CHAPTER EIGHT

14 4 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺

'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakubu (Milhaat)'''
08111791471

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
*AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukarwa ne ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️

'''PAGE''' 7️⃣0️⃣↪️8️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
A tsawace Abba yace "Meyasa Zaki boye masa?" Sai ya Maida kallon sa ga Yarima yace "Kai kana jina? Nasa an kulle su da ita da Mahaifin ta"
Zaro ido Yarima yayi,Cikin muryar kuka Yarima yace "Abba meyasa? Me suka maka?"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Abba yace "Khaleed Wai meyasa baka da hankali ne? Yarinyar da tayi kokarin kashe ka shine har ka tsaya kake wani damuwa da ita?"
Yarima Kallon Abban sa yake cike da Rashin fahimta yace "Abba kisa Kuma kamarya?"
Abba yace "Abinda kunnen ka yaji Husnah tasa maka guba a abinci"

Wani irin Murmushi yayi Yarima yayi yace "Haba Abba, Husnah ce zata kashe ni? Abba Husnah ko kiyashi baza ta iya kashe wa bare Mutum a cikin mutanen ma ace Ni?" Yana Nuna kansa, ya d'aura da fad'in "Ni Husnah Zata kashe? Ni fa masoyinta ne baza ta cutar dani ba"
Khairat tace "Hakane Yaya Husnah bazata cutar da Kai ba"

Abba yace "Ku fad'i duka abinda ya muku, Zan hukunta su hukunci mafi Muni"
Umma tace "Dan Allah Ranka ya dad'e ka rabu da mutanen Nan"
Abba kallon Umma yayi yace "A tunani na munyi maganar Nan dake ko? Na fad'a Miki ki Daina samin Baki a maganar Nan"

Umma Tace "Usman Wai Yaushe ka Zama haka ne? Gaba ki d'aya ka canza daga Mai Tausayi zuwa Mara Tausayi, Mai imani zuwa Mara Imani, Mai tausayi zuwa mugu, kaji tsoron Allah ka sani idan ka cutar dasu sai Allah ya tambaye ka."
Ta Tashi tayi tafiyar ta, Abba Baki a bud'e ya bita da kallo murya a kasa yace "Usman? Yau Ni Sa'a ta Kira da suna na Kai tsaye, tabbas ranta ya b'aci"
Yarima yace "Abba Dan Allah ka barni naje na gan ta ko hankalina zai kwanta"
Abba yace "Zan barsu su tafi Amma da Sharad'i"
Yarima yace "Ina jinka"
Abba Yace "idan na sa aka bud'e su baxa ka sake kula ta ba ka yarda?"
Shiru Yarima yayi a ransa cewa yake "Ya zanyi bazan iya Rayuwa ba tare da ganin Husnah ba,kwana
d'aya idan nayi ban ganta ba ji nake kamar Zan mutu"

Husnah tace "Yaya tunanin me kake ka amince kawai Husnah fa a kulle suka kwana, ka amince dan Allah"
Kallonta yayi yace "Kina da gaskiya" ya ja dogon Numfashi Yace "Abba na amince Dan Allah ka kyale su su tafi"
Abba yace "Toh za su ji amma ka sani daga yanzu baza ka sake zuwa inda take ba,baza Kuma ka fita daga cikin fadar Nan ba har sai kayi aure."

Yarima hawaye ne suka zubo Masa kallon Abba yake, ya rasa dalilin da yasa Abba ya tsani Husnah cikin murya Mai Sanyi yace "Abba Dan Allah ka sassauta min hukuncin Nan yay min tsauri Dan Allah" ya hard'e hannayen sa alamun roko, Murmushi irin na su na manya Abba yayi sannan yace "Khaleed na Riga na gama magana babu Kuma Wanda ya Isa yasa na canza ra'ayi na Ina fatan ka gane?" Yana Kai Nan ya tashi ya fita.

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now