KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.8K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 15

254 19 4
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 15*

*FREE BOOK*

Abunda idanunta ya faɗa kai ne yasa tayi hanzarin ɗaukewa tana runtse idanu, mace a kan jikinshi? Daga gani ma ba musulma ba?
Innalillahi wainna ilahi rajiun.. Wani irin rayuwa suke yi a gidan nan?..

Tayiwa kanta tambayar tana iya kokarinta wurin hana jikinta  ɗaukar rawar da ya fara, zaune yake bisa couch na ɗakin me taushi sanye da pants/boxers wadda be kai gwiwa ba kana iya ganin murɗaɗɗiyar jikinshi gabaɗaya, wadda gargasa yake nan kwance lublublub, a kan faffaɗar kirjinshi wata kyakyawar yarinya ce daga ganinta bata san me wani talauci ba, ta ci gayu ga nails an yi fixing dressing rabi jiki a waje kwata a rufe..

Daga idanunshi yayi ya sauke a kanta se ya ɗan tsaya yana nazartarta ganin yadda tayi wuri wuri, jikinta na rawa idanunta a runtse, magana yake shirin yi Wayanshi ya sake daukar kara..

"Handsome pls pick this phone samu mu huta da ringing.."

Dauka yayi cikin yanga ba wai don Kimorah tayi magana bane yasa yake so ya ɗauka no kawai ya ga ya kamata ya ɗaukan ne ya ɗaga..

"Daadida please.. Don't spoil my mood yanzun nan, I don't really know what's ur problem mutumin nan tun farko fari yace baya so na, yace he hates me nd hates everything abt me and I also fucking hates him..! You lied to me akan baki da lafiya u made me went to Nigeria but at last u saw what happened... I promise idan baki dena min maganan mutumin nan ba zan yanke duk wata alaka da zaki sameni ta waya am damn tired with ur stress..."

Shiru yayi yana sauke numfashin masifar da yake yana jin muryar matar na Kuka cikin kunnuwanshi wadda yake ji har tsikar jikinshi na tashi, yana son ta har ranshi itace mace guda da yake jinta har tsakiyar zuciyarshi kuma ita ce kadai ta rage mishi bayan yaranshi sede abunda take so daga gareshi shine yake kara nesanta su, be taɓa ganin macen da bata zuciya akan abu ba se akan Daadida she spent years tana abu guda bayan babu haske..

Zata yi magana yace
"I have to pray, good night"
Daga haka ya yanke wayan.

Mikewa yayi ya wuce toilet, Kimorah da take ta kallon Hidayat tun fara Wayanshi tace
"ke! Wacece ke?" Cikin harshen turanci don baturiya ce..

"New nanny!"
Tsaki ta ja tana kallon irin kyaun fuska da na sura da Hidayat ɗin ke dashi Dukda a cikin hijab take, wani abu ne ya tsaya mata a wuya, haka kawai hankalinta be kwanta da nannyn ba.

"Go to Paul ki ce mishi ya baki food ɗin ki kawo min am starving"

Fita tayi Paul shine cook ɗin masu aikin gidan kuma shine yake yiwa Oga abinci, ƙasa ta sauka a kitchen na kasan ta same shi tace ga abunda wata dake ɗakin oga ta ce..

Yana murmushi yace
"Kimorah.. Is her name she's the only fiancee of oga, ita kaɗai ta ciri tuta a cikin dubban matan da suke crushing a kanshi from different part of the world"

Kai kawai ta gyaɗa, banda faɗuwa babu abunda gabanta yake.. Zuciyarta ke tirsasata shiga hurumin da ba nata ba sede fa idan ta tuna da tarihin nan na mutanen annabi Musa waenda aka hana su kama kifi ranar Asabar se ranan Lahadi da kuma sauran ranakun se su je su ajiye abun kamun kifin ranar Juma'a se ranar Lahadi da safe se su zo su ɗauka wai su zasu yiwa Allah dabara..

A cikin mutanen sun kasu ne kashi uku, kashi ɗaya sune masu kamawar, kashi na biyu su ne waenda suka gani ana yi sun kuma san ba kyau se suka ce Babu ruwan mu, kashi na karshen kuma sune waenda suka gani suka kuma yi magana..
Da Allah ya tashi se ya hukunta masu yi ɗin da waenda suka gani suka ce babu ruwan mu, a musulunci babu maganan ba ruwanka idan kaga ɗan uwanka na abunda ba shine ba ka faɗa mishi karka yi fushi ka cigaba da faɗa mishi har Allah yasa ya gyara Allah shi kadai ya san sakamakonka a ranar gobe..

Karɓar tray ɗin tayi ta koma sama, a gefe ta ganshi sanye da wata jallabiya me kyau da daukar idanu navy blue kirar Kasar Qatar ba karamin kyau ya mishi ba barin ma da ya saka hulan nan na taɓani kaji hadisi.. Sede abunda ya girgizata har ya so sakata sake tray ɗin shine yadda yake gabatar da sallar cikin rashin natsuwa da kuma watsar da ka'idoji masu yawa na sallar..

Innalillahi wainna ilahi rajiun ta dinga maimaitawa ba karamin abun tashin hankali bane gareta ganin namiji har namiji ga kuɗi har kuɗi ga kyau sede babu addini, yana mutuwa yau wuta fa za shi... Hawaye ne ya fara kwaranya a fuskanta cike da tsoron Allah lallai in ka tsinci kanka a wani jarabawar ka gode Allah sbd naka me sauƙi ne..

Da alama la'asar, magrib da isha ya hada don har ta gaji da tsayuwa ta duƙa a ƙasa, bayan ya idar ya kira sunanta wadda ya sa gabanta wani irin dokawa.

"Miss hidayat!"

"Na'am sir"

Yace
"Na tashi ban san wani farin ciki ba har Seda na samu yaran nan nawa guda biyu na san wani abu wai shi farin ciki, they are all I've got a duniya, ɓata musu kaman ɓata min ne, ina tausayin ki hakan yasa kika kai har yanzu a gidana kiyi kokari kiyi blending da yaran nan within a short period of time in ba haka ba you will loose this job"

Kanta kasa ta sa hannu ta share hawayen da ya zuba mata, kan tace
"in shaa Allah zan yi iya kokarina kayi hakuri pls"

Kuka na daga cikin abunda Sam baya so, ganin yadda hawayen wani ke bin wani yasa ya kau da kai yana lumshe idanunshi masu yanayi da me jin bacci, yace
"tomorrow ki shirya Aisha they will be going together with Farrah na yi mata komai, interview zasu mata su bata uniform and rest"

Bata san sadda murmushi ya subuce mata ba har dimples ɗinta na bayyana ga kuma hawaye a idanunta, sossai taji daaɗi ta dinga mishi godiya..

Sake dauke kai yayi yace.
"U can go"
Ta mike ta fito..

Ɗakin Farrah tayi ta samu tayi bacci, gyara mata kwanciya tayi ta kashe wutan ta fito ta shiga ɗakin Norah..

Zaune ta sameta tana kallo, a hankali ta zauna bakin bedside ɗinta tace
"Norah..! Please ki bani mintuna biyu cikin lokacinki ina so zamu yi magana"

Seda ta ɗan kalleta kan ta ɗauke kai kaman bazata bada hankalin nata ba se kuma ta tsayar da kallon tace
"am all ears"

Hidayat tace
"Norah kin san wanene Allah?"

"Almighty God?"

Ta tambaya, tana wara idanunta..

Kai hidayat ta gyaɗa, Norah tace
"the creature of everything I guess"

Hidayat ta kaɗa kai tace
"Subhanallah..! Norah karki ce haka ba'a jingina mahallici da irin waennan kalmomi za kiyi saɓo.."

Norah cikin mamaki tace
"To waye Allah?"

"Allah shi ne makaɗaici.." Da turanci take mata maganan sbd ba fahimtar hausa take ba..

Tace
"to a ina yake?"
Norah ta sake jefa mata tambayar

"Allah yana sama, kuma shi kaɗai ne ake Nufin sa da buƙata"
Hidayat tayi maganan tana jin daaɗin yadda yarinyar ta fara nuna interest, abun ku da karatun Turai yaransu idan suka sa interest akan abu se sunga karshen shi..

"To wayene ya haife shi?"

Hidayat ta girgiza kai tace
"Astagfirullah..! Be haifa ba kuma ba'a haife shi ba, kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gareshi... Yana da aljanna da yake sa masu aiki na kwarai kuma yana da wuta wadda yake saka masu saɓa mishi.."

Shiru yarinyar tayi cikin tunani,
Tace
"ya wutan yake? Irin wadda ake cooking?"

Hidayat tace
"uhm uhm.. That fire is more than that, Seda aka wanke wutar Jahannama sau dubu saba'in kan aka jefo mana ita duniya muke anfani da ita"

Tsorata yarinyar tayi tace
"and nima Ina saɓawa Allah?"

Hidayat tace
"kwarai kuwa Norah, babban saɓawa ubangiji shine Haɗa shi da waninsa, abunda ke saurin kai mutum wuta kuwa shine rashin yin sallah duk wadda baya sallah baya shiga aljanna..."

Mikewa tayi ta dawo wurin hidayat kawai ta rungumeta ta fara kuka..

"Please I don't want to be burn Miss hidayat"

Shafa kanta hidayat take yi tace
"bazaki shiga wuta ba in shaa Allah, am here and I will guide you ok?"

Kasa kwanciya ɗakinta Norah tayi saboda tsoro haka ta bi hidayat suka kwana a ɗakinta..

Ko da asuba da Hidayat ta tashe ta ta ki tashi se tace mata..

"wutar gayyah shine makomar me jinkirta sallah ko marar yinta"

Da sauri ta miƙe
"menene wutar gayyah miss hidayat?"

Hidayat tace
"yana daya daga cikin kofofin wuta guda bakwai.. Up kar mu makara"

Toilet suka shiga alwalar ma Seda hidayat tayi hawaye wani irin ɓakar ɓacacciyar rayuwa suke yi? Da taimakonta Norah tayi alwala, suka zo sallar ma se bin hidayat kawai tayi..

Tare suka je kitchen da Hidayat Da Aisha, Norah tace
"Miss hidayat I want to learn qur'an that u r reciting"

Hidayat tace
"I will teach u, as from today da yamma babu bacci zamu ringa yin karatu so that wutar Allah ba ze ci ki ba"

Da gudu ta fice taje tana tada Farrah wai kar Allah ya kona ta..

Har hidayat ta gama musu girki kan suka dawo, ga mamakin hidayat Norah tayiwa Farrah wanka, ganin kallon da take musu ne yasa Norah tayi murmushi tace

"Ina so muyi sauri muje mu dawo ki cigaba da faɗamin waye Allah"

Hidayat daaɗi ne ya kamata, abincin ta shirya musu se ga babansu ya fito, a dining suka zauna lokacin shima Paul ya kawo mishi nashi abincin..

"Miss hidayat u said Allah na da Annabawa da manzonni right?"

Kai ta gyaɗa mata tace
"sossai Norah, Allah ya ambaci annabawa guda ashirin da biyar a Alqur'ani, nd lemme tell you there stories are superb..."

Norah tace
"Wow it's getting interesting, can't wait.."

Tayi maganan tana tsalle fuskar ta fall murmushi.

Cikin tsantsan mamaki Raed ke Kallonsu wow, ya jinjinawa Hidayat har Norah ta fara sakewa da ita haka? Sam hankalinshi be kai kan Hirar da suke ba, babban abun dama yaran su sake da ita ne kuma tunda sun fara ai shikenan..

Farrah ce dai har yanzu bata wani sake ba, zasu tafi Hidayat ta dauko baby hijab ta sawa Aisha ta ce mata ko an bata uniform she shouldn't remove the hijab duk wadda ya tambaye ta tace she is a Muslim, kai ta gyaɗa suka fice..

Ita dae hidayat na Kallonsu barin ma Norah da ta fara girma ta kusa balaga sede gashi a sake da mini skirt haka suka fice, a hankali in shaa Allah zata gyara duka waennan..

Cikin farin ciki ba kaman jiya ba ta hau ayyukan da ya kamata bayan ta gama musu abincin rana lokacin suna gab da dawowa ta ɗauko iPad ɗinta ta fara searching wa'azuzzukan turanci irin na su Ahmad deedat, Bin uthman, yasir Khalid, zakir naik da dae sauransu tana ta downloading saboda yaran..

Eib Grenelle international school..

Dab ake da tashi fitowansu daga jolly phonics class kenan suna dawowa normal class ɗinsu, ita da friends ɗinta ne suke tafiya, ɗaya daga cikin tace cikin harshen turanci..

"Farrah wannan new Comer ɗin I saw her talking to u did u knew each other?"

Cikin manyancenta na yaran da suke ido a buɗe Tace
"she's a daughter to our nanny and I hate her"

Ɗaya daga gefe tace
"why?"

Farrah tace
"my dad started to share my space with her, I'm jealous abt that"
Tana magana har ranta fuskanta kaman zata yi kuka..

Wacce ta fara maganan tace
"she's also cute and talented, and her name is sweet Aisha..!"

Farrah tace
"Ina so su bar gidanmu I don't really know what to do gashi Sis Norah started to get close to them"

Na gefe ne tace mata ta kawo kunnenta taji, raɗa tayi mata wadda ya saka su kwashewa da dariya suka tafa, class tayi cikin jin daaɗi...

Kingsworth international school.

Norah ce zaune suna ta manyance akan samari da sauransu da ƴan class ɗinsu, fitsari ne ya matse ta ta kallo friends ɗinta guda biyu tace su zo su je su yi fitsari, mikewa suka yi suka nufi toilets ɗinsu suna cigaba da hiransu, suna zuwa Stephen tace bata ji so se ta tsaya daga bakin kofan da Norah ta shiga cikinshi yayinda faith ta shiga d'aya toilet ɗin...

"Oh no!"
Ta ambata daga ciki..

Stephen tace
"what?"

Ta sake cewa
"oh please oh no..!"

Stephen tace
"Norah..! Open the Door just let me in.."

Kuka Norah ta fashe dashi da karfi tana maimaita
"oh my God. Oh pleaseee"

Da gudu Stephen ta je office na mistress ɗinsu ta kirata se gata da wasu officials na makarantar yin duniya Norah ta ƙi buɗe kofan se kuka take cikin tashin hankali wadda basu san me ya sameta ba..

Se kuma ta fara cewa
"mom..! Mom oh my God"

Hankali a tashe mistrees ɗinsu ta koma office ta ɗauki waya ta fara kiran residence na Norah, Seda ya kusa katsewa Hidayat ta ɗauka itama hankalinta tashi yayi jin yadda suke exaggerating ɗin abun, da sauri ta nemi gyale ta yafa tare da saukowa lokacin kuma Miss Mary ma ta fito don itama ta ɗaga landline ɗin kuma Seda ta kira Raed kan ta fito..

Makarantar suka yi gabaɗayansu, Hidayat ce ta tsaya daga bakin kofan tace
"Norah!"

Cikin kuka tace
"Miss hidayat..oh please help me! Please help me!!"

Hidayat tace
"the door is locked Norah, I can't get in you have to unlock sweetheart, open up and tell me what's wrong with you?"

Kuka kawai take tana shesheka ta ma kasa magana, lallashinta hidayat take cikin dabara, da kyar ta samu ta yarda zata buɗe kofan amma se kowa ya tafi, girgiza kai hidayat tayi tana Tunanin rayuwar Turai ji yadda ta ɗagawa kowa hankali amma maybe ba wani abun arziki bane ya same ta, waje duk suka fita kan kofan ya buɗu....

#Vote
#share
#comment

                   🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

57.3K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...
1.1M 27.6K 45
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
7.2K 254 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin lit...
20.6K 1.5K 40
labari ne akan Najma, wacce hasada, kyashi da yayu nata ya sanya a suka mata auren dole , inda zata fuskanta k'alub'e iri-iri a rayuwa. ku biyoni don...