7&8

300 4 0
                                    

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
    _na ɓata rayuwata😭_

      Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD

*😂😂😂wai akace soyayar shan minti ake cewa ba soyayyyar minti ba, nidai tom na sake mashi suna🤪*

*Wannan page din nakine Auntyna Binta Umar Abbale ta  Allah ya kara daukaka da girma gami da  lafiya mai amfani Amin*

*Gaisuwa ban girma gareki Zainab Abu-Kareem My Zee ina maki fatan alkhairy ta wajena*

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 7⏩8

Tunda su Yaya Jamilu suka shiga gida suka tadda Mama bata dawo ba, zaunawa sukayi zaman jiran ta kowa ya shiru da abunda yake sakawa a zuciyarshi.

Ita ko Mama tana zuwa ta tadda Alhaji Salahu bayan sun zauna ta fara magana tana cewa. "Daman Alhaji zuwa nayi ka rufaman asiri kamar yanda Allah ya rufa maka." cikin kuka Mama take maganar dan ita gani take idan ba aure tayi man ba to hankalin ta ba kwanciya zaiyi ba, kallon Mama yayi sannan yace. "Hajiya Hafsat mai yafaru lafiya kike kuka? Dan Allah kiyi shiru ki gaya man abunda ya kawoki a wajena." ce mashi Mama tayi. "Daman Alhaji dan Allah so nike ka auri Khadija idan kana so, dan Allah karkace aa ka rufaman asiri kamar yanda Allah ya rufa maka."

Cikin murmushi da jindadi Alhaji Salahu yace. "Haba Hajiya daman abunda kika zo kice man kenan harda kuka? Ai ba wani abu bane daman na jima da son Khadija a cikin zuciya ta gayawane kawai banyi ba amman ko maiyasa kike son aura man ita." cikin farinciki da sakin fuska yayi maganar dan shi gode ma Allah yake cikin zuciyar shi, cikin tsoro Mama ta fara maganar. "Alhaji ba zan boye maka komai ba tunda kaine wanda zata aura, Khadija dai ciki tayi amman a halin yanzun cikin ya zube tana asibiti so nike tana dawowa ta ida samun sauki sai ayi bikin naku ko lefe karda ka kawo sadaki kawai zaka kawo dubu 20."

Washe kazamin bakin shi yayi sannan yace. "Idan wanann ne ai ba damuwa, shikenan amman ina son a daura auren nan da sati biyu masu zuwa Hajiya." cikin jindadi Mama tace. "Insha Allah, Alhaji nagode sosai Allah ya ƙara girma da buɗe, yanda karufa mana asiri kaima Allah ya rufa maka." washe baki kawai yake haka ya rako Mama har kofar gida yana ce mata sai ya shigo ganina idan muka dawo daga asibiti dan shi baya son zuwa asibiti da can ma yaje ya fara duba lafiya ta, ita ko Mama sai dadi takeji gani take ta gama yi man gata ta samaman wanda zan aura ya rufa man asiri a cewarta.

Koda taga motar Yaya Jamilu da ta Yaya Fatima a kofar gida tasan suna cikin gida shiyasa ta chanza fuska ta dauki mataki tun a waje dan tace ba wanda ya isa ya hanata aura mani Alhaji Salahu koda dangin mahaifinane dan basu tsinata mata tsiyar komai ba lokacin da Babana ya rasu dan haka basu da iko a kanmu daman tasha cewa haka shiyasa ba wani zuminci muke da dangin Baba ba saboda rashin jituwa dake tsakaninsu da Mama.

Koda ta shigo samun waje tayi ta zauna ta kama kallonsu daya bayan daya sannan tace. "Jamilu ya jikin Auta fatan dai komai yana tafiya dai dai."?  Kallonta yayi sannan yace"lafiya lau Mama, amman muna son muyi wata magana dake dan Allah Mama." duk da tasan maganar da zasuyi mata dan tasan Yaya Amina ta gaya masu yanda sukayi da ita, amman sai ta wayance tace masu. "Ina sauraranka Jamilu wani abu ke faruwa ne? Duk na ganku kamar ba lafiya kodai wani abu ke faruwa da Auta ne."?  Girgiza mata kai Yaya Jamilu yayi yana hawaye, saukowa yayi ya durkusa kasa ya kama kafafunta yana hawaye yace. "Dan girman Allah Mama, ki duba maraicinmu bamu da kowa sai ke, ke daya ce muke gani muji dadi nida yan'uwana mahaifinmu ya rasu, dan Allah Mama munzo neman alfarma a wajenki dan Allah karda kice ba zaki yi mana wannan alfarma ba Mama."ya ida maganar yana kuka dan Mama tasha gaban shi sosai tunda itace mahaifiyarmu dole ya bita a sannu dan ya shawo kan matsalar a sannu da dai ace ba Mama bace wata ce daban to da karfin tsiya sai ya anso man hakina amman yanzun dole su bi a hankali su shawo kan Mama ta fasa auraman Alhaji Salahu .

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now