Koda mukaje taimaka mashi nayi yayi wanka sannan muka ci abunda ya kawo mu, dan kuwa na gurzu wajen Nurandeen kuka kuwa nayi mashi bansan adadi ba, dan Nurandeen ba daga baya ba wajen sex ba, ashe ranar da nazo gidan Nurandeen ranar akayi mana fiddo mana result ni ban sani ba ana can ina soyayya da Nurandeen, koda Dejja taji labarin fitowar result din yan medicine da saurinta taje ta duba man, amman abun mamaki tana zuwa taga duka course din na nike na faɗi wasu ma an saman empty ma'ana banyi attending  ba, kuka Dejja ta fashe dashi a wurin dan danan kallo ya dawo wajenta, bata damu da kallon da akeyi mata ba, haka ta juyo tana tafiya tana kuka kawarta Jamila tana bata hakuri room din mu tayi ma tsinke, ko sallama batayi ba ta banka ta shigo Aziza ta iske tana chanza kaya, kallon Dejja tayi sannan tace “ke Dejja lafiya zaki shigo kana kuka ko wani aka ce maki ya mutu."!? Cikin tsoro tayi tambayar da ta tsorata da yanda taga Dejja tana kuka, wurga mata harara Dejja tayi sannan tace “hankalinki ya kwanta Aziza kin ɓata rayuwar Aunty Auta kin sanyata a gurɓataiciyar hanya kij koya mata bin maza kinsa ta manta da abunda iyayenta suka turota, kinsan komai kuka bani sane ku? Nasan halin da ake ciki bansan har karatu kin hanata ba sai yau da naga result dinta, ko kinsan bansan wacece ke ba Aziza? Nasan wacece ke dan nayi bincike kanki sosai a makarantarnan ke ba kowa bace face karuwa mai lasisi wanda take ɓata rayuwar yaran mutane ance idan kika damki yarinya sai kinga kin koya mata karuwanci sannan hankali yake kwanciya, kamar yanda aka koreki a makarantar nan, shekara uku kenan da korarki ke ba student bace, zaman iskanci kike a hostel dina to abunda baki sani ba wallahi bakiyi ma Aunty Auta haka a banza ba, tun yau zaki fara nadama da nasani marar musaltuwa." Dejja na gama faɗin haka ta sheƙe wuyan Aziza ita da Jamila suka fara bugunta tun tana ramawa har takai da bata iya ramawa dan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi sai da su Dejja sukayi ma Aziza kace² cikin jini sannan suka barta, ihun da takeyi ne ya jawo da hankalin security din hostel, nan aka kama su Dejja ita kuma Aziza aka kaita hospital, da yake dare ne nan aka anshi registration number dinsu akace ranar monday suje senate danyi case din.

Ni kuwa hankali na kwance bansan wainar da ake toyawa ba sai soyayya muke sha Nurandeen haka nayi mashi weekend ranar Monday da safe ya maidoni hostel, tunda na shigo naga mutane suna kallo suna nunani take sai na tsirgu da kaina ina shiga room din naga banga Aziza ba, ban damu da inda ta tafi ba nasan ta da iya soyayya nasa tana wajen samirinta shiyasa wanka kawai nayi na kwanta na fara bacci ina cikin baccin naji an tabka man bugu a baya, firgigi na tashi naga Dejja fuskarta a murtuƙe nima murtuƙe tawa fuskar nayi sannan nace “wai Dejja bakiga bacci nike ba kika zo kika tadani ba."?  Murmushi tayi mai ciwo sannan tace “nasan baki san abunda ke faruwa ba shiyasa harki samu damar yin bacci." dafe kirji nayi sannan nace “na shiga uku mai ke faruwa Dejja."!? Hawaye naga Dejja ta farayi ta samu waje ta zauna tace man “Aunty Auta an fiddo maku result kuma baki ce komai ba, duka f9 gareki." hannu na aza bisa kai na fashe na ihu ina cewa “na shiga uku na lalace karya ne Dejja ban yarda ba cutata akayi wallahi." share hawayenta tayi sannan tace “Aunty Auta ba wanda ya cuceki sai dai ke kika cuci kanki kika biye huɗubar Aziza kika dauki turbar da ba taki ba, kina bin maza kowa yasan a hostel dinan kena neman maza nima a hanya na tsinci labarin, hakan yasa shekaran jiya nazo na tadda bakinan banyi mamaki ba nasan kina wajen namiji na tadda Aziza dawowarta kenan daga wajen iskancinta na gaya mata maganganu sanann nayi mata mugun bugu wanda nan gaba ba zata sake ɓata tarbiyar wata yanzun haka tana hospital ana treatment dinta, ni kuma registra din school dinan saurayina ne yace yana sona kuma aurena zaiyi shine na gaya mashi duk halin da ake ciki yanzun ance abunda nayi ma Aziza dai dai ne, sannan kuma yace zaki ajiye wannan semester din, ki zauna har ayi hutu mu tafi dake gida, idan za'a sake bada admission sai a baki ki dawo 100 level amman bai zama dole a sake baki medicine ba."

Bansan sanda na rungume Dejja ba ina kuka, dan take naji na tsani da Aziza da halin da nike yi haka ta gama bani hakuri tace bata gaya ma kowa tunda ansamu solution din problem din na, haka na kama zaman hostel bani zuwa lecture tunda ni nayi dropping din year din baki daya, tunda na koma wajen Dejja nabar kula Nurandeen duk da yana kirana kuma yana yiman text amman ban mashi reply duk ina sonshi, itama Aziza hukumar makaranta ta koreta ance karda a sake ganinta a hostel haka ta kwashe kayanta ta koma gidan Nurandeen da zama suna sheƙe ayarsu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya bani kula kowa kuma na kasa sama raina soyayyar Aminu, idan na tuna da rayuwar da nayi da Aziza nakanyi kuka da nasani sosai Dejja take bani hakuri tana nuna man cewa kaddara tace tazo a haka, watarana zamu kasuwa nida Dejja zamuyi ma su Mama tsaraba dan sun gama exams gobe zamu gida su zasuyi hutun season ni kuma zani dawo level one, bayan mun gama sayen komai muna tsaye bakin titi wata unguwa ce inda ba mutane sosai, dan mun jima bamu samu abun hawa ba, ji mukayi an watsa mana wani abu a fuska daga nan bamu sake sani inda kaimu yake ba, koda muka farka gani na nayi kusa da Nurandeen zaune shida Aziza sai iskancinsu suke da inalillahi na fara magana ina kallon su, nan itama Dejja ta tashi itama inalillahi tace, gani nayi Nurandeen yana son yayi  reaping din Dejja wai ita ta hanashi ya ida cima burinshi a kaina, bari itama yayi abunda yakeyi dani, ni kuma hana ina kuka ina bashi hakuri haka nai ta kuka itama Dejja tana kuka nan yace ya hakura amman sai yayi sex dani ko kuma yayi da Dejja, take na yarda dan bansan rayuwar Dejja ta lalace kamar yanda na lalata tawa, da Dejja taso yin gardama da yake nasan halinshi idan yace zaiyi abu sai yayi da naga Dejja tana son ta hanani bashi kaina bansan sanda na wanke ta da mari ba ina cewa “kinfini son kaine Dejja? Rayuwarki nike duba maki ni tawa rayuwar  tazo karshe kuma ba zan taɓa barin naga taki ta lalace ba kamar tawa ko kin manta kinsha gaya man haka tawa kaddarar tazo ba? To ki dauka komai ya faru dani a rayuwa kaddara ce." kuka kawai Dejja take, haka Nurandeen ya wulakantani a cikin parlour din gidanshi dan Dejja kasa kallo tayi sai ma juyawa da tayi tana kuka, tun ina kuka ina bashi hakuri har na samai ido, sai yayi yanda yake so sannan ya kyaleni kuma yace kafin ya buɗe idonshi mu barmashi gida ko kuma ya dawo kan Dejja, haka muka kwashi kayanmu Dejja ta kamani tana kuka ina kuka haka muka koma hostel ko Jamila Dejja bata gaya ma abunda ya faru ba, kawai dai tace naped ce ta faɗi damu, haka nayi wanka na kwanta ina aikin kuka take naji na tsani Nurandeen duk duniya ha wanda na tsana kamarshi shida Aziza.

Washe gari muka dawo gida, kowa yayi murna da ganinmu Dejja taso mu wuce gidansu amman ni nace aa gida zani wajen Mama, haka ta kyaleni ba dan taso ba na wuto gida itama ta wuce gidansu, bayan na dawo da sati biyu ba fara ciwo kala kala daga wannan sai wannan haka Mama ta kaini asibiti nan akece muje ayi mana awon ciki, cikin mamaki Mama tace ciki kuma namai bayan ko aure banda shi, amman likita yace aje dai ayi aiko anayi sai gashi ina da ciki na sati biyu da kwana ɗaya tun a asibitin na fara ganin tashi hankali wajen Mama, haka muka dawo gida ni kuka Mama kuka ba irin tsinuwar da Mama batayi man ba, daga karshe Yayata Aisha tazo nan Mama ta gaya mata suka yi man taro suka kama bugu a ranar cikin Nurandeen ya zube a jikina kuma na samu matsalar mahaifa, ina cikin kuncin ciwon da ya samaini naji Mama tace aure zatayi man da wani tsoho a unguwarmu ni kuma naji ban iya dauka shine nazo nan garin har Allah ya hada ni dake, kinji Abun da ya faru dani....

*karku manta na gaya maku litafin sanadin soyayya minti ya faru da gaske, amman ba komai yake gaskiya ba 20%true life ne, Khadija da kanta ta gaya man labarin nata tana son na rubutu akanki shi dan masu irin halinta su daina idan ma akwai masu niyar yi su fasa ni kuma 80%fiction ne na Kara shi dan na kara ma mutane jin tsoron yin abun a zuciyarasu kuma su ƙamaci abun har abada, kuma Khadija tana cikin group din duka biyu da a sanadin soyayyar minti fans da kuma sanadin soyayyar minti 2 duk tana ciki sai dai bata yarda da na bada number dinta ba, dan haka ina maku fatan alkhari kuma ku dauki abu mai amfani da yake ciki nagode*

Share
Comment
And
Vote

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now