-Bari na rakaki.
Cewar Abdul.

-A'a!
Ta fada da karaji.

-Lafiyarki kuwa Jinah?
Cewar Sarah cike da kulawa.

-Eh lafiya nake, kar ku damu, ina son na dan fita ne na sha iska kuma ni kadai nake son tafiya. Dan Allah Sarah ki kular min da yarana.

Kalamanta na karshe sun sanyaya jikin kowa, amma ganin dai tace ba dadewa zata yi ba suka barta ta tafi ita kadai. Tana fita daga gidan, Fally ya bace da ita. Zuwa cen sai gasu sun bayyana a cikin wani surkukin dajin da babu kowa sai kukan namun dawa. Fita yayi daga jikin Jinah, wani daki ne ya bayyana a gabansu, ya dauketa ya kwantar da ita a ciki, har yanzu ba'a hayyacinta take ba. Shima zaunawa yayi dirshen a kasa yana kallonta. Yanayin dakin ne, ya tuna mashi da ranar aurenshi da Jinah, ranar da suka yi alkawarin zama na har abada, alkawarin soyayya har abada, ranar da suka yi alkawarin har abada dayansu ba zai ci amanar daya ba.

-Amma kuma ita taci amanata!
Ya fada da kakkausar murya kamar yana magana da wani.

-Ta yaudare ni! Ya sake fada. Me nayi da na cancanci haka, shin ban sota ba fiye da yadda kalmar so take ba, ban kasance mai kulawa da ita tun daga yarintar ta ba, ban sadaukar da abubuwa da dama saboda ita ba, wace irin wahala bace ban sha ba saboda ita, meye ban rasa ba saboda ita? Me yasa ba zata iya sadaukarwa daya ba saboda ni, sadaukarwa daya... Ta cancanci ta wahala kamar yanda na wahala, ta cancanta, ta cancanta...

Kalamar karshe yayi ta maimaitawa domin tabbatarwa zuciyarshi.

Zafin ma abun gareshi, yanzu babu wata alaka dake tsakaninsa da ita face yan biyu. Alakar auren dake tsakaninsu ta tarwatse, eh sosai ma, domin wanann shine a matsayin fansar kasancewarsu duka hudun a raye. Wannan yake kara sa wutar dake ci cikin zuciyarshi tana kara azalzala. Cewa yake, yanzu shikenan Jinah zata iya tarayya da kowanne irin namiji da take so, ba tare da wani abu ya samesu ba kamar a baya. A takaice dai bai san me zai yi ba, amma a halin yanzu zai nisantata da kowanne namiji, sannan zata biya bisa cin amanar da tayi.

(.....)

Har karfe tara na dare yayi, babu labarin Jinah, hankalin Sarah duk ya tashi, tana tsaye bakin kofar gida, tana kai kawo.

-Har yanzu bata dawo ba?
Cewar nafisa da suka nufo inda Sarah take, ita da dan uwan ta.

-A'a.
Sarah ta bata amsa a takaice.

-Mama ba zata dawo ba yau.
Suka ji muryar Aya a bayansu. Juyawa suka yi suna binta da kallo.

Ayu ne ya kara da cewa :
-Mama ta tafi neman magani, ba da dadewa ba zata dawo.

-Aya, fada mana ina mama?
Abdul ya dan durkusa yana tamabayar Aya.

-Ban sani ba, amma lafiya take.

Dan uwanta ya kara da cewa :
-Eh ku kwantar da hankalinku.

Shuru kowannen su yayi, kowa da tunanin da yake kafin Sarah ta katse shurun ta hanyar cewa :

-Toh ku tashi ku ci abinci kar yayi sanyi.

Washe gari ma, shuru babu labarin Jinah. Sarah bata samun damar runtsawa ba tsawon duka daren. Rana na fitowa, bayan sun gama karin kumallo, ta fita ita kadai neman Jinah, tana tambayar makota da masu wucewa amma shuru ba labari. Haka ke ta faruwa har tsawon kwana biyu. Sarah tabi duk ta rame, bata iya cin abinci, bata samun wani cikakken bacci. Su kuwa yan biyu basu gushe ba suna fada mata, mamarsu tana nan lafiya.

-Kar fa yaran nan da gaske suke?
Cewar Abdul.

-Jinah bata san kowa ba sai mu, bata tuna komai na rayuwarta ta baya, ta yaya zata iya irin wannan tafiyar?
Sarah ta fada tana goge kwalla.

 JINAH (Matar Aljani)Where stories live. Discover now