KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 14

242 23 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 14*

*FREE BOOK*

*Afuwan today I wasn't myself abubuwa sun cunkushe min ayi hakuri da wannan*

No.1.3 Le Marais
4th Arrondissements, Saint Thomas d'Aquin.

Shine sunan home Address da taga sun yi horn daga bakin hadaddiyar gate ɗin, gabaɗaya layin gidajen ba kananun Gidaje bane, Gidaje ne da suka haɗu suka kuma gaji da haɗuwa daga nan inda suke suna kallon Effile tower dab dab dasu kaima ka san me zama kusa da Effile tower ba karamin abun duniya ya tara ba..

Harabar gidan kaɗai abun kallo ne, riƙe da hannun Aisha suka sauko kaman yadda aka buɗewa Moh Raed ya sauko rungume da Junior, ma'aikatan gidan ne a jere cike da tsantsan girmamawa suke mishi welcome..

Hannu kawai ya ɗaga musu ya juya ga wata farar baturiyar mata yace
"Miss Mary this is the new nanny, show her around..!"

Cike da girmamawa tace
"Noted sir..!"

Daga haka ya miƙa mata junior ta zo ta karɓe shi cikin taka tsantsan, Juyawa yayi ya wuce rike da hannayen girls ɗin nashi kowacce na zuba shagwabanta da complain ɗinta..

"You welcome, am miss Mary I am the house keeper, can I please show you around Miss...."

Hidayat tayi murmushi tace
"Hidayat.. Thank you nice meeting you"

Miss Mary ta sake cewa
"Wlcm miss hidayat"

Daga haka suka nufi ciki bayan ɗaya daga cikin mazan da bata san aikinshi ba ya turo musu akwatunansu, babban parlor ne wadda ya haɗu iya haduwa komai na more rayuwa akwai a cikinshi banda sanyin Ac da kamshin freshener babu abunda yake tashi. Daga gefe suka hau wani steps zuwa sama shima again wani parlorn ne different design da wadda suka bari shima a kyau kam karshe ne har kasa tantance wanne yafi kyau hidayat tayi..

Aisha dake rike da Ɗayan hannunta jikinta yayi sanyi wadda hidayat ta san musababbin ganin su Farrah da basu yi welcoming nasu bane, sbd yarinyar haka take idan ka nuna mata baka sonta tana iya yinta wurin ganin ta kaurace maka duk zakwaɗinta kuwa..

Babban ɗaki ne me ɗauke da gado da wardrobe, coffee table da haɗaddun kujerun su, white curtains da beddings ne se sanyin Ac ke tashi har da TV akwai a ɗakin. Miss Mary tace

"this is ur room Miss Hidayat freshen up nd I will show u to d kitchen nd the girls rooms"

"thank you!"

Abunda hidayat tace kenan, bayan Miss Mary ta fita hidayat ta fara yiwa Junior wanka kan tayiwa Aisha, itama tayi suka sauya kaya suka yi sallah nan ma fa se guessing gabbas tayi sbd bata ga dae musulmin da zata tambaya ba kab gidan..

Suna nan zaune Aisha na wasa da kumatun Junior aka yi knocking hidayat ta mike ta je ta buɗe wata mata ce daban ta mata murmushi tare da mika mata tray ɗin dake rike a hannunta na abinci..

French fries ne da chicken se ketchup da ruwa, karɓa tayi tare da godiya.
Bayan sun gama cin abincin miss mary ta dawo tace sir yana son ganinta..

Mikewa tayi tare da gyara gyalen kanta ta ɗauki Junior Aisha ta biyo bayanta suka fito, relaxed suka same shi a parlorn na saman hannunshi news paper ne yana dubawa ya sauya kaya zuwa three quarter da armless shirt, kanta ƙasa ta zauna a kan center rug ɗin tace

"weldone sir.."

Ɗagowa yayi se yaga Aisha zaune a gefenta cikin sakin fuska yace
"hey! Are u avoiding Daddy today? Oya zo nan"

Mikewa tayi ta je wurinshi tana kallon yadda Farrah ke mata wani kallo, yace
"as from today kinga wurin zamanki in ina gida, this is ur sister Farrah..!"

Ya juya ga Farrah yace
"Farrah say Salute(hello)to your sister Aisha"

Cikin low voice tace
"hello"

Kallon hidayat yayi ya nuna babban ƴarshi yace
"Miss hidayat this is Norah and this Farrah, I hope u will give ur best in d job"

"Farrah, Norah this is Miss hidayat ur new nanny as u knew the old one is gonna leave today"

Hidayat tace
"in shaa Allah zan yi iya kokarina"

Norah tace
"what is she speaking?"

Farrah tace
"that Nigerian language I think..!"

Kallon da yake musu ne yasa Norah tace
"hey miss hidayat"

Farrah tace
"hello" tana yatsina fuska.

Ya kalli hidayat da kanta ke kasa tana wasa da ƙasan veil nata yace
"I hope kin nazarci document da na baki?"

Tace
"yes sir!"

Yace
"ok ur work will start tomorrow morning Philip will take u to a nearby street to get phone nd iPad"

Godiya ta mishi, ba tare da ya sake kallonta ba miss Mary ta zo suka wuce, Seda ta nuna mata rooms ɗin yaran da kowanne da kalar haduwarshi ta kuma nuna mata na baban su dake wani corridor incase Dukda basu shiga ciki ba, kitchen ta kaita da store taga komai, har Gym ɗinshi na saman sun shiga kuma ta ce mata akwai wani a parlorn ƙasa, daga nan suka fito waje..

Mutumin da ya haura mata da kayan wadda shine Philip ɗin ya ɗauke ta zuwa shago shike kula da shefenen gidan kuma shi yake kai yaran school, already akwai Atm na Moh Raed dake hannunshi dashi yayi anfani ya saya mata waya Samsung da kuma IPad na Apple a wurin aka yi mata setting komai da Sim na Paris..

Ko da suka dawo bacci tayi sbd a gajiya take Lis, da dare ta shiga kitchen ta fara duba Time table na yaran kowacce da abunda take ci kuma da abunda take tafiya dashi school, waenda bata iya ba ta fiffitar ta koma wurin miss Mary ta nuna mata yadda zata yi Googling recipes, Seda ta koyi anfani da Google da kuma YouTube ta dawo ɗaki ta hau bincike don sossai take son yin aikin, she really needs a bright future for herself nd for the kids..

searching a Google tayi yadda ake duba compass sbd kallon gabas kuma Allah ya taimaka akwai a iPad ɗin ta duba kuma taga da yardar Allah ashe daidai take yi, da asuban fari ta farka Dukda ba masallaci kusa sede sabo da tashi, sauƙa daga gadon tayi tana Adu'a kan ta mike tayo alwala ta zo ta fara nafilfili, Seda ta duba time na lokacin sallah taga lokaci yayi kan ta mike ta tada Aisha ta tura ta toilet

A hankali ta buɗe kofan na ɗakinta ta fito, ɗakin Norah ta fara turawa ta sameta tana bacci rungume da teddy bear ɗinta, gefen gadon ta je ta zauna tare da sa hannu ta ɗan shafa kanta tace cikin sanyin muryarta
"Norah..! Norah wake up it's time for prayer"

Wani wawan tsaki Norah ta ja tare da Juyawa cigaba da tashinta tayi sede fir ta ki tashi daga karshe ma ihu ta mata da swear wadda ya saka Hidayat fita daga ɗakin, ɗakin Farrah ta shiga itama same abunda Norah tayi tayi mata ganin zata makara yasa ta kyale su ta shiga ɗaki tayi sallah, ita da Aisha suka shiga kitchen ta fara Haɗa musu wadda zasu karya..

Na Norah Tea ne da sandwich se na Farrah fried indomie and egg, hannunta ya riga ya faɗa da girki sossai hakan yasa ko yaya tayi girki yana daaɗi, dukda this is her first time she's very sure ze ciyu..

A dining ta je ta ajiye musu daidai lokacin wani alerm me karfi ya fara kaɗa duka gidan wadda dad ɗinsu ne yayi setting in ba haka ba suna bawa nanny's ɗinsu tought time wurin tashi, aiko alerm ɗin be bar ringing ba seda suka fito dukkansu biyu bakin kofofinsu cike da bacci suka Haɗa baki wurin kiran
"Daaaaad"

Tsit alerm ɗin yayi, tsaki Norah ta ja ta juya yayinda Farrah ta tsaya tana kallon Aisha dake gyara dining ɗin, lallai ma does this nanny mean they r eating what this little kid cook?.

Hidayat ce ta fito ganinta tsaye yasa tace
"hey Farrah good morning..!"

Ciki ciki tace
"morning."

Hidayat ta ajiye abun hannunta tace
"let's go nd shower u r getting late to school"

Juyawa tayi ta shige hidayat ta shiga, da taimakonta tayi wanka Dukda da gangan Farrah ta ringa jika hidayat ɗin da ruwa har seda Fararen pjams ɗinta riga da wando masu faɗi suka jike, bata damu ba ta fito ta shirya ta cikin uniform ɗinta, wadda ko hula babu a matsayinta na ƴar musulma...

Hidayat tace cikin harshen turanci

(Kuyi hakuri da turancin kaman yadda novel din ya zo amma zan ta yin hausa instead of turanci ku de saka a zuciyarku yaran da uban su ba wani jin hausa suke ba har gwara uban ma)

"Farrah ya kamata kiyi sallah, kinga ba kyau rashin yin sallah Allah na ƙona duk wadda baya sallah"
Kallon hidayat kawai tayi ba tare da ta fahimta ba ta fice abunta..

A dining suka tarar da Norah sanye da shorts uniform ɗinta itama da yayi mugun karabarta sbd yaran kyawawane kaman babanta yayi khaki ya tofar, daidai lokacin babansu ya fito sanye da jersey alamun suna da wani abun yi da sassafen nan don har takalmi da socks na Club ɗinsu duk sanye a jikinshi kamshi kawai yake zubawa..

Baya Hidayat ta matsa tana kame jikinta dake jiƙe shakab ya wuce ta ba tare da ya kalleta ba, cikin sanyin muryarta tace
"Good morning Sir"

Yace
"Morning Miss hidayat"

Lumshe idanu tayi sbd yadda jikinta yayi wani iri da yadda ya kira sunan, bata taɓa jin wadda ya iya ambaton sunan nata irin shi ba, ta gwammaci ya cigaba da amsa mata da morning kaɗai da ya Haɗa da sunanta.

Zama yayi daidai lokacin Farrah ta kai abincin bakinta da sauri ta dawo dashi tana tari, a ruɗe Raed yayi kanta yana bata ruwa tare da shafa bayanta yana cewa
"sorry dear..!"

Tace
"WTF is this..!"
Lumshe idanu hidayat tayi jin yadda yarinyar karama ke magana wadda be dace ba Sam, yace
"menene?"

Tace
"Daad Indomie ɗin half done I can't eat this"

Kallon Norah da itama ta ajiye tea ɗin yayi itama tana ɓata fuska tace
"too sugary"

Hidayat da jikinta yayi mugun sanyi ya ɗaga idanu ya kalla se ta rikice gabaɗaya ta ruɗe ta fara cewa
"am sorry.. Wlh nayi iyakar kokarina ban taɓa girki half done ba nd ban wani cika sugar ba"

Norah ta jefar da spoon ɗinta har yayi kara tace
"did u mean we r lying?"

Girgiza kai hidayat tayi a rikice ganin har lokacin kallonta Raed yake da idanunshi da suke kara rikitata tace
"No! No am sorry please! Ba zan sake ba"

Ajiyar zuciya ya sauke ya kauda kanshi tare da Kallonsu yace
"girls let's eat outside, will drop u at d school myself "

Norah tace
"amma Daddy kayi warning ɗinta, haka fa da asuba ta zo tana wani tashina tana disturbing peace ɗina I don't like that"

Ya juya yana ɗaga Farrah suka fice, Aisha dake tsaye bakin kitchen ta zo ta kama hannun mamanta, kallon yarinyar tayi se ta sauke ajiyar zuciya tana maida hawayen da ya cika mata idanu..

Da sauri taje kitchen ɗin ta ɗauko lunch box ɗinsu tayi waje, yana kokarin tada mota ta karasa tare da knocking glass ɗin hakan ya sa shi saukewa, cikin sanyin muryarta ba tare da ta kalleshi ba tace
"Sir their lunch box"

Kaman ba ze ce komai ba se yace
"sa a baya"

Buɗe back seat tayi ta saka tana Kallonsu har suka fice, ciki ta dawo ta samu Miss Mary na aikinta na shara da goge goge, sannu ta mata ta haura a nan suka karya da abunda yaran suka bari, wanka suka shiga sukayi tare da sauya kaya ta zauna ta sake fara karanto abubuwa da yaran suke so da wadda basa so..

Ta Tabbatar se tayi da gaske kafin yaran suyi blending da ita har wani shakuwa ya shiga tsakaninsu, yaran suna bukatar uwa tsayayya in ba haka ba rayuwarsu akwai matsala babba..

Ɗakin su ta gyara musu tsab kan ta fara duba abunda zata ɗaura musu na lunch Seda tayi ta kallo tana maimaitawa kan ta zo ta fara cikin taka tsantsan, wuraren ɗaya ta gama ta shirya a dining, tana gyara kitchen ɗin taji shigowar su babu ko sallama, fitowa tayi tace
"girls annabi yace idan zaka shiga wuri dole Kayi sallama ga ahalin wurin kuma amsawa dole ce ga dukkan musulmi da yake wurin, kunga sallama na da kyau kenan hakanan In kayi sallama kana da lada me yawa kunga wadda kuma ya tara lada ne kaɗai ke shiga aljanna"

Duk kallonta suke baki hangame kan Nora tayi tsaki ta wuce, Farrah kuwa dake jin yunwa dining tayi, abincin hidayat ta zuba mata ta diba zata kai baki hidayat tace

"pray first"

Se ta lumshe idanu hidayat bata ji abunda tace ba banda in Jesus name daga karshe, wara idanu tayi tana rike spoon ɗin da sauri a fili tace
"Na shiga uku!"

A tsorace Farrah ke kallonta tace
"Farrah please say bismillah, u r a muslimah so be acting like one wannan ɗabi'ar ba namu bane"

Seda ta kalli hidayat ɗin kaɗan kan tace
"bismillah!"

Ta fara cin abincin, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tana dafe kanta ba karamin aiki ne a gabanta, haka suka yi da Norah ma da ta fito cin abinci amma ita bayan tayi bismillahn se jikinta ya ɗan yi sanyi wadda hidayat bata san na menene ba..

Da dare ma kusan yadda aka yi da safe suka yi don Seda babansu ya fita dasu amma yanzu harda Aisha ya kira suka fita, bayan sun dawo a gajiya suka kwanta bacci landline ɗin ɗakinta ne yayi ƙara da sauri ta ɗauka yace yana son ganinta..

Gabanta na faɗuwa haka ta ɗauki hijab ɗin ta ta saka, hanyar waje tayi tana jin sanyi sanyi na neman rufe ta bata son ɓata mishi rai har yayi mata faɗa gashi daga fara aiki yau har tayi laifi, bata ganshi a parlor ba hakan ya ƙara faɗuwar gabanta..

Kofan dakin shi tayi ta tsaya daga bakin kofa tayi knocking mintuna biyu yace "Come in" cikin hadaddiyar voice ɗinshi me kaurin nan, hannunta har rawa yake ta sa a handle tare da murdawa ta sanya kai kamshin da ya buge ta da sanyi Seda ya sakata lumshe idanu...

#like
#share
#comment

                    🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

616K 64.1K 25
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...
57.7K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...
261K 10.7K 37
Complete story of a young girl Ummy.
2.3K 100 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...