CHAPTER FOUR

26 3 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukar ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ ❤️

'''PAGE''' 3️⃣0️⃣↪️4️⃣0️⃣
Tafiya ta ke hannun ta rike yake da tulu a yayin da ta rike wata doguwar sanda da D'ayan hannun ta tana Wasa dashi,ji tayi ana Kirin sunan ta, tana juyowa taga Shariff ne ji tayi kamar ta nitse kasa a yayin da take Jin tsanar sa na karuwa a cikin zuciyar ta, ya karaso inda take

Yace "Husnah yanzu dan Allah kin min adalci Kenan? Kin zab'i Yarima akaina, sabida Kinga Yana da mulki?"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Wani irin kallo ta Masa irin na baka Kai d'in Nan ba sannan tace "Sharif, Sharif sau nawa na Kira sunan ka?  na fad'a maka bana son ka Yarima nake so, Kuma ba don Komai ba sai dai halinka , halinka ne bana so dan Allah ka rabu dani ana Dole ne?"

"Husnah kice yaudara irin taku ta Mata ne ya tashi Mun fi Shekara 2 muna Soyayya baki San da halina ba sai yanzu?"
"Na dad'e da sanin hakan Shariff kawaii bani da mafita ne, Amma Yanzu Allah ya kawo min it's, kaga bazan yi Wasa da dama ta ba, Dole na yarda kwallon mangoro na rabu da kid'a,yanzu na gane ban bancin so da Kuma takura, ka takura Ni Sam ka hanani sakewa, sabida haka kaje ka nemi dai dai kai bani ba" tana wurga Masa harara.

Yace "Toh Shikenan tunda kince haka Kuma Wallahi sai Kinyi dana sanin abin da Kika min sai na sa kin tsani kanki"

"Karyan ka Sharif baka Isa kayi min abunda Allah baiyi ba, kayi kad'an"
"To shikenan Husnah mu zuba mugani"
"In ka fasa Wallahi kaji tsoro" ta jaa dogon tsaki tayi tafiyar ta.

Sharif na barin wurin ya nufi gidan su aminin sa Mai suna  Isah, Yana Isa gidan ya tarar da Isah da abokin sa Mai suna mansur, bayan sun gaisa Isah ya ce "Abokina ya na ganka haka wa ya tab'a Mana kai?"

Shiru yayi na d'an wasu lokuta sannan yace "Kai dai bari wannar Yarinyar ce Husnah"

"Me ta maka? Kun sake samun matsala ne?"
"Eh Amma wannan karon na daban ne" gyara Zama yayi Yana magana cikin tsawa Yana yarfa hannu, "Wai Ni" Yana tab'a kirjin sa "har Ni yarinyar Nan zata gani tace bata Sona wai Yarima take so"

Isah yace "Kuma ka barta baka tattaka ta ba? Ai wallahi da ina wurin Nan bata Isa ta kalli idon ka tace maka haka ba,duk fad'in garin Nan babu Wanda ya Kai ka rashin ji da rashin tausayi, kawaii don ta samu Allah ya d'aura Maka sonta sai ta tsaya tana wulakanta ka"

Mansur yace "Haba Isah wannan wani irin magana kake?Kai Kuma Shariff har dad'i kake ji ana ce maka baka ji, baka da kunya, Isah,Kai da ya kamata ka rarrashe shi Kan nuna Masa matar Mutum kabarin sa ce Amma kana Nan kana Kara b'ata ta a gunsa"

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now