A DAREN AURENA(SABON SALO)

By MissDmk

1.7K 68 1

Based on True life event More

Complete story(chapter 1-21)
Page 1
Page 2
Page 3
page 4
Page 5
Page 7
Page 8
Page 9
10
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21

Page 6

89 5 0
By MissDmk

*A DAREN AURENA*
          _SABON SALO_


    BY

MissDmk✍🏻

Page 6

Lab Tech ta kawo result din tana murmushi, kafin tace congratulations Mr and Mrs. The results are perfect..

Mujaheed was impatiently waiting for her to read the result, please read it out, he muttered under his breath..

Well Negative for HIV test and... Jin numfashi na yana sama tsabar fargaba da nake ciki ba san lokacin da na zube kasa unconsciously ba, farkawa nayi na same samar gadon asibiti, ga Mimi a gefe na..

Da kyar na iya bude bakina da yayi min nauyi nace Mimi ina Hamman ki?

Mimi tace Alhamdulillah kin farka bara naje na kira Doctor, tana fadin haka ta mike ta nufa kofa..

Haryanzu ban daina fargaban abin da yake cikin result din ba, ina cikin wannan tunanin, I subconsciously sense his fragrance emanating from the room, cikin hanzari na dago da fuskar towards the door direction, inda na gan sa tsaye as usual, wanni tsoro da fargaba ne ke tunkaro ni a yayin da yake takowa izuwa gare ni... Zai magana kenan Doctor ya shigo dakin yace..

You're awake? Yayi maganar yana murmushi kafin yace please ki rage tunanin kinsa condition din ki ba at your age bai kamata ace jinin ki ya kai 130/90 ba, tunanin mai kk yi haka? Bacin kina da sugar? Indai kina son kiyi controlling sugar ki dole ki kula da blood pressure sabida ku san a tare suke tafiya, ni kuma bana son na daura ki kan drugs yanzu is too early, ga kuma ulcer duk ke daya?

Malam please a kiyaye a daina barin ta cikin damuwa da tunanin she's too young for that.yana fadin haka ya nufa hanyar fita sai kuma ya dawo yace  kafin wuce ku biyo office na, yana fadin haka ya wuce..

JayD the pregnancy test is....?

Wannan ba damuwar ki bane. Idan mun koma zaki ga result din...

Hadiye wanni abu mai daci nayi kafin na runtse idona, ina karanto inna lillahi wa ina ilaihi rajiun under my breath..

Bayan Sati Daya

Muka bar asibiti izuwa gida saide abin mamaki ba gida naga mun nufa, gidan Ummah muka sauka..

Biyan kudin Napep yayi kafin yace mun shiga, ganin ina kallon sa, yasa ya shige ba tare da yace dani komai ba, bin bayan sa nayi, na tarar dasu zaune samar tabarma shi da Ummah

Durkusawa nayi na gaida ta, ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar, kafin tace ki tafi dakin ki, ki huta..

My jaw almost dropped out of shock ganin inda take nunamin..

Hala baki da labarin cewa kun dawo nan da zama? Mujaheed ba ka sanar da ita ba? Mujaheed yace Ummah yau fa aka sallamo ta daga asibiti, ina jira ne ta natsu ka... Dalla gafara can kana abu kamar gillu? Nace tsoranta kk yi da ba zaka gaya mata ba?
Ke Aisha. Ɗana ba mai arziki ba ne da zai kama gida irin waccan, ganin yana ta kokarin cike kudin hayar kafin a koro ku daga gidan yasa nace ya amsa sauran kudin watanin yazo ya gyara dakin sa ku zauna, saura kuma yayi noma tunda de na san nan bada jimawa ba zaki haihu..

Ji nayi zuciya ta na bugu kamar zata fito fili tsabar tashin hankali, haihuwa? Cikine dani ko-ko maine? Bansa ina hawaye ba sai da naji Ummah na cewa to muguwa algunguma so kike ki kashe min ɗa na ko? So kk yayi ta miki bauta? Dalilin aurenki da yayi yanzu ko garin masara bamu da shi a gidan nan, akan auren ki, ya je ya sayar da gonar gado akan auren da bai da riba? To ta Allah ba taki ba kinji..

Ya hakuri Ummah nayi maganar ina kokarin goge hawayen da su ka sa tsayawa...

Hakurin zamu ci? Ni dalla ki tashi ki bani gu, ba shiri na bar gun ina kuka...

Ummah Dan Allah ki daina mata haka, tana da lalura yanzu likita ya gama min kashedi akan lafiyar ta, Mujaheed yayi maganar a tausashe

Dalla can, duk karya su keyi, daga ita har likitar, so suke su karar maka da ɗan kudin ka, Ummah tace yanzu ya maganar zuwa duba gonar Jaɓe? ka ga damuna yana hararowa..

Gobe in shaa Allah zan wuce Ummah yayi maganar cike da girmamawa..

Ummah tace yanzu naji batu, Allah ya kaika lafiya ya kuma bada sa'a, ya amsa da Amin Ummah, Ummah ba abinci ne akai mata?

Tamke fuska Ummah tayi kafin tace Maryam zo ki kai mata abinci, mikewa Mujaheed yayi ya nufa dakin ya sameni sai kuka na keyi, ina ganin sa nayi saurin goge hawaye na...

Ke ba yanzu likita yace ki daina wannan tunanin da koke koke ba?

Mujaheed yanzu irin rayuwar da ka zabar mana kenan? Bani da kima da daraja a idonka yanzu kenan?
Lefin mai nayi maka da kake azabtar dani haka?
Lefi ne dan na cece namijin da nake so? ko-ko Lefi ne dan na auri wanda nake so?

Aisha akan zama gida daya da mahaifiya ta kk wannan haukar ko-ko maine? Yayi maganar a zuciye, look Aisha I didn't force you to marry me? Ai kina sanne da cewa ban dashi kk aure ni? idan kin ga ba zaki iya rayuwa dani ba zaki iya tafiya, yana fadin haka ya bar dakin....

Kuka na keyi bana wasa ba har Mimi ta shigo dakin, Aunty dan Allah ki rufa wa kanki asiri ki bar kukan nan? Kuma karki ga lefin Hamma, Ummah ne ta dage lalle saide ku dawo nan da zama shiyasa...

Uhmmmm Mimi kenan...

Mimi tace Aunty ki bar sa kome a ranki dan Allah, ki cigaba da hakuri kuma kina adu'a, mai hakuri shike da riba in shaa Allah...

Nagode Mimi, but ina sauran kayana...?

Kujeru da sauran kayan wuta ya sayar, tudan nan ba space da zaki sa su,  sauke ajiyan zuciya kawai nayi ina karkada kaina..

10pm

Ina samar khimar ya shigo dakin hade da ajiye kudin a gabana yace ga kudin kayan da aka sayar, nan 300k ne.

Ba abinda zanyi da shi, ka rike kudin na karasa maganar ina daura kaina a samar guiwa ta...

Baice dani kome ba ya hau samar gado ya zauna, daukar kudin nayi na mika masa..

Aisha sannin kanki ne cewa abin wani bai dame ba koh?

Yes I know you're not materialistic person but you sold out my property without my consent? Who does that Mujaheed?

Kina numfi ban issa da kayan ki ba kenan? Yayi maganar yana hade giransa gu daya..

Ba abinda nake nufi ba kenan, ina da right na sanni ai..

Ke karki ga ina maki sanyi ki nema ki raina ni, yana fadin haka ya mike zabar dakin nayi saurin durkusawa a gaban sa nace Dan Allah kayi hakuri ka zauna, har zuciya ta na bar maka wannan kudin, gara kai ka rike kudin kayi jali da shi muna samu muna rufa wa kanmu asiri...

Shuru yayi ya na kallona kafin ya mikar dani daga durkushe da nake, to shikenan Aisha zanyi yadda kk ce amma ki daina wannan kukan sabida lafiyar ki, je ki wanke fuskar ki kizo ki kwanta..

Da mamaki nake kallon sa dan ba zan iya tuna when last JayD yayi min magana cikin taushin murya ba irin yanzu...

Zuwa nayi na wanke fuska ta, hade da dauro alwala na dawo dakin na sama yayi shimfida a kasa, na san kishina ke sa shi yin haka amma in shaa Allah I'll win back his heart in no time, adu'a barci nayi kafin na kwanta amma sam barci yaki zuwa, kamar yadda na kasa barci haka yake Agun JayD..

He just can't take that night incident off his mind, the thought of it, is making him sick, he sighed deeply....

Da sake sake cikin raina har barci barawo ya sace ni, bani na farka ba sai karfe bakwai, ko da na farka ba shi dakin, nayi maza na tashi na dauki buta na fita nayi alwala kafin na dawo ciki nayi sallah, ina samar khimar ina azkar Ummah ta bude kofar tace ina kwana uwata kuma isashiya, tunda ke kinfi karfin ki zo ki gaishe ni, ni gani na zo na gaishe ki...

Ya hakuri Ummah yanzu nake idar da sallah, ina kwana na yi maganar cikin taushin murya

Sai kizo ki daura mana abinci safe baki abin magana, tana fadin haka ta bar gun, mikewa nayi na nike hijab da khimar na gyara dakin kafin na fito, na nufi dakin ta...

Ga kulun koko can, sannan kiyi dumame shi zamu ci yau, amsawa nayi da toh kafin na fara hada hadan yin abin karin kumalo, sai wajan after 8 na gama kome kafin na kai mata daki...

Bani da appetite amma hakanan na tura abinci sabida yunwa, ina zaune kiran Ya Fahad ya shigo waya ta, amma na kasa dagawa tunawa nayi da kashaidin da JayD yayi min.

Bayan wanni lokaci naji ance ana sallama dani, nide iya sanni na bani da wani da zai nema ni, Ya Fahad ma baya kasar balle nace ko shine, da wannan tunanin na zira Hijab na fito, saida na sanar da Ummah kafin na fita inda na ga....










Thank you
09074267236
©MissDmk

Continue Reading

You'll Also Like

11.1K 1.1K 26
"ඒ රිදුම් නිවී මා හදේ ඈ ළඟින් රැදීලා වගේ සීරුවෙන් ළයේ පෙම් මල් පීදුනා" අමිත්‍යා × උපුනි
813K 16.3K 112
Yaszy Romano has been through so much pain and suffering her entire life but it makes her who she is. Dark Angel...Dangerous, Powerful. An Assassin...
16K 1.6K 18
" ඇයි අයියෙ ඔයා කොයි වෙලෙත් මාව සුදු අරලිය මලකට සමාන කරන්නෙ.." මං අයියගෙ මූන දිහා බලන් අහනකොට එයා මගෙ ඇස් දෙක දිහා බැලුවා.. මගෙ අයියගෙ මූනෙ ඇඳිලා තිබ...
50K 6.6K 55
"ඒයි ඇටිකිච්ච ඔහොම ඉන්නවා" "නේත්‍ර, නේත්‍ර... මගේ නම නේත්‍ර" "මොකද උඹේ කට ඔච්චර සද්දෙ, මට ඔය වයසට වඩා උඩ පනින්න දඟලන ඇටි කිච්චන්ව පේන්න බෑ. ඒ නිසා මට...