Shima maida mata martani yake yana k'ara matseta a jikinsa,ganin yana son fara rikicewa yasata fara kok'arin tashi daga jikinsa,Amma gam ya rik'eta yana kok'arin since towel d'in dake jikinta saurin rike masa hannu tayi tafara kok'arin tashi.

Ahankali  yace".......plss wifey  tace".... Plss stop kadaina kaga ba a gida bane,yace".....I knw nanma ai gida ne.

Tashi tayi daga jikinsa tace".... Zansaka kayana kaje kar a ga ka dad'e ko,yace"..to ina ruwansu ba matata bace,tace".. Amma da kunya yace"... Ke kika santa  dariya kawai tayi don tasan inta biyeshi saisu kwana anan.

Tana gama maida kayanta tayi hanyar fita yace"..... Ina zakije kibarni?tace".... Waje zanje yace"... To jirani  tace"... Haka kawai zeyi magana tafice daga d'akin tana dariya,murmushi yayi ya tashi ya fita.

A parlour ta tadda kowa a zaune kunya duk ya isheta,shikuwa ba ruwansa  yazo ya wuce ya zauna cikinsu Fahad.

Fahad yace"....... Guy karkana takurama kanwata  fa,Hisham yace".... Wlh irinkune ze zubar da cikin matansu mutum sai jaraba."

Deen yace"......to ina ruwanku kuma nasan mekakema Angel d'ina ko kuma kai nasan mekakema Y'ar uwata,don haka kowa ya rik'e nasa banason  saka ido.

Dariya suka kwashe dashi duka,sannan Hisham yace"..... Ikon Allah Ashe Ihsna y'ar uwarmu ce,Deen ne yakai kallonshi ga parlour gaba d'aya yace".... Abin sha'awa Allah ya k'ara donk'on zumunci da k'auna amin suka amsa duka."

Su Fatima sunyi girki anci ansha aka had'asu gaba d'aya bayan sunyi sallar isha'i,aka musu nasiha mai ratsa zuciya  sannan aka sallemesu kowa ya kama hanyar gidansu.

Suna isa securities suka bud'e musu  gate saboda yanzu bayan mai gadi sun k'ara security,Suna parking kowa ya fito ya nufi b'angarensa kowa rik'e da hannun matarsa wow amazing Couples.

Suna shiga tafad'a wanka ta shirya cikin wani silky sleeping dress pink in colour yayi matuk'ar yi mata kyau,da sallama yashigo d'akin sandarewa  yayi yana kallonta saboda tayi mat'ukar kyau kuma tatafi da imaninsa.

Hannuwansa ya bud'e mata ba musu ta je tafad'a a kirjinsa ya maida hannuwansa ya rufe yana shak'ar kamshinta mai kashe masa jiki,Dukda k'irjinta na bugawa amma ta kudirci cewa bazata taba nuna gazawarta ba.

Wuyanta yafara shinshinawa yana bata hot kisses,tun suna tsaye harya d'auketa tsam kamar baby yakaita kan gado ya kwantar.

A hankali cikin sanyinsa saboda komai nasa a nitse yakeyinsa,romancing d'inta yakeyi daga nan kuma suka Lula duniyar masoya,ganin hakane yasani rufe musu kofa na zauna a parlour don na huta.

Bayan  wani lokaci nashigo Tana kwance akan kirjinsa yana Shafa gashin kanta yace"..... Allah yamiki albarka Wifey  u a so sweet.

Murmushi tayi tareda shafa sajensa tace"....Aini takace,yace".... Can we go again?.

Kai  ta gyada masa nan suka k'ara lulawa   duniyar nan, saida tafara gajiyane tafara masa kukan shagwaba .

Rungumeta yayi yamata kiss a kumatu sannan sukaje sukayi wanka suka kwanta.

Haka Rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali ga so da kaunar juna ,haka ma a b'anharensu Fahad ma komai yana tafiya dai-dai yadda yakamata.

3_ Months Later(Bayan wata uku.
❄❄❄❄❄❄❄❄
Kwance take akan cinyarsa tana wasa da wayarta shikuma yana aiki a laptop dayake yau weekend ne babu aiki, saurin tashi tayi da gudu ta shiga toilet d'in dake parlour tafara sheka amai,Da sauri yabi bayanta a tsugunne yasameta tana kakarin yin amai,taimaka mata yayi ta wanke bakinta yana ta jero mata sannu.

Wifey what's wrong with u?a hankali tace".... I don't know nima,yace"... Ko zamuje asibiti ne? Tace"... Basai munjeba ai zan samu sauki."

Haka suka zauna bayan sallar Azahar jikinta yayi zafi kuma takasa cin komai,Kaya ya canza mata yakaita mota ya nufi asibitinsa da'ita dayake ba'a rasa mutane.

Suna zuwa ward d'insa ya nufa da'ita ya d'auki wayarsa yak'ira wata nurse bata wani dad'eba tashigo ta rissina tare da gaidashi sannan ta gaida Ihsan,had'e rai tayi ganin yadda yarinyar takemasa murmushi.

Fuska a d'aure yace inason kikawomin kayan aikine nan yafad'a mata ,kallonshi take yadda yake turanci kamar abakinsa akayi .

Bayan kamar minti biyar saiga yarinyar ta dawo ta bashi kayan aikin,gwaje gwaje ya mata sannan ya bukaci dayake tayi fitsari ta kawo,bayan ya gama ne ya d'agata sama yana kabbara yace".... Am happy  Kinabani komai arayuwa nikuwa dame zan godemiki,ganin bata gane inda ya dosa bane yace mata Wifey I mean we are pregnant we are going to be Mummy nd Daddy.

Zuciyartace ta hau bugawa don tuno Mamarta gun haihuwa ta rasa ranta,amma ganin yanda yashiga farincikine yasata murmushi  tace"... Am happy too,kallonta yayi ganin tana kok'arin share hawayen fuskarta yace".... Wifey what happened? Tace".... Uhm mama na tuno,Hannunta ya r'ike don ya gane metake nufi yace".... No karkiyi tunanin komai itama haka ajalinta yazo kowa da tasa kaddarar don haka kidaina tuna wannan kuma kinsan likita yace".... Damuwa yana saka hawan jini musamman ga mai ciki plss Dear kicire wannan tunanin aranki kinji,Insha Allah Dear zan daina.

Tun kafin sukai gida yak'ira su Hashim yafad'a musu haka yak'ira su Meesha,Farha tace"... Munanan zuwa ,yana kok'arin k'iran gidane tayi saurin dakatar dashi tace"... Plss karka fad'a yace"... Why? Tace".... Da wane ido kakeson ina kallon su mama yace".... To miye acikin tace"..... Walh da kunya plss kadaina yace".... To shikenan naji.

A hanya ya tsaya don siya mata kayan kwalama ,daga haka suka zarce gida a compound d'in gidan suka tadda   su Hishma .

Ganin kallon da Angel take matane yasata b'oyewa a bayan sa,Dukansu suka k'araso suka musu  congrat, Angel tace".... Sannu Matar bro Allah ya sauke lfya.

Fahad yace"..... Sannu kanwata Allah ya raba lfya a kunyace tace".... Amin dariya yayi yace"....to yau kuma kunyata akaejine.

Dariya dukansu sukayi daga haka suka wuce b'angaren su Deen.

Tnx Fanz I love u all.
Queen Deeja Musa.
Dah chocolate lover
[1/23, 8:45 PM] Khadeejaht hydar Novelist:

IHSANWhere stories live. Discover now