END PAGE

37 4 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫
_(Ni da Yarima)_😭
(_A love & a Sympetic story_)
'''Story and written'''
*By*
'''Fadeelah Yakub''' *(Milhaat)*
Wattpad @Milhaat

🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION📚🖊️*
            *M.W.A*
       Kungiya d'aya tamkar da dubu.💪🏻
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________
     '''Wannan labari kirkirarren Labarine, ba yi shi don wata ko want ba, idan Labarin yazo dai dai da naka to akasi ne'''
        '''Ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ba ta ko wani siga yin hakan babban kuskure ne.''' *don haka a kiyayye*

_Ina godiya ga Allah daya bani iko da na fara littafin Nan, yadda na fara Lafiya ya Allah kasa na karasa shi Lafiya Ameen._

    '''Wannan labarin Sadaukarwa ne ga masoyana,Allah ya bar kauna'''❤️

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
      *PAGE* 1️⃣4️⃣0️⃣↪️1️⃣5️⃣0️⃣
Umma tace "Ya ana muku magana kuntsaya kuna kallon mu" cikin matan d'ayar tace "Kuyi hakuri Rai yayi halin sa Sarauniya Husnah ta rasa ranta, tana haihuwa ta mutu don ko ganin abinda ta Haifa bata yi ba"
  Umma na Jin Hakan ta yanke jiki ta fad'i.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Fad'iwar Umma yayi dai dai da shigowar Hafsah, da gudu ta karaso tana Kiran sunan Umma, Yarima wuri ya samu ya zauna, sauran matan sukayi kokarin d'aga Umma suka Kai ta d'akin ta, d'ayar Kuma ta karb'i jaririyar, Yarima tun da ya zauna bai ce komai ba ya d'aukin tsawon minti goma, Kan ya tashi da gudu ya Shiga d'akin ya hango Husnah a kwance jiki a sanyaye yake tafiya tamkar Wanda kwai ya fashewa a ciki,cikin Rawar murya ce "Husnah!!!" murya kasa kasa, "Husnah!!!" Amma bata amsa ba, har sai da ya karasa inda take idon ta a rufe fuskar ta d'auke da murmushi, Shima murmushin yayi yace "Dama na San Baki mutu ba Husnah ki tashi Dan Allah"
        Husnah bata motsa ba, durkusawa yayi ya riko hannun ta ya ji jikin ta a sake  cikin sauri ya sake hannun ta ya d'aura hannu a Kai ya kurma ihu, Bello da sauran dogarayen na jin ihun sa suka shigo d'akin da gudu, Bello sai dube dube yake ya duba Nan ya duba chan yace "Ha'ah Ranka shi dad'e me ya faru? Munjiyo muryar ka sannan ba mu ga kowa ba."
           Yarima na d'aga kansa Bello sai da ya tsorata don tunda yake bai tab'a ganin Yarima na kuka har Haka ba, ajiye addan dake hannun sa yayi ya durkusa a gaban Yarima yace "Yallab'ai me ya faru? Me ya same ka?"
          Yarima d'an yatsan Sa ya d'aga Yana nuna Husnah, cikin Rashin fahimta bello yace "Me ya Sami Sarauniyar?"
         Cikin kuka Yarima yace "Ta mutu" dukkanin su sukayi salati, d'aya daga cikin su yace "Tabbas anyi Rashi, inaga shiyasa Sarauniya ta suma"
Cikin sauri Yarima ya d'ago Kan sa.....
       B'angaren su Hafsah Kuma tunda suka Kai umma d'aki ta tsare unguzoma da tambayoyi, tace "Me ya Sami umma?"
   Cikin kuka tace "Taji Labarin mutuwar Sarauniya Husnah shiyasa ta Suma"
Zaro Ido Hafsah tayi tace "Husnah ta mutu" tace Mata "Eh ta mutu sai hakuri, Kema kiyi hakuri rasa d'an uwa ba dad'i"
             Hafsah kirkiran kuka tayi har da ihu tana birgima, ji sukayi ance "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
Hafsah d'ago Kai tayi da sauri Tace "Mene ne?" cikin kuka unguzoma tace "Ita ma ta rasu"
A tare duk sukace "Mata Waye?"
Tana kuka tace "Sarauniya ta rasu, yau ya Sarki zaiyi ya rasa Mata da uwa a lokaci d'aya" sai duk suka fashe da kuka, d'aya daga cikin su tace "Allah ya jikan ku, ita Kuma yarinyar da Husnah ta Haifa ya Raya ta"
Suka amsa da Amin.
       Hafsah a razane tace "Husnah ta haihu?" Sai Wacce ta rike 'yar ta miko wa Hafsah, Hafsah kallon yarinyar tayi da kyau a ranta tace "tabbas jinin Husnah ce ga Nan Kama Amma gaskiya yarinyar ta fi Husnah kyau, ai ban ga ta Zama ba Dole ita ma ta mutu" Tashi tayi ta Mika musu Yariinyar ta fita cikin sauri.
         'bangaren su Yarima Kuma yace "Kana nufin mahaifiyata ta suma?"
Ya amsa da "Eh Ranka shi dad'e" da gudu Yarima yafi ta, ya na Shiga d'akin yaji ana cewa "Allah ya jikan su da rahama, har naji na tausayawa Sarkin mu"
Kallon su ya fara yi d'aya bayan d'aya yace "Allah ya jikan su? Wa Kuma ya rasu?"
Babu Wanda ya amsa Masa, zuwa yayi ya tsaya Akan Umma dake kwance Akan gado yace "Bata farfad'o ba har yanzu?"
        'daya daga cikin su tayi karfin Hali Tace "Ranka shi dad'e ai baza ta farfad'o ba kullu Nafsin za'ikatul Maut, mahaifiyar ka ta rasu sai dai muyi hakuri" ta karasa maganar cikin kuka,Yarima na Jin Hakan ya fad'i sumamme.
            Hafsah na fita bukkar rabaka ta nufa, tana Shiga Tace "Husnah ta mutu Amma ta haifi abinda ke cikin ta na d'auka tare zasu mutu" Dariya rabaka tayi tace "Idan baki manta ba Kwanaki nace Miki bazan iya cutar da abin cikin ta ba,tun tana ciki bare yanzu da ta fito duniya, yarinyar Nan tafi Karfi na"
Rai a 'bace Hafsah tace "Toh Ni yanzu ya zanyi kaga yanda yarinyar take Kama da Uwarta Kuwa, gaskiya Mai kyau ce don tafi mahaifiyar ta, gashi na tsani ganin fuskar ta"
         "Idan Kika yi yin kuri cutar da ita zaki mutu" Rai ba b'ace ta Mika Mata wata Yar karamar jaka, Rabaka tace "mene ne Wannan?"
Hafsah tace "Gwalagwalai ne da lu'u lu'u ladan aikin ki"
Wage baki rabaka tayi tace "ajiye shi anan" ta nuna Mata wani babban kwarya, aciki Hafsah ta ajiye ta tafi, Rai duk ba d'adi, a fili Tace "Ko ba komai na gama da uwar hankali na ya kwanta yanzu zanyi bacci Mai kyau,ai kinyi babban kuskure da Kika Auri Yarima na da baki aure shi ba da Kila kina Rayuwar ki" ta kyalla kyale da dariya, tana Isa dai dai layin gidan su, ta arce da gudu, tana Kiran sunan Mama,"Mama!!! Mama!!!" tana kuka da sauri Mama ta fito "Hafsah me ya faru? Wa ya biyo ki?" Tana kokarin leka bayan ta,Amma ba ta ga kowa ba.
        Hafsah kuka take har da majina, Tace "Mama meyasa? Meyasa mutuwa zai d'auke Adda ta"
Mama Tace "Mutuwa? Addar ki?" Cikin kuka Tace "Mama Husnah ta rasu wurin haihuwa" mama ta rungumi Hafsah tace "kiyi hakuri Hafsah ki daina kuka" Mama itama kukan take.
           "Mama meyasa mutuwa zai d'auke ta yanzu a dai dai lokacin da komai ya Fara tafiya dai dai, shekara da shekaru ba mu san inda take ba sai da ta dawo gare mu" Mama wuri ta samu suka zauna ta kwantar da Kan Hafsah akan cinyar ta, Mama na kuka Hafsah na kuka.
        Yarima ya fi awa d'aya a sume kan ya farfad'o,anyi wa Umma da Husnah sutura, da kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" ya farka, goshin sa ya rike, ya na d'ago Kan sa suka had'a ido da Bello, Bello yace "Sannu Ranka shi dad'e" Yarima yace "Dan Allah Bello kace min mafarki nake Husnah bata mutu ba" Kai a kasa Bello yace "Kayi hakuri Husnah da Mahaifiyar ka lokaci yayi, yanzu Haka an musu wanka Ana Shirin a sallace su ne"
              Jiki ba Karfi Yarima ya Tashi ya fita, Yana fita ya hango taron mutane Yana karasa gun ya ga mutane biyu a kwance an rufe su da likafani, bud'e fuskar d'ayan ya ga Umma ce ya maida ya rufe Yana bud'e fuskar d'ayan Kuma yaga Husnah ce, anan ya fashe da kuka yana fad'in "Shikenan shikenan na Zama maraya ba Uwa ba Uba, ba Mata Umma meyasa kuka min Haka? Meyasa zaku barni cikin duniyar Nan Ni kad'ai wayyo Allah na yazanyi da Raina" ya sa hannun a Kai.
                 Abba ne ya taso Mahaifin Husnah, ya dafa Yarima a baya yace " 'dana Kayi hakuri Dole Kayi kuka Amma Dan Allah ka daure ka  Zama na Miji, addu'ar mu suke bukata a yanzu"
          "Abba Kar nayi kuka fa kace? Abba taya za'a yi na daina kuka? Husnah ce fa da Umma ta, yau Abba bai kai wata biyar da rasuwa ba sai Kuma Husnah da Umma suma su bi bayan sa, Wallahi Abba Nima mutuwa zanyi bazan iya Rayuwa ba Husnah itace Rayuwa Ta "
          "Kaiyaa ban so kace haka ba a matsayin ka na Mai ilimi da sanin ya kamata,ya kamata ka sani duk Mai Rai mamaci ne addu'a zamu musu, ka fi kowa sanin yanda nake son Husnah dalilin Soyayyar da nake yi Mata yasa na ki yin aure gudun halin Mata, yanzu ka maida hankalin ka gun tarbiyantar da 'yar ka"
        Zaro Ido yayi yace "Innalillahi Abba kaga na manta Husnah ta haihu ko kallon 'yar banyi ba" murmushi irin nasu na manya Abba yayi yace "Ku miko Masa ita"
          Wata Mata Ce ta miko Masa 'Yar ya Kare Mata kallon a ransa yace "Tabarakallah Masha Allah burina ya cika Husnah ta haifa min Mai kamata da ita" wasu hawaye ne masu zafi suka sauko Masa ya sumbaci goshin ta, yace "Masha Allah, Allah ya Raya min ke ya Miki Albarka" duk aka amsa da amin.
        Bayan an sallace su, aka kai su makwancin su, Umma aka Fara sawa  bayan an rufe ta aka d'auko Husnah za'a sata Yarima ne yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" a tsorace Husnah ta farka, tace "lafiya me ya faru?"  Zufa ne ya ke to wa Yarima Husnah ta matso kusa dashi tace "Dan Allah ka fad'a min me ya faru?"
         Yarima Numfashi yake saukewa da sauri sauri kamar Wanda ya Sha gudu, kallon ta yake yi yace "Wani mummunan mafarki nayi Wai....." Husnah ta katse shi Tace "Tsaya Kar ka fad'amin kasan ba kyau a fad'i mumunar mafarki ko?"
       "Na sani Amma idan ban fad'a Miki ba, hankali na bazai tab'a kwanciya ba"
"To naji yanzu ka Tashi Muje muyi al'wala muyi sallah ko da raka'ah biyu ne, kaga idan muka idar sai ka fad'a min ko?"
Ya ce "Toh" bayan sun idar sun dad'e suna addu'a musamman Yarima da shi ka d'ai yasan me ya gani bayan sun gama Husnah Tace "Uhmn Ina sauraron ka me ka gani?"
    Yace "Mafarki fa nayi Wai Abba ya rasu, bayan rasuwar sa Umma ta kamu da ciwon zuciya dakyar muka samu magani da ya kwantar da ciwon ke Kuma kina haihuwa Kema Kika mutu, sannan Umma Jin mutuwar ki ita ma ta mutu, Kuma Wallahi duk sharriin Hafsah ne"
      Murmushi Husnah tayi tace "bakayi addu'a ba sanda zaka kwanta ba kuma ka sa Ranka cewar Hafsah zata cutar dani sau da dama abinda ka kwanta dashi a Ranka shi zai dawo maka"
        Kallon ta yayi yace "Hakane Kuma kin San da Rashin lafiyan Abba na kwanta don a lokacin na fito daga d'akin sa ne bayan haka Kuma munyi magana da Umma akan Hafsah mu lura da abincin ki sannan mu lura da shige da fitan ta Ina ga shiyasa nayi Wannan mumunar mafarkin, abun mamaki gashi yanzu cikin naki d'an karami idan manta ba wata biyar Kenan ko?"
     Dariya Husnah tayi tace "ko dai ka Fara...." Kallon ta yayi yace "Kinyi shiru na Fara Zama me?"
"A'a bakomai" Shima Dariya yayi yace "Mace fa Wai Kika haifa min kyakkyawa Mai Kama da Uwarta"
        Kad'a Kai Husnah tayi tace "Kai Ko Dan Allah ka cire maganar Hafsah a Ranka komai ya wuce Kuma na tabbata baza ta cutar Dani ba"
    "Allah yasa"
"Ameen"

*Washe gari*
Yarima na idar da sallah ya Shiga d'akin ya tarar da umma da Abba na Hira, ajiyar zuciya yayi ya gaida su  suka amsa yace "Abba ya jikin naka?"
Abba yace "Da sauki ka ga yau da kaina na zauna har na samu naci abinci kaga sauki ya samu"
"Alhamdulillah Allah ya Kara maka tsawon raai yasa kaffara ne"
Murmushi Abba yayi yace "Ameen"

Kamar yanda Yarima yayi mafarkin Husnah ta haihu mace a zahiri ta haifi mace kamar yanda ya gani kamannin bai canza ba, bayan ta haihu Yarima yace "Husnah kin gani ko? Wallahi itace na gani a Mafarki na"
Umma Tace "Wani mafarki kuma?"
Nan ya Shiga bawa Umma labarin mafarkin da yayi, Murmushi Umma tayi Tace "Allah yasa mu cika da imani" duk suka amsa da Amin anyi shagali sosai yarinyan taci suna *NIHAAL*  Su Khairat, Khadija habiba da sauran Yan Uwa duk sun halarci bikin anci an Sha, Abba ya samu sauki, Husnah da Yarima Soyayyar su suke Sha sannan suna kula da 'yar su yanda ya dace ta Tashi cikin Jin dad'i da gata, Hafsah ta samu miji a cikin garin Deba Haka ma Khadija.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya gwanin ban Sha awa.
Wataran ayi kuka wataran a yi dariya.

Alhamdulillah!!!
Alhamdulillah!!!
Alhamdulillah!!!

Anan ne na kawo karshen littafi na Mai Suna *RAYUWAR* *HUSNAH*

Allah ubangiji ya bamu ikon amfani da darusan da ke ciki, ya Allah ka yafe min dukkanin Kurakuren da nayi , Abubuwan da na fad'a dai dai Kuma ya Allah ka bani ladan shi, Ameen.

Kuyi hakuri don na yanke Labarin sosai sabida wasu dalililai,Nagode sosai Fans da da irin goyon bayan da kuka bani.

Godiya ta musamman ga
*UMMU ABDALLAH*
*UMMU JAWAD*
*AYUSHER*
*MARYAM*
*BARRISTER ANISA*
*UMMU HANAN*
Nagode sosai Allah ya bar Kauna.

Ku kasance tare dani domin yanzu zan Fara kawo muku littafai masu dad'i Wanda zai nishad'antar daku ya fad'akar ya Kuma ilmantar daku.
*A RANAR AURENA* (Ta gujeni)
*MAHFUZHA*
*A SANADIN FYADE* (na rasa budurci na)

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now