To inna asha race lafiya.

❄❄❄❤❄❄❄
A asibiti kuwa bayan ya k'ara mata ruwa a office d'insa yana k'arewa ya had'a mata shayi tasha yabata magunguna,Zaunar da'ita yayi ajikinsa tare da rungumeta ahankali ya tab'a goshinta yace".... Ya jikinnaki?baki ta turo bata bashi amsa ba ya kai hannu mararta yana shafawa yace".... Wannan Babyn nawa yasaki rashin kunya ko?.

Tace".... Ni bana rashin kunya bakaine innace kadaina tab'aniba sai kak'i tak'arasa da shagwabarsa dake tafiya dashi,yace".... How can I stop touchiny what belongs to me? Kema kinsan is impossible.

Tace".... Nide ka kyaleni yace".... Ki kwanta ajikina tace".... A'a banaso,ni kuma inaso.

Kuka tafara masa a zuciyarsa yace".... Mutum daga Abu kad'an kuka saboda kuka Sam baya basa wahala,Amma afili yace"....toh let's sleep kinsan jiya banyi bacci ba tace".... A office d'in zakayi bacci yace".... Nd so is my hospital I can do what ever I like tace".... Naji kaje kaga marasa lfya.

Tace"... Nika kaini gida dariya yayi yace".... Kinmanta inna na gidanne,ido ta zaro tace".... Inna kuma wace inna?,yace"... Inna daya de nan yafad'a mata komai.

Jikintane ya hau rawa tace".... Hubby tazo tazubarmin da cikina Dan Allah karka bari ta......shhhh yad'aura hannuwansa akan labb'anta yace".... Kafin mu koma zata fita ki kwantar da hankalinki.

Dak'yar ya lallab'ata tayi shiru tukun suka kwanta,Duk da tak'i yarda ta kwanta ajikinshi.

Tashi tayi tana dudduba d'akunan amma kowanne a kulle,k'ofar data gani a karshe taja sai taga ya bud'u tasaka kai kenan taga abinda  ya firgitata.

Jin ihunta yasaka su Angel barin k'ofar suka koma can nesa suka tsaya,Da gudu ta juya baba mai g'adi kuma ya saki karen ya Mara mata baya.

Juyowa tayi taga karen na binta ai saita fasa ihu, tafara gudu dakyar abinka da mai k'iba.

Guduwa take tana zagaye falon don tarasa k'ofar fita shikuwa Karen sai binta yake yana haushi,dak'yar tasamu k'ofar tafito a guje tana ihun Neman agaji babu mai aimaka mata saboda Angel tahana duk masu aikin gidan.

Mai Angel zatayi inba dariya ba Fatima na tayata,inna ganin compound d'in gidan babba gashi ta gaji ga karen na binta sai kawai ta fad'i kasa tana ihu.

Ganin babu Sarki sai Allah ka karen na zuwa da haushinsa mai firgitarwa yasata tashi tafara gudu ta nufi gate batare da sanin zaninta ya kwance ba,Hhh zo kuga inna ba zani Allah yasota da Skirt aciki  gashi ta gaji dak'yar take gudu tana nishi.

Tana zuwa gate iska ta buga gate d'in ya kulle ,juyawa tayi taga yana zuwa ganin namans  a nason ya tsere gate d'in tafara jijjigawa amma sam yak'i buduwa wani ihu ta kwala jin Karen yakaimata  cafka a cinya  nan ta fad'i tana ihu tana neman guduwa.

Da ky'ar tasamu ta gudu bayan gate d'in ya bud'u tafita a 360, duk fuskarta kwarzanen karene ga jinyoyinta duk jini ga babu zani.

Nikuwa nace gobema ki k'ara kaimusu Visit.😂.

Baccinsu sukasha sai karfe sha biyu suka tashi,shiya fara tashi ya kalli yadda ta bararraje akansa tana bacci murmushi yayi   ya fara Shafa fuskarta,bud'e idanuwanta tayi a hankali tare da sakar masa murmushi shima murmushin yamata shima yace"....kinsaka yau banyi aiki ba daga karshema kika sani yin bacci.

Baki ta turu tace".... Basai da nace ka tafiba kak'i,yace".... Uhmm tashi muje kiyi wanka lokacin sallah ya kusa mukoma gida.

Tashi tayi ta fara tafiya se yaga tayi saurin zaunawa,da sauri ya k'arasa gunta yace"....meyafaru?tace".... Jiri ne ya d'ibeni yace"...sorry muje natayaki wankan,tace".... A'a kabari zanyi yace"....to tashi kije.

Tashi tayi tafara tafiya yana biye d'aita fad'uwa zatasakeyi yayi saurin tareta tare da d'aukarta zuwa band'akin,saida yasha wahala kafin yamata wanka don k'in yarda tayi wai yabarta tanajin kunya,dariya yayi yace".... Nifa mijinkine to waima miyene banganiba?rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana dariya,Murmushi shima yayi yad'akko ta kamar wata Baby ya ajiye abakin gadon dake d'akin.

Kayanta ya tayaya maidawa  sannan yace"... Me zakici tace"....zansha ruwan Lipton yace".... No wannan ba abinci bane kifad'i wani abin,tace".... Ni shi nakeso yace"....ohk tare da d'aukar wayarsa yabada umarnin akawo masa ruwan Lipton d'in.

Ba'afi minti biyarba sai sukaji knocking tashi yayi yaje ya k'arbo sak'on ya dawo,Da kanshi yabata tasha sannan ya saka mata hijab d'inta har k'asa blue in colour Wanda ya mata kyau saboda yadda tayi haske fuskarta tayi fayau tak'ara kyau sanadiyyar jaririn cikin dake jikinta ga dama ita akwia kyau.

Kulle k'ofar yayi ya rike mata hannu suka fara tafiya,duk inda suka gifta sai an kallesu,dai_dai sunzo gurun y'an matannan wata acikinsu ta zunguresu tace"...Ku k'alli can.

Dukansu suka juyo don kallon abinda ake nuna musu,Wow sukace  Masha Allah wata tace"....Perfect match Kallesu abin sha'awa.

Ganin irin kallon da Mata keyiwa mijintane yasata d'aure fuska ta juyo tace".....wayyo Allah kafata ,da sauri ya juyo  duk ya gigice yace"... Meyasameki inake maki ciwo?,tace".... Bigewa nayi,duk sun zuba musu ido suna kallon mezeyi.

Ita kuwa tayine don susan cewa the Guy with blue eyes is for her only,D'aukarta yayi kamar y'ar baby yana mata sannu ya wuce gabansu baima damu da kallon da'ake binsu dashiba.

Wata Christian  ce tace"... Amman wannan guy din ba d'an Nigeria ba,Wata bahaushiya tace"..... Wallahi he is Kanuri not Hausa.

Dayar tace".....Masha Allah,Allah yayi kyau anan wata tace".... Shifa Sam baya dariya amma kalli yadda ya gigice akan wannan yarinyar,Amma ai matarsace dole ne amma Allah ya had'a,Nande suka karaci  gulmarsu,nace kwayi Ku gama de Ihsandeen forever.

Tnx fans.

Like.
Share.
Vote.

Ur Queen Deeja Musa.
Tauraruwace.
❄❄❄❄❄❄❄❄💦💦💦💦💦💦💦💦🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸💧💧💧💧💧💧💧💧💥💥💥💥💥💥💥💥🌤🌤🌤🌤🌤🌤🌤🌤
[1/28, 10:02 PM] Khadeejaht hydar Novelist

IHSANWhere stories live. Discover now