Daukar motar yai sannan yanufi gidansu AYUSH dayake bawani nisa tsakaninsu shi gidan Barr habeeb a garki 2 yake,yana xuwa yai parking motar tareda yiwa gateman magana kan yayi maso xuwa ciki,sannan yafuto yace ance kashiga,yana xuwa yaxauna a parlor din dasuke xama tareda dakko ledar cards din ya ajiye akan center table din dake parlor din.nadia tashigo da sallamarta TA ajiye mai lemo da ruwa,tadan sunkuya kadan inayini?se asannan yadago idanuwansa yasauke akanta,lapia qlau ,nasameku lapia???lapia Lou Alhmdlh..Tana xuwa kadanyi hakuri,,NAUFAAL yai murmushi abakomi I'm not in a haste..koxansan sunan sister in law,,Nadia tai Daria sunana Nadia..NAUFAAL yace toh Nadia nagode sosai nisunana NAUFAAL.nadia tace Tohm NAUFAAL Nima nagode sannan tamike tafice,,kodata hau sama samin AYUSH tai cikin bargo ta lulluba,lapiar ki kuwa AYUSH???ayush ta girgixa mata Kai period pain nake Dan Allah kira mommy Tamin allura pls ,,Nadia tace toh sannan kitashi ki gyara mijinki yana kasa...dukda azabar ciwon da mararta keyi hakan besa tadago ta hararetaba,nide umarni nabaki ki kiramin mommy..Nadia tafice xaune tasamu mommy na ninke sallah tai sallah,mommy AYUSH ce wai pp dinta yaxo wai allura xaki mata,mommy tace toh inaxuwa,sannan Nadia tace mommy NAUFAAL kuma yaxo wajenta yana guest parlor nafada mata tace ita batada lapia..

Mommy de Batai magana ba illah hada allurarta datai sannan tanufi saman,tabude dakin Tana kallon AYUSH data kudindine kamar kayan wanki,tashi namaki alluran,mikewa AYUSH tai sannan mommy tai mata,,kallon Kayan jikinta mommy tai atamface orange me xanen flower chill green,bude drawer tai taciro mata hijabi green TA mika mata saka kije kasa kinyi bako yana guest parlor,sannan tai ficewarta,mikewa AYUSH tai ga mararta se azabar ciwo take mata.hijabi ta zumbula tana tafiya akan stairs tana mita azuciarta lalle wannan sokake musa kafar wando daya dakai,mutum bashida lapia dolene.janyo fuskar hijabinta tai tadora akan hancinta ba aganin komi se idonta (irin yadda yammata suke  insunajin kunya )sannan tashiga parlor din tareda sallamarta iya ciki tanufi can karshen kujera taxauna tareda saukar da kanta kasa,,,NAUFAAL yai murmushi ganin yadda tai da hijabinta kamar Wata yarinya,,bedamuba yace malama hawwa'u nasameku lpy??sannan Nabeelah auta tace tana miko sakon gaysuwarta sosai,se asannan AYUSH tai magana to nagode Nima Ina gaysheta...NAUFAAL yatashi da kansa ya aje mata katinan daurin aure agabnta gashi wannan koxakiba abba irin namu sample din naji gateman dinku yace yayi tafiya.

AYUSH tace uhm..NAUFAAL yace tohm batin events yaxasu kasance kenan??ayush tace ni babu event din dankeso mugidanmu ba yan bidi'a bane rana daya ake gama Komi...dukda maganar datai ta bigeshi amma yashare kawai ohh really?!nidanake cikakkaken Dan ahlul sunnah Inani Ina bidi'a dama Dan karkice ankwareki ne amma nima bawannan a schedule dina,,,to kaman nawa kike bukata na abubuwan daxaki gudanar na biki???AYUSH itade kanta akasa Tana wasa da yan yatsunta babu abinda nake bukata Nagode,,,sauri tai tamike Dan maganarsama Kara mata wani tukukin bakin ciki take bata yadda sunhada Ido ba takauda kanta gefe tare da fadin my regards to your sisters sannan tasakai xata fice NAUFAAL yai saurin dakatar da ita Dan Allah to danturomin Nadia...sannan tasakai tafice ,a kofar kitchen tahadu da Nadia wadda tasoyo wainar fulawarta Akan plate.kije inji shi yana jiranki,Nadia tace lapia ??ayush tace oho muku inkinje kyaji,,plate din hannunta ta ajiye tanufi parlor din itakuma AYUSH tai sauri tadauke tanufi sama da gudunta tareda mirza key adakin tanata dariar mugunta musamman dataga yadda wainar tasha hadi harda yankakken tumatir da albasa a gefe ga yaji,,,

Haka AYUSH taci gabada dariar ta sannan tadakko ruwanta a mini freedge din dake parlor ,taxauna tafaraci tanaci tana dariar mugunta,sedata gama cinyewa tsaf sannan ta ture plate din gefen gado hade da tashi tawanko hannunta jinta tai dam cikinnta yacika ga marar tadena ciwo.hawakan stool din dressing mirror tai taxauna tana murmushi yau na mutu gashasshiya idan Nadia takamani sannan tai sauri ta kunna tv hada dasa Korean series film din the mask sannan tai kwanciyarta tana kallo hankali kwance .

Nadia nashiga parlor din da sallamarta sannan tanemi waje tazauna.naufaal yace Yawwa  nadia naji dadin zuwanki,munyi magana da hawwa_jiddah Akan shirye shiryen biki tanunamin ita she's not interested.shysa nace to barin miki magana ko akwai abinda kukeso nagame da bikin Kinga lokaci na kurewa yaufa  saura kwana 8.nadia tai murmushi toh gaskia bikin event daya xa'ai in aka daura aure da safe to karfe 2:30 xa'afara kamu da yamma kuma za'ai lunch shikenan ,se dare akai amarya..amma bnsaniba ko xa'ai bridal shower dinnan na xamani?kasan brides biyu xa'ai biki xa'ahada da neerah half sister dinta so inaga shysa tace maka ba komi,NAUFAAL yace to atleast de ai xaku Danyi amfani da kudi ko???nadia tace ehh ba mamaki,amma da Baka wahalar da kankaba brother in law babaa yabada Komi Wlhy..

NAUFAAL yace ai ba roka kukaiba ni nayi niyya sannan yaxaro wrapper din shegu bugun abuja 100k cif yamika mata tareda dakko leda yamika mata gashi ki bata wannan kudin koki rike a hannunki dan nasan hardly ne takarba sannan wannan ma kibata me pink gidan nakine...sannan ya mike nixan wuce kigaida mommy naso mugaysa amma Kinga yau xankoma flight din 8 ne sena koma tagidan abokina nagode sister in law,,Nadia tace brother in law harda wahala?!mungode sosai Allah yasaka da alkhairi seyaushe kuma??naufaal yace a'a I don't think xansake zuwa may be se ranar biki saboda akwai abubuwa daxanyi dayawa,Nadia tace toh Allah yabada sa'a mungode..sannan tarakashi yatafi...(nikwa miss xoxo nace Nadia kinfiya shisshigi dayawa ,NAUFAAL de na AYUSH ne ita kadai)

Koda Nadia takoma bata wuce dakinsu ba wajen mommy tanufa,tana zaune Tana karanta wani littafi dietetics,sallama Nadia tai sannan tashiga,mommy dake karatu tadago takalleta,Nadia tace mommy Kinga NAUFAAL mijin AYUSH ne yace nakai mata dawannan kudin wai na shirye shiryen biki koxata bukata.mommy tarufe littafin Tana kallon ledar Kai wannan yaro baya gajiya da wahala duk wannan lefen daya lafta kaya kaman ba gobe shine yakuma bada kudi abata?sunyi yawa Wlhy.se asannan Nadia tabude leden kwali kwara uku ne daya yellow daya purple daya pink..Nadia tace wai yace me pink gidan nawane I wonder meyema?budewan daxasi wasu tsadaddun kayane dogwayen riguna Wanda su mommy dinma basu taba ganiba duk yadda akai couture ne irin na America dinnan,me yellow kwalin bakar rigace dawasu shegun stones anyi kwalliya dasu basuda mayafi sede turban haka,itama purple din haka take hartafi yellow dinma Kyau sannan pink dinma nada Kyau sosai.

Mommy tace sunyi Kyau Wlhy angode amma wannan kudin jeki nuna mata kikawo gaskia sunyi yawa,Bari alhaji yadawo yakira shi baban NAUFAAL din,haba wannan wahalar har ina?aa baride alhajin yadawo!!!nadia tafice Tana Daria a'a mommy mu kibarmu mu dandali arziki,,tana tafe tana hango ranar daxa tasaka Kayan abiki tadubi bench din data Dora wainar fulawarta ba ita ba alamar ta.hawa saman tai a fusace tashiga dakin,zaune tasamu AYUSH shabe shabe Tana kuka..kekuma meye hakan?!AYUSH tagoge hawayen fuskarta haba wannan makirci har ina kalli yanda Kim ha joon yakesan yi kyung amma makircin seo yeon tayi kane Kane tashiga tsakani.

Mtscew Nadia taja tsaki ke wannan yashafa wadda batada aikinyi se kallon Korean film,ki xauna de kina Bawa kallo hakkinsa bakisan ciwon kankiba,,abinka da marar gaskiya itade AYUSH shiru tai tasan wannan fadan na Nadia dan tacinye mata wainar tane amma azahirin gaskiya nadia batada zafi.nadia tace sannan Abu na biyu nasha wahala nayi wainar fulawata meye naki nacinyewa?!wallahi tallahi kinji rantsuwar musulmi narantse da Allah sekin biyani kuma ayau dinnan irin wadda nayi kuma inba sokike infadawa baabaa ba.AYUSH tai shiru naji xanbiyaki barin karasa wannan episode din se insa shemau tasoya maki,,Nadia takalleta tareda hararta wacce shemau kenan bade shemau me aiki ba yarinyar da wanka Ma batayi se juma'a juma'a,kinaki tunmuna sheda juna nidake Wlhy babu Dan aikin daxe soyamin tunda basu sukaciba kedah kika zauna kika cinye dukkoda kinsan babaki naiba haka zalika xaki shiga kitchen kisoyamin Wata kamar yadda naiwa tawa hadi.

AYUSH se wiki wiki take da Ido to to naji xansoya maki naji,shikenan??nadia tace ehh shikenan sannan tadauki ledar tadora mata Akan Cinya gashi inji mijinki wannan kudinma yace abaki ki hidimar biki da ita,inkingama kallon komeye a ledan na pink kwalin tawace. AYUSH tai wurgi da kudin da ledar data Dora mata xaki iya amfani dasu duka Ma wannan ba matsala na bane ,Nadia tace umarni akamin bawai Neman shawarar ki nakeba,,,AYUSH tamike tareda sa purse a kallon datake,Bari inga abinda ake umartata akansa,sannan ya zazzage tsayawatai Tana naxarin Kayan tabbas sune Wanda akai tallonsu a Cyprus jia basuma xo Nigeria ba ga shegen tsada amma taurin Kai da girman Kai Irin na AYUSH hakan besa TA sadudaba sema daga  kafada datai sannan TA turawa Nadia ledan,kirike bana Kayan sallah gwajab dake banaso lalle kudin ustax sunyi aiki sannan tasakai tafuce a dakin barin soya maki wainar fulawarki yadda kika tsareni da Ido haka kamar ungulu..itade nadia Daukan nata abayan tai sannan tasakawa AYUSH nata a drawer.

Seda Nadia tai sallah sanann TA nufi kasa danmaidawa mommy kudin ,xaune da sami mommy da baba a parlor,karasawa tai da sallamarta ,baba barka da dawowa?mommu ga kudin na nuna mata,mommy tace Yawwa alhaji gasu sauran kayanma suna sama..justice kamal yadau wayarsa yakira mahaifin NAUFAAL sunjima suna magana sannan ya kashe yana godia,mommy tace ya akai?baba yace Wlhy nayi nayi yace Wlhy baxasu karbaba aibadan wani abin bane,ai kanwarsace sannan yace yarinyar Ma ai yar' sace suxasu aurarda ita Kinga mexance??yariga yagama magana..,mommy tace toh Allah yasaka da alkhairi,,sannan tabawa Nadia ungo kaimata,,Nadia tace Allah mommy AYUSH baxata karba bafa??baba yace to kebase kirike a hannunkiba duk abinda yatashi na sabgar daxakwi seku cira ciki,,sannan Nadia tamike bayan tawa baba godia tawuce sama.

NAUFAL (THE CHARMING) (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now