CHAPTER 1

119 5 0
                                    

💫💫💫💫💫💫💫💫
*RAYUWAR HUSNAH*
💫💫💫💫💫💫💫💫

_(Ni da Yarima)_😭

_(A Love & sympathetic Story)_
🥺🥺

*Daga Marubuciyar* ✍🏻
'''MATAR AURENAH
SAIRAH DA SARAH
DALIYAH DA DANIYAH'''
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
            *AND NOW*
'''RAYUWAR HUSNAH''

*RAYUWAR HUSNAH*_ '''Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......'''

*Note* _'''Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba
'''
🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️

     M. W. A

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne

'''Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.
'''
_Wannan labarin sadaukar ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE*1️⃣🔁1️⃣0️⃣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Nigeria, cikin Jahar Gombe a karamar Hukumar Yamaltu deba, garine mai tarin Albarka da kwanciyar hankali, anyi wani adalin sarki mai tarin dukiya,  USMAN YUNUSA SANI d'an sarki jikan sarki, Yana matukar son jama'un sa sannan Yana mulki yadda yadda dace kowa Yana yabon kyawawan halayensa hakan yasa Babu kamar sa a yankin.

Kamar kullum zaune suke a fada dashi da fadawansa Hira suke Cikin nitsuwa kana ganin su kasan akwai kwanciyar hankali, sarki na zaune Akan gujerar sa yayin da fadawansa na tsaye a kansa sauran manyan mutanen gari Kuma na zaune a gefen sa, bayan sun gaida sarki ya amsa cikin satin fuska sai ya Fara bayani kamar haka.

"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah a yaune ya kamata a sa Ranar da Yarima zai zab'i amaryar sa kamar yadda al'adar mu ta tanadar, idan Allah ya ara Mana Rai gobe a dai dai wanna lokacin Yarima zai zab'i amaryar sa"

Jama'ar wurin kowa ya Fara fad'an Albarkacin bakin sa, "Allah ya jaaa zaminin sarki, Allah ya nuna Mana"

'daya daga cikin fadawansa ya Tashi yace "Ina Mika sakon gaisuwata ga sarkin da dukkan mutanen da suka hallarci taron Nan,Ina fatan Allah ya kaimu gida Lafiya kamar yanda muka Zo lafiya"

Duk suka amsa da Amin, sai ya d'aura da fad'in "Allah ja zamanin sarki, Ina so a bani izinin zuwa kauyen KURI don gayyato mawaka da masu rawa don ba a yin zab'en gimbiya ba tare da anyi amfani da kid'a da rayeraye ba"

Sarki yace "Tabbas hakane, ka ga har na manta da al'adar an baka izini" ya Karasa maganar cikin dariya.

"Toh ranka shi dad'e" Nan take yaje har kauyen KURI, Yana zuwa ya gaiyaci mawakan duk matane.

Washe gari

A fadar sarki kowa da kowa yazo yara da manya, sannan akwai emmata shida Wanda acikin su Yarima zai zab'a, rawa ake sosai ana raye Raye ana ciye ciye da shaye shaye, ana cikin hakan ne d'aya d'aga cikin fadawa Yace "Rawar ya Isa Haka yanzu lokacin da Yarima zai zab'i gimbiyar sa" wurin ya kaure da tafi da gud'a.

Tun da aka Fara wasanni Yarima Hankalin sa baya Kan Emmatan da ya kamata yayi zab'in sa aciki, duk Hankalin sa ya Koma Kan d'aya daga cikin masu Rawar, a zuciyar sa cewa yake "ita ce zab'ina"(Ni ko nace Anya Yarima Kai da aka zab'a maka kyawawan gari har shida Amma Kuma kake kallon Wata daban)

RAYUWAR HUSNAH Where stories live. Discover now