Chapter 1

161 4 0
                                    

A cafeterian makaranta suke suna shan drinks da snacks. Yanmata ne su biyu sunata hira abunsu. Daya daga cikinsu fara ce doguwa siririya me matsakaivin kyau, sunanta Zainab Musa Alqali. Dayar kuma wankan tarwada ce mai manyan idanu kuma tana da jiki. Sunanta Aisha Abubakar Yari. Dukkanninsu dalibai ne a Jami'ar FUBK dake garin Kebbi. Sababbbin dalibai ne yan UG1, Aisha na studying English while Zainab na studying History a nan makarantar. Zainab yar asalin garin Kebbi ce a karamar hukumar Aleiro, amma a Birnin Kebbi suke zama tare da iyayenta. Aisha kuma yar Kaduna ce. A unguwan rimi suke zama inda karatu ya kawota Kebbi take zaune a hostel din makarantar.

Iyayen Zainab masu hali ne daidai gwargwado kuma suna kokarin yi mata duk abinda takeso in baifi qarfinsu ba. Mahaifinta Alhaji Musa Alqali cikakken dan kasuwa ne kuma very busy mutum ne shi. Mahaifiyarta Hajiya Safiya kuma irin matannan ne da keda sakaci akan ya'yansu mussamman ma dayake Zainab kadai ce 'yar da ta haifa. Kwata kwata bata yi mata fada kuma tana barinta tayi duk abinda taga dama.

Aisha kuwa iyayenta na a cikin kashin mutanen da za'a kira da lower class people, Wato wadanda basuda wadata sosai. Mahaifin ta Malam Abubakar ya rasu tun tanada shekaru 10 a duniya. Mahaifiyarta Mama Halima ta sake yin wani auren inda ta haifi 'ya'ya biyu da sabon mijin ta Malam Musa. Sunan 'ya'yan Shehu da Khadija. Wannan kenan.

"Aisha, yakamata ace fa mun tashi daga wurinnan mun tafi class kinsan Mal. Nura ba mutuncine dashi ba" cewar Zainab tana kokarin saka wayarta cikin jaka. "Dadi na dake wallahi kin cika tsoro. Toh mala'ikan mutuwa ne shi? Ace lecture din gst ma sai an takurawa mutum mtss". Cewar Aisha tana ta yamutsa fuska irin bata damunnan ba. "Naji dai ki tashi muje nikam". Hakadai badon Aisha taso ba tabi Zainab suka nufi auditorium inda ake lectures din. Sun shiga suka tarad lecturan baizo ba. Shigarsu keda wuya sai gashi ya shigo yayi lecturen shi ya basu assignment ya tafi abinshi. Koda aka gama lecturen lokacin sallah yayi sbd haka direct suka tafi school mosque don gabatar da sallar Azahar. Dayake wannan shine lecture na qarshe a ranan, Zainab ta nufi bus stop ta wuce gida Aisha kuma ta koma hostel. Aisha na shiga room dinsu ta ajiye jakanta ta shiga bayi tayi wanka. Bayan ta fito ta dafa indomie taci tashirya taje classes inda a can ne takeyin assignments dinta. Tana zaune tana browsing a wayarta taji anyi mata sallama. Da farko ta share sai da ya kuma yin sallamar a karo na uku sannan ta dago ta kalleshi tare da amsa masa sallamar. Dogowanta keda wuya ta furta 'hasbunallahu wa ni'imal wakeel' a cikin zuciyarta saboda kyaun halittar dake gabanta. SULTAN kenan wanda yan makarantar keyima laqani da 'mai martaba' kasancewarshi 'da ga Sarkin Argungu, Kebbi. Ganin ta tsura masa na mujiya yasashi dan bata fuska. Sun dauki 5 seconds a haka kafin yace "malama pls ki dubamun cikin locker nan na bar makulli a ciki". Jin abinda yace ne yasa Aisha kawar da idonta daga kallonsa da takeyi, tasa hannu a cikin lockern ta dauko wani makullin mota. Miqa masa tayi tare da tambayarsa in wannan ne key dinda yake nema. Bai ce komai ba ya gyada mata kai kawai. Karba yayi ya juya ya tafi abinshi inda Aisha taji haushinshi don duk daukanta toasting dinta yazo yi. A haka dai ta gama assignment dinta ya wuce hostel cike da mamakin wannan guy din.

University Divas (A Hausa Love Story)Where stories live. Discover now