CHAPTER SIX

18 3 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️
Dan Allah in kin San baza kiyi comments ba Kar ki karanta Rashin comments na b'ata group na marubuta.

'''PAGE''' 5️⃣0️⃣↪️6️⃣0️⃣
Yarima yace "A'a Abba ai tunda ka haifi Husnah Nima ka haife ni na d'auke ka tamkar wanda ya haife Ni"
Murmushi Abba yayi yace "Masha Allahu, Allah ya maka Albarka ya bar ki tare"

Duk suka amsa da Amin.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Sun dad'e Suna hira a yayin da bello na gefe Yana kallon su sai washe Baki yake, a ransa fata yake Shima Allah ya bashi Masoyiya kamar Husnah, bayan sun Gama Hira Yarima ya koma gida.

Washe Gari

Emmata Bakwai, shida daga cikin su sune zab'in da akayi wa Yarima, Hafsah, Zainab,Fateemah,Aisha,Salma da Amina, na tsaye da d'ayar wacce fuskanta a rufe yake, magana suke Rai a b'ace sai Hafsah tace "Wai Dan Allah ya akayi Yarima ya yarda da yarinyar sosai har haka ne? Shirin Nan Bai kamata ace ya tashi a banza ba dakyar fa muka samu har hakan ta faru "

Fateemah tace "me kuwa Banda asiri, asiri ta Masa Mana, kina ganin yanda ya haukace akan ta"

Amina Tace "Wallahi Ni kaina na yi mamaki na d'auka shirin da aka shirya  mata Zai kawo karshen wannan abun"

Wannar wacce ta rufe fuskanta Tace "Asali ma Kara musu shakuwa yayi don kusan kullum sai yaje gidan su" D'aga Zanin da ta rufe fuskanta da Shi tayi zaro idona nayi da kyau don na tabbatar da abin da Ido na ke gane min kamar Habiba nake gani,  tabbas ita ce murmushin mugunta tayi Wanda tsana, haddasa da bakin ciki ya bayya na a fuskar ta, Hafsah ta maida kallon ta ga Habiba tace "Habiba kina bani mamaki Husnah ba kawar ki bace?"

Murmushin gefen baki tayi Tace "Eh kawata ce"
Amina Tace "Amma Meyasa kike Mata haka, ko Kuma duk a cikin had'in bakin Kune da ita?ki Zama Yar leken asiri"

A tsawace Habiba Tace "Allah ya sauwaka na had'a Baki da ita, duk Duniya Babu wacce ma tsana kamar Husnah na tsane ta burina a kullum shine naga tana cikin bakin ciki da kuncin Rayuwa, Rayuwar Husnah barazana ne ga Rayuwata, duk abunda da nake so Kan na Ankara ta same shi, A ko da yaushe ita ce ta ke samun Nasara, Samarin kauyen mu duk Wanda Kika tab'a sunan ta Zaki ji da Islamiyya kowa Husnah, Ina mutuwar Son Shariff Amma Sabida Wannar mayyar Ya ki karb'an Soyayya ta, a islamiyya itace d'alibar da ta fi kowa har muka Gama,Haka ma a kungiyar mu na rawa, taya za'a yi na so ta?" ta karasa maganar tana huci.

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now