KOWA YA GA ZABUWA...

Oleh Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... Lebih Banyak

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 12

253 21 0
Oleh Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 12*

*FREE BOOK*

*Afuwan Na ji na shiru da kuka yi jiya🙏*

Cikin tsananin tsoro da fargaban abunda ze iya faruwa da su ta fara ambaton Allah..
"Allah gani gareka ya Allah, da kai na dogara Allah kuma a gareka kaɗai nake bukatar taimako, ya Allah ka karemu da zuri'a ta ya Allah....."

Kaman daga sama suka hango mota na zuwa da mugun speed, gabanshi ta shiga ba tare ma da ta sani ba, wani wawan birki aka taka a daidai lokacin mutanen suka iso su.

Zaune yake yana ƙarewa situation ɗin kallo cikin son fahimtan abunda ke faruwa, abu irin haka baya gaggawa sbd yanayin shi na famous mutum celebrity, ana iya tricking ɗinshi cikin sauƙi Dukda babu mahalukin da ya san ma yana Nigeria banda yaranshi se wanchan tsohuwar da ta sashi zuwa, tuna haka kaɗai ƙona mai rai yake.

"Dan Allah karku cutar damu babu abunda muka muku!"

Hidayat ta faɗi tana Haɗa hannunta wuri guda cikin roko.

"Muma don Allah kiyi hakuri babu yadda kika iya hanyar samun mu kenan!"
Ɗayan ya faɗa.

Kara kankame Aisha hidayat tayi a hannunta tana girgiza kai tana cewa..
"Ba zan taɓa Bari ku taɓamin yarinya ba, ba zan bari ba sede in kasheni Zaku yi ku ɗauke ta.."

"Hakan ma se ayi ai! Abunda muka sani yau se mun ɗauki yarinyar nan!"

Buɗe kofar motan akayi wadda duk ya saka su maida hankali kai, Seda ya shafe seconds kan ya sako kafafunshi ƙasa ya sauko cikin wani salo na burgewa.

Sanye yake da track suit riga da wando na Fendi me tsananin taushi da tsada, dark Ash ya saka hulan a kanshi yadda ya rufe giranshi da rabin idanunshi hancinshi sanye da facemask as usual cikin dakakkiyar muryarnan tashi yace

"Says who?"

Duk Kallonshi suke kan na farko yace
"kaman ya says who? Mu muka ce haka kuma dole mu ɗauke ta malam ka kama gabanka ba ruwanka... Baba kamo ta mu wuce.."

Hannu wadda aka kira da baban ya miƙa da nufin kamota se Charab yaji an riƙe hannun, wani wawan juyi yayi ya murɗe hannun tare da sauke mishi naushi da kafa ɗaya a fuska, ihu ya kwala yana zubewa sauran suka yo kanshi laga laga yayi musu su huɗu kan suka mike suka gudu.

Duk wannan dukan da ya musu ko hulan kanshi be faɗi ba bare Hidayat da ta kara rukunkume Aisha ta ga fuskanshi, hakanan yana dukan ne kaman irin wadda baya so hannunshi yayi datti ɗinnan.

Hannaye yasa a aljihu ya tsaya yana Kallonsu, so yake yayi magana sede ranshi a ɓace yake da abubuwa dayawa, tsaki me karfi ya ja ganin Hidayat ta fara jan Aisha zasu tafi a tsakar daren nan.

"Shiga mota!"
Ya faɗi maganan cikin dakakkiyar muryar salon bada umarni.

Chakk hidayat ta tsaya gabanta na dukan tara tara muryarshi kaɗai ya haifar mata da wani kalar faɗuwar gaba bare umarnin da ya Bayar, shi kuma da wanne ya zo?

Watsar dashi tayi ta sake jan Aisha tana jijjiga Junior da yake ta kuka.
"I said enter the damn fucking carrr!!"

Kawai se ta fashe da kuka me karfi saboda tsoratar da tayi hakan yasa Aisha ma fara sabon kuka.

Wani tsakin ya kuma ja kaman ya wuce yayi tafiyar shi sede tunda ya gane Aisha daga cikin mota yaji ba ze iya tafiya ya kyale su ba hakan ne ma ya saka shi fitowa taimakonsu but look at what her mother is doing...! Be san wasu irin mutane ne a Nijeriya ba har yanzu mamakin waennan da suka zo satar Aisha kiri kiri yake, haka ƙasar mu ta lalace?

Kallon Area ɗin yayi Gidaje ne manya manya na masu hannu da shunin garin Kano, ko wani gida ka kalla zaka san ba ƙaramin kudade aka kashe wurin ƙerawa ba, sede rabi da kwata Gidajen empty ne duk ana Abuja ko Lagos ko ma kasashen waje, wurin yayi shiru dayawa da za'a iya kashe mutum a binne ba tare da kowa ya sani ba ko da kuwa da rana ne bare dare.

Hulan ya sauƙe, gyararren ponk ɗinshi rinanne ya bayyana, hannu ya sa ya shafa kan tare da zare facemask ɗin yana zuƙar iska tar kyakyawar fuskanshi ta bayyana, diamond ear ring ɗinshi na shining..

Aisha dake Kallonshi kaman yadda hidayat ke Kallonshi ta fusge ta ruga da gudu taje ta faɗa jikinshi tana cewa
"Daddy!"
wara hannu yayi ya chaɓe ta se ta fashe da kuka.

"Shhh! Shhh Shhh it's OK you are safe honey.."
Se a lokacin hidayat dake Kallonsu ta dukar da kai tana ɗigar da hawaye..

Shine Daddy? Shine wannan mutumin da ya taimaka mata a sharafan mutuwa, shine wannan wadda ta sanadiyar shi take numfashi har kawo yanzu, shine ya taimaki Usman a sadda ya ɓata garin nema mata taimako, shine wadda ya taimaka mata zuwa kai Usman Asibiti ya biya bill ya kuma biya Ambulance da ya maida su har gida, shine ya ciyar da mutane daga aljihunshi har mutane suka ci suka sha zuwa ƙarewar makokin Usman, sannan shine ya taimaka musu a yanzu da ake kokarin cutar dasu... Lallai Tarihin hidayat baze cika ba idan ba'a kira sunan wannan bawan Allahn ba, shi ɗin kaman mala'ika ne a wurinta da Allah ke turo mata a duk sadda take buƙatar taimako ita yanzu baiwa take a gareshi saboda ya mata abunda babu wadda ya mata a duniya...

Hannun Aisha ya saki yana shirin wucewa tunda mahaifiyarta bata bukatarshi da sauri Aisha ta sake rike hannunshi tana kuka tace
"Daddy karka tafi ka barmu, bamu da inda zamu je, Abba wai ya saki mama mun je gida umma ta koremu ni tsoro nake ji.. Karka tafi Daddy..!"

Ɗago ido yayi ya kalli hidayat dake Kallonsu se tayi saurin duƙar da kai ba tare da ta bari sun Haɗa idanu ba, hannun Aisha ya riƙe ya zagaye ta ya je ya buɗe gaban motanshi ya ɗaga Aisha ya ajiyeta ya rufe kofan tare da xagayewa yaje ya shiga mazaunin driver, gwiwa a sage hidayat ta buɗe baya ta shiga sanyi da fitinannen kamshin motar na dukanta, kunce junior da har ya gaji da kukan yayi shiru tayi tare da saka shi a kirjinta, jakukunan kayansu duk sun zubar garin gudu gashi bazata iya ce mishi su je su duba ba ta ya ma zata fara?..

Se a lokacin ta lura da unguwan da suka kawo kansu, wasu irin mahaukatan Gidaje da bata taɓa gani ba take gani har suka isa wani golden Gate me kyau sossai daga motar ta ga ya ɗauki wani abu ya danna se gate ɗin ta zuge da kanta..

Kutsa kan motar yayi ya Parker a tsakankanin wasu mahaukatan range Rovers, fitowa yayi ya zagayo ya buɗewa Aisha tare da riƙe hannunta suka dan yi gaba, se hidayat ma ta sauko cikin mamakin irin kalar shi shi kuma kaman kurma?

Cikin takunshi na xaratan maza yake tafiya hakan yasa hidayat kara sauri har suka isa kofan shiga gidan, kofan karan kanshi abun kallo ne, daga kasa taga ya danna kofar ta kawo wuta ya saka wasu numbers waenda suka bayyana a flat screen na lock ɗin se kofar tayi magana tare da buɗuwa, karasa turawa yayi ya shige hidayat ta bisu a baya.

Wani kalar haduwar da parlorn ke dashi ya sakata dakatawa gabanta na dukan tara tara, da wa Allah ya Haɗata? Anan parlorn ya saki Aisha yace
"seat"
Yana nuna mata kujera da idanu, kafaɗa ta make tana sake rike hannunshi gani take kaman ze gudu ya bar su, hidayat ta matso tace
"Aisha me haka?"

Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata ya sake rike hannun Aishan suka yi wani kofa...
Mintuna biyar suka fito suka haye sama da kallo ta bisu har suka ɓace ta sake dawo da idanunta ta golden color staircase ɗin har ƙasa tana cewa Abba na da kuɗi ashe shi kam ba kuɗi yake dashi ba..

Maganan da aka yi ne ya dawo da ita hankalinta Dukda dai hankalinta rabi na kan Aisha da ya haura da, bata san waye shi ba Dukda tayi trusting ɗinshi sede fa a tsorace take dashi Allah ya gani.

"Madam Oga said I should show u a room"
Juyawa tayi ta kalli me maganan namiji ne, binshi a baya tayi zuwa wani ɗaki a nan ƙasa ɗakin babu abunda babu har TV kuma tsare yake a tsabtace.

A ƙasa kan center rug ta zauna se ga mutumin ya sake dawowa da kayan cook ya ajiye mata tray da varieties of Food wadda ba Nigerian dishes ba yace mata
"this is only what we have if u can't eat then I should cook u something different ma"

Kallon tray ɗin tayi abinci har kala biyar Dukda ba yawa yawa sede yace bazata iya ci ba? Wacece ita? Uhmm girgiza kai tayi tace
"is ok I will have this"

"thank you ma."
Yace kan ya juya ya fice.

Cin abincin tayi sossai saboda yunwa da dama take ji kaman mene, tana gamawa ta sake zama ta shayar da Junior cikin tausayin rayuwarsu.

Tana nan zaune har wuraren ɗaya taji knock a hankali, miƙewa tayi taje ta buɗe se idanunsu suka sarƙe wuri guda, sassanyar kamshinshi ya daketa, sanye yake da silk riga da wando na bacci cream color sede ba karamin kyau yayi ba, bata san me zata ce ba se ta nemi duburcewa Aisha dake ɗauke a kafaɗanshi ya nuna mata da hannu yace a ƙasaitance
"can I put her on bed?"

Miƙa hannu tayi zata karɓe ta ya mata kallon uku saura kwata ya wuce ta ya nufi gadon ya shimfiɗe ta, ya zo ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba.. Se da ya fita ya ja kofan kan ta sauke numfashin da take rike dashi mene? Gani yake bazata iya ɗaukan Aisha ba ko me? Amma lallai mutumin nan ya raina ta.. Taɓe baki tayi ta shige zuwa gadon tana kallon kayan bacci masu taushi da Aishan ke sanye dasu ba karamin kyau ya mata ba, shi kuwa Allah andi inda ya samo shi.

Bayi ta shiga shima tana mamakin kyaun shi, duk abubuwan anfanin ciki bata taɓa gani ba tunda ita ba kallo take ba, kuma gidansu akwai na zamanin sede fa ba irin wannan ba, da ɗan dube dube da taɓe taɓe ta samu ta yi tsarki tare da alwala bata san gabas ba amma ta so tayi shafa'i da wutiri kafin ta kwanta haka dae ta kwantar da Junior akan gadon ta kashe Acn da wutan kan ta kwanta, tunani ta faɗa na yadda zasu yi rayuwa, tana so ta rayu ko don daukar fansar Usman tana so ta zama wani abu ko don su umma, sede ta ina zata fara shine bata sani ba. A wannan dare bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauke ta ba wai don tayi niyyar yi ɗin ba.

Da asuba ma se hasashenta tayi tayi sallah, tana nan zaune tana azkar har gari yayi haske, Aisha ta tayar ta kaita bayi tayo fitsari da alwala, kayan ta na jiya bata dawo dasu ba babu ko hijab haka hidayat ta cire nata ta bata ta saka tayi nata sallar.

"Aisha wani hali kuma Kika ɗauko wadda ban koyar dake ba? Kin san shi a ina da zaki maƙale mishi? Sannan wannan bakin ban hana shi zuba zance anyhow ba?"
Da faɗa take maganan hakan yasa Aisha fara hawaye.

Tsaki hidayat tayi kan tace
"magana fa nake miki!"

Baya ta ja tace
"Mama Daddy ne fa..!"

"Daddyn gidanku? Kin....."

Shiru tayi sbd knock da aka yi, mikewa tayi ta sanya hijab ɗinta ta je ta buɗe cook na jiya ne da abinci a tray, ajiyewa yayi da muryarshi na yarbawa yace
"Good morning ma, Ma Oga said I should call Aisha for him"

Tun kan ya rufe baki Aisha tayi waje da gudu, gyaɗa kai hidayat tayi tace zaki dawo ki sameni, amsa mishi gaisuwar tayi ya juya ya fita..

Oat ne se bread da kuma omelet, madaran oat ɗin a wani karamin jug me garai garai se suger cubes suma a bowl daban, ga fork da spoon da kuma tissue..

Bismillah tayi ta karya, sossai ta koshi kuma taji daaɗin karin junior ta ɗauko ta bashi Nono, tana nan zaune cikin saƙa da warwara ta ji maganan Aisha daga parlor Dukda bata ji nashi ba amma yadda Aishan ke magana ta san dashi take maganan.

Mikewa tayi ta maida waist bag ɗinta ta ɗaura a kwankwaso ta saka Junior a baya, tare da sanya hijab ɗinta suka fito..

Zaune yake yayi relaxing bisa kujera sanye da kananun kaya three quarter da armless black cotton shirt hankalinshi na kan system da yake operating yayinda Aisha dake rike da pop corn tana zaune daga gefenshi tana surutu sede ya gyaɗa kai ko yayi murmushi, daidai fitowanta Wayanshi ya dauki ringing.

Ɗagawa yayi ya kara a kunne yace
"what again?"

Bata ji me aka ce ba ya wani ɓata fuska yace
"wait.. Daadida you kept me at this country for long... Ba zan iya zuwa wani wuri ba kuma yanzu after all I didn't fucking care abt his health or well being..."

Daga inda ta ɗan duƙa tana jin tsawar da aka mishi wadda ya saka shi lumshe idanu se kawai ya zare wayan ya kashe gabaɗaya.. A kausashe yace
"I see no reason da zan bi abunda kike so woman... He hates me nd I fucking hate him more"

Yana maganan yana danna wayan da sauri ya kara a kunne..

"Buy me a ticket of any available flight to Paris now!"
Ba tare da ya jira amsa ba ya kashe tare da wurga wayan kan kujera yana ji ana ta kira sede be sake kallon ko ta ɓangaren ba.

Ita dae hidayat a tsorace take da mutumin nan wani irin mafadaci ne wannan Allah na? Ta ayyana a ranta tsoron mishi magana ma take, in ka kula da kyau zaka ga yadda jikinta ke rawa..

Da kyar ta iya cewa
"Ina kwana!"

Be amsa ba se ta dauka baya jin hausa jin yadda yake turanci, sannan ko yayi hausar ma ba fita take da kyau ba ta sake cewa
"good morning!"

Se a lokacin ya ɗago se idanunsu suka faɗa cikin na juna, janye nata tayi tana jin kaifin idanun nashi a jikinta kwarjininshi duk ya cika parlorn.. murya chan ƙasa yace

"morning!"

Tace
"Dama.. Ina so ne in maka godiya bisa taimakon da kayi mana, ubangiji ya raya zuri'a, Allah ya saka da alkhairi ya sa a mizani."

Lumshe idanunshi yayi yana tuna Usman, lokaci daya yana mamakin yadda ta iya turanci don da turanci tayi maganan, akwai abubuwan da suka ɗaure mishi kai a kansu sede bashi da lokacin saurara ko bincike tunda be shafe shi ba.

Kai ya gyaɗa mata kawai, wasa da fingers ɗinta ta cigaba da yi feeling uncomfortable kan tace
"mu zamu tafi.. Allah ya biya da gidan Aljanna"

Aisha da bata san ya aka mata wanka ba sanye da hoodie na kamfanin Nike purple color tayi rau rau da idanunta..

Harara Hidayat ta zabga mata wadda ya sakata mikewa ta nufi Hidayat ɗin hannunta ta kama tace
"se anjima"
Suka nufi kofa abun su...

#share
#like
#comment

🖤Gureenjo🖤

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

67.4K 7.4K 58
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta b...
436K 24.1K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
1.1M 28.4K 45
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
2.3K 100 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...