35&36

152 4 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 35⏩36




Tunda muka koma makaranta muka sa karatu a gaba ba kama hannun yaro, dan nima na ture komai  na jindadin duniya nasa karatuna gaba, dan yanzun  an sake man course an maidoni microbiology 100 level, tabbas hakan ya sosa man zuciya amman na barma Allah kuma nasa a raina kaddara rata ce tazo man haka, kuma na manta da baya nasa gaba ina rokan Allah ya bani sa'a da nasara a gabana albarkacin Annabi Muhammad S. A. W, bani da ƙawa sannan kuma bani kula kowa duk da samarin suna yi man magana amman bani kulasu dan na barma Allah zaɓi kuma ina addu'a.

watarana  ina zaune Dejja ta shigo tace "Aunty Auta yaushe zamuje kasuwa wai? Naga kayan miyarmu duk sun kare amman baki ce komai ba." kallonta nayi sannnan nace "wallahi Dejja ina sane, amman bansan shiga cikin gari dan ni tsoran mutanen kano nikeyi." Murmushi tayi sannan tace "Allah yana tare dake Aunty Auta dan Allah tunda yau bamu da komai tashi mu tafi mu je kasuwa pls." kallonta nayi sannan nace "amman Dejja baki gani... "Haba Aunty Auta dan Allah ki karkiyi gardama ki tashi mu tafi ko mundawo." ba dan naso ba na tashi mu duka ba wata kwaliya mukayi ba poder ce kawai muka shafa sai dan lipstick sannan muka saka dogayen ruguna muka mukayi rolling muka tafi kasuwa.

Tunda muka fito gabana yake faduwa, tun ina hakuri har yakai da na kasa nayi, sai da nayi ma Dejja magana nace "wallahi Dejja bakiji yanda gabana yake faduwa ba, ji nike kamar wani abu yana shirin faruwa dani fa." Murmushi tayi sannan tace "kiyi addu'a Aunty kuma insha Allah ba abunda zai faru dake sai alkhari.".... "Allah yasa." nace mata sannan muka cigaba da labari, ji nayi tace "wai kinsan Dr Umar yana sonki kuwa."? Sosai na tsorata kuma gabana ya kara faduwa sosai cikin tsoro nace mata "na shiga ukuna, wane Dr Umar din."!? Lura da yanayin da nike yasa tayi dariya sannan tace "haba Dan Allah Aunty Auta sai kace wanda aka gaya ma sakon mutuwa, Dr Umar na depertment dinku shi ya gayama registra yana sonki kuma aurenki yake so yayi shine ya gaya mashi abunda ya faru dake, amman yace yaji a haka yake sonki, shine jiya da yazo wajena yake gaya man wai Dr Umar ya matsa mashi shidai zai bashi number dinki, amman nace kina da wanda zaki aura sai yace ai matar mutum kabarinsa idan Allah yasa Dr ne ba yanda za'ayi kinji yanda mukayi." numfashi na sauke sannan nace "ya kike ganin za'ayi kenan Dejja."?  Ceman tayi "ki bashi dama kawai, mu cigaba da addu'a Allah ya tabbatar da abunda yafi zama alkhari.".... "Amin ya Allah." daga nan bance komai ba, shiru mu duka mukayi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarshi har muka iso kasuwa.

Tunda muka iso kasuwa nike jin kaina wata iri, dan ba abunda yake man dadi amman kawai tafiya nike haka muka kama shiga shaguna muna sayaiya amman da an kalleni ansan ina cikin damuwa sosai, kuma ban san abunda yake damuna ba, addu'a kawai na cigaba da yi dan itace tafi dacewa dani a wannan lokacin da nike ganin shine daidai.

Har mun gama yin abunda ya kawo mu Dejja tace ita dole sai na raka ta wani shago ta saya turare naso nayi mata gardama amman kuma sai na hakura nace mata mu tafi, tafiya mukayi mai dan nisa kadan sannan muka iso shagon muka shiga muka fara tambayar turaren da ya kawo mu,  ji nayi ance "Alhmdulillahi Khadija ashe zan kara ganinki a rayuwata? Allah nagode maka da ka maido man da Khadija a lokacin da nike bukatar a tare dani." a tare muka jiyo nida Dejja kayan hannun na saki ina kallonshi na kasa motsin komai, cikin fushi da zafin nama Dejja ta ture ta maidani bayanta sannna ta kalleshi tace....


*wata sabuwa kuma shin waye Auta ta gani a kasuwa, sannan ga kuma Dr Umar nan ya kutso kai a rayuwar Auta 🥴*


Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now