ZAHRAH HATAY...1/2

174 13 4
                                    

_*ZAHRAH_HAYATYY......_*🌷

_*BY~AUFANA_*
_Wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent Writers Association_*

_*Aslm...Alkm....my people._*
_*Alhmdllh....am back again,nasake dawo maku da sabon book d'ina mai taken ZAHRAH HAYATY...wanda yake d'auke da sabon salo mai cike da rikitarwa rud'arwa tashin hankali hargitsi soyayya dakuma ban tausayi._*

_*And then ZAHRAH HAYATY...is free novel, so bana kud'i bane,and dik mai buk'atar complete na MUJARRABI akwaishi yanzu haka ak'asa,so if u like saika biya kud'i 300 kacal kokuma recharge card 200, idan kana buk'ata saikaman mgn,09097978183 WhatsApp No._*
 
_*Ina mik'o sak'on gaisuwa da jinjina ta bangirma ga zak'ak'urai fasihai kuma jajirtattun marubutan matashiyar k'ungiyarnan ta Intelligent Writers Associaion, hakika kuna matuk'ar kkr Allah yak'ara maku basira da lfyr rubutu,Allah kuma yak'a kareku daga sharrin mak'iya da mahassada ameen,Love u all_*💔

   _Page 1/2...._

Kebbi State.....
Birnin kebbi Local Gvmnt.
6:45pm.....
Zaune yake akan kujera cikin office d'insa yadafe kansa da d'ayan hanunsa kujerarda yake akai kuma tana juyi dashi left to right.

Da'alama dai yai zurfi sosai acikin duniyar tinani wanda yasanyashi shiga wani yanayin nadaban,duhun magrib yana shigowa gashi wajen yai tsit bakowa sai kukan tsintsaye dakake jiyowa.

Bai ankaraba kwatsam yafarajin saukan ruwan sama marasa k'arfi,hakan ne yadawodashi daga duniyar tinani izowa duniyarsa,dasauri yamike dagakan kujera yaje gun window yana lek'on wajen saiyaga ashe kowa ya watse,danhaka yadawo yad'akko wayarsa yashiga dialing d'in wata number.

Bugu d'aya ana biyu aka d'aga saiyafara magana ahankali cikin murya mai rauni "broz kazo kad'aukeni pls...ina office banzo da motanaba yau" banji abunda akaceba a d'ayan b'angaren saiyace "ok...am waiting for u" daganan yakatse wayar sannan yazauna.

Still sake dafe kansa yai amma wannan karon kan sama yad'agasa alamar yanacikin damuwa matsananciya yayinda kuma lokaci bayan lokaci yake sauke nannauyan numfashi.

Bayan dakamar 15mnts saiga wanda yakira yaiso yana murmushi yak'ariso yana fad'in "hey broz...what's happening men naga dik kawani hargitse haka kaman ba HAYAT....d'inda nasani ba" d'an murmushi kawai yai yad'auki rigarsa da jakarsa da wayarsa sannan yajuya yana fad'in "hmm....bari kawai mutallab,muje mota kaji sauran zancen" mutallab yabi bayansa yana murmushi.

Koda suka fito bakowa a waje wurin yai tsit sai kukan tsintsaye da sanyin shuke shuken dake harabar wajen saikuma securitys dake kai kawo awajen suna aikinsu, da'alama dai wurin company ne sbd naga asama anrubuta hayat international nigerian companyn Lmt. hakan ya tabbatar da tabbas company ne.

Ginin companyn kowa ak'alla zaikai hawa ashirin ga ginin yamatuk'ar tsaruwa dakuma had'uwa,shape din ginin kamar zanen kifi Lol.

Atare sukai saurin shiga mota sbd ruwanda akeyi dikda ba masu k'arfi bane sosai,nan mutallab d'in yatada motar sukabar wajen.

Ahankali suna tafiya mutallab yace "inajinka hayat,meya farune naga tsintsar damuwa bayyane a fuskarsa" numfashi hayat yasauke sannan yafara magana cikin yanayin damuwa "mutallab waccan matsalardaice wacca kasani tin a baya,mutallab ina matuk'ar son fatima kuma itace nakeda burin tazama uwar yayana, amma mutallab bansan yazanyi nashawo kan matsalarta ba,inaso nataimaketa kota halin k'akane" d'an gyara zama mutallab yai sannan yace "hayat...taya zaka iya taimakon fatima bayan ka tabbatarda cewa itace ke aikata waennan laifukan, kasanifa dik ranarda asiri yatonu mutane da police sukasan cewa itace ke aikata waennan laifukan, to tabbas ba makawa hukuncin kisa shine hukuncinta, to taya zaka yarda ka aureta, dikda cewar kowa zarginta ne yake bawanda yatabbatarda hakan amma ni dana san gsky kana tinanin zan bari ka auretane bayan nasan gakyr lamarin....?".

ZAHRAH HAYATY Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum