KOWA YA GA ZABUWA...

By Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... More

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 7

230 21 0
By Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 7*

*FREE BOOK*

Abba yayi nadamar hukuncin shi gareta yafi abunda ya fi a kullum se ya zub da hawaye in ya ganta, rashin kula da rashin suturu duk sun haɗu sun maidata tsohuwar da bata kai ba, yayi nadamar rashin sauraren ta kuma a kullum in har zata je gareshi ta kan karanci irin rokon gafararta da yake da idanu, shine kaɗai take kalla tayi farin ciki ta kuma buga kirji tana da wani a duniya shima yanzu ya tafi, bango mafi girma a rayuwarta ya zube tas bata da karfin fara wani tubalin bare ta sake gina makamancinshi a rayuwarta...

DAWOWA LABARI

Cikin wani irin yanayi take kukan, kuka ne wadda duk wadda ze kalleta ze san akwai abu mafi girma da ya sameta na rayuwa ganin yadda ko la'akari da jama'ar dake kai kawo bata yi, wata mata ce ta matso ta tare da dafata tace

"baiwar Allah kiyi hakuri! Duk tsanani yana tare da sauki ki duba condition naki it's not good for you da irin wannan kukan da kike"

Kallon matar take da idanun rayuwa daaɗi yake miki ni tawa rayuwar bata da sauran anfani banda na yarana, ba tare da tacewa matar kala ba ta mike ta nufi gate tana tafiya kaman iska ze ɗauke ta, da Kallo matar ta bita cikin tausayawa duk yadda akayi matarchan tana cikin depression me girma.

Har ta isa gida bata dena zub da hawaye masu zafi ba, a kofar gida ta ga Usman da Aisha zaune da gudu suka zo suka mata oyoyo, tana share hawaye wani na bin wani ta rungumesu itama, cikin sanyin murya tace
"Usman me yasa baku shiga ko wurin Asabe bane kuka zauna a kofar gida tun yamma?"

Aisha tace
"ba mun je ba su Lantana suka koremu wai tunda bamu da gado mu bar musu gida"

Bata sake cewa komai ba, hannunta na rawa ta fiddo key sede ta kasa buɗewa se Usman ne ya karɓa ya buɗe suka shiga, akwai wutar nepa alwala tayo suma duk suka yi cikin karfin hali a zaune haka ta miƙa sallar magrib da isha da ake ta kira.

Bayan sun idar tana jin yaran na azkar sede ita bakinta be iya yayi ba se a zuciya take binsu, bayan sun gama Usman yace
"Mama baki da lafiya ne?"

Aisha ma tace
"Mama kina ta kuka Ko Abba ya biki ya bugeki ne a unguwar da kika je?"

Rungume Aisha tayi ta saki sabon kuka, duk yaran ma se suka soma kuka, da kyar ta dakatar da kanta tace

"Usman, Aisha ina kun san Abbana na gidan umma?"

Aisha tace
"Umman Abbanmu wacce itama take dukanki?"

Lumshe idanu tayi tace
"Aisha ba na hana ki cewa ana dukana ba?"

Shiru yarinyar tayi, se Usman yace
"Abba da be da lafiya mama?"

Kai ta gyaɗa tace
"shine yau ya rasu, ya tafi ya barni ƴaƴana bani da kowa se ku se kuma Allah...."
Ta fashe da wani irin kuka.

Aisha tana shafa bayanta Usman na share mata hawaye, sun jima a haka Kan Aisha tace
"Mama malam yace haramun ne in mutum ya mutu a yi mishi kuka ko Ya Usman?"

Usman yace
"Eh Mama, muma ya ce mana duk hawaye da ze diga daga fuskanka kaman azabar wuta kake karawa wadda ya mutun"

Gyaɗa kai tayi tace
"Na dena! Na dena kunji?"

Kai suka gyaɗa mata tace
"daga yau in kun yi sallah karku manta saka Abbana a Adu'a kun ji?"

Kai suka sake gyaɗawa, Usman ya je ya ɗauko musu abincin da seda ta girka musu kan ta tafi wurin Abban nata, shi ya zuba musu Aisha ta ɗauko cokali sede duk yadda suka yi da Maman tasu ta kasa ci ko kaɗan.

Ita kadai ta san irin azabar da take ciki na nakuda, yadda cikinta ke yi kaman ze barka fata ya fito, gumi kawai take Haɗawa cikin dauriya irin na wadda ya Rayu cikin azaba ya girma cikin azaba tayi ta zama har suka gama cin abincin tana ta Kallonsu.

Bayan sun gama ta kalli Usman tace
"Usman je ka kiramin Asabe don Allah"

Fita yayi yaje gidan ya dawo ya samu abu kam fa kara tsanani yake don ko buɗe idanu se tayi da gaske suke buɗuwa, yace
"Mama Su Habiba sun koreni"

Lip ɗin ta dake cikin haƙorinta ta saki da kyar tace
"ka ce su taimakeni nakuda nake yi"

Aisha na rike da Hannunta tana kuka ya fice, Seda ya jima kan ya dawo yana zub da hawayen halin da ya zo ya tarar da maman sun yace
"Mama kowa ya ki zuwa ya taimaka mana, duk korata suka yi Zulai har da cewa ki mutu ma in kin ga dama, Mama ai ba zaki mutu ba ko?"

Kai ta gyaɗa cikin dauriya tace
"In shaa Allah, ka fita....ka samo napep don Allah ka kula Abban mama"

Ficewa yayi da gudu, Aisha ta kalla tace
"ɗauko jakan baby da na Haɗa"

Ɗaukowa tayi jakan gwanjo ne ta sayo ta Haɗa ƴan abunda baza'a rasa ba, a ciki akwai dubu uku uwar kudin jarinta kenan da dama gawayin zata sake sayowa, ko da Usman ya dawo kan ta samu ta mike Seda tayi da gaske kafafunta sun kasa motsi, da kyar da taimakon Allah da dafa bango ta samu ta fito suka shiga adaidaitan bayan ta saka Usman rufe gidan cikin karfin hali.

Me adaidaitan se Kallonsu yake cikin tausayawa yace
"ko a unguwa babu wadda ze iya raka ki asibiti kan ƴan uwanki su zo? Yaran nan ai sun yi kananan kai ki haihuwa"

Hawayen da ya zubo mata ta kai hannunta  da shima nauyi yake mata ta share tace
"Bani da kowa se Su se Allah"

Shiru yayi ya ja machine ɗin, har suka isa asibitin da anan ne take awo babu wadda ya ce komai, sun sauka yaki karbar kudin haka ya tafi, da taimakon yaran nata suka shiga asibitin sede abun takaici babu wani wadda yayi attempting attending ɗinta tunda ba masu kudi bane, tunda ba wasu suka sani ba bare a san su.

Ko da suka samu ta zauna Aisha ce tayi gudu ta rike hannun wata senior nurse da bata kula dasu ba tace
"Aunty mamana zata mutu don Allah ki cire mata babyn nan"

Da sauri ta kalli maman nata ta sake kallon Aishan ganin yadda take zub da hawaye gata kaman almajira yasa ta juya ta nufi Hidayat,
"sannu baiwar Allah, ina katinki?"

Jakar ta kalla cikin karfin hali, buɗewa nurse ɗin tayi ta fiddo shi tare da Juyawa seda ta kwashe mintuna masu yawa kan ta dawo ta kama hidayat suka nufi wani daki, mata sun yi goma a ɗakin gashi banda karni babu abunda yake yi na haihuwa, sossai tsabtan yayi karanci.

Fitar dasu Aisha tayi tace su zauna a kan bench ɗin, ita kuma ta koma ta duba Cm na Hidayat sede fa haihuwa ba nan kusa ba, kallon hidayat tayi tace
"Daurewa zaki yi baiwar Allah yadda kika jikkatan nan idan haihuwar ta zo kuma se yaya?"

Kallonta kawai hidayat take yi ita kadai ta san me take ji, in banda abun ya fi karfinta daga Usman har Aisha a gida ta haifi kayan ta babu me kaita asibiti in banda taimakon zuwa awo da ko yanke cibiyar Usman bata san ta yadda zata yi ba ga kananun shekaru.

Hijab ɗinta ta cire sbd sauro da taga suke yawo kaman kuda ta Mikawa nurse ɗin tace da kyar
"Don Allah ki bawa yarana su lulluɓa"

Kallonta matar tayi kan ta karɓa, ita kuma Hidayat ta ja zanin gadon ta kwanta a kan gayar ledan gadon.

Usman na Zaune Aisha na kwance bisa cinyar shi a haka bacci ya kwashe su bayan sun sha kuka, Hidayat kam bata iya ta rintsa ba, tun kan asuba ta fara wani kalar jijjiga tana taune harshe da haƙorinta idanunta na kakkafewa.

Nurses ɗin ne suka ruga suka kira likita, yana zuwa ya fara faɗan rashin kiranshi tun kan hakan ya faru, dukufa suka yi a kanta da kyar suka samu ta dena jijjigan sede tana cikin mummunan hali, fitowa yayi lokacin ana kiran sallah yace
"Ina waenda suka kawo ta?"

Wata nurse tace
"Naji dae senior nurse kan ta bar shift tace yaran chan ne suka kawota"

Dayake government hospital ne sun saba ganin irin haka yaje ya samu Usman ya bubbuga shi yace
"Ina babanku?"

Usman yace
"ban san inda yake ba"

Likitan yace
"Toh maman ku na bukatan aiki cikin gaggawa idan har ta kai awa shidda a haka ko ta haukace ko ta mutu"

Kuka suka fara, wani ya kalli likitan yace
"be kamata ka faɗawa yara irin wannan maganan ba bawan Allah kaman ba likita ba?"

Likitan be ce komai ba banda taɓe baki ya juya ya fice.

Aisha ta kalli Usman da fuskanta da yayi jaga jaga da busashun hawaye da majina tana sakin sabon kuka, hawayenta ya share mata yace
"Ki dena kuka zan je in nemi Abba ya zo ya biya kar ta mutu ko ta haukace"

Kai ta gyaɗa mishi, ya tashi ya fita.
Ita kuma an musu clock a basic science kuma mamansu ta koya musu yadda ake reading na clock saboda shine a ɗakinta.

Agogon ta kurawa ido tana kallo tana kirga awanni shida da ya bayar, wasa wasa saura awa ɗaya lokacin da ya bayar ya cika, fitowa tayi ta tsaya a bakin ward ɗin yadda tana kallon gate kuma tana kallon agogo a lokaci ɗaya tana kuka.

Bata yi mintuna sha biyar da tsayuwa ba aka wangale mashigar asibitin, wasu rantsatstsun motoci Prado bakake siɗik guda biyar suka shigo a jere banda ɗaukar eyes babu abunda suke sbd sabunta da kyalli, parking suka yi Seda aka dauki seconds kan kofofi takwas na biyu daga cikin motocin wadda suka saka ɗaya a tsakiya suka buɗu, wasu manyan bouncers majiya karfi sanye da bakaken kaya suka diddirko suka zagaye motar dake tsakiyan..

Mutane da suka san dama cikin lokaci irin wannan ne Allah ke jefo musu wannan bawan Allahn suka shiga zagaye motocin daga nesa.

Seda suka yi mintuna biyu da yiwa kansu matsaya kan ɗaya ya karasa ya sa hannu ya buɗe bayan motar, a hankali na ciki ya sako wani irin haɗaɗɗen kafanshi waje, Seda ya kwashe wasu seconds ɗin kan ya fito gabaɗaya, Wow..

Wani kalar gallant man ne a tsaye a wurin, dogo tsayayyen namiji sanye da wasu hadaddun jersey navy blue me tambarin kwallon kafan nan na Paris saint German wato (PSG) kafafunshi sanye da cover irin na ƴan kwallo na kamfanin PUMA, bazaka kirashi fari ba sede Sam baya cikin jerin bakake yana da wani kalar lafiyayyen fata ne wadda ya haɗu da zama Kasar ketare ya bada wani kala me daukar hankali, kanshi wata kalar aski ce irin ta ƴan kwallo an kwashe gefe da gefe tsakiyar aka yi mata wani kalar gyara se kuma ya rina ta zuwa kalar brown daga sama, gashin yana lilo har bisa kyakyawar goshinshi, kunnenshi na hagu sanye da wata tsadaddiyar Dan kunnen Diamond.

Dukda sanye yake da facemask me matukar kyau kana iya zayyano kalar kyaun da Allah ya mishi, yana da wasu irin idanu masu fusgan hankali haka ma hancinshi dogo ne me kyaun gaske, daga gwiwanshi har idon sawunshi dake waje zuwa hannayenshi da suke waje duka akwai wasu kyawawan gashi a kwance bakake sidik.

Murɗaɗɗun damatsanshi da suka yi kaman zasu yage hannun jersey ɗin zuwa faffadar kirjinshi kaɗai zaka kalla ka san eh lallai wannan ma'abocin motsa jiki ne bana wasa ba juya baya da yayi Zuwa cikin motar ne ya bani Daman kallon rubutun dake bayan Rigan inda aka rubuta
"MOH RAED" da kalar ruwan gold se katon number 7 daga tsakiya.

Tattausan hannunshi masu dauke da wasu irin dogayen yatsu zuwa faratunshi dake tsabtace ya Mika cikin motar bayan ya sauka se ga wani karamin hannu an sanya cikin nashi, gimtsewa yayi, tare da taimakonshi kyakyawar yarinyar da bata wuce 5/6 yrs ba ta sauko.

Masha Allah, itama kyakyawa ce sossai sanye da track suit pink masu layin fari fari na kamfanin Nike ne sanye a jikinta, bata sa hulan ba se gashinta da ya sha gyara zube har kafadunta katon pink headphone ne a kunnenta kafafunta sanye da Fararen boot suma na Nike.

Hannun babanta ta rike suka fara tafiya cikin tsantsar kasaita da ji da kai da kuma kuɗi.

"Allah me hallita! Lallai Allah shi ya san abunda ya ajiye anan mene!"
Wani ya faɗa cikin mamaki, wani matashi a gefen yayi dariya yace
"amma da alama baka kallon kwallo ko?"

Mutumin yace
"ana ta kai wa ke ta kaya?"

Wani daga gefe yace
"Dukda haka dae na san bazaka rasa jin sunan MOH RAED a Nijeriya ba"

Zaro idanu dattijon yayi yace
"Wai shine wannan? Allah sarki bawan Allah ai ko in har kai mazaunin nan Kano ne dole ka san sunan ko baka san shi a fuska ba, mutum me tausayin talaka da tsantsar taimako ashe yana zuwa irin wuraren nan?"

Wani chan yace
"Aiko in kana son ganinshi ta sauki ma se a irin wuraren nan ya kan taimaki asibitoci sossai"

Wani yace
"Amma fa an ce rayuwarshi akwai sarkakiya me karfin gaske hakan yasa kwata kwata a fuska bashi da fara'a idan ba yana tare da yaran nan nashi guda uku ba, sannan da chan da "R MAI NAGGE" yake anfani daga baya aka ga ya sauya zuwa wannan sunan"

A tare suka fara mishi Adu'ar Allah ya yaye mishi suna kallon ɗaya motar da wasu suka fiffito da jakukkuna masu girma girma suma duk sanye da kayan bouncers suka fara binshi a baya duk inda ya wuce za'a Mika maka envelope ɗaya.

Har ya Gota ta kaɗan se ya sake dawowa baya ya zuba mata kawatattun idanunshi, yarinya ce karama da bazata wuce sa'ar Farah ƴarshi karama dake rike da hannunshi ba, yadda take kuka yake kallo se kawai ya tsinci kanshi da karasowa gareta zata gudu yayi saurin rike hannunta yace cikin taushin muryarshi me sanyi da zaka ji daga makogoro yace
"hey! Calm down baby, what's ur problem? Where is u mama?"

Wow daga accent ɗinshi zaka san wannan ba kalar turancin da ake jin irin su a Nijeriya bane harshen shi a lankwashe yake wadda ko hausan yake in ba kunne ka sa ba ba lallai ka fahimta ba, wannan turancin nashi ko ni ba fahimta nayi ba seda na zura da gudu na nemo Ameeratuh(ƴar gayu ƴar Abuja) ta fassaramin me yace.

Farah ta ɓata fuska tana kallon majina da hawayen Aisha tace
"Dad please let's go, she's disgusting 'Donc je ne la'ime pas'"

Wara idanu nayi jin harda Faransanci tana nufin tayi kazanta dayawa shiyasa bata son ta.

A ko yaushe maganan yaranshi shine gabanshi duk abunda suke so shi yake yi musu yanzu ma baze fara kin sauraran ta sbd wannan ba, mikewa yayi daga kyakyawar durkuso da yayi suka nufi ciki.

#like
#comment
#share

                      🖤Gureenjo🖤

Continue Reading

You'll Also Like

261K 10.7K 37
Complete story of a young girl Ummy.
1.1M 28.1K 45
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
1.7M 95.2K 87
Daksh singh chauhan - the crowned prince and future king of Jodhpur is a multi billionaire and the CEO of Ratore group. He is highly honored and resp...
2.3K 100 16
wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani...