KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 13

256 18 2
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 13

*FREE BOOK*

*Adda Haneefa and herlieymertouh this page is for you😍🥰❤️*

"Ina zaki je with this 2 little kids? Wai ni kam are you in ur right senses? How can you be so reckless abt ur kids well being? Do u really want them death as Usman?"
Maganan ya mugun dakarta, hakan ya sakata tsayawa Chak...

Me yake nufi? Zuciyarta yayi matukar zafi, ashe wani ze iya ganin laifinta akan yaranta? Yana ɗauka sakacinta ya saka kullum take cikin matsala? Bata ga laifin shi ba don ba shine a shoes ɗin hidayat ba, bata ga laifin shi ba saboda be san wacece hidayat ba..

Hawayen da take zubarwa ta sa hannu ta share, ba tare da ta juyo ba tace

"I never wish anything bad to them, na yarda akwai sakacina wurin rasa Usman sede ya zanyi? Ina zanje? Wurin wa zan je? Duk ban sani ba, bani da kowa bani da komai taya zan fara duk ban sani ba...! Don Allah ka gayamin ta ina zan fara???"
Ta karashe tana zubewa kan gwiwowinta tare da fashewa da kuka me tsananin cin rai, idan ta tuna sanadiyar kare mata duka Usman ya tafi se taji kaman ta kashe kanta ta huta sbd dacin zuciya...

"Who are you?"

Ya watso mata tambayar yana kallonta fuskanshi da little bit tausayinta da ya fara kama zuciyarshi daga ganin yadda take kuka she's terrified, and restless.

Kasa magana tayi se kuka, Aisha na duke a gabanta tana goge mata duk hawayen da suka zuba, hakan se ya motsa zuciyarshi...
Ganin kaman bata da niyyar amsa mishi tambayar yasa yace cikin cool voice

"I just wanna help, nd I cannot trust you with the work am gonna give you in har baki gayamin wacece ke ba!"
Yayi maganan yana maida idanunshi kan system ɗinshi, zafi zafi yake operating system ɗin a hankali yaji maganan ta cikin sanyi da karaya ta fara bashi labarinta tun daga farko yadda ta tashi ta ganta har zuwa kawo yanzu..

Tun yana yin typing ɗin sauri sauri har ya dawo a hankali a hankali daga karshe hannayenshi ne kawai zube bisa keyboard ɗin, ya lumshe idanunshi be taɓa jin labari makamancin wannan ba, yana Tunanin nashi labarin shine mafi munin labari ashe ba haka bane..! Ashe nashi azabar kaɗan ne shi namiji ne for that matter gashi yayi building career ɗinshi yayi kuɗi fiye da uban nashi..

Ashe akwai mutane haka? What a world are we living in.. Ya rabb.

Duk wannan Tunanin a zuciyarshi yake saboda kukan da take yi jin tsikar jikinshi yake a matukar tashe, har rawa zuciyar shi yake... Yarinya karama ce sossai wacce sa'anninta suna nan suna building career ɗinsu but nata is already shattered..

"How... How can I help you?"

Fuskanta da ya kumbura ta share, tace
"I want revenge!"

Da sauri ya ɗago ya kalleta jin yadda tayi maganan daga muryarta zata san har cikin zuciyarta abunda take nufi kenan..

"Da kaina nake so in bi ma Usman hakkin shi... Usman died bcs of me! Usman ya tafi saboda kare min duka how can I forget that?"

Kallonta ya cigaba da yi ba tare da ta kalleshi ba ta sake cewa

"Ina so in nemi aikin yi ko wani iri ne wadda za'a dinga biyana da wahalana, I want to study I want to be a barrister ta yadda zan dawo rayuwarsu kaman dirar mikiya!"

Lumshe idanunshi yayi, yana nazari he can trust her with his kids sede su Norah fa? Ya san su sarai they don't want people from Nigeria.. But bari ya bata chance he loves her kids sbd wayaun su da tarbiyar su...

"Can you nanny my kids? As a job?"

Kanta ƙasa sbd idan har ze kalleta ita bazata iya Kallonshi ba, kai ta gyaɗa tace
"in shaa Allah, zaka sameni yadda kake so wurin baiwa yaranka kular da ta dace!"

Kaman ya ce mata they are not regular kids, rayuwarsu irin na Turai ne sbd ko wata babu wacce ta taɓa yi a Nigeria a cikinsu sede yayi shiru, she says she can then let's see...

Waya ya janyo yayi kira...
"Patric I wanna see u now"

Ba'a yi mintuna talatin ba se ga Patric, already hidayat ta koma ciki cook ɗinshi ya aika ya kirata.

Kuɗi ya zubewa Patric yace
"take them to super market, they should buy anything like komai na bukata she will be Norah nd Farrah nanny so please guide her u knew their taste... From there u take her to immigration office for international passport and start processing her visa we r leaving together"

"Yes sir!"
Patrick ya amsa.. Tare da cewa
"shall we go ma'am?"

Kai ta gyaɗa suka fice ta so ta ce mishi ko ta gode ne sede fuskanshi tsoro yake bata, rashin sakewar fuskan tayi yawa gashi da I don't care attitude don har suka fita ko Patrick ɗin be sake ɗaga kai ya kalleshi ba..

Da ɗaya daga cikin Zafafan motocin shi suka fita, ita dae a muzance take jinta Dukda hijab ɗinta ba abunda ya same shi sede fa ta san rayuwar nan da ta shigo ya fi karfinta, nanny..! Allah andi yaran har nawa ne.. Rayuwar ƙasar waje kuma ya ze kasance mata?

Sayayya na fitan hankali Patrick ya sa matar tayi mata, suna da spa a wurin ya sa suka mata facial and body scrub, dayake ta cewa matar duk dressing da za'a hada mata ba ta son me bayyana tsiraici se matar tayi mata haɗi masu kyau, har da su suits sede ba me kama jiki ba sannan da baby hijabs ko veils, har veils ɗin seda ta koya mata different design na yafa su sbd Patric ya gayamata yaran zasu iya mata mugun raini idan ta je a yadda ta je and they can deny her as nanny baban su kuwa be taɓa turning against their decision ba..

Kayan da taje da su Patrick yasa aka watsar, har junior sayayya shi daban, ita akwati medium da kit ɗinshi ash na zamani, na Aisha medium na yara pink me hoton frozen, se Junior wani jaka ne me kyau har da carriage na yara wadda ake daure su a gaban nan ya sa aka saka musu sbd ya san turawa basa goyo kaman yadda mu muke yi, man shafa, turaruka duk na matsakaitan kuɗi ya sa aka sa mata..

Fitowa suka yi hidayat sanye da peach English gown da yayi mata kyau sossai me dogon hannu, gyalen tayi mishi yafin ƴan kasan Oman sanye da Junior cikin carriage ta gabanta, hannunta rike da Aisha da bata chanza daga kayan Farah da Raed ya saka mata ba..
In ka kallesu zaka ɗauka asalin su masu kuɗin ne kyaunta yayi mugun bayyana Dukda ramar da tayi da kuma fatan ta da yayi duhu kaɗan..

Immigration office suka je aka yi mata passport abun ka da kuɗi awanni biyar aka basu zasu karɓa, Patrick ya maida su gida da sayayyarsu yayiwa Raed bayani a waya don ya riga ya bar parlorn..

Hidayat na ɗaki sede har washegari ko kofa bata leƙa ba, abunda yayi keeping ɗinta busy kuwa shine System da Raed ya aiko cook dashi da takarda da biro abubuwan da yaranshi suke so ne da waenda basa so, yadda suke yin breakfast, lunch, dinner.. School ɗinsu da komai dama duk.nanny ɗinsu da zata bar aiki zata yi documenting komai ta tura mishi yadda next nanny zata ɗaura daga nan, tun yamma take abu ɗaya har washegari nan ta fara sarewa, daga gani yaran nan ba kananun ƴan gata bane irin su kuma ta tabbatar they would be rude.. Sede zata yi hakuri da komai saboda cikar burinta..

Abunda bazata riƙe ba se ta rubuta a cikin hardcover da ya haɗo ta dashi, shi ya san yaranshi in bata musu ba se su hautsina mishi lissafi, and yana tausayinta apart from the nanny be san me zata musu na kuɗi da ze iya biyanta ba..

A cikin 3days komai nata ya kamalla, kuma har kwana ukun nan bata sake sanya shi a ido ba, Aisha dae tana mata wanka zata fice se dare cook ke dawo da ita wani lokacin kuma ta dawo da kanta kan magrib, farkon abunda ya fara ɗaga mata hankali shine idan Aisha ta dawo ta tambaye ta.

"Kin yi sallah?"

Se yarinyar tace
"A'a"

Hidayat tace
"me yasa kina ji ana kiran sallah bazaki tashi kiyi ba? Ko bakya ganin daddyn nayi ne da zaki zauna bazaki yi sallah ba Aisha fa."

Se yarinyar tace
"Mama ai shima be tashi yayi ba..!"

Hidayat bata kara magana sbd tsoro da fargaba da take shiga, Aisha bazata yi karya ba amma me yake hana shi yin sallah? Ko de ba musulmi bane? Toh ya akayi sunanshi Muhammad kuma..!

Kwakwalwanta a sarƙe yake har ranar da zasu tafi, Adu'a kawai take Allah ya sa wannan rayuwar ya zame mata mafi alkhairi kar ya zama wani baabin mummunar kaddarar kuma daga cikin shafuskanta na rayuwa..

Sanye take da shirt nylon tare da palazzo trouser me faɗi se ta saka kimono marar nauyi wadda be gama kaiwa ƙasa ba aka yi wani style daga kasan ba karamin kyau tayi ba dake mayukan da take anfani dasu masu kyau din ne ga cima me kyau da take samu, ta shirya Junior cikin kananun kaya farare da ya amshe shi sossai yaron ba de kyau ba..

Aisha a wurinshi ta shirya cikin kananun riga da wando kanta ba ɗan kwali tana shigowa hidayat ta kama ta ta saka mata after dress saman kayan tare da sa mata baby hijab se tayi wani kyau abunta..

Fitowa suka yi suka tsaya daga bakin kofa, ba'a yi minti biyar  da tsayuwar su ba fitinannen kamshinshi ya fara musu sallama kan tsayayyen figure ɗinshi ya bayyana tafiya yake cike da ginshira da wani kalar ƙasaita hannayenshi sanye cikin aljihu..

Sanye yake da crazy Jean blue me kyaun gaske ya ɗan kama shi se wani silk shirt me zanen art emerald green me guntun hannu, kafafunshi sanye cikin emerald green combus daga gani ka san ba na karamin kuɗi bane, kanshi sanye da same color face cap ya saka baƙin sunglasses da facemask sbd ɓadda kama, ɗan kunnenshi se walkiya yake hakanan zoben azurfa dake hannunshi..

Agogonshi na Fendi dake ɗaure a hannunshi na hagu ya kalla it's almost time ba tare da ya kalli ko ɓangaren dining da cook ɗin shi ya shirya mishi abinci ba ya riƙe hannun Aisha da taje wurinshi da gudu suka nufi waje yana kallon dressing ɗin ta da ya mishi kyau, ko inanta a rufe se ɗan karamin baby face ɗinta, dab da ze fita hidayat da ta biyo bayansu tace

"Good morning sir"
Yace
"morning"
Suna karasa fita, Patrick ne ya buɗe bayan zazzafar Porsche ɗinshi suka shiga, yayinda hidayat ta shiga gaba ya ja suka fice daga gidan dama tun ɗazu ya saka kayayyakin su a booth sanin ogan shi ba tafiya da kaya yake ba..

Saboda shigan dake jikinshi babu wadda ya gane shi a Airport ɗin ma har suka shiga VVIP, ita dae hidayat banda bat bat bat babu abunda zuciyarta ke yi, bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba se gata yau ita ce zata shige shi, daga ganin inda suka shigo ma ta san cewa ba wurin regular mutane bane zama yayi kaman a parlornshi briefcase da Patrick ya rako shi dashi har seat ɗinshi ya janyo ya ciro system ɗinshi ya hau operating yayinda Aisha ke zaune kujeran dake facing nashi tana mishi tambayoyi yana amsawa a takaice  anan hidayat ke gane wasu abubuwan..

Har za'a tashi ya ɗan kalleta bata ɗaura seat belt ba and a labarin da ta bashi he's quit sure bata taɓa hawa jirgi ba abunda ya fara kwantar mishi da hankali a tafiya da ita shine bata da hayaniya, button na gefen shi ya danna se ga one of the cabin crew ta shigo..

"How can I help you sir!"
Tayi tambayar cikin tsananin girmamawa da taka tsantsan, kallon hidayat yayi yace
"give her the safety guide"

Da sauri tace
"ok sir"

Wucewa tayi wani cabinet ta ɗauko ta zo ta baiwa hidayat cikin girmamawa, karantawa hidayat ta fara se taji ma ana maimaitawa ta loudspeaker ɗin jirgin, da sauri tayi yadda aka ce da belt ɗin tare da gyara junior ta rufe idanunta har jirgin ya ɗaga sararin samaniya, shi da kanshi ya riƙe Aisha har aka daidaita ya tashi ya maidata Ɗayan kujeran ya gyara mata don already sun kashe wutan jirgin nasu..

A Lagos suka tsaya for about an hours Dukda basu sauka ba su bata dae san sauran mutanen jirgin ba kan suka sake ɗagawa sun tafi sun tafi har taji ta gaji, ga ciwon kai ga jiri da take ji, shi kam ko don ya saba ne aikinshi kawai yake abun shi, ita kuma Aisha tayi bacci, chan cabin crew ta zo ta tambayeshi me yake so ya faɗa, se ta matso ta tambayi hidayat rasa me zata ce tayi se tace ta kawo mata anything Nijerian dish..

Abincinshi ne ya fara zuwa har ya gama tsakura ya fara kurɓan coffee, junior da ya gaji ze fara rikici ne ta ɗaga tana ɗan mishi rawa da waka se yaron ya bangala dasori yana dariya, a hankali ya sauke idanunshi kan yaron, dariyarshi gwanin kyau, farar ɗaya yaji ƙaunar yaron fiye da yadda yake ƙaunar Aisha, yana so yace ta kawo shi sede bakinshi yayi nauyi, yadda take mishi wasan ya kalla hakwaranta dake jere farare tas a waje hakan ya ba dimples ɗinta duka biyu Daman loɓawa..

Ɗauke kai yayi ya cigaba da kallon Junior cike da sha'awa daidai lokacin aka kawo mata abinci, ajiye mata aka yi sede junior baze barta ta ci ba don ya iya janye janye gashi se son sauka yake yana ta tsalle yaron is full of energetic..

"Can't u give the child to his father so that u can eat peacefully?"
Cabin crew ɗin tayi maganan, rikicewa hidayat ta so yi ta fara kame kame.

Tsam Raed ya miƙe ya zo ya saka hannu ya karɓe shi yana chilla shi sama yaro kam ba se ya bangala dariya ba shima murmushi yayi yace mata

"his name?"

Tace
"junior"
Baki ya taɓe ya nufi kujerar shi dashi wasa yake ta mishi, har ta gama cin abinci aka kwashe abubuwan ta kishingiɗa a take bacci ya sureta, yaron ya gyara a kirjinshi suka kwanta a haka idanunshi a lumshe..

Tafiyar 6 hours ten minutes ya kawo su Paris sun gaji tilis, barin ma hidayat da Aisha da basu saba tafiye tafiye ba, a hankali suke saukowa idanun hidayat na buɗuwa da tsananin kyaun Airport ɗin na Charles de Gaulle(CDG) Aéroport de Paris..

Wasu rantsatsun baƙaƙen GLS 460 4matic baƙaƙen sidik ne suka yi parking gabansu guda biyu bayan sun fito daga terminal ɗin masu ɗaukan trolleys ture da chart ɗin dake ɗauke da kayan su Hidayat, kofofi biyu daga ciki suka buɗu wata kyakyawar matashiya da zata yi 14yrs ce ta fara fitowa sanye da leggings da shirt pink kafafunta combus ne pink se gashinta da ya sha gyara kan karama wacce bazata wuce Aisha ba ta fito itama irin dressing ɗin yayarta ne jikinta rige rige suke yi sede turus suka dakata ganin Daddyn nasu riƙe da wani yaro da basu sani ba..

A tare suka ce
"Daaaaad!" Da wani expression a fuskansu..

Hannunshi ɗaya ya wara musu Farah taje ta shige yayinda Norah ta ja gefe tana kallon Hidayat da kuma Aisha ta sake kallon junior da baban su ke rike da shi tace
"daad Qui est-ce?(Who are they?"

Ba tare da ya kalleta ba yace
"ur new nanny nd her family"

A tare suka ce
"Whattt?"

Ɗan ɓata fuska yayi yace
"manners girls and parlez lentement, s'il vous plaít"(speak slowly please)

Ya faɗa yana shiga motar da aka buɗe mai, duk a tare suka kalli Aisha da Hidayat da suke ji sun muzanta don kirkiri yaran suka nuna basu musu ba, hidayat bata san sadda ta wara idanu ba jin sun ce
"Disgusting...!" A tare suka yarfa hannu suka shige motan da baban su ya shiga...

#like
#comment
#share

                    🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

2.3K 100 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...
12.3K 568 13
Love, romance, destiny, paid
2.5K 85 19
Wani numfashi yasaki mai ƙarfi agigice yajawota tafaɗo kanshi cikin karaji yace nashiga uku indo sa hannu kija zai fita idan kikayi haka . Kamo hannu...
617K 64.3K 25
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...