GAMON JINI

By Gureenjo6763

3.4K 87 5

Read and find out💃 More

Shafi Na Daya
Shafi Na Biyu
TALLAH
Shafi Na Hud'u
SHAFI NA BIYAR
Shafi Na Shidda
Shafi Na Bakwai
Shafi Na Takwas
Shafi Na Tara
Shafi Na Goma
Shafi Na Sha d'aya

Shafi Na Uku

253 7 0
By Gureenjo6763

⚡️*GAMON JINI*⚡️

*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*FREE PAGE THREE*

*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*

*****

Zubawa khalid lulu eyes d'inshi yayi Yana kallon shi da kyar khalid ya iya cewa
"She's unconscious again sikila ce tana bukatar jini har bag biyu"
Runtse idanunshi yayi yana jin tsantsar tausayinta a ranshi kallon khalid yayi yace

"Mu je lab"
Sanin jininshi O+ ne yasa ya furta da confidence, Khalid ya kalleshi yace
"Amma yayanmu kai jininka ya zuba be dace a...."
Shiru yayi ganin irin kallon da Abrar ke mishi be sake sauraranshi ba ya wuce, ba yadda khalid ya iya haka ya bi bayanshi....

Duk wani karfin hali nashi ya tattara yake driving d'in kaman baze kai ba, duk yadda khalid ya so ya huta bayan gama transferring jinin ya ki ko da kallonshi, Kai tsaye gida ya nufa bayan tabbatar mishi da dr Alfa yayi zatayi atleast 11 hours Bata farka ba...
Narasawa GRA ya nausa wani layi ya shiga da gidajen wujajen ma kawai abin kallo ne, a bakin wani tankamemen Iron Golden gate ya danna Horn, da sauri gate man d'in dake sanye da blue and black uniform ya leko kanshi, da gudu ya koma ya fara kiciniyar bud'e gate d'in, be kai ga gamawa ba ma Abrar ya kutsa kanshi ciki, parking lot da motocinshi ne kawai ciki ya nufa ya parker motar dukda yadda hasken fitilu ya haskake faskeken gidan tarrrr kaman rana hakan be hana shi ganin duhu duhu ba kaman ze yi passing out..

A sukwane ya nufi sashen sa bakinshi be dena kiran sunan Allah ba, dab da ze sa hannu akan kofar parlon nashi yaji muryarta runtse idanu yayi yana jan tsiririn tsaki..
"Baby Lafiya?"
Rinannun idanunshi ya watsa mata na second biyu kan ya murd'a kofan yana shirin shiga tayi saurin rike kofar tace cikin karyar da murya..

"Haba soja na, ban chanchanci haka daga gareka ba fa tunda na ji Abba babba na fad'awa hajiya yaya tahowarka nake zarya tsakanin sashenmu da sashenka duk kawai sbd na ganka wlh nayi kewarka ka tausaya min ko kalma d'aya ce naji na kyautatawa daga gareka ko zanji sanyi.."

Hannunta dake kofar kawai ya kalla cikin wata iriyar murya da ya had'u da gajiya da kuma jirin da yake ji na shirin zubar dashi yace
"Saki kofar nan"
Sanin halinshi yasa ta saki ta tabbatar tunda yace ta sake d'in In Bata sake ba ranta ne ze fi haka 'baci..

Bud'ewa yayi ya shige tana ji ya sanyawa kofar key, hawayen da ta kakaro ta share tare da murmushi se kuma ta had'e rai... a fili ta furta
"Na rantse da Allah se na d'aid'aita rayuwarka Abrar se na tabbatar ka rasa duk wani Farin ciki na duniya... ba zan yi fushi ba kuma ba zan karaya ba.. Sannu Sannu Bata hana zuwa sede a jima ba'a je ba.."

Tana kai nan ta juya ta d'auki wani tsiririn hanya me d'auke da flowers masu d'auke hankali gefe da gefe... irin girma da kawa da gidan ke dashi na tsaya kallo, daga gani babban family house ne sbd yafi karfin na mutum d'aya, sashe sashe ne had'add'u masu d'auke hankali sun yi guda 12 a tsare a kuma kawace, sam ba'a wargaje suke ba, akwai tarin parking lots masu d'auke da motoci masu d'auke hankali sbd babu kananun motoci a wurin sede Tabbas na Abrar yafi kowanne d'auke hankali motoci ne guda Biyar a cikin parking lot d'in daga Lexus 2021 model, McLaren MP4-12C, Audi A8, Jaguar XJ, Range Rover Apart from BMW da ya shigo dashi...

Da sauri na dakata da bin motocin da suka kawata akalla parking lot shidda d'in dake gidan, nan na bi bayan buduruwar da ban san sunanta ba, Sanye take da wani had'add'en material golden d'inkin doguwar riga me yanayi da wrap gown se black gyale da ta yafa, Don kyau kyakyawa ce, gata da tsawo da diri Masha Allah, seda ta wuce akalla parts hud'u ko tsoron daren bata ji ko Don sbd gidan be da maraba da rana ne sbd yawan kwaiyaye da hasken wutan lantarki ne ban Sani ba, ta isa wani part kofar ta tura ta shige...

Karo taci da tamkamemen parlor me d'auke da royals kujeru masu d'auke hankali wucewa tayi ta dining area ta fita wani corridor dake jere da kofofi biyar, na biyu daga damanta ta shige inda tayi arba da wata mata Suna had'a ido ta girgiza kai tace

"Yau ma ba Nasara ko Nadra?"
Zubewa tayi bakin gadon tana dafe kai tace
"Hajiya Yaya ban san yadda zan yi da Abrar ba, ba zan ta'ba karaya ba har se na cimma burina na tarwatsa mishi rayuwa... Na tsaneshi tsanar da ban ta'ba yiwa kowa irinshi ba.."

Murmushi tayi tace
"Sannu Sannu dae, na gayamiki Ai Nadra... Asiri uwarshi take kema kin san wad'an da suka fito daga gidan malaman nan se a hankali, Na tsanesu fiye da yadda kike ji Kin tsanesu Nadra, Ina zaman lafiya da mijina ta zo ta tarwatsamin gida ta aure min miji, ta fara haihuwa kafin Ni ta haifa mishi yaran maza ta kwace arziki da soyayyarshi babu wadda yake kauna nan duniya Apart from Hajiya babba se ita... wannan hujja be kai in dasa karan tsana a kanta ba? Kina gani yadda yake hidima da tada hankali idan aka ce munafukin Asthma da yaki kasheta ya tashi..."

Hawaye ya zubowa Nadra tace
"Amma dae Hajiya Yaya kin san be kai ya Rai ba ko..? Ran ma har na Mutum biyu..."

Kuka ta fashe dashi, kusa da ita Hajiya Yaya ta matsa ta dafa kafad'arta tace
"Karki damu Zamu yi Nasara a kansu ko da buzu suke yawo, kaman yadda na fad'a ne Sannu-Sannu bata hana zuwa.."
Kiran sallar Asuba ne ya dakatar dasu, wannan daré na d'aya daga cikin Sleepless nights da suke samu sbd hassada da kyashin wasu, sun d'aurawa kansu tsanar waenda basu ma san suna yi ba...
A maimakon su tashi su gabatar da sallah se Hajiya Yaya ta kwanta tana cewa
"Ni kam bari In runtse kad'an ko zuwa Goma ne na mika sallar.."

Itama Nadra mikewa tayi ta fice zuwa d'akinta dake facing na Hajiya yayar...

Duk da yadda yake jin rashin karfi da bacci dake kwasar shi be kwanta ba, wanka yayi tare da d'auro Alwala, yana shiryawa ne yaji ana kiran sallar Asuba baze iya fita ba so jallabiya kawai ya zura ya taka a natse zuwa inda ya ware musamman sbd sallarshi kan lallausar farar darduman ya tsaya ya tada sallah, seda ya yi raka'atainil fajir kan ya mika Sallar Asuba d'inshi ko Azkar be iya natsuwa yayi ba ya mike ya cire jallabiyar, ya nufi tamfatsetsen gadon da tsarinshi da yanayinshi kawai abin Kallo ne, tattausan burgo ya ja zuwa kanshi bayan ya kara karfin Ac dama ko da ya shigo be kunna wuta ba sbd tabbas idan ya kunna baze iya baccin yadda ya dace ba yanzu... be yi kyakyawar mintuna biyar ba bacci ya kwasheshi...

Da Misalin karfe Goma sha biyu ya fito a shirye cikin yadi me taushi Ash simple d'inki irin na maza da yayi mugun amsarshi, fuskan nan kaman kullum ba wani fara'ar kirki sede bakinsa be dena motsinshi ba, a natse yake tafiya daga nesa kwarjini da haibarshi na fita kanshi a kasa ya nufi sashen mahaifinsa yau Saturday a tsarin gidan nasu duk weekend mazan gidan basa zuwa ko Ina idan ba ya kama tilas ba ko kuma aikin ka na dole ne zuwa weekend d'in..

Kusan iyaye mazan basa wuce sashen Abbun ko sashen Hajiya babba Baya son zuwa sashen sam sbd basa wanyewa da daad'i da ita, a cewarshi ta cika hayaniya, A bakin kofan suka kusa cin karo da Jabir, da sauri ya matsa gefe yana cewa
"Ina yini yayanmu an zo Lafiya?"
Kallo d'aya ya mishi yace
"Lafiya"

Be jira wani gaisuwar ba kaman yadda iya amsa gaisuwar kenan, parlorn ya tura da sallama a bakinshi amsawa sukayi tare da zuba mishi idanu dukkansu, tsiririn tsaki ya sake yana sake had'e rai sbd ganin Hajiya babba a parlorn, kan one seater ya zauna, yana kallon mahaifinshi yace
"Abbu mun sameku lafiya?"

Abbu be kai ga amsawa ba Hajiya babba ta cha'be..
"Auu rashin Arziki da ta ido da kakewa matan Babanka ne yanzu ya tsallako kansu ya dawo kaina? Kai Tuzurun banza tuzurun wofi ka sani fa ni ba matar uba bañe ga mahaifinka a cikina na haifesa bare kace zaka ke wani ciccimin magani kana sha min kamshi, bazaka zo ka sameni a wuri cikin gidan nan ka fara gaida ubanka ba ban lamuntar iskancinka kaman Su yawuro(Hajiya Yaya)"

Ba tare da ya kalleta ko sau d'aya ba yace
"Barka da rana.."
"Uwarka ne dake kwance a gadon asibiti zaka yiwa wannan gaisuwar rashin kunyar ba ni ba, ja'iri kawai tuzuru rike kayanka bana so.."
Runtse idanunshi yayi yana Jin zafin sako Amah da tayi, da ba don ya san ran Abbunshi na iya 'baci ba da ya tashi ya fice a parlorn, tabbas da ya san tana nan da be shigo ba ma...

Mikewa tayi ta ka'be zaninta tare da rike sandarta ta nufi kofa tana me ci gaba da mita da zagin shi da mahaifiyarsu da tun aurota ta tsaneta ba gaira ba dalili, bayan fitanta Dad (Al-Mustapha Iman Magashi) wadda shi ke bi ma Abbu yace
"Abrar ka dinga hakuri da Hajiya kuma ka samu ka fidda mata kayi aure ko wani fad'an ze ragu ba wai mun zuba maka ido bane duk tsawon lokacin nan sbd bamu isa da kai ba, mun kyaleka ne sbd mu ma magabatanmu basu cika takura mana akan abinda yake ra'ayin mu ba but yanzu enough is enough ka fidda mace ko mu za'ba maka wacce muka ga ta mana"

Uncle Maraq da suka fi shiri da Abrar d'in wadda be girme mishi har chan ba hakan ya sa suke shiri sossai tun tashinsa kusan shi kad'ai yake fahimtar yaren Abrar a gidan bayan Amah, shine Auta a wurin Hajiya babba, bayan Dad akwai Mata hud'u kan shi d'in...

"In Shaa Allahu yaya mun gode"
Ya amsawa Dad d'in da hakan, Abbu yace
"Shi Abrar d'in be da baki ne da kullum kake ara mishi baki ka ci albasa Murtala?"
Har yanzu be d'ago ba ko wuyanshi baya mishi ciwo ne oho ya saba kai a kasa kullum kaman Sabuwar Amarya, cikin hargitsatsiyar murya yace
"Ohk Dad."

Mikewa yayi ze fita Abbu yace
"Abrar...!"
Dakatawa yayi tare da juyowa ya kallo mahaifin nashi, a idanunshi ya fahimci manufar kiran dawowa yayi ya zauna yace
"Mun sameku lafiya?"
Yin maganar yake kaman an mishi dole..

"Lafiya kalau ya wurin aikin naku?"
Yace
"Alhamdulillah"
"Dad mun sameku lafiya?"
Shima irin tambayar da Abbu ya mishi yayi same amsa kuwa ya bayar, Uncle Maraq ne ma ya iya er doguwar gaisuwa dashi, ya mike kenan Abdulkadir ya shigo...

Gaisheshi yayi ya amsa yana sauraron sakon da yake bawa Abbu na ya dawo da Amah d'in ya baro ta da khalid da jabir shine ya taho ya gayamishi, fita yayi ya nufi sashen mahaifiyar tashi...
Tun daga kan varender d'in sashen zaka fara jin kamshi me sanyi na turaren wuta er gaske, wannan ya zama kaman permanent kamshi to her side yadda Bata rabo dashi har ya kama gidan nata...

Ciki ciki yayi sallama Amah dake zaune kan kujera ta amsa, tana kallonshi kallo d'aya ta mishi ta san a hargitse yake sede natsuwarshi sam
Baze bari ya nuna ba, ganganta ya zo ya zauna tare da kakalo murmushi yace
"Amah ya jikin?"
Tace
"Na ji sauki Lamido, ya naka? Se kuma ka shiga hidimar bada jini alhali kaima ka zubda dayawa? Yanzu na san baka ci wani abu ba bari In tashi In Samar maka..."

Khalid dake shigowa biye dashi matarshi ce Aisha sanye da lafaya hannunta rike da basket yace
"Amah ki huta na sa Aisha ta had'amishi tun kan mu taho, ga magunguna da ya kamata ya sha ma..."

Harara ya watsawa khalid d'in Shi kuwa ya kunshe dariya sbd ya san yadda ya tsani magani kuma Tunda suka shiga hannun Amah se sun kare tas zata kyaleshi, Amsa gaisuwar Aisha yayi ba tare da ya kalleta ba, Amah na mata Sannu ta karasa da kwanukan dining, Bata kai ga zama ba Abdulkadir da khadija suka shigo itama rike da basket bayan ta gaida Amah da jiki ta gaida Abrar ta karasa ta ajiye kan dining, daga ita har Aisha kasa suka zauna dukda Amah Bata son hakan sede sun kasa denawa...

Jabir ne ya dawo ranshi ba daad'i ya samu wuri ya zauna, Khalid yace
"Kai kuma Lafiya? Kai kichin kichin da rai?"
Kan ya amsa Sadiq da Maher suka shigo suna rige rigen isa ga Amah sede  tozalin da sukayi da Abrar yasa suka wani jan birki suna zazzare ido, dariya Khalid da Abdulkadir suke yi, Amah tace
"Auta na zo"
Karasowa yayi ya zauna gefe yana rungumeta yace
"Welcome home Amah, please karki sake ciwo..."
Murmushi tayi tace
"Ai ciwo na Allah ne.."
daga nan ta amsa gaisuwar sadiq tana kare mishi kallo shine ya fita d'an rawan kai a cikin yaranta dukda yanzu yake 20 sede idanunta ko yaya ya matsa a kanshi se kaga changi a d'abi'arshi...

Yana Sosa kai ya gaidata kan ya gaida Abrar shima yana kallonshi ya amsa, daga nan Amah ta sa duk suka hau dining, wasu yanzu zasuyi breakfast yayinda wasu kuma lunch kenan, bud'e kulolin Amah da kanta tayi ta sawa d'an nata
Potato salad, da shinkafa kad'an se kidney sauce...

Lipton ta had'a mishi sanin baya ta'ba cin abinci be sha lipton ba kaman ka'ida ne a rayuwarshi, Maher ne ya d'auka ya ajiye mishi, kowa yayi serving abinda ze iya ci, Don Hindu ma er aikin Amah d'in wadda da chan tun Abrar na karami mahaifiyarta ke mata aiki kusan tare suka haifi sadiq da Hindu, Amah tana da cikin Maher dake 13 yrs yanzu iyayenta sukayi hatsari suka rasu a hanyar zuwa kauye harda en uwanta biyu ita kad'ai ta tsira dama tun kan rasuwan mahaifiyar ta kan zo gidan ta tayata aiki yarinya ce me kazar kazar ga ladabi, hakan yasa Amah ta ci gaba da riketa kaman 'ya ta d'auke ta dukda Aikatau d'in take yi...

Kan tahowarsu daga asibiti Amah ta sa Abdulkadir ya kaita ta zauna da Amatullah bayan ta gama girki da gyare sashen...

Yana shirin sa Abinci a bakinshi ya dakata chak tare da kallon Khalid da lumsassun idanunshi yace
"Amatullah...."
Se yayi Shiru tsab sun san tsarin maganarshi In yayi d'aya kan yayi na biyu se ran kowa ya kusa 'baci, Khalid be jira ya lalu'bo abinda ze fad'a d'in ba yace
"Zuwa 1pm Tests d'in da dr Alpha ya mata zasu fito anan zamu san matsalarta sbd dukda karfin Allurar da aka mata tayi ta firgita da surutai musamman kan gari yayi haske d'in nan kaman ta samu matsala a kwakwalwa ne..."

"Waye kuma da matsala a kwakwalwa...?"
Lumshe idanu Abrar yayi yana jin fitan abincin daga ranshi... ita kuma wa ya gayyace ta? Me nata?....

****

*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...

*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*

*Da Kuma*

*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*

*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*

Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
    Se a turo shedar biya ta wannan layin
09039206763
Note: Banda Recharge card.

🖤Gureenjoh🖤

Continue Reading

You'll Also Like

4.6M 522K 58
{Both Zg&Uni} အသေမခွီးရတောင် တစ်ချက်တော့ပြုံးမိဖို့ အာမခံပါတယ် ..💚 Start - { 11,8,2020 } End - { 25,11,2020 } အေသမခြီးရေတာင္ တစ္ခ်က္ေတာ့ျပဳံးမိဖို႔...
41.4K 1.6K 36
Amma kin san akwai karatu ko ko kyalkyalen banza kike so Ni de aa wallahi bazan iya ba Ta mike Ya biyo ta *DEAR* ta juyo yaya na gaji tafiya xan y...
643K 60.8K 88
ရုန်းမထွက်ချင်မိတဲ့ မျက်ဝန်းသေတွေ၊ လှုပ်ရုံမျှပြောသည့် နီဆွေးဆွေးနှုတ်ခမ်းလေးနှင့်အတူ ထွက်ပေါ်လာသော နွေးထွေးနူးညံ့သံ။ မမလွမ်းကို တွယ်တာမိတဲ့ခဏတာမှာ ဖ...
272K 6.5K 74
တောင်ပေါ်သားနဲ့ မြေပြန့်သူ ဇာတ်လမ်းလေးပါရှင့်