokacin da ɓacin rai sossai a fuskanshi.

Hannun Farrah ya sauke daga fuskanta wurin kuwa yayi ja, Junior dake bacci ya ajiye bisa kan gadonta ya ɗauki Farrah zasu fita Hidayat ta sake kokarin kare kanta sbd bata taɓa jin zafin a jingina ta da abunda bata yi ba irin yau, sossai abun ya mata zafi wadda ta rasa dalili haka kawai take jin kaman zata yi hauka idan har ya fita da wannan fushin da kuma Tunanin ta taɓa mishi yarinya..

"Sir..! Please believe me wlh ban taɓa ta ba.."

A tsawace yace
"then why her chin shows that? Kalli kumatunta.. I can take anything but not hitting my child ni karan kaina ban taɓa saka musu hannu ba so ba zan yarda common nanny like you ta dakesu ba, If you can't do the job then you should please silently leave tun baki Harzukani ba"

Yana kai nan ya juya ya fice, kuka hidayat ta fashe dashi tana jin ba daaɗi har kasan ranta, idan kuwa bata faranta mishi sbd taimakon da ya mata ba ba zata ɓata ranshi ba, Norah da Aisha ne suka zo wurinta suna share mata hawaye.

Norah tace
"I belive you miss hidayat you can't hit Farrah she's probably lying bcs she doesn't like you"

Zama tayi kawai tana rufe fuskanta da tafukan hannunta tana cigaba da kuka, this is a minor thing a rayuwarta sede ya fi kona mata zuciya fiye da abubuwan Yusuf menene hakan?

Aisha ficewa tayi ta je ta same shi yana ta rarrashin Farrah, a hankali tace
"Daddy mama will never hit Farrah bcs ko mu bata taɓa dukanmu ba, she always says hitting someone is never a solution and will not ever be, gashi yanzu tana ta kuka har Ya Norah ma started to"

Se yaji wani iri, dukda be san Hidayat ba sede Aisha bazata mishi karya ba, idan har bata taɓa dukansu su yaranta ba taya zata fara dukan Farrah, ya san irin yadda ta tashi sbd ya fuskanci abu makamacin hakan shiyasa shima be taɓa dukan yaranshi ba, idan har ze daga hannu da nufin dukan wani se Tunanin mugun mahaifin shi ya darsu a ranshi hakan yasa kwata kwata baya so yaji ko maganan duka ne..

Farrah ya kalla yace
"Baby u knew na faɗa muku lying is a very bad habit right?"

Kai ta gyaɗa, yace
"then tell Me the truth did miss hidayat Hurt you?"

Shiru tayi yace
"I won't be mad ok? Tell me.."

Se tace
"bata dukeni ba, I just don't like her shine friends ɗina gave me idea yadda suka gani a wani film da yarinyar bata son stepmom ɗinta da tayi hakan her dad divorce the stepmom shine nima nayi"

He's so shock da abun, taya yarinya kaman Farrah zata yi acting so fine kaman da gaske hidayat ɗin ta Mareta? Se yaji be ji daaɗi ba sede sbd yarinyar tayi kuka kuma baya so ya sake sakata wani kukan se kawai yace mata
"don't repeat that again is a bad habit kin ji?"

Kai ta gyaɗa ya juya ya kalli Aisha yace
"tell miss hidayat am sorry"

Daga haka ya miƙe ya shige toilet ɗinshi..

Fita Aisha tayi ta koma wurin hidayat da ta samu tana sallah, Norah na zaune daga gefen gadonta, alwala Aisha ma taje tayi ta dawo suka yi sallar tare, bayan sun sallame Aisha tace

"Mama Farrah is lying dad ya gano hakan and he said I should tell you sorry"
Dukda haka zancen be sakata farin ciki ba sbd sanin ranshi dae ya riga ya ɓaci sbd ita, aika Norah tayi ta kirawo Farrah se ta dawo tace mata tana bacci..

Qur'ani ta sa suka buɗe a iPad na Norah don babu a gidan gabaɗaya suka fara karatu seda ta karawa Aisha kan ta fara koyawa Norah daga Fatiha sbd sallah..

Ba karamin farin ciki Norah ke yi da sabbin abubuwan da take koyo ba, kan kwana bakwai ya zagayo da zata gama al'adar ta hidayat ta koya mata wankan tsarki ta kuma tabbatar da ta iya Fatiha fluently da qulhuwa, falaki da nasi.

Ita kanta hidayat na jin daaɗin yadda Norahn ke koyo sbd abunda ya kamata ta koya yanzu kenan, dukda a gefe guda tana fuskantar wasu halayya irin na turawa Farrah ke dashi sede bata taɓa maida hankali ba, kwanakin da ya biyo baya tun daga ranar da Farrah ta Haɗata da Mahaifinsu bata sake sanya shi a idanu ba.

Sede ya kan aiko Norah ta dauka mishi junior da yanzu suka fara sabo sossai da yaron, haka Aisha tana karatun ta hankali kwance Dukda abunda take ɗan fuskanta na kyara daga wurin Farrah..

Yau Asabar wankin da Hidayat ɗin tayi a washing machine ta sauka kasa don son shanyawa, bata taɓa ma zuwa ta ɓangaren igiyoyin nasu ba se yau, bayan banda shuke shuke da katuwar Mikano ɗinsu se ƴar lilon dake kada kanshi da kanshi cikin kyakyawar field dake shimfiɗe da grass carpet se wasu kujeru haka na shan iska babu abunda yake wurin.

A natse take shanyar har Farrah ta zo ta wuce ta gefenta bata tanka ta ba, chan bayan inverter ɗin ta tafi se gata da wani katoton police dog brown color me baƙin baki banda dilalar da miyau babu Abunda bakinshi yake.

Wani irin faɗi gaban Hidayat yayi gashi su kaɗai, yadda Farrah bata ƙaunartan nan tana da tabbacin in ta gane tana tsoron kare zata sakar mata shi wannan karen kuwa yadda yaken nan se ya cinye ta tsab..

Ganin da gaske nufota suke yasa ta fara ambaton Allah, jikinta na daukar rewa suna isowa wurin kuwa karen ya fara zuwa wurinta yana shunshuna ta, duk yadda take kokari wurin ganin bata firgice ba hakan be yiwu ba, wani ƙara ta saki tana kiran Sunan Allah a take karen yayi kanta bata tsaya ba ta saka gudu wadda ya sa Farrah tuntsirewa da dariya..

A gigice hidayat ke zagaye wurin karen na bin ta, kokarin barin wurin take se ta harɗe ta nufi faɗuwa wadda yayi daidai da isowar Raed wurin sbd tun ihun farko ya ji kuma ya ji haushin kare ya kuma san Bingo ba sanin hidayat yayi ba idan kuwa hakane cizonta ze yi..

Cikin hanzari ya sanya hannayenshi biyu ya riƙe mata kafadu don hanata faɗuwa sede dayake a gigice take bayanta take kokarin Juyawa taga ko karen ya iso ta aiko ganin gashi ga ita yasa ta sake sakin ihu tana runtse idanu hawaye wani na bin wani duk ta ruɗe shima se ta ruɗa shi, da sauri ya janye ta ya maidata bayanshi ta kama Rigan shi ta riƙe kamkam kam..

"Bingo!"

Ya kira sunan karen ganin shima kokarin bin hidayat ɗin yake, sarkar wuyan shi ya kama yace
"is ok, she's not a bad person oya back to your cage"

Juyawa karen yayi ya fara gudu yana karkada bindi, hakan ya saka Raed kokarin juyowa sede Hidayat ta ki sake Rigan shi har lokacin idanunta a runtse hawaye wani na Bin wani, daga yadda suke tsaye yana jin bugun zuciyarta..

Idanunshi ya kai kan yadda ta riƙe mishi riga kamkam hakan ya saka shi sakin murmushi..

"Ya tafi fa!"
Yayi whispering yana sake kallon ɗan karamin farin hannunta dake rike da riganshi, da sauri ta saki tana matsawa baya..

Juyowa yayi ya kalli fuskanta yadda yayi kaca kaca da hawaye ɗan karamin bakinta red se motsi yake alamar Adu'a take, hakan ya sa be san sadda wani murmushin me yanayi da dariya ya sake subuce mishi ba a fili yace

"duk wannan tsoro ne?"

Da sauri ta juya ta nufi ficewa daga wurin don abubuwa dayawa ne suka haɗu mata, ga tsoro dake barazanar sumar da ita ga kusancinsu dake haifar mata da wani yanayi marar misaltuwa ga kunyan yadda yaga take kuka sbd kare ga kuma wani dariyar da yayi da bata taɓa ji ko gani daga gareshi ba sbd shi mutum ne me ƙarancin fara'a..

Shi kuwa Juyawa yayi har lokacin yana murmushi ganin wai kuma kunya taji, faɗa ya fara yiwa Farrah don ya san ita ta fito dashi se ta kama kuka wai yana fififita nanny sama da ita daga karshe rarrashi ya koma sbd yana son yaranshi fiye da misali..

A daren ranar tana kitchen tana tattare abubuwan da tayi anfani dasu na abincin dare ya shigo, ƙasa ta soke kanta tare da cewa
"Barka da shigowa sir, akwai abunda kake bukata ne?"

Girgiza kai yayi ba tare da ya kalleta ba yace
"no cigaba da aikinki"

Fridge yaje ya ɗauki ruwa sbd na parlor ya kare ya kuma kira Paul akan a kawo, har ya kai kofa yace
"ehen when u r done meet me at my room"

Kai ta gyaɗa, har ya fice bayan ta gama ta wanke hannayenta tare da nufan ɗakin shi da take jin hayaniyar junior da su Norah, a kan couch ta same shi yana duba system da ya ajiye akan center table yaran kuwa suna kan carpet suna wasa da Junior yayinda Farrah ke kallon cartoon a TV ɗin ɗakin...

A ƙasa ta zauna ɗan nesa dashi kanta kasa sbd daga shi se shorts jikinshi ba riga kaman yadda ta ga yake kaunar zama haka, banda murdaddun muscles ɗinshi da shafafen cikinshi har kwantacciyar gashin dake jikinshi babu abunda take iya kallo..

Wasu takarda ya Mika hannu ya ɗauka tare da mika mata, a ladabce ta karɓa yace
"it's for ur studies, kin samu gurbin karatu a Paris science et lettres"

Wani irin sanyin daaɗin da bata taɓa ji bane ya rufe ta, cikin tsananin farin ciki ta fara mishi godiya, murmushi kawai yayi ta juya tana nunawa su Norah da Aisha suma murna suka taya ta..

Haka Hidayat ta kwana yiwa wannan bayan Allahn Adu'a, wasa wasa abu kam ya zama gaske se ga hidayat a one of the best universities na duniya, karatunta be hana ta kula dasu Farrah yadda ya dace ba..

Tun kan asuba zata fara Haɗa musu breakfast ta saka musu na makaranta ta zo tayi wanka ta gabatar da sallar asuba ta je tayiwa Farrah wanka ta zo tayiwa Aisha da Junior duk su shirya, a sadda zasu fita tafiya makaranta kuwa a sannan itama zata fita tafiya school, bus take hawa kuma Alhamdulillah ba karamin fahimtar karatunta take ba..

Da yamma take yiwa su Norah karatun Qur'ani da ƴan tarihin annabawa, wadda Farrah bata cika maida hankali ba amma Norah na matukar so, Junior kuwa har ya fara buɗe baki a ƴan watannin nan da suka yi yanzu watanshi takwas da sati biyu, da Daddy ya fara buɗe baki wadda yake gani kaman shine Mahaifinshi..

A ɓangaren career ɗin Raed banda cigaba babu abunda yake gani, don sede idan baya cikin wasa za'a kira musu faɗuwa, ji dashi ake sossai a PSG har wasu clubs ɗin na fafutukar sayanshi...

Kwatsam wani ranar Laraba Raed da kanshi ya fita dasu da yamma sbd rikicin da Junior ke yi yasa yace duka su zo su je su sha iska kadan, Norah ce ta saka Hidayat dole suka fito..

Sanye take da red palazzo trouser se white shiffon shirt me dogon hannun ta yafa red mayafi se ta saka white Shoe, duk cikin irin sayayyar da in har ya fita da yaran tare suke fita se ya ce itama ta ɗauka..

Yaran duka suna zaune cikin wata kyakyawar runfa bayan sun yi ordering ice cream flavor ɗin da kowa yake so, bayan an kawo se Farrah ta ɓarar wa Aisha da nata wadda ya so sakasu faɗa shine Hidayat ta bata hakuri ta mike ta fice don samo mata wani..

Ta fito kenan riƙe da ice cream ɗin shi kuma ze shiga wani karo suka ci ba tare da duk sun ankara da juna ba..

"Subhanallahi..!"
Shine abunda ya fito daga bakinta wadda ya saka shi saurin kallonta don be tsammaci jin sunan Allahn a irin wurin ba..

Karab idanunsu ya faɗa cikin na juna.

#like
#share
#comment


                  🖤Gureenjo🖤

Pokračovat ve čtení

Mohlo by se ti líbit

1.7M 95K 87
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...
417K 25.3K 20
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
2.5K 85 19
Wani numfashi yasaki mai ƙarfi agigice yajawota tafaɗo kanshi cikin karaji yace nashiga uku indo sa hannu kija zai fita idan kikayi haka . Kamo hannu...
82.9K 4.4K 59
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm...