GAMON JINI

By Gureenjo6763

3.4K 87 5

Read and find out💃 More

Shafi Na Daya
Shafi Na Biyu
Shafi Na Uku
TALLAH
Shafi Na Hud'u
SHAFI NA BIYAR
Shafi Na Shidda
Shafi Na Bakwai
Shafi Na Takwas
Shafi Na Goma
Shafi Na Sha d'aya

Shafi Na Tara

189 3 0
By Gureenjo6763

⚡️*GAMON JINI*⚡️

     *NA FATIMA MOH'D GURIN*
               *GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE NINE*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****

Baya manta watarana ya shigo cikin garin magashi da misalin karfe shidda na yamma a gajiye yake be da wani buri se na ya ga yayi salla ya kwanta ya huta, yana saka kanshi cikin gidan yaga Zainab er shi ta fari da Rumasa'u ta biyu suna rike da saudat d'iyar da bata fi shekara da wata biyar ba se kuka take muryarta ko fita baya yi da alamu ta jima tana kuka, suma duk se hawaye suke yi.

Da sauri ya karasa kansu yana cewa
"Zainab me ya same ta? Ina mamarku?"
Cikin kuka Rumasa'u tace
"Bamu sani ba Abbu ta fita tun da safe, gashi tun azahar saudat ke kuka har yanzu bamu san me ke damunta ba"
Surar Saudat d'in yayi yace
"Ku zo mu je"

Mota suka shiga a rud'e yake jin yadda jikin yarinyar yayi wani irin zafi be yi tunanin yunwa bane, kano suka koma dayake ba wani Nisan kirki bane, asibiti da suke da NHIS ya kai saudat a take aka kar'beta sede lokacin ma ta fara convulsion a rud'e ya kira Almustapha ba'a jima ba se gashi, shine ma ya iya sake tambayar su Rumasa'u dake kuka me ya sameta?

Rumasa'u tace
"Tun jiya kaman bata da lafiya dama tunda Mama suka fara fad'a da Abbu kullum in baya nan se ta fita ta barmu da saudat sede muyi ta bata ruwa har ta dawo da dare, to jiya duk yadda mukayi tayi shiru taki da mama ta dawo muka gayamata tace ta mutu ma in ta so, uban da yasa sunan buduruwashi yazo ya bata mama..."

Hanci ta ja tana shesheka er shekara biyar ce ke musu wannan bayanin yayinda muniba dake da bakwai bata ce komai ba se kuka, seda Almustapha yace
"Ehem se me ya faru yau kuma?"
Ta cigaba
"Se yau zata fita nace Dan Allah tayi hakuri ta fita da saudat bata da lafiya tace in ban rufe mata baki ba zata ci ubana, kuma daga ni har Zainab muka kuskura muka fad'a maka in ka dawo zata yanka wuyanmu"
Sossai ranshi ya 'baci jikinshi har tsuma yake me yasa wasu mata kishinsu ke zama hauka akwai wadda ya haifa mata yarinyar ne? Ta cire tausayi da imani ta ajiye gefe sbd banza kishi..

Be gama tunaninshi ba likitan ya fito jikinshi a sanyaye yace
"I'm sorry we lost the baby, ciwon ciki da zuwa yanzu bamu san musabbabi ba shi yayi ajalinta"

A firgice ya mike yana ambaton sunan Allah hawaye na zuba a idanunshi yace
"Dr. Kisa ne please kuyi filing case, call the police immediately..."
Jiri ne ya d'ibeshi a take ya nemi zubewa se Almustapha ne ya tareshi a take ya suma...

Ba karamin rikici akayi ba kwananshi biyu a asibiti, ya dankara ma halima saki biyu kuma ya rantse da Allah se sun yi shari'ah, da kyar Malam Imam ya sauko dashi itama halimar kwananta d'aya asibiti sbd rud'ewa bata ta'ba tunanin zata rasa yarinyar ba a tunaninta idan uban ya gaji da halin da take yi ya fasa auren, maidata kam duk yadda malam Imam yayi Muhammad yaki yace ba yanzu ba...

A tsakankanin ya karasa ginin gidan da yake a cikin kano wadda Almustapha ne kawai ya sani a lokacin ne kuma suka rasa kaninsu Murtala d'an shekara bakwai sanadiyar Amai da gudawa me tsanani, Muhammad ya nuna it's high time su bar magashi sbd rashin ingantaccen ruwa ne yayi sanadiyar Murtala, Malam Imam ya nuna baze iya barin magashi ba, ba yadda Muhammad ya iya haka aka yi aurensu da Saudat be bari sun zauna magashi na kwana biyu ba suka koma cikin kano, da Almustapha da muniba da kuma Aisha waenda saudat ta maidasu en d'aki kuma abokan hirarta sossai take sonsu..

Bayan watanni uku Mairo ta sake haihuwa aka maida murtala a lokacin Saudat na da cikin wata biyu, ba fa wai Mairo ta saduda da tsanar da tayiwa Saudat bane se ma karuwa da yayi, a ganinta bakin jininta ya janyo mutuwar jikarta da kuma raba auren Muhammad da Halima, hakan yasa ko kallon saudat batayi idan ba bakar magana zata ya'ba mata ba, gashi Muhammad baya iya 'boye son ta hakan ke kara kona mata rai ta tabbatar asirin da ake maganar en Gombe da iyashi shi tayi ma d'anta.

Har cikin saudat ya shiga watan haihuwa baza'a wayi gari a kai dare bata yiwa Muhammad maganan maida auren halima ba, ranar wata juma'a ta tashi da nakuda Almustapha da su Zainab suka kaita asibiti sbd Muhammad na kasuwa ta sha wahala sossai kan ta haifi santalelen yaronta na miji, se kiran Muhammad akayi aka sanar dashi ta haifi yaro namiji, farin ciki ba'a magana musamman yadda yaron ya kwaso kamannin ta sak, har hasken fatar sa'banin Muhammad dake wankan tarwad'a.

Ba irin 'barin kud'in da be yi ba a kan Yaron, danginta suma sun yi rawar gani kyaututtuka da ya samu ba'a magana sbd mai martaba na mugun ji da Saudat yasa duk makusancinshi seda ya san haihuwar, sarki kuwa da kanshi ya sanar da albishir ba'a bada tukuici me tsoka ba ai be yi ba, kan ranar suna yaro ya mallaki filaye da gidaje, a kano da Gombe.

Ranar suna kuwa Muhammad ya saka sunan babanta, baze ta'ba manta karamcinshi na bashi ershi alhalin shi ba kowan kowa ba bayan sarakuna da 'ya'yansu bila adadin sun nemi hannunta a aure ya hana yace se shi tunda shi take so, en uwanta ne suka mishi lakabi da Abrar. Ma'anar Abrar (me gaskiya, me tsoron Allah kuma nitsatse)

Bayan kwana biyu da suna malam Imam ya taho da kanshi don kallon jikan nashi me sunan babanshi dukda ba ainihin sunan yaci ba sede Muhammad dae Muhammad ne kuma gud'a d'aya jal d'in nan ake wa takwara wato fiyayyen hallitta, adu'a sossai ya mishi ya kasa d'auke idanunshi daga kan Abrar har Muhammad ya kasa shiru yace
"Malam na lura Abrar ya kwace duk wani matsayi na kowa a zuciyarka"

Murmushi yayi yace
"Ni kad'ai na san abinda na gani ga yaron nan, sede ba lallai in kai lokacin da abubuwan zasu bayyana ba, ina mishi fatar alkhairi kuma ina mishi adu'ar duk wani kaddara tashi ze yi kokari ya tsallaketa ba tare da yayi kuskure ba"

Da mamaki Muhammad ze kara magana malam ya mikawa Saudat dake zaune yace
"A kowani lokaci ki zama me fahimtar wannan aboki nawa, bakinki kuwa kar ya furta mummunar kalma zuwa gareshi duk tsanani Allah yayi muku albarka duka"

Suka amsa suna kallonshi, mikewa tayi ta fice ya dubi Muhammad yace
"Kayi hakuri babana ka dawo da Halima gidanka shekara d'aya yaci ace yanzu ka huce da mutuwar saudat, kuma halima nadama sossai ya bayyana a gareta kullum tana yawan samuna da in baka hakuri don haka ina Neman mata alfarma"

Shiru yayi kanshi a kasa shifa ta riga ta fice mishi a rai har ga Allah, sbd son kau da maganan yace
"Mustapha yayi maka maganan wacce yake so ya aura an ce ya turo kuwa a gidansu?"
Murmushi yayi yace
"Ka san Almustapha da kunya, ai yanzu kai matsayin uba kake a garesu har yayyunka mata ma, kayi duk abinda ya kamata mu namu zuwa mu tambayar mishi ne idan komai ya kamallu"

Duk yadda Muhammad yaso ya kwana yaki haka ya tafi, Muhammad na shirin tafiya massallaci sallar magriba kenan aka kirashi da mummunar labari Malam Imam yayi hatsari a hanyar komawanshi Allah ya kar'bi abunshi, iya rud'ewa familyn sun shige shi...

Har akayi bakwai d'in malam Muhammad be dawo daidai ba, da taimakon saudat ya warware ya kar'bi kaddara, bashi da masaniyar abinda saudat take fuskanta a zamansu na kwana bakwai d'in nan, ya de san ta ta'ba samun attack sau d'aya na asthma d'inta wadda ba don Allah ya taimaka Rumasa'u tayi gudun nemanshi ba da be san me ze faru ba har allurai ta sha, ita kuwa fuskantar matsalar mahaifiyarshi take tun bata gama jegon yaron ta ba ake sheganta mata shi ake jefarshi da maganganun da ba kowacce uwa bace zata juri ji.

Har cewa sukayi wa ya sani ko ribar asiri ne shiyasa daga zuwa ya d'auke mata malam, tunda da be je kallonshi a kano ba da be mutu ba, tayi kukan wannan magana sossai sede bata nunawa Muhammad komai ba, bayan kwana goma da rasuwar aka maida Aurensu da halima saboda alfarmar karshe kenan da ya nema daga gareshi, washegari suka koma Kano.

Wani irin zama sukayi marar daad'i Saudat hakuri ya mata yawa yayinda Halima take zazafa abu a ko yaushe tana cikin cutarta, hakan yasa tausayi da kauna kullum Muhammad ke karawa akan saudat tana bashi tausayi matuqa ya rabota da gidansu cikin gata da arziki ya kawo ta inda a kullum tana cikin kunci da damuwa in ba daga Almustapha ko gareshi ba babu inda take samun sauki, gwara goggonshi Asma'a tana sonta amma daga yayyunsu har mahaifiyarshi matarshi da 'ya'yan da yanzu mamansu ta gama hure musu kunne fitsara kala kala suke yiwa saudat d'in idan ba Mustapha ne ya gani ya zane su ba to fa sede ta kauda kai.

Bayan shekara hud'u ta haifi Abdulkadir a lokacin Halimatu ma ta haifi Hauwa'u sossai ta kwallafa rai akan samun namiji sbd ganin yadda arzikin Muhammad ke bunkasa sede kash Allah ya riga ya tsara abunshi, tsakanin ne Muhammad ya dawo da mahaifiyarshi gidan dukda ya sani basa son saudat to ya ze yi mahaifiyarshi ce kuma ba'a chanzawa, saudat d'in ce ma take karfafa mishi gwiwa idan jikinshi yaso yin sanyi hakan yake kara mata kima da daraja a gareshi bata ta'ba kawo karar halima ba bare Mahaifiyarshi da yayyunshi.

A hankali suka fara fahimtar halin Abrar wadda Halima ce ta fara fargar dasu dukda yawan shirun shi da rashin kiriniyarshi ke sa mahaifinshi da Almustapha ke ce mishi Saraki sa'i da loakci a cewarsu jinin sarauta da mahaifiyarshi bata kwaso ba shi yayo hundred percent, ba zaka ganshi a cikin kiriniyar yara ba ko yaushe yana d'aki idan ba yana karatu ba yana zaune shiru, ko be da lafiya sede Amah yadda yake kiranta ta fahimta ta tambayeshi da kyar ze fad'a mata abinda ke damunshi, shiyasa take kaffa kaffa dashi wadda Daga Mairo har Halima gani suke so take ta nuna musu ta haifi d'a namiji shiyasa ko kunyar d'an fari bata nunawa.

Wata rana yana tafiya a hankali idanunshi a kasa tilawar karatunshi na hadda yake sbd be wasa da qur'ani, Zainab  ce ta taho ganinshi yasa ta karaso da sauri ta bangaje shi har ya kai kasa, mikewa yayi ya ka'be jikinshi ya zagayeta ze wuce ta dawo dashi baya tace
"Kai Dan uwark...."

Bata karasa ba ya sauke mata naushi a baki yace
"Duk randa kika karasa se na fasa miki baki Amah ba tsarar ki bace"
Juyawa yayi ya karasa garden da zashi, Ashe bakinta ya fashe da ihu ta karasa wurin halima take gayamata abinda Abrar ya mata, a zafafe ta mike suka tafi yuu zuwa gareshi yana zaune ta fisgoshi ta fara durawa Amah zagi, idanu ya kafa mata yaki kaucewa, mari ta kifa mishi sede be kauda idanun ba, janshi tayi fuuu zuwa parlornta Me aikinta dake Iron ta fisgo ta nana mishi a hannu abun mamaki Abrar be yi kuka ba kuma be kauda idanunshi ba, Almustapha da ya shigo kar'bar sakon da Muhammad yace ya bar mata ne ya saki salati ya karasa da gudu ya fisge iron d'in yayi wurgi dashi a zafafe yace

"Me wannan? Wani irin rashin imani ne hakan maman Zainab? Me ya miki da zafi haka da bulala be isa hukunci ba?"
Harara ta zabga mishi tace
"Bugeni se in fad'a ubana ko"
Janshi yayi da sauri yana fidda waya ya kira Muhammad yake shaida mishi a take yace gashi zuwa, har suka isa asibiti akayi treating na hannun nan pim Abrar be ce ba se wani irin huci yake idanunshi a bushe kamas se ma Saudat ce ke share hawaye.

Tsoron halin Abrar ne ya fara shigarsu kan suyi sabo da hakan, ba zaka ta'ba ganin dariyarshi ba idan ba da Amah ba ita d'in ma se de in su biyu rakk, haka doguwar magana baya sonta, da yayi magana gwara ya aiwatar a gani a aikace, ga kokari a makaranta be da aboki ko guda d'aya, daga islamiyya, boko se gida wurin Amah ya sani, gwara idan sun had'u da Uncle d'inshi murtala kasancewarsu sa'anni kuma murtala baya fushi da halinshi hakan yasa suka saba nan ma idan Mairo ta gansu tare ta dinga masifa kenan tana cewa shi ya kashe ubanshi amma ya rasa wadda ze likewa se shi.

Miskilancinshi na mugun bawa mutanen gidan haushi suke d'auka iskanci ne, idan Mairo zata kwana fad'a Mawuyacin abu ne Abrar ya d'aga ido ya mata kallon arziki bare halima, daga Abbu har Amah sun yi mugun fahimtar halinshi akwaishi da mugun son iyayenshi ya taso da tausayinsu musamman Amah da ya san ba a sonta a gidan, bayan Amah ta haifi Abdulkadir Halima ta haifi Hauwa'u suka sake haihuwa kusan tare tare, Amah ta haifi Khalid yayinda Halima ta haifi Asiya(takwarar yayar Muhammad) nan fa suka shiga cewa asiri tayiwa halima kada ta haifi maza sbd ta samu ta mallake gida habaice habaice kala kala daga danginshi da dangin Halima nata kuka ne ta share hawaye, se kuma yawan ciwo asthmanta a kullum kara chronic yake zama.

Bayan haihuwan ne suka sake samun ciki a tare Amah ta haifi Jabeer, halima ta haifi Fatima, a lokacin cewa tayi se ta kashe Amah seda Muhammad yayi rantsuwar da gigi ta ta'ba Amah a bakin igiyarta d'aya da ya saura a hannunshi kan ita da en uwanta suka saduda, tashin hankali ba irin wadda Amah bata gani dasu ba sede hakuri ya mata yawa, ta samu ciki tsabar fargabar karta haifi namiji yasa cikin 'barewa be yi karfi ba, sossai Muhammad ya ji takaici sbd likita ya gayamishi damuwa ce ta sawa ranta.

Har Halima ta haifi Muniba, a lokacin ne Wani malamin Abbu ya bashi mata Saddiqa, duk yadda ya so ya zillewa auren abu be yiwu ba Allah ya riga ya tsara, ba wadda ya kai su Mairo farin ciki sede sun Shaka ganin wacce suke murnar zata muzanta ko a jikinta itace ma ta tsaya akan hidimar har aka watse wadda darajarta ya kara ninkuwa a idanun mijin, tashin farko ta saddiqa da suke cewa Aunty ta haifi en biyu mata Amrah da Ameera, yayinda Halima ta haifi Aisha.

A lokacin Almustapha yayi aure da d'a d'aya Muhammad(junior) sbd sunan Abbu yaron ya ci, bayan shekara biyu Amah da siddiqa suka sake haihuwa Amah ta haifi sadeeq yayinda Siddiqa ta haifi Hadiza, after 2 years again aka samu Maher seda ya shekara Saddiqa ta haifi Waheeda daga nan kuma dukkansu haihuwar ta tsaya chakkk.

Abrar ya nuna soja yake son zama so tun yana kananan shekaru mahaifinshi yayi enrolling d'inshi NDA yaro ne me kwazo da kafiya muddin ya sa abu a gaba se ya cimmasa hakan yasa farat d'aya yake shiga ran mutane sede kash shi d'in ba me iya sabo da kowa bane, kannenshi duka babu wadda be tsoronshi har da yayyunshi sbd akwai lokacin da ya gurd'a rumasa'u sbd ta zagi Amah, dama Zainab ta ta'ba Shan naushin shi so duk wani mugun tsoronshi suke yi...

Bayan tsawon lokaci kowa ya fara kama abinda ya kama, murtala Likitan yara ne yana aiki a wani private hospital da yake da share matarshi Mufy da yara uku(Maryam, saudat da Muhammad) Inda Abdulkadir ya za'bi zama Accountant yana aiki a reshen CBN na kano yayi Aure matarshi Ruqayya da yara uku (Amrah, khausar da walida), se khalid da ya karanta medicine and Surgery shima yayi aure matarshi Aisha da yara biyu(Aslam da saudat suna kiranta Afra), jabeer business ya za'ba don haka shi ya kar'bi Abbu matarshi Sumayya da karamin ciki, yaran matan d'akin Hajiya Yaya (halima) babu wacce tayi sama da diploma da NCE suke tuburewa su ce se aure a takaici duk sun yi aure cikin kano d'in banda Muniba da Aisha, Amrah da Ameera suna shakarar karshe a Bahrain inda Amrah take Psychiatric(Likitan kwakwalwa)Ameera take Cardiology(likitar zuciya).

Hadiza tana First year a Nile university inda take karatanta psychology, yayinda sadeeq da ya tsayar da rashin ji be samu admission ba.

Cigaban Labari

"Allah seine barkama..!"
Amah ta fad'a tana jijjiga shi sbd yadda yayi zurfi a tunani, runtse idanunshi da suka rine yayi a tsorace Amah tace
"Me ya faru haka?"
A hankali yace
"Wata masifar ke shirin tasowa bayan wacce ta faru a baya da tayi sanadiyar rayuka Biyu"
A firgice tace
"Kana so kace wannan masifar ma ta shafi mutuwar Fadila da Auwal?"
Wani zazzafar iska ya fesar tuna tashin hankalin da suka shiga a lokacin yace
"Hajiya Babba(Mairo) tayi min umarni in dolanta Abrar ya auri Nadra a matsayin fansar ran Fadila"
Cikin wani irin tashin hankali da baze ce ya ta'ba gani a fuskanta ba tace
"Whaaaatt? Fansar rai? Muhammad ne ya kashe Fadilar? Wani irin zance ne wannan?"

Be ta'ba ji ta kira Abrar da Muhammad ba se yau abunda yake gani a idanunta yake kara tsintsinka zuciyarshi tabbas hakurin Saudat na dab da karewa in ta jura a baya da matuqar wuya ta jura a yanzu, mikewa yayi ya riketa yace
"Calm down Hayatee, it's high time mu dena zubawa yaron nan ido har yaushe mukarrama zata fita a ranshi har yayi aure ina ganin sha...."

"Please Baban Zainab..! Idan har kace bayansu zaka goya a wannan karon zamu samu matsalar da bamu ta'ba samu ba, ba zan ta'ba bari a cutar min da yaro ba... I can't" kuka ne yaci karfinta da sauri ta fice ta kofar da ze sada ta da part d'inta da kallo ya bita, yana ji kaman yayi kuka for the first Saudat ta fara maida mishi magana... me ke shirin faruwa ne nan gaba?

****

*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...

*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*

*Da Kuma*

*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*

*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*

Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
    Se a turo shedar biya ta wannan layin
09039206763
Note: Banda Recharge card.

🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

1.3M 93.6K 126
credit to original author Shui Qian Cheng. This story belongs to Rosy0513 . I am just a translator. This cover photo is not belong to me.
456K 23.5K 51
အခြေအနေတစ်ခုကြောင့် လက်ထပ်ဖြစ်ခဲ့ကြတယ် အန်တီက ရိုးရဲ့ ဇနီးမယားပါပဲ... အေျခအေနတစ္ခုေၾကာင့္ လက္ထပ္ျဖစ္ခဲ့ၾကတယ္ အန္တီက ရိုးရဲ႕ ဇနီးမယားပါပဲ...
141K 16.8K 65
Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya...
41.4K 1.6K 36
Amma kin san akwai karatu ko ko kyalkyalen banza kike so Ni de aa wallahi bazan iya ba Ta mike Ya biyo ta *DEAR* ta juyo yaya na gaji tafiya xan y...