ZAHRAH HAYATY....3/4

120 8 3
                                    

_*ZAHRAH_HAYATYY....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_
_Intelligent writer's association_

*Assalamu Alaikum y'an uwa masoya dakuma abokanan arziki.*
*Hak'ik'a naji dad'i matuk'a gameda yanda kuka nunaman kulawarku,musamman ATK PALACE, ZAHRAH HAYATY FANS CLUB, AYSHA GARKUWA HAUSA NOVELS, AUFANA TRUE FANS, INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION, ZAUREN SAINAH and others.*
*Tabbas bakasanin cikekken masoyinka dakuma cikekken mak'iyinki saika samu kokuma ka rasa.*
*Bazan iya cemaku komaiba sai Allah isaka da alkhairi yabar k'auna dakuma zumunci, nagode nagode sosai,waenda suka kirani nad'aga dama waenda bansamu damar d'agawaba dik ina matuk'ar gdy kwarai, mahaifiyata tasha kyakyawan adduoinku ubangiji ya karb'a yakuma saka maku da mafificin alkhairinsa ameen.*
*Tabbas kimanin sati uku anshigo nahud'u kenan danarasa mahaifiyata 😭abar k'aunata my first teacher in the world, ubangiji mai rahama ya lullub'eta da rahamarsa ameen.*
       *Nagode...Nagode...Nagode sosai.*👏❤️💔🌷

   _Page 3/4...._

Yana fitowa saiya had'u da mutallab shima zaije masjid d'in, danhaka suka fice atare.

Basu dawo gidaba sai kusan 9:00pm,kai tsaye side d'in mahaifansu suka fice domin gaidasu sukumayi dinner, makeken side ne wanda yake d'auke da manyan d'akuna da parlors barkatai waenda wasunsuma bakowa acikinsu rufe kawai suke.

Gidan kantameme ne iya kallonka iya ganinka bazaka iya kallacesa lokaci daya ba sbd girmansa da had'uwarsa, awajen gidan koina korayen shuke shuke ne masu kyan kallo, greens carpet yarufe koina saikuma flowers green masu kyau diffident colors.

A daidai tsakiyan gidan akai tamfatsetsen gini mai d'auke da side uku da boys quarters aciki, d'ayan side din na bak'i ne saikuma d'ayan yayan gidan maza,saikuma dayan wanda yafi kowanne shine na iyayen gida da yaya mata.

CIKEKKEN LABARINSA....

HAYATUDEEN HASHIM MATAWALLE shine cikekken sunansa, d'an asalin jihar kebbi haifaffen garin yola adamawa, yayi karatinsa na primary da secondary a yola inda yaje turkeysh international university a kasar Turkish yai degree dinsa na farko sannan yadawo gida.

Alhj hashim matawalle wanda akafi sani da matawallen fulani dakuma hajiya Asma'u ibrahim wacca akafi sani da hajiya jod'a sune iyayensa dikansu yan asalin jihar kebbi ne zama yakaisu yola acan kuma aka haifi aunty mamu da hayat, daga baya kuma suka dawo kebbi.

Hayat su bakwai iyayensu suka haifa kuma shine na biyu a haihuwa bayan aunty maryam wacca suke kira da aunty mamu, sai shi hayat sai hairan sai humaira sai hunaiz sai hashim mai sunan mahaifinsu suna kiransa da gid'ado sai auta mud'ia.

To saikuma yayanda abbansu ya d'akko na yan uwa, mutallab uthman, abbakar dakuma siyama.

Aunty mamu tai aure tanada yaya uku, Akeelah, Ahlan, Ammun, saikuma k'anwarsa hairan itama tanada yaya uku, Aysha Aryan dakuma Noor, humaira ana gab dayin bikinta itama.

Danhaka gidansu hayat family house ne.
Mahaifinsu lauyane mai zaman kansa mahaifiyarsu kuma house wife ce kawai, kakansu kuma wanda shine ainahin matawalle chiefe justice ne a babbar kotun k'olu dake babban birnin tarayya habuja.

Abbansu hayat su ukune kacal agun mahaifinsu justice Abubakar matawalle, barrister hisham matawalle sai Doctor hashim matawalle sai barrister hidayatu matawalle, kowannensu akalla yanada yaya shida zowa bakwai hidaya ce kawai keda biyar mutallab ne nafarko sai muwaddah dakuma sauran kannensu.

Hayat shine jika namiji nafarko a ahalin matawalle shys aka d'auki san duniyar nan aka d'oramasa, kowadai hayat kuma komai hayat, dikda daga baya ansamu yaya mazan amma hakan bairage soyayyarsaba ko kadan, musamman kakansa justice matawalle, yanamatukar kaunar hayat aransa.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now