Chapter 25

646 56 7
                                    

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by  Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 25

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Kwanaki da dama sun shude, har yanzu babu wani labari akan Jinah. Yan biyu har sun fara fidda ran sake ganin mahaifiyar su. Sarah da su Abdul kullum cikin neman ta suke, amma shuru, babu alamun ta.

Wata rana da yamma, sun dawo daga neman Jinah, kamar kullum babu wani labari mai dadi. Yan biyu da Infa suna cikin dakin da ya sauka, su kuwa sauran yan gidan suna zaune tsakar gida, sun yi shuru kowa da tunanin da yake. Suna cikin wannan yanayin ne suka ji an budo kofar shigowa gidan. "Jinah" kowane da tunanin ita ce, sai dai Dauda suka gani ya shigo.

Hankalin Dauda ya tashi ganin yanayin da yan gidan suke ciki, kuma babu alamun Jinah da yan biyu.

-Ina Jinah ta take? Ina kuma yan ta......

Abinda ya fara fitowa daga bakin sa kenan. Sai dai bai kai ga karasa maganar shi ba, yaji wani ya rike kafar sa, idanun shi ya saukar a kasa, Aya ya gani. Rage tsawo Dauda yayi, sannan ya rungume ta, anan yaji a jikin shi irin damuwar da 'yar tashi take ciki.

-Me ya faru gimbiya ta? Me yasa kike kuka? Ya tambaye ta cikin sanyayar murya, duk da cen cikin ran shi, zai iya cewa ya cenki amsar tambayar sa.

-Mama ce, ba mu ganta ba, mun nema ko'ina amma bamu ganta ba. Ka nemo mana ita dan Allah. Nayi kewar ta sosai.

Dan janye ta yayi daga jikin sa, yasa hannun sa ya goge mata hawaye, sannan ya sake rungume ta, tare da yi mata alkawarin nemo mahaifiyar ta.

Karawa yayi da cewa :
-To ki daina kuka kin ji, kin san bana son ganin yar karamar gimbiya ta na kuka, kin sani ko?

Goge hawaye ta shiga yi tana gyada kai, dan uwan ta ne ya karaso wajen, Infa a bayan shi.

Ayu shi ma yaji dadin ganin Dauda, kuma shi ma kamar Aya, yayi masa alkawarin zai nemo mahaifiyar su. Hakan ya sakawa Ayu, digon kwarin gwiwa, domin yana tantamar wai Dauda zai yi abinda su suka gagara yi. Amma da yake suna son ganin mahaifiyar su, sai basu raina ta Dauda ba.

Dauda juyawa yayi ga bakon gidan, gaisawa suka yi, sannan Dauda ya tambaye shi daga ina yake kuma ya aka yi ya samu kan shi a cikin wannan gidan. Nan Infa ya fada masa, yana kan hanya ne, shi ne ya sauka anan domin ya dan huta kafin ya wuce. Hankalin Dauda bai kwanta da Infa ba. Tantamar tashi bata karu ba, har sai da suka yi musabaha, hannuwan su suka hadu. Nan kowane yaji wani abu game da dan uwan nasa.

-Nasan akwai gajiya gareka Dauda, je ka huta.

-A'a Sarah, ba zan iya ba, zan je na aje kayana sannan na fita neman Jinah.

-Amma ai dare yayi yanzu Dauda...
Cewar Sarah.

-Ba zan iya runtsawa ba da sanin cewa bansan inda Jinah take ko halin da take ciki ba.
Da fadar haka, ya nufi dakin su shi da Jinah, amma kafin nan sai da ya wuce gurin su Nafi ya tabbatar masu da zai nemo Jinah.

Dauda bai jima cikin dakin ba, Infa ya shigo.

-Waye kai?
Infa ya tambayi Dauda.

-Kai ma, kai waye?
Ya bashi amsa da irin tambayar shi.

 JINAH (Matar Aljani)Where stories live. Discover now