ZAHRAH HAYATY....7/8

35 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *7/8*
Daganan Kai tsaye gida suka isa, saidai mutallab kam yana sauke hayat yakoma hospital domin akwai aikinda yabari acan mai tarin yawa, danhaka can yawuce a tinaninsa ma can zai kwana.

Hayat kowa yana shiga Kai tsaye wanka yashige bayan yafito jallabiya kawai yasaka yafice masjid.

Baidawoba har saida yai sallar isha sannan yadawo gida, kai tsaye side din mahaifansa yafice kamar yanda suka saba,saidai yaukam abinci kawai yaci sbd  d'an uwansa bayanan bayajin dad'i sbd atare suka saba ci.

Danhaka yana gama cin abincin yadawo side d'insu, wayarsa yaciro yashiga dialing No din Fatimar sa, bugu d'aya ana biyu tad'aga, cikin fara'a da jin dad'i tafara mashi magana "Halloo....gud evening my darling broz" wani irin farinciki yaji ya mamayeshi sbd jin zazzak'ar muryar abar k'aunarsa "evening my lovely baby, hope baby na tawuni cikin k'oshin lfy" cikin yanayin murmushi tace "Lfy klw nawuni my love, hope kaima hk" yace "yes.....am fine.

Fira sukayi sosai anan take gaba daya yamanta da damuwarsa, hayat yana matuk'ar abar kaunarsa fatima haka itama tana sanshi sosai, acikin firarsu yake cemata "baby na, Insha Allah nasamo maganin matsalarmu, inaji ajikina matsalarmu tazo k'arshe, inagab da mallakarki amatsayin matata" wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyarta cikin zumudi da d'oki tace "kabani lbrn inda kasamo maganin matsalarmu, menene shi maganin...?" murmushi yai kamar yanda yasaba yace "ki kwantarda hankalinki, idan komai ya kammala zanfad'a maki, but....now inacigaba da bincike ne."

D'an shuru tai nawasu mintina kamin tace "hayaty.....bansan meyasa ubangiji yake jarabtana ba da waennan matsalolin, wlh ni bansan Ina kashe kowaba ni bantab'a sanin Ina kisaba, Amma Sai ayita fad'a wai ni ina kisa Ina kashe mutane" tak'arisa zancen cikin yanayin kuka da zubda kwallah.

Nannauyan numfashi hayat yasauke Hmmm........! sannan yace "ki kwantarda hankalinki Fatima kidaina kuka, Allah zai kawo mafita, kishare hawayenki ni namaki alk'awarin saina wankeki daga zarginda ake maki, amma kafin nan Inaso kifad'amin gskyr wani lamari".

Dasauri tace "mekenan.." gyara zamansa yai sannan yace "fatima Inaso kifad'amin gsky, shin kinada yar uwa ko kanwa wacca kuke kamanceceniya daita, kokuma shin ke twins ce ma'ana tagwaye....?" kamar zowan bazata haka taji tambayar tasa.

Cikin mamaki tace masa "meyasa kamin wannan tambayar hayaty...?" ahankali yace "bakomai, kawaidai inaso nasani ne sbd wani kwakkwaran dalili" hmm.....tasauke numfashi sannan tace "a'a nikam nikad'ai momy na tahaifa sannan koda a family namu banida wacca muke kamanceceniya kamar twins" murmushi yai sannan yace "Ohk....abar zancen".

Mamaki yacika fatima sosai da tambayar hayat, amma sbd sanin halinsa yasa tabar zancen kamar yanda yabuk'ata.

Firarsu sukacigaba dayi tsawon lkc kamin daga bisani sukayiwa juna sallama.

Washe gari kamar yanda yasaba yashirya yafice office, saidai harya fita mutallab baidawoba, danhaka yana fita yakirasa a waya, bayan sunyi waya sannan yafice office.

Yaudai kusan atare suka dawo gida shi da mutallab,sakamakon dik basuda wani aiki sosai ayau, cikin sa'a kuma saisuka tarar ayaune mahaifinsu zai dawo daga habuja, danhaka cike suke da tarin farinciki.

Tinda suka dawo suna cikin gida tareda mahaifiyarsu da yan uwansu, around 6:30pm sukaje airport d'aukoshi, ummi kowa sai hidima take da shirye shiryen tarban maigidanta, tatsala wanka sai k'amshi take, nikwa nace ummi harda ku bazaku barmana ba mu yara, hhh Lol.

7:00pm dot jirginsu yasauka, cike da tsintsar farinciki yarungume yaran nasa suma suka rungumesa cikin farincikin dawowar mahaifinsu, nan suka kwa shi kayansa suka d'aukosa suka dawo gida.

Adaren dai haka sukai kusan rabin sa suna murna da farincikin dawowar mahaifinsu, atare sukai dinner sunatashan fira a babban parlonsa itadai ummi sai kallonsu take tana murmushi.

Can abba yadubesu yakira sunan hayat "Hayatudeen.....!" saiya kalli mahaifinsa cikin nutsuwa tareda amsawa da "Na am abba..." abba yagyara zamansa sannan yace "babban dalilinda yakainu habuja gun matawalle a wannan karon shine, matsalar yarinyarda kace kanason aura wato Fatimah" sadda kansa yai k'asa yana sauraren mahaifin nasa cikin nutsuwa.

Cigaba abba yayi da magana "hayatudeen.....inaso kasani, kaifa d'an babban gidane kafito ne daga tsatso mai kyau, sannan karka kamanta Kaine d'a namiji nafarko damuka haifa a wannan familyn, kaine za'aga abu agunka ayi koyi, ma'ana k'annenka na baya, sbd haka wannan ahalin bamu bazamu tab'a yarda kadakko wani ahali mara tushe da kyakkyawon tsatso ka kawo mana acikin gida, kasani fatima bawai asali mai kyau ne batada ba, a'a wannan matsalar tata ta maita tasamo asaline tindaga wani kaka nata wanda shine mahaifin kakanta, danhaka kasani wlh bazamu tab'a yarda ka aureta, kaje kanemo dik wata y'a a duniyar nan ka kawomana mukuma zamuje koma inane mu auro maka ita Amma ba fatima ba".

Tinda abba yafara magana da hayat ya sadda kansa k'asa baid'agoba harsaida yagama, kuma bai iya cewa uffan ba, hakama mutallab, ummi ce tace "ahto k'ara fad'amasa dai, kananik'ewa yarinya d'aya kamar yar gwal, ga tarin yammata nan masu kyau yayan alfarma, ga yayan abokanan mahaifinka nan dakuma na abokanaina, gakuma tarin yammatanda keta nunamaka so amma fafur yaron nan kakafe sai wata wai fatima".

Mutallab dai hkr yashiga bama ummi sbd dama ita akan wannan matsalar tad'auki zafi sosai, gogan kowa bai iyacewa komaiba.

Har saida abba yace sutashi suje su kwanta sbd gobe akwai office, koda hayat yad'ago kowa, fararan idanuwan nan nasa sunkad'a sunyi zajir,nan sukamasu saida safe suka fice side dinsu.

Koda suka isa can side din nasu, kwanciya yai yad'aga kansa sama yana sauke nauyayan numfashi atare, mutallab yadafasa tareda fadin "Cool down broz" yad'ago ya kallesa sannan yasake juyawa.

Adaren ranar haka yakwashesa batareda yasamu isasshen bacci ba, washe gari kuma tinda sassafe yashirya yafice office, anan yabar mutallab domin yace sai rana zai fita.

Around 3:00pm dot yabaro office dinsa yaje yad'auki mutallab a gida, kai tsaye k'auyensu zahrah suka fice.

Hmm..........! Is just the begng🥰 just follow me guyz.

#Aufana for life❤️

ZAHRAH HAYATY Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz