KALLABI..! A tsakanin Rawuna...

By Mai_Dambu

37.7K 9.5K 1.7K

The gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to wi... More

Hello's my Fanmily
BABI NA DAYA
BABI NA BIYU
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA
BABI NA GOMA
BABI NA SHA ƊAYA
BABI NA SHA BIYU
BABI NA SHA UKU
BABI NA SHA HUDU
BABI NA SHA BIYAR
BABI NA SHA SHIDA
BABI NA SHA BAKWAI
BABI NA SHA TAKWAS
BABI NA SHA TARA
BABI NA ASHIRIN CIF
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA UKU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
BABI NA ASHIRIN DA TARA
BABI NA TALATIN CIF
BABI NA TALATIN DA DAYA
BABI NA TALATIN DA BIYU
BABI NA TALATIN DA UKU
BABI NA TALATIN DA HUƊU
BABI NA TALATIN DA BIYAR
BABI NA TALATIN DA SHIDA
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
BABI NA TALATIN DA TAKWAS
BABI NA TALATIN DA TARA
BABI NA ARBA'IN CIF
BABI ARBA'IN DA DAYA
BABI NA ARBA'IN DA BIYU
BABI NA ARBA'IN DA UKU
BABI NA ARBA'IN DA HUƊU
BABI NA ARBA'IN DA BIYAR
BABI NA ARBA'IN DA SHIDA
BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS
BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI
BABI NA ARBA'IN DA TARA
BABI NA HAMSIN CIF
BABI NA HAMSIN DA DAYA
BABI NA HAMSIN DA BIYU
BABI NA HAMSIN DA UKU
BABI NA HAMSIN DA HUƊU
BABI NA HAMSIN DA BIYAR
BABI NA HAMSIN DA SHIDA
BABI NA HAMSIN DA BAKWAI
BABI NA HAMSIN DA TAKWAS
BABI NA HAMSIN DA TARA
BABI NA SITTIN CIF
BABI NA SITTIN DA DAYA
BABI NA SITTIN DA BIYU
BABI NA SITTIN DA UKU
BABI NA SITTIN DA HUƊU
BABI NA SITTIN DA BIYAR
BABI NA SITTIN DA SHIDA
BABI NA SITTIN DA BAKWAI
BABI NA SITTIN DA TAKWAS
BABI NA SITTIN DA TARA
BABI NA SABA'IN CIF
BABI NA SABA'IN DA DAYA
BABI NA SABA'IN DA BIYU
BABI NA SABA'IN DA UKU
BABI NA SABA'IN DA HUDU
BABI NA SABA'IN DA BIYAR
BABI NA SABA'IN DA SHIDA
BABI NA SABA'IN DA BAKWAI

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

379 144 16
By Mai_Dambu

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

*Mun gode sosai da addu'ar ku Allah ya bar zumuncin*

Inna Marwa bata yarda zai iya daina zuwa fada ba, sai da aka kawo mata karan shi, kamar tayi ihu a nan ne tasa aka kira shi tayi mishi fada, tana kawo zancen Bingel ya kalle ta, sannan ta ce mata.
"Inna Marwa kyamarta nake ji, wallahi ba zan iya mu'amala da baiwa ba, kazamtar ta nake gani don Allah kar ki takura min"
Shiru tayi tana kallon shi, jinjina kai tayi sannan ta ce ya tafi.
Bata wani Jima sosai ba, ta koma sokkoto. A wannan lokacin ne wasu abubuwan marasa dadi suka fara kunno kai, tsakanin yan majalisar shi, akan na lallai sai dai ya san yadda zai yi da aminatu ko ya sauka akan kujeran da yake, bai yi musu ba, suka ga ya fara kokarin mikewa suka ce sun dakatar da shi, amma zasu kai hari masarautan Gombe.

Ya zata wasa suke mishi sai da takai ta kawo wata ranar laraba ta fito taga ana shirin yaki.
A lokacin labarin ya isa ga Fulani Aminatu, za a yaki masarautan ta domin sarki yaki mu'amala kowacce mace sai ita, ba mamakin anyi mishi asiri ne tunda sun san cewa bata haihuwa. Fitowa tayi ta nufi shashinsa, yana sanye da kayan yaƙi.
"Ina zaka? Wannan ba kome bane idan ka dauki shawara na matsalar zata wuce, na had'a ka da Allah ka amshi Yahanasu. Wallahi bana jin kome akan ta, nayi imani da Allah ba zai tab'a wulakanta ni ba"
A fusace ya juyo tare da wani matse ta.
"Haka kika son nayi mata?" Ya fada da mugun karfi.
"Ya xan yi? Kana zaton zasu kyale koda yaro me shan mama ne a cikin masarautan ne? Ina son ka amma yakin da za ayi da ahalina ba abu ne mai sauki ba, don Allah ka yafawa zuciyar ka ruwan sanyi. Babu abinda zata dauka a jikin ka" ture ta yayi domin ran shi ya gama ɓaci, ya nuna mata ta fita. Gidan galadima ta nufa wannan shine karon farko a rayuwarta ta tab'a fita. Tana shiga cikin gidan yana tsaye da matan shi, ta zube akan gwiwar ta.
"Idan nice bana Haihuwa zan iya hakuri da duk bukatar ku, amma tab'a ahalina shine abinda ba zan iya dauke kai akan shi ba, don Allah ka roke shi ya amshi ya hannu'" babu d'igon kwalla a idanun ta, sai ma wani irin hakuri da juriyar da Allah ya daura mata a ranar.
Shigowa yayi ya kai hannun shi dukkan biyu ya d'ago ta. Sai lokacin ta fashe da kuka, kamar ranta zai fita.
"Don Allah Baffa'm kayi yadda suke bukata wallahi idan ta kama ka kara aure ne na yarda"
Bakin shi ya kai kunnen ta.
"Karki damu na amince na karɓe ta" kuka take kamar ranta zai fita, Abinda ya faru bayan fitar ta. Nufi gidan Chiroma dama abinda yake bukata kenan, ya cusa tsoro a zuciyar Aminatu, yadda zata d'agawa Sarki Bello hankali shi ya amince da bukatar shi. Ya kuma tako yazo har gidan ya nime Alfarmar akan lallai ya amince da Yahanasu.
Lokacin da ya shiga gidan babu kayan sarauta daga shi sai kayan shi. Na zaman rubutu ya shiga cikin gidan, kallon Chiroma yayi, sake bai shiga da fushi ba.
_(Note asalin damuwar da yake cikin labarin da wasu kananan fitintunu wallahi ya faru a daular Gobir, labarin ya faru da gaske akan sha'anin mulkin su, don haka ba wai dan yana gidan sarauta ba, a'a da wannan yanayin aka ragewa daular karfin mulkin ta a nahiyar Afirka baki daya. muje zuwa)_

Cikin sanyin murya ya ce mishi.
"Ban san me natsare maka ba, bayan haka bani da wata manufa da kai, Chiroma nayi Imani da Allah kana barci da zuciyar ka, domin idanun ka basu barci. Ban zo dan na gaya maka zan amshi kwarkwarah ba, naso da naga Aminatu anan sai na yanke kan ka daga jikin ka zai Allah ya kwace ka, tsohon kawai
"
Dariya yayi sannan ya ce mishi.
"Ba zan yi fada da kai ba, amma nasan lokaci na zuba da zan yi fada da kai" bai saurare shi ba, ya bar zauren.
Gidan galadima ya nufa yaji yadda take rokon kar a tab'a ahalinta. Wani irin tsanar Bingel da yaji da shi ya kudiri Aniyar sai ya saka mata wani irin tsoron shi. Dan haka yana mai da Fulani Aminatu sashin Taz ya gayawa Innayoh bukatar shi, bata yi musu ba ta saka aka shirya Bingel aka kaita wurin shi. Dake ran shi ta gama ɓaci gashi dai an janye yakin baki daya dan haka cikin fushi da fusata, ya daure ta, sai da ya gana mata azaba bayan ya rufe mata bakin ta, ba duka ba zagi daura ta yayi ya a daure na tsawon kwana biyu cur ba ruwa ba abinci. A ranar na ukun ne bayan ya dawo fada, ya kunce ta ya zuba mata abinci a ƙasa, haka yayi ta cin abincin tana kuka. Wani irin kyamarta yake ji shi yasa ya gaza kome da ita, tana gama cin abincin, ya farmata mata kamar tsohon zaki babu d'igon imani kamar yadda ta saka iyayen ta da matar shi kuka haka yake far mata, yana gaya mata magana masu zafi tare da alwadar din ta, duk wani cin zarafin da ya dace ayiwa mutum ya mata. Sai da ya kai wani lokaci yana mata wani mugun aikin da bata san tana duniya ba ko tana lahira bane, dama sabida haka ya sha maganin kara kuzari da lafiyar shi ma ya aka kare balle ya kara da wanda ya kara haukata shi.

Sai da ya shafe kwana goma tana dakin ban da azaba babu abinda yake mata dan ko tafiya bata yi sai rarrafe, a wulakance ya kira Innayoh ya ce mata.
"Matukar kika mata wani abu sai na baki mamaki,a kaita shashin bayi marasa gata da galihu wanda suke cikin masifa da tsangwama ta zauna a can bata cancanci zaman fada ba, domin kazamtar mace ce da tayi cuɗanya da wasu mazan bana son ganin ta"
"An gama ranka shi dade" daga nan aka wuce da Bingel, zuciya irin ta uwa yasa Innayoh ta saka wasu bayi suka kula da ita, domin kowa sai da yasan sarki ya tsani Bingel. Sai da ya dauki tsawon sati Daya bai leka waje ba, sabida tashin hankali, kuma ya hana kowa zuwa gare shi.
"Innayoh haka zan cigaba da ganin shi a cikin kunci, zanje koda zai Kore ni ne" ta fada tana bar bangaren ta, nufar bangaren shi tayi ta samu kofar shi a dan bude, shiga tayi tana tafiya a hankali har cikin dakin ta same shi zaune ya bata shiru gwanin ban tausayi. Zuwa tayi ta zauna a gaban shi.
"Baffa'm" kamar jiran ta, yake ya riko hannun ta, ya damke sosai yana kallon ta da rinannnun idanun shi ya fada a sanyayye ya ce.
"Balagaza ce, shashasha ce bata bata rike kanta ba, ta lalata kanta kafin zuwan ta gare ni" rufe mishi baki tayi tana girgiza mishi kai,. mikewa tayi ta rungume shi. Hawaye na zuba mata, bata hana shi kanta ba, bata kuma kokarin tuno mishi kome ba, amma tabbas ta yarda babu wata mace bayan ita a rayuwar shi, domin yadda ta susuce mata kamar bai yi mualama da wata mace ba, domin baki daya ta samu gyaran jiki yadda ta dace haka suka mance da kowa.

Wani irin riko ya kaiwa K'ugunta, dama mazan gobirawa Allah yayi musu Baiwar kula da mace a gado, idan kaga Aminatu da zungurerren baffa'm din ta ita yar mitsitsiya shi kuwa kamar tsohon bishiyar kuka, ba tare da tuna kankantar shekarun ta ba, abinda ya rasa a can ya ke samu anan, itama tai wani irin kewar shi, ko tari bata yi ba ya cigaba da zuba mata aikin arziki, a yadda yake mata ta fahimci yana cikin matsanancin kewar ta da bukatar ta.
"Aminatu me aka yi da macen da ta sayar da kanta domin biyan buƙatar kanta?" Girgiza kai tayi dan kamar huce haushinsa yake a kanta.
"Duk rintsi duk wuya, nan nawa ne" ya fada kamar me fisgar numfashi, ya cigaba da abinda yake.
"Daga ranar da na fahimci ba ni daya nake tare da mace ba, har duniya ta tashi bana tare da ita don Allah karki hada ni da kowa wallahi idan kika ce baki son zamn nan zan ajiye kome da kowa mu tafi mu rayu dake" ya fada lokacin da ya haɗa fuskar shi da na ta, a hankali ya sake mata wani irin kuka, kamar ba shi ba. Fadar abinda ake mishi yake yana kuka yana gaya mata yadda zuciyar shi take ji, gaya mata yake, ita kanta kuka take Sabida damuwar shi damuwarta ce, farin cikin shi farin cikin ta ne, haka suka makelewa juna ya kalli yadda take kuka ya ce mata.
"Aminatu! Makiya sun saka ni a gaba! Ban san abin yi ba, na rasa me zan musu"
"Ka cigaba da gayawa Allah kukan ka zai share maka hawayen ka" ta fada cikin matsanancin kuka, rungume ta yayi yana jin wani sabon kaunarta yana huda zuciyar shi tana shiga duk wani lungu da sako na ruhin shi.

Sai da ya huce kwanakin shi da baya tare da ita, lokacin tayi wani irin sanyi suka shiga wanka tare, har lokacin tana kwance a jikin shi, shi kuma yana shafa bayan ta, bayan ya sheka musu ruwa. Yadda ya ganta tayi wani luf bai san lokacin da ya daura hannun shi akan Zariyar shi ba, ya shiga tab'a ta. Bai ki ya kare rayuwar shi a tare da ita ba, ba zai tab'a gajiya da niman hutu ba, yana mugun kaunarta.
*
A bangaren Bingel kuwa ba karamin jinya ta sha ba, karshe bayin da suke wurin wani wanda ya damu da ita sai Innayoh, ranar karshe da zata daina zuwa wurin ta, ta ce mata.
"Ban san meye a kasar zuciyar ki ba, Aminatu ta gaya min gaskiya haduwar ku, amma ina had'a ki da Allah ki tsaya ina inda Mai Martaba ya ajiye ki, domin idan kika kuskura kika shigo a karo na biyu artabun ba zai mana kyau ba"
"Innayoh! Gargadi kike min ne? Tsoro kike ji kar sarki Bello ya mai da ita bora?" Dariya Innayoh tayi sannan ta ce mata.
"Ai Aminatu ba zata tab'a zama bora ba" , kallon inda take a wulakance Innayoh tayi sannan ta ce mata.
"Ina da yakinin daren da Mai Martaba ya kwana dake ba mamaki rijiyar abu de take, tunda gashi a madadin samun yanci sai aka bige da shashi mafi muni a masarauta. Idan har nayi zurfin nazari fanko ya tarad, ina kuma yar da aka haife ta a cikin mutunci da kamala cikin tattali da gata, ina kuma wacce ta tsare wa kaddaran ta hau na a mizanin hankali mana?"
"Innayoh" ta kira sunan Innayoh da karfi tare da yin kan Innayoh, wasu kartin dogarai suka shigo dakin.
"Ku kyale ta, ta ci albarkacin mai Martaba, daga yau ki kame kanki idan ba haka ba tabbas zaki ga abinda zai biyo baya"

Fita Innayoh tayi bata kuma bin ta kanta ba, haka rayuwa ta cigaba da tafiya har tsawon wata guda, sarki Bello da kan shi ta bada Umarnin a dauki Bingel a mai da ita wurin iyayen ta, a aurar da ita.

A gefe guda kuwa caa yan majalisar shi suka mishi. Yadda ya Haukace musu yasa baki daya suka shiga hankalin su dan da bai da fada babu zafi amma tun daga ranar da yayi tarayya da Bingel ya zama mafadacin dole, domin haushin kowa yake ji musamman su da suka saka shi ya zauna da ita, ya tsani yarinya sosai.
Shigowar Sarkin gida ya tafi wurin Sarkin fada ya gaya mishi sakon Innayoh. Shi kuma ya kalli Mai Martaba ya tako har kusa ea kunnen shi ya gaya mishi abinda Sarkin gida ya gaya mishi. Cak yayi numfashin sa yana barazanar daukewa, baki daya yaji duniyar ta tsaya mishi a fusace ya ce mishi.....🙄😹🤣😂
_

PAGE BIYU ZAN BAKU YAU AMMA FA WALLAHI SAI NAGA VOTE AND COMMENTS IDAN BABU MU JONE GOBE INSHA ALLAH_
#Mai_Dambu

Continue Reading

You'll Also Like

269K 18.1K 155
The Divine woman Draupadi was born as the eternal consort of Panadavas. But we always fail to treasure things which we get easily. Same happened with...
14.8K 1.2K 34
Disclaimer: this is a work of fiction. Every characters (beside my OCs) belongs to Maharishi Ved Vyas. "RAGHUKUL REET SADA CHALI AAYI, PRAN JAYE PAR...
A Secret Ambition By Laura

Historical Fiction

122K 11K 33
Before giving herself over the the inevitable marriage mart that is the London Season, Lily Beresford is determined to make a clandestine foray out i...
My Sin By XxMeixiangxX

Historical Fiction

1.7M 69K 65
Liu Quiaqio, the Empress of the Jin Dynasty has given his heart, soul, and body to the emperor, he loved him to the point it exhausted him, but the c...