GAMON JINI

By Gureenjo6763

3.4K 87 5

Read and find outπŸ’ƒ More

Shafi Na Daya
Shafi Na Biyu
Shafi Na Uku
TALLAH
Shafi Na Hud'u
SHAFI NA BIYAR
Shafi Na Shidda
Shafi Na Bakwai
Shafi Na Tara
Shafi Na Goma
Shafi Na Sha d'aya

Shafi Na Takwas

171 3 0
By Gureenjo6763

⚡️*GAMON JINI*⚡️

*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE EIGHT*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****
Malam Imam Muhammad magashi shine asalin mahaifinsu, su biyu kachal iyayensu suka haifa da shi da kanwarshi Asma'u, mahaifinsu asalin shi limamin massallaci ne a nan garin magashi na jihar kano, sana'arshi kuwa saida kayan hatsi ne ba kuwa ta kirki ba sbd ko buhu d'add'aya na hatsi a lokacin be kai ba sana'ar tashi, kaman yadda ya tashi ya samu gidansu da karatu haka shima yake kokari sossai akan ilimin addini, mahaddaci ne hakan yasa ko hanya ake ganin kimarshi ana mamakin matashi irinshi da irin ilimin addini na ban mamaki.

Wata rana ya fita a hanyarshi ta zuwa kasuwa yabi ta wani lungu ya samu rikici ya kachame tsakanin wata me saida abinci da wani customer d'inta d'an garuwa ya ci yace karfinta ya kwatar mata, dukda yadda ake rirriketa haka take daddagewa ta watsar da kawayen nata dake talla tayi kan shi shima maza sun rirrikeshi, a natse ya karaso yayi mata sallama, murgud'a baki tayi gefe tare da juya mishi keya..

D'an murmushi yayi yace
"Baiwar Allah be kamata kina musulma kuma d'iya mace ki tsaya a tsakiyar unguwa kina rikici har dambe da namiji ba, muryarki alaura ce kaman yadda jikinki yake duba kiga..!"
Ya nuna ta sama har kasa Gyale na yashe a gefe, Dan kwali taci d'amara dashi, d'age kai gefe tayi tare da murgud'a baki cikin kunkuni tace
"To ni se aka ce ya ci kayan sana'ata yaki biya ai.."

Wani dattijo yace
"Ke Mairo, har yaushe zakiyi hankali ne? Yanzu aka barki da me Ruwan kina tunanin zaki iya dukanshi ne? Kuma ki duba wadda ke miki magana amma kike mishi kunkuni?"

Kuka ta fashe dashi tare da zubewa kasa tana ta zabga kuka, murmushi Imam yayi ya karasa ga me Ruwan yace
"Kaji tsoron Allah ka sani duk hakkin da kaci ba naka ba se ka ga ba daidai ba tun anan duniya kan aje lahira, wlh a duk lokacin da ka ce zaka sanya haram cikin jarinka kana juyawa bazaka ta'ba ganin riba ba, ina anfanin ciyar da iyalanka da haram? Ka sani duk fatar da haram ta gina ta to tabbas ta tabbata makamashin wutan jahannama"

Jikin kowa ne yayi sanyi shi karan kanshi me Ruwan yaji ya muzanta, kud'i ya cire ya karasa wurin Mairo dake ta jan hanci ya mika mata tare da karawa da
"Kiyi hakuri"
Kar'ba tayi tare da mikewa ta d'au gyalenta, kallon Imam me Ruwan yayi yace
"Na gode"
Dukda tabbas ze girme ma Imam ba na wasa ba sede ya san yaron Allah ya bashi abinda be bawa kowa ba.

Murmushi kawai yayi tare da wucewa kasuwa ya kar'bi mahaifinshi inda shi kuma ya koma gida, nan da nan jama'a suka fara tururuwa a gaban shagon, ana mugun son sayan abu a wurinsu Imam basu kasance masu tauye mudu ko sayar da abinda be da kyau ba sau dayawa sun gwammaci su yi asara da su sayar da abu marar kyau ba tare da sanin me ciniki ba, hakan yasa ake martaba su ake kuma sayan hatsi wurinsu, wadda hakan ke sawa sauran en kasuwan bakin ciki, dama haushin Imam d'in suke ji a duk sadda ya ga sun tauye mudu se yaje ya musu nasiha ba ruwanshi ga kwarjininshi ke hana su iya ta'buka komai ko da sun gama cikawa juna baki kuwa.

Wani abun mamaki tunda Imam ya raba fad'ar mairo da me ruwa ya kasance be da aiki se tunaninta a duk sadda ya tuna ta se yaa saki murmushi a hankali hankali ya maida hanyar da take saida abinci hanyar bi da kad'an kad'an ya fara sayan abinci kawai sbd ya ganta a duk lokacin da ze ci abinci ze tsinci kanshi da yawan kallonta ita kuwa se ta kasa natsuwa sbd kwarjininshi wasa wasa wani irin mugun shakuwa ya shiga tsakaninsu har ya juya ga soyayya daga nan se maganan aure.

Kaman ko wani aure sun fuskanci kalubale en uwanshi sun nuna basa sonta tana da rashin kunya sede abun nasu be yi wani tasiri ba sbd Malam Muhammad be d'aukeshi hujja ba, an yi aurensu inda suka tare a gidansu me d'akin ginin kasa guda biyu da kitchen da bayi, zamansu yayi kyau sossai sbd dama Allah ya san me ya had'a tana mugun son shi kuma duk masifarta bata iya mai sbd kwarjininshi da kimarshi da ake gani, a haka suka haifi yara mata hud'u Asma'u wadda yayiwa kanwarshi da yake mugun ji da ita, itama tayi aure a Magashi d'in se Aisha mahaifiyarshi..

Hasiya da Zuwaira suka biyo baya kan Muhammad(mahaifin Abrar) se Almustapha da Murtala, kab cikin yaran ba kaman Muhammad shi ne ya d'auko Imam sak karatun addini har yafi mahaifinshi musamman qur'ani, shine kuma yana girma ya kar'bewa mahaifin sana'a yace ya huta shi yaci gaba da juyawa dukda haddarshi da ta bunkasa yana zuwa gari gari musabaqa, da musabaqa ya ci yo kujerar hajji inda nan take ya baiwa mahaifinshi, cikin kankantar shekaru ya zamana yana cikin alqalan musabaqa na kasa sbd har representing Nigeria yake a kasashe kuma ya ci yo, kaman yadda mahaifinshi ke da albarkar kasuwanci haka shima a take a lokaci d'aya sana'ar saida hatsinsu ya bunkasa ya zama suna da shaguna sama da hud'u ya saka yaran gida suna jujjuyawa ya kuma d'aukewa gidansu komai da komai...

A lokacin ne mahaifiyarshi ta fara mishi maganar aure, ya nuna shi ba wacce yake so a ranshi amma duk abinda ta zartar shi me biyayya ne, ita ta za'ba mishi Halima kanwar matar kaninta, su ma kuma en nan magashi ne, Halima yaran nan ne masu tsananin zafi, kishi da hassada tana mugun jin zafi idan taga wani ya samu abunda bata samu ba wadda bata iya boyewa ga tsiwa, ya de yi biyayya ya aureta zamansu na daad'i sbd be ta'ba tauye mata duk wani hakki nata na matarshi ba, bayan ta haihu biyu ne ya bud'e wasu shaguna a cikin birnin kano manya ne kuma sossai yake samu so se kawai ya bar magashi yana dae zuwa ya dawo, gwargwado yana da ilimin boko iya diploma.

Almustapha dae yayi enrolling d'inshi BUK kaman yadda yake fatar Murtala ya fita Nigeria ya samu karatu, idan kaji turanci a bakin Muhammad zaka d'auka ya wuce degree a karatu ko don fita kasashe da yake kuma an yi ittifaqi da matuqar wuya ka samu me ilimin addinin da boko zata wani bashi wahala har ta d'ad'ashi da kasa, cikin tsakankanin ne aka tashi yin musabaqar qasa a Gombe.

Isanshi daidai kofar massallacin da zasu gudanar da musabaqar da karamar motanshi a lokacin, isar wata had'add'iyar mota da alokacin ake ji da ita, da kallo ya d'an bi motar kan ya sauko ganin dogari drivern wani dogari dake zaune wurin zaman banza ya sauko ya bud'e owners sit, a hankali ta sauko da hijab har kasa kafafunta sanye da safa kaman yadda fuskanta yake rufe ruf da niqab, be san me yake fusgarshi garesu ba sbd shi ba mutum bane me shiga sha'anin mutane, gani yayi ta d'an yi magana da dogarin da ya bud'e mata kan ta juya ta shiga massallacin su kuma suka tafi.

Massallacin ya shiga suka cigaba da gudanar da abubuwan da be kammallu ba har lokaci ya shiga aka fara, tun safe se bayan isha aka yi kiran Saudat Muhammad Lamido, da kallo ya bi ta tabbas itace yarinyar da dogarai suka sauke da safe, Ashe itama musabaqar zatayi, zama tayi a natse ta sa hannu ta d'age niqab d'in fuskarta sbd asthma da take dashi bazata iya doguwar karatu da abu rufe da hancinta ba, niqabin ma ba ko yaushe take iya sawa ba.

Cire niqabin da bugun zuciyarshi ya tsaya, be ta'ba ganin macen da ta shiga ranshi farat d'aya ba kaman saudat ya kasa d'auke idanunshi kanta, seda aka ta'bashi ya ja mata baki bayan ta gama bayanin Hafs zatayi izu arba'in, seda yayi gyaran murya kan ya ja mata, daga tayi bismillah zuciyarshi ya shiga bugawa sauri sauri har suka gama karatun be samu natsuwar zuciya ba, ya kuwa jinjinawa haddarta duk yadda yake hankalce da ita se da ta 'bace mai da aka tashi se 'bacewar motarsu ya gani sossai ya ji takaici.

A takaice dae a ranar da tunaninta ya kwana haka ya tashi har kwana biyu da suka yi suna musabaqa be kara ganinta ba randa za'a gama aka sanar da waenda suka ci gasar gagarumin taro sukayi wadda har sarki aka gayyata, ya tabbatar a ranar kam ze ganta hakan yasa yake ta dube dube, chan cikin tawagar sarki ya hango ta, da wata mata da alamu mahaifiyarta ce tana biye da su a baya sanye da alqayyaba kasanshi doguwar riga ne me yanayi da na sarauta kirar kasar Oman, sossai tayi kyau har suka zauna be dena kallonta ba.

Ba 'bata lokaci aka fara gudanar da taron inda aka fara da sanar da daga izu na kasa kasa ana isowa izu Arba'in kuwa aka kira sunanta, mikewa tayi ta fito ta kar'bi kyautanta a take mahaifinta ya bata kyautar umura, se murmushi take hakorin makkar ta dake sanye a hakorinta uku daga dama se kyalli yake, ta tafi sossai da hankalinshi wadda har wani abokinshi ya fahimta yace
"'Diyar sarki ce"

Jikinshi yayi sanyi sanin shi d'in ba kowan kowa bane, hakan yasa har aka watse taron be iya tunkararta ba, kujeru uku mahaifinta ya rabar a ranar hakan kad'ai ya isa sanin ita d'in ba tsararshi bace, a haka ya koma kano ya cigaba da kasuwancinshi sede a ko yaushe da tunaninta yake kwana yake tashi bayan shekara d'aya a lokacin Halima ta haifi 'yarta na uku ya saka mata suna saudat, soyayyar saudat sirrin zuciyarshi ne kila ma tayi aure sede baze ta'ba mantawa da ita ba.

A tsakankanin ya tafi musabaqar qasa again, a bauchi kaman daga sama ya ganta ta zo representing Gombe kuma full izu sittin zatayi, tana zaune cikin massallaci jikinta a sanyaye ji take kaman asthmanta ze tashi sbd yawan mutane kuma massallacin be da yalwa dama fanka da Ac ke taimakawa kawai se aka d'auke wuta, kan a kunna inji ta fara fita hayyacinta ta sa hannu a jaka tana Neman Ventolin d'inta jakar ta subuce ta fad'i kayan ciki suka watse sbd rawa da jikinta ke yi.

Kallonta da yake yawan yi yasa ya fahimci halin da take ciki tun kan a d'auke wutar ya mike ya nufota ya kusa karasawa gareta kenan aka d'auke wutar, wayanshi ya kunna tare da dukawa ya d'auko inhaler da ya gangaro kafanshi da sauri ya sa mata yana shaka mata bata san ta rike hannunshi tana kara matsawa ba, tausayi da kaunarta suka sake samun wuri a zuciyarshi, a hankali ya zame hannunshi dae dae lokacin aka kunna inji, dukawa yayi ya kwashe mata duka kayan da suka watse ya sa a jakar, komawa yayi kan table d'inshi ya d'auko ruwa ya bud'e ya mika mata.

Ta sha sossai kan ta sauke ta mika mishi se suka had'a idanu murmushi ya sakar mata itama ta d'an yi murmushi tace
"Jazakallahu khairan"
Yace
"Ameen, Allah ya qara sauki zan sa sunanki kiyi kawai ki samu kije ki huta"

Kai ta gyad'a ya kuwa sa tayi d'in, tana gamawa ta tafi a takaici taron be watse ba seda shakuwa me tsanani ta shiga tsakaninsu wani irin kulawa yake bata, tun tana jin kunya har take sakewa tayi hira dashi sossai, kan ta tafi sukayi exchanging numbers, wasa wasa wani mugun soyayya ya qullu..

Basu fi wata biyar ba yaje Gombe dukda lokacin ya bunkasa in ana kiran en kasuwa a kano dole a sako dashi sede yayi mamaki matuka kwarai na irin tarbar da ya samu daga iyayenta, babanta ya nuna be so su wani ja lokaci ana soyayya in ya shirya kawai ya turo.

Bayan komawanshi yayiwa mahaifinshi Imam magana nan suka tsara da sati biyu iyayenshi zasu tafi Gombe, sati biyu na zagayowa suka je kuwa suka dawo da dumbin arziki na irin karamcin gombawa an basu Saudat aure suka tsayar wata biyu masu zuwa, baze manta ranar da Halimatu taji zancen nan ba be kwana a gidan ba sbd gudun zuciya, mahaifiyarshi ma tace bata san zance ba ai mutanen Gombe an ce suna asirce maza su rabasu da iyayensu, ganin yadda halima ta haukace yasa ta bata hundred percent goyon baya suka ce sede a chanza sunan saudat Ashe dama buduruwashi ya sawa...

Ba don Malam Imam ba da sun tada garin magashi tsabar kumfar baki seda ya nuna musu 'bacin ranshi kuma yace sunan saudat ya zauna har abada ko da wasa yaji wani na kiranta da wani suna, yayi musu nasiha sossai sede duk be shiga ba musamman Halima idan ya zo magashi abinci wannan se de ya saya sbd Mairo bata amsa gaisuwarshi ma bare ta bashi abinci, Halima kuwa ko ruwa ne yace bani ruwa zata ce Wacce zaka aura ta kawo maka.

Baya manta wata rana....

****

*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...

*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*

*Da Kuma*

*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*

*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*

Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se a turo shedar biya ta wannan layin
09039206763
Note: Banda Recharge card.

                    🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

54K 2.9K 53
labarine akan wata yarinya RAIHANA da masoyinta SALEEM wanda yake sonta sosai itama tana sonshi amma daga baya abubuwa suka chanza sanadiyan shiganta...
766K 64K 52
α€—α€­α€―α€œα€Ία€‘α€±α€¬α€„α€Ία€’α€„α€Ία€”α€Ύα€„α€Ία€·α€™α€™α€Όα€α€„α€Ία€Έα€€α€­α€― inspireα€šα€°αα€›α€±α€Έα€‘α€¬α€Έα€žα€Šα€Ία€·boy loveα€α€α€Ήα€α€―α€α€…α€Ία€•α€―α€’α€Ία€–α€Όα€…α€Ία€žα€Šα€Ία‹ ၁၉၄၂ခုနစ်နဲ့၁၉၄၅ခုနစ်ဝန်းကျင် α€™α€Όα€”α€Ία€™α€¬α€”α€­α€―α€„α€Ία€„α€Άα€€α€­α€―α€–α€€α€Ία€†α€…α€Ία€‚α€»α€•α€”α€Ία€α€­α€―α€·α€›α€€α€Ία€…α€€α€Ία€α€²α€·α€ž...
1M 56.3K 47
α€‘α€™α€­α€”α€Ήα‚”α€…α€Šα€Ήα€Έ+α€žα€α€Όα€•α€Ήα‚α€­α€―α€Έ ( α‚α€½α€„α€Ήα€™α‚ˆα€”α€Ήα€Έα€”α€Άα‚”α€žα€¬) α€‘α€™α€­α€”α€·α€Ία€…α€Šα€Ία€Έ+α€žα€α€½α€•α€Ία€›α€­α€―α€Έ ( α€›α€Ύα€„α€Ία€™α€Ύα€―α€”α€Ία€Έα€”α€Άα€·α€žα€¬) ခြင့္ျပဳခ်က္မရပဲ α€„α€«α€·α€‘α€”α€¬α€Έα€€α€‘α€Όα€€α€Ήα€α€Όα€¬α€α€Όα€„α€Ήα€·α€™α€»α€•α€³α€”α€­α€„α€Ήα€˜α€°α€Έ α€‘α€žα€€α€Ήα€”α€²α‚”α€α‚αΆα€¬α€α€Šα€Ήα€»α€™α€²α€±α€”α€ž...