8

190 9 0
                                    


Mahbub ya kwana yana sake² a ransa yana tunanin miye dalilin da yasa wa in nan mutanen suka je masa gida,iyakar tunanin sa yayi amma be fahimci kome ba,shi dai baya da abokin fada bare yace turo masa akayi,a ransa yace koma dai waye Allah baya bacci kuma zaya tona asirinsu da gaggawa,da yaga kwanciya akan sofa baze masa ba,toilet in palour ya shiga ya dauro Alwalah tare da jera na filfili,yana rokon Allah ya kare su daga tarkon azzalumai,ya rufa masu asiri ya kabe  ko wace fitina a aurensu ya basu zaman lafiya shida Fatima.

A dai² wannan lokacin kuwa Gwaggo na can tana aikin siddabarun da boka ya bata,ta fitar da bakar tukunya daga karkashin gadon da fanta take kwance akai tana bacci,dama boka yace mata tayi yanda zata yi Fanta ta kwana a dakinta,ta dade Rana wasu surutai na tsafi ka fin ta kira sunan Mahbub Dana Fanta ta saka a farar tukunya,sunan Mahbub kuma da Izzy a bakar tukunya,bayan ta gama ba tare da dubawa ta tura a karkashin gado tare da kwanciya cikin tsananin farin ciki.

Abban su Mahbub kuwa a ransa yana matukar mamaki meya lalata dakin Mahbub kuma bayan da kansa ya shiga dakin kuma ya gansa lafiya qlau,amma meyasa Hajiya tace haka cewa da gwaggo,a ransa yace koma dai me take nufi ai zangani,a ransa yaji dadin komawarta dakin ta don a nasa dakin takura masa take yi ta zame masa karfen kafa.

    Mahbub yana duke yana kai kukansa ga Allah har saida aka kira sallan asuba sannan ya mike tare da yin raka'atainul fijr, sannan yayi shirin zuwa masallaci,dai² lokacin da Mahbub ya bude kofar falonsu da niyyar zuwa masallaci yayi dai² da fitowan Abbansa wanda a tare suka jera zuwa masallaci.

Gwaggo kuwa kaman jiraye take su Mahboub suje masallaci ta sauko da sauri daga kan gadon ta,ta jawo tukunya ta fita da sauri zuwa bayan gida,ta daga tukunyar ta saki a kasa tana fashewa seda gidan ya girgiza

Shamo yakalli mahbub ,kadau motarka da megadinka bama bukatar sake ganinku,biliya sa su ahanya.har parking space biliya yakaiku,sannan mahbub yashiga yatada mota Fanta agaba sambo megadi abaya,jikinsu se rawa yake .bayan sunhau titi ne mahbub yakalli fanta,fatima Dan Allah kiyi hakuri kedana kukannan dakike ai kamata yai mugodewa Allah dayasa basu hallakamuba kosu nakasta wani barin ajikinmu.ko bahakane baba sambo?

Sambo megadi Wanda shima jikinsa rawa yake dakyar yaba mahbub amsa,kwarai kuwa mahbub addu'a itace,mahbub ya girgixa Kansa kawai Allah de yashiga tsakanin nagari da mugu amma tabbas wa'innan mutanen sundade da shiga gidan baba sambo inaga lokacin kana bacci sukashigo ko katafi masallaci yin sallah.

Baba sambo yace mahbub tabbas wa'innan mutane nagansu naga kuma sanda sukaxo,mahbub yakalleshi kallon mamaki sannan yajuya yacigaba da driving dindayake,baba sambo yace wato mahbub nafuto daga masallaci kenan xanshiga gidah se aka hasko fitila ta haske min Ido to senasa hannuna nakare ,nashiga cikin gidah shigata kedawuya aka fara bubbuga kofar gate,naxata baki akayi ma,to budewata keda wuya sukashigo ciki,nake amasu suwaye sukace banida bukatar nasani,babban cikinsu yasa suka kamani yace wani dagacikinsu yadura mani Valium(maganin bacci)akakawoshi a gora suka kamani iyakar kokarina nayi nakwace amma nakasa haka suka duramin duka to wallahy bankara sanin inda kaina yakeba seyanxu damuka shigo mota,tun karfe 8 seyanxu karfe 1:30.

Mahbub yace Allah ya kyauta kosuwaye ubangiji Allah yatona masu asiri,tabbas baba sambo daxu damuka dawo senine nabude gate nakulle nattattashekama Baka tashiba senai tsammanin bacci ne yadan daukeka,ashe abunda suka maka kenan...hmm yanxu de bari muje gidah kawai idan Allah yakaimu dasafe semusan yadda xa'ai..

Karfe 2:00 Dede nadare mahbub yai horn kusan sau uku sannan danjuma megadi yatashi dakyar yana mitsiitsike Ido sannan yabude masu gate din ganin motar mahbub ce ,mahbub ne yabude motar suka futo ,mahbub yacewa danjuma megadi ga baba sambo nan yakaishi dakinsu su kwana.sannan yarike hannun Fanta sukai hanyar shiga cikin gidan Wanda nanma akullen yake😩

Bubbugawa yai nanmade shiru ,bugunne yai yawa Wanda baba yamike daga kangado yakunna fitila,kunnawar futalar kenan gwaggo tatashi itama.baba yakalleta hindatu kema kinji karar bugun kofako?gwaggo wadda ita allale itama batasan suwaye ba se pretending data karayi😏hadda dafe kirji to waye haka atsohon darennan?sede musamman mugani kila danjuma ne megadi....

Sauka Kasan sukai atare,gwaggo tadakko key tabude,ja bayatai hade da salati,mahbub kune haka atsohon darennan?baba was speechless ma kallonsu kawai yake,Fanta tagayshesu duk kunya ta isheta gata ha sirikanta.mahbub ya kakaro murmushin dole,mune gwaggo abinde sede godiar Allah dakuka ganmu ma daranmu da lapiar mu.

Shiga ciki sukai duka sannan suka xauna Akan kujeru Banda Fanta wadda akai akai taxauna taki.atake Alh sulaiman yaji yarinyar takara shiga ransa tabbas ya yaba da hankali fantan kwarai..baba yakalli mahbub kasamu aduhu mahbub meyafaru??baba wallahy barayi ne suka shigo mana gidah.gwaggo tace tayaya ba akwai megadi ba?ehh akwai megadi ai forcing dinsa sukai yabude masu gidan tunmisalin karfe 8 nadare sannan suka dura mashi valium to be Farka bade saiyanxu damuka taho,baba yace to ba abinda sukaimakude ko?

Mahbub yagirgixa kansa ba abinda sukai mana baba,illade sunce karmu sake mukoma gidan Dan inde muka koma to munshiga mafarin MATSALAR RAYUWAR mu.sunbarni nataho da mota ta ma.amma nabarsu cikin gidan.sede da safe nai wa police magana ai investigating Akan hakan.baba yace to Allah yatona asirin kosuwaye.gaba daya sukace amiin..

Baba yace to seku xauna anan gidah kafin asamu wani wurin shi wancan din se asashi akasuwa kawai.mahbub yace eh dama haka nai planning kawai Dan jiama naga Cyprus sunyi emailing dina Akan offer tafuto,so xanje may be by next week naji yadda akecikiba.Allah yatemaka amma da ita matar taka xaka tafi ko?a'a baba saboda nayi planning xansata a school.baba yace eh hakanma yayi.mikewa Alh sulayman yayi yahau sama bayan yace suma suje su kwanta dare yayi.se gwaggo dayabari agunsu.

Mahbub yamike yanadan Sosa keya to Bari nimade na kwanta,gwaggo talura so yake tatashi yacewa matarsa sutafi.gwaggo itama mikewar tai to seda safe mahbub ai dama a parlor ka kwana dakinnan Bakaganiba shirgi ne fal aciki aibaxeyuwu Akwana acikiba,ita fatiman seta kwana adakina kafin dasafe delu tagyara nakan,bayadda mahbub ya iya dakyar ya iya furta hakanma yayi gwaggo Allah yatashemu lapia.

Hawa saman sukai itada Fanta shikuma yakakkabe kujerar yakwanta,ransa inyayi dubu abace yake,gwaggo tabata Mai moment......

MATSALAR RAYUWA(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now