Family house

908 51 10
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.


                    *♡MANAR¸.•💥*
               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA
  

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.*
    
   *ⅅⅈՏℂℒᗅⅈℳℰℛ:Any resemblance to actual person living/dead or even reality is purely coincidental.*
   
    *Alhamdulillah alaa kulli halin! All thanks is to Almighty Allah for giving me the chance and ability to start this book,may Allah's peace & blessings be upon to the great ambassador prophet Muhammad bn Abdullah (p.b.u.h) & his family & his companions as well.*
      _My special greetings goes to my lovely Mom Hajiya Maryam Haroun Sulaiman and my sweet siblings... Ahabbakum-thiir._
   

🎉🍻🎂

     _If i had the money i would have hired a flight,flown into the skies above and written in the clouds *'Happy Birthday Sister'* But since i'm not so well off yet,please accept my genuine and humble wishes... Happy Birthday *MAMAH ZEE* whish u Allah's khair and blessings now and always._

                                🎁🎈🎊

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu),alkhairin Allah ya isar miki uwa ta gari,har kullum ina alfahari da ke.♥_

_Bestowed to Fateema Abdulmajid.💞_

                                01.

#Family house..

             A hankali cab d'in yake gangarawa daga saman babban titin ya sauka line da ya shiga katafaren Housing estate d'in da yake nan shiru kamar babu masu rai cikinsa,su biyu ne zaune back seat daga y'ar dattijuwar da shekarunta za su kai 70+,sai wata y'ar kyakyatawar budurwa wacce shekarunta baza su wuce 15yrs ba,duk da a zaune take hakan bazai sa a kasa gane doguwa ce ba,y'ar kewayayyiyar fuskarta dake d'auke da manyan fararen idanu mammalakan wasu irin dogayen eyelashes,ga wanda bai santa ba zai yi tunanin tana k'arawa da artificial but haka halittar ta yake,hancinta da yake nan d'an dai² a fuskarta ya sha wani had'ad'd'en ring-shaped,sai y'an k'ananun lips d'inta da suke bayyanar da murmushi da suka sha red chapstick,duk da k'arancin shekarunta kyaunta a bayyane yake sam ba abune da yake a b'oye ba,tun da suka shigo arean take lek'en hanya,yanda ta matsu motar ya tsaya,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta fita daga motar,d'auke kai dattijuwar tayi daga kallonta ta tab'e baki,kafin wani cikinsu ya samu damar magana driver ya tsayar da motar a bakin makeken get d'in gidan,ko gama gyara parking bata jira ya yi ba tayi sauri ta bud'e ta fita cikin wani irin zumud'i da gudu ta nufi get d'in gidan tana dariya,da duka k'arfinta ta hankad'a k'aramar k'ofar,ba tare da ta tsaya rufewa ba ta wuce k'ofar ya koma da kansa yayi wani k'ara mara dad'in ji,a nutse take bin ko ina na gidan da kallo,babban compound ne sosai dake d'auke da shuke² masu d'aukar hankali,kai kana ganin gidan kasan naira ta zauna,makeken tsakar gidane dake d'auke da apartments har uku,a tsakanin kowane apartment akwai tazara mai nisa,duplex ne babban gaske sai parking space dake can gefe,tsarin gini da komai na apartment biyu iri d'aya ne hatta da fenti babu ta inda suka bambanta sai d'ayan apartment d'in dake can k'arshe wanda yake flat mai kyaun gaske,wani irin kallo ta dunga k'arewa apartments d'in kamar mai son tuna wani abu,a hankali tayi wani murmushi cikin harshen larabci da y'ar siririyar muryarta ta furta "anaa halla ja'eeh.." Waiwayawa tayi da niyyar mata magana,kamar aljana ta nemeta ta rasa da sauri ta kalli hanyar get da yayi k'ara,baki bud'e cikin wani irin takaici kamar za ta fashe da kuka ta furta "O'o! Allah ga-ni (inji kishiyar mai doro),ni dai *AZUMI* ina ganin ta kaina,yarinya kullum sai girman kawai amma hankali walaa.. Ya Allah ka mana maganin abunda yafi k'arfinmu" mai cab dake sauraren mitar ta bai san sanda ya saki wani murmushi ba,yana ci gaba da sauke manyan jakunkunan dake saman motar da booth yace "kayya dai Hajiya ai yaran yanzu addu'ah kad'ai ake musu" wani k'wafa tayi mai ciwo tace "ai kuwa dai d'an nan,tou Allah shirya mana zuri'ah" yace "ameen" kafin ya gama sauke kayan tace "Malam audu kake ko?" Dariya yayi yace "a'a Hjy hala dai sunan kakanki kenan?" Tayi murmushi tace "k'warai kuwa" mai cab yayi dariya yace "ko da na ji" tace "tou kai ya ne sunanka d'an nan?" Yace "Usman" rik'e baki tayi da wani murya tana kallonsa tace "Allahu akbar.. Sunan mai gidana gareka!" Yayi murmushi yace "dara ya ci gida kenan" tayi murmushi tace "ai kuwa ya ci" mai cab sai murmushi yake bai sake cewa komai ba har ya gama sauke kayan,yace "tou Hjy zan tafi ni" kallonsa tayi saurin yi tace "yawwa! Ko za ka d'an jire min kayan na lek'a ciki na samo y'an jikoki na su kwasar min,wallahi duk na gaji ko tsinke ni dai ba na iya d'auka a nan,tafiya ce muke ta yinta za'ayi baza ayi ba,sai da na gaji da zaman jira kafin shegen jirgin ya kwaso mu,da muka d'auko hanya kuwa ni gani nayi kamar za'a bar duniya da mu" mai cab yayi murmushi yace "toh Hjy! Allah sa baza ki dad'e ba dan sauri nake" kyab'e baki tayi tana masa wani kallo a kaikaice tace "yo to duk saurin da kake ai dai za ka jira na fito ko? Baka tafi ka barmin kaya b'arayi su sace ba" yayi murmushi yace "tou a fito lafiya" tace "yawwa! Ko kaifa" shi dai bai sake ce mata komai ba,bata sake masa magana ba itama ta wuce tana d'ingisa k'afa ta barshi nan tsaye,da get keeper d'insu ta fara had'uwa yana tsaye bakin k'ofar d'akinsa yana sababin tsoratasa da akayi,ta masa wani kallo jin yana zage² ta had'e rai da fad'in "kai da waye haka kuma Yaro?" Da sauri ya fiddo idanu yana yana kallonta yace "Hajjaju ku ne tafe?" Sanda ta tab'e baki ta d'auke kai tace "to ko mu koma ne ba'a son ganinmu?" Yaro ya sosa backhead d'insa yana sakin murmushi mai kama da na yak'e yace "wane mutum Hajiya? Barka da zuwa,an zo lafiya?" Ci gaba da tafiya tayi a dak'ile ta amsa masa "lafiya" daga haka ta wuce ta barsa tsaye,sanda ya tabbatar ta wuce yana lek'en hanya yace "annoba ta dawo,Allah sa da wuri za ku koma!" Sanye take da Arabian gown da mini hijab bak'ak'e da ya tsaya iya wuyanta,zaune a balcony ta hangosa saman farin plastics chair yana amsa kira a waya idanunsa akan laptop dake ajiye saman wani k'aramin table yana operating,matashi ne dogo sosai kyakykyawa wanda bazai haura 30yrs ba,kana kallonsa ka ga bafulatani usul,tana yi masa wani kallo ta ware manyan idanunta cikin k'arajin murna sanda ta tabbatar shi ne a gurin ta kwala masa kira *"Yaya!"* Then ta kwasa da gudu tana dariya ta nufosa,kamar a mafarki ya jiyo maganarta ya d'ago kansa daga kan computer dake gabansa suka yi idanu hud'u,mamakin ganinta a dai² lokacin yasa shi ware sexy eyes d'insa dake d'auke da wasu irin dogaye kuma zara²n eyelashes,gashin girarsa da suke cikakku masu duhu kamar anyi masa curving a d'age ya dunga mata wani kallo,fad'awa jikinsa tayi ta saki dariya cikin harshen larabci ta furta "na yi kewarka sosai Yaah *WALEED!"* Wani kyakykyawan murmushi ya samu kansa da yi ba tare da ya yi mata magana ba ya rungumeta firmly had'e da lumshe idanunsa cikin wani irin shauk'in kasancewarsu a hakan,within 3 seconds murmushin dake kan kyakykyawar fuskarsa ya dunga disashewa sanda yayi turning zuwa yanayin b'acin rai mai wahalar fassaruwa yayi saurin bud'e idanunsa,babu zato ya hankad'eta daga jikinsa,fad'uwa tayi a k'asa dai² lokacin dattijuwar ta sawo kai idanunta suka hango mata abunda ke faruwa,cikin wani irin b'acin rai ta dunga tahowa inda suke ba tare da ta yi magana ba,k'ara ta fasa kafin ta saki wani kukan da kamar ana zare mata rai ta fara birgima tana turje² a k'asa,Waleed yayi saurin mik'ewa yana aika mata mugun kallo ya fara tattare belongings d'insa zai bar gurin,fahimtar abunda yake shirin yi yasa ta ci gaba da kuka bil'hak'k'i,takaici ne yasa shi d'agowa zai yi magana idanunsa suka hango masa tahowarta a mamakance da wani murya yana zaro idanunsa ya furta *"DADDA!"* Sanda ya sake bud'e idanunsa yana kallon yadda take tahowa cikin tsananin b'acin rai da sauri ya juya zai shige apartment d'in,d'aga murya tayi cikin masifa tace "amma dai wannan yaro kai dai ba d'an arziki bane,Allah wadaranka ya wadaran mai hali irin naka" cak ya tsaya a bakin k'ofar yace "Allah ya dawo dake ai" cikin masifa dao² ta k'araso gurin tace "to ko za ka kore mune?" Bai tankata ba ya bud'e k'ofa,Dadda ta k'arasa inda take kwance a k'asa ta d'agota b'acin rai k'arara a fuskarta ta ci gaba da mita "yanzu idan banda bak'ar mugunta *MANAR* ba k'anwarka bace da za ka daddage ka hankad'eta? Kai da za kaga wani yana cutarta ka hana,amma shi ne tsabar iya shege yarinya daga zuwanta za ka fara zaluntarta? Wanda duk bai ji tausayin maraya ba dai,Allah ma bazai tausaya masa ba.." Juyowa yayi saurin yi yayi mata wani kallo yace "waye marayan?" Tsuke fuska tayi idanunta a kansa tace "ban sani ba" ya tab'e baki yace "kin sani mana tunda ga shi kin fad'a" tsaki tayi ta juya ta ci gaba da mita "yarinya tana murnar tazo ta ganka,kullum ba ta da magana sai tambayar yaushe za muzo Nigeria,daga zuwa ka ce bari na ci ubanki,babu tausayi ka daddage ka jefar min da ita k'asa... Yanzun da ta ji ciwo kai ko uwarka ne za kuyi jinyarta?" Wani kallo ya mata a fusace yace "wai Dadda da kike min masifa daga zuwanki,ni kinji na ce miki ina son ganinta? Ko wani yace miki ya damu da zuwanta?" K'ara volume d'in kukanta tayi,Dadda tayi k'wafa saboda haushin da maganarsa ya ba-ta bata iya ce masa komai ba,ta juya baki cikin harshen larabci ta fara yiwa Manar fad'a "kema maganinki ai,mutumin nan kin sansa ba mutunci ya cika ba,tun farko kuma sai dana kwab'e ki akansa baki ji ba,idan yaji miki ciwo kya tafi gurin uwarki kiyi jinya ni babu ruwana bazan iya wahala ba.." Sakin baki Manar tayi ta dunga kallon Dadda dake karkad'e mata jiki,bata ce komai ba ta juya ta kallesa,suna had'a ido ya aiko mata harara ya juya yayi shigewarsa ya rufe k'ofar,tab'e baki Dadda tayi ta rik'e hannunta tace "muje.. Dama kuma zan sake fad'a miki bazan gaji ba,babu ruwanki da duk wani d'an iska a gidan nan,kinji na fad'a miki,na raba ki da su,duk wanda ya takaki ki rama,kada ki kuskura ki zo min kina kuka,bazan jurewa sauraren kukan ki ba ko yaushe,idan kin ga baki iyawa mutum yafi k'arfin ki,wannan dai ki masa Allah ya isa ki gudo wajena,naga shegen da ya isa tab'a ki a gaban idanuna.." Zumb'ura baki tayi tak'i cewa komai,Dadda ta kalleta tace "kinji me nace miki?" Kamar wacce akewa dole ta gyad'a mata kai,Dadda tace "babu ruwanki da shiga shirgin su,idan baki san su ba ni nan na san da su waye muke zaune,babu wanda ban san halinsa ba,shekarun da muka yi da su ba banza ba,duk y'an bak'in ciki ne da kike ganinsu,d'an tafiyar nan da kika yi zuwa harami shi sukewa hassada,Allah ya kiraki su bai kira su ba,mak'iyinka wata rana bafadenka,kada shegen da yazo ya nuna miki so yanzu kika yarda da shi,munafukai sun fi yawa a gidan nan masu fuska biyu,sai kin kula sosai kinji na fad'a miki.." Kallon Dadda tayi saurin yi da fuskar kuka tace "har da Yaya?" Dadda ta saki baki tana kallonta da sauri tace "ke ni ban ce miki shi ba,amma dai uwarsa da k'annensa babu ruwanki da su duka kinji na gaya miki dama" gyad'a kai tayi saurin yi suka k'arasa apartment d'in k'arshe,Dadda ta d'auko mukulli daga jakarta da take rataye da shi irin na zamani ta bud'e,Manar tayi sauri ta shige tana kalle²,Dadda ta saka k'afarta cikin parlon tana washe bakinta da yasha hakor'in makkah har hud'u,biyu sama biyu k'asa tana lumshe idanu ta furta "O'ohhh! Gida kenan.. Malam bahaushe yayi gaskiya da yace kowa ya bar gida,gida ya barshi.." Fitowarsa kenan ya hango mutum tsaye gurin,matashi ne kyakykyawa dogo kamarsu da Waleed har ya b'aci sai dai shi skin d'insa ya d'an yi duhu,Waleed kuma ya girme sa da 2yrs,idan ba wanda ya sansu ba sai yayi zaton they're twins,bud'a idanu yayi ya dunga kallonta sanda ya kusa k'arasowa gurin da murnarsa yace "Dadda!" Waigawa tayi saurin yi ta kalleshi tayi mitsi² da idanu tace "waye wannan kuma?" Wani murmushi ya saki yace "Haba matar *AMAAR* ne fa,ya idon na ki?" Washe baki tayi tace "A'ahh! Kace min d'an Fodiyo ne,mai gidana na kaina,ai da farko na d'auka wancan mutumin ne ya sake dawowa nayi masa fata²" murmushi yayi yace "Waleed wai?" Tsuke fuska tayi tace "waye kuma Waleed?" Yayi dariya yace "haba Dadda *MUHAMMAD* d'in ne baki sani ba?" Tace "to ni ka ce min wani Waleed? Waleed ai ba suna bane" dariya yayi because ya san halinta haka take cewa idan suka samu matsala,yace "kun had'u da shi kenan?" Tace "ai tunda kaji ina wannan maganar kaima ka sani" yayi murmushi yana gyad'a kai yace "yanzu kuke tafe?" Tace "wallahi fa.." Da wani murya tace "Afff! Yi sauri d'an albarka kaje waje ka kalle min mai motar can kada ya sace mana kaya" wani kallo ya fara mata kafin yace "sata kuma Dadda?" Tace "yo to idan yaga babu idanun mu a kansa ai sai ya sace su,ka san mutane ba gaskiya suka cika ba" Manar dake tsaye cikin parlor tana jin zancen da Dadda keyi ta tab'e baki bata ce komai ba,Amaar yace "a'a Dadda ba zai sace ba,ba shi ya kawo ku ba?" Tsuke fuska tayi tace "yo dan shi ya kawomu,rubutawa akayi a goshinsa bazai sace ba?" Amaar ya fara dariya,tace "Ai ka ji matsalarka,sai ana magana ka farawa mutum dariya,kana nan ma ai tuni sai ya gudu da su" juyawa yayi saurin yi ya ci gaba da dariya ya nufi hanyar get yana fad'in "bari dai naje na gani" tace "yawwa! Hanzarta kaje dan Allah kada ya b'ace mu shiga uku.. Uban dukiyar mu kad'ai ya gudu da shi ai ya cuce mu.." Ta shiga parlon tana ci gaba da mita "wallahi kuwa da sai na sa Yaro yasa an nemosa duk inda ya shiga ya biya mu dukiyar mu,idan yak'i kuwa dama cewa zanyi da alk'ali ya d'auresa kawai har sai ya fito mana da dukiyar mu,ina dalili? Zan zauna na zuba ido mutumi ya gudu da dukiya ya barni na shiga uku?" Haushi ne ya ciko Manar ta d'ago tana had'e rai tace "dan Allah Dadda kiyi shiru,tunda ba'a ce miki ya gudu ba,mitar me kike yi kuma?" Wani kallo ta wurga mata tace "kuji min mata kamar na kasa da ita! Ai kiji in gaya miki idan ba cewa akayi mutumin yana nan ba,idan kinji na yi shiru Allah tsinemin,uban dukiyar nan da muka zo da shi,banda nawa ko iya naki kad'ai ya gudu da shi,danginsa kaf birni da k'auye sunyi hannun riga da talauci bare ya sace duka.. Kuji min mahaukaciyar yarinya wai na bar magana" hararta Manar tayi tace "ai sai kiyi ke kad'ai" ta tashi a fusace za ta fita,Dadda ta rakata da mugun kallo tace "a gaida na gaba.." Bata kulata ba ta fita,a hankali take tafiya kamar mai counting steps d'inta sanda taje k'ofar gidan ta tsaya balcony,kusan mintunanta biyar tana ta tsaye a gurin ta kasa shiga,Amaar dake shigowa da almajirai yana nuna musu inda za su kai kaya ya hangota tsaye yace da d'aya a cikin su "idan kun gama ku jira ni" yace "toh" ya k'arasa gurin yana kallonta yace "K'anwata me kike yi a nan?" Juyawa tayi da sauri ta kallesa tayi masa murmushi tace "Yaah Amaar!" Yayi mata murmushi shima yace "ai na d'auka Dadda ita kad'ai ta zo,ashe tare kuke?" Ta gyad'a masa kai tace "ehh" yace "ya hanya?" Ta fara gaisheshi kafin ta amsa,yace "ba shiga za kiyi ba kika tsaya a nan?" Ta gyad'a masa kai tace "laa! Wajen aunty fa zanje" gyad'a kai yayi ya bud'e k'ofar yace "muje tou" ta fara wucewa,a dining ta hangosa zaune shi kad'ai yana cin abinci,ta bisa da kallo kamar mai jin tsoro,suna had'a ido ya d'aure fuskarsa,Amaar ya kalleshi yayi murmushi cike da tsokana yace "brother! Dadda tana nemanka" bai kalli direction d'insu ba yace "me zan mata?" Amaar yace "i don't know,sai dai kaje kaji" tab'e baki yayi bai sake magana ba yaci gaba da cin abincinsa,Manar ta kalleshi ganin sai had'e rai yake ta kasa masa magana a sanyaye idanunta suna kawo k'walla ta wuce hanyar stairs,ganin Amaar ya tsaya gefe ta d'aga kai da sauri ta kalli dalilin tsaiwarsa,bin matar dake sakkowa da kallo tayi wacce baza ta haura 52yrs ba har ta gama sakkowa,satan kallon Manar da ta k'i kallonta ta dunga yi ta tab'e baki ta wuce,a hankali Manar ta d'aga kai ta d'an kalleta da wani murya tace "ina yini?" Cikin izza matar tana kallonta tace "lafiya" haushin amsar yasa Manar ta d'ago da sauri ta kalleta tayi k'wafa a ciki tace "idan na sake gaisheki ki amsa duk yadda kika ga dama" idanunta akansa sanda ta k'arasa cikin parlon tana masa wani kallo tace "Waleed! Me nake gani?" D'ago kansa yayi saurin yi ya kalleta yak'i cewa komai,ta had'e rai tace "am i not talking to Waleed? Ko ni sa'ar wasan ka ce da za kamin shiru kana kallo na ina magana?" Sunkuyar da kai yayi a hankali yace "i'm sorry" tana ci gaba da kallonsa tace "d'azu dana sa a tambayeka me kace min?" Saurin d'agowa yayi zai yi magana ta d'aga masa hannu tace "iskanci ne yasa kace ma Diyanah azumi kake?" Yace "ba haka bane Mama,ciwon ciki ne yasa ni sauke azumin,amma banyi miki k'arya ba" idanu ta zuba masa tana masa wani kallo cike da tuhuma tace "wane irin ciwon ciki ne haka lokaci d'aya har ya tafi?" A dake yace "kawai zuwa yayi" numfashi ta sauke ta gyad'a kai tace "Allah sawak'e" ba dan ta yarda da abunda yace ba ta nemi guri cikin parlon ta zauna ta d'auki remote tayi powering TV,juyawa yayi ya kalli direction d'in da Manar take tsaye har sannan ya aika mata mugun kallo kafin ya d'auke kai,Amaar da ya kula bata biyoshi ba ya waiwayo,tsaye a k'asa ya hangota ba ta da niyyar tahowa ya girgiza kai yace "Manar! Me kika tsaya kallo?" Saurin juyawa tayi ta bi bayansa,yayi knocking k'ofar bedroom d'in,daga ciki aka basu izinin shiga,tura k'ofar yayi ya shiga da sallama,ta bisa a baya suka shiga tare,y'ar kyakykyawar budurwar dake tsaye wacce baza ta wuce sa'ar Manar ba tana nad'e kayan dake zube saman gado ta waigo ta amsa,tayi masa murmushi tana ci gaba da nad'e kayan tace "Yaa Amaar aunty tana nemanka" yace "where's she?" Tace "tana toilet" Manar ta lek'o daga bayansa tana sakin murmushi tace "Marhaba uktiiy!" Saurin waigowa ta yi jin magana kuma,she thought shi kad'ai ne ya shigo da farkon,dai² lokacin Amaar ya wuce gaban mudubi yana shirin janyo kujera ya zauna,idanunta suka sauka kan Manar dake tsaye tana kallonta sai murmushi take mata,wani ihu ta fasa ta saki kayan hannunta da gudu ta taho suka rungume juna,daga toilet Aunty da ta jiyo ihunta tayi magana "Ameerah! Kin samu tab'in hankali ne kike min ihu?" Cikin farin ciki tana rik'e da hannun Manar tace "Aunty u know what?" Aunty tace "sai kin fad'a" tayi murmushi tace "surprise! Fito kiga" tsaki Aunty tayi saboda sanin shirmen Ameerah,ta gama d'aura alwala ta bud'e k'ofar ta fito,tsaye tayi a door way ta dunga kallon Manar da mamaki tace "daughter! Ke ce da gaske?" Tashi Manar tayi da sauri ta k'arasa ta shige jikinta,Aunty ta rungumeta back tana sakin murmushi tace "saukar yaushe?" Manar tace "yanzu!" Gyad'a kai Aunty tayi ta fara amsa gaisuwar da take mata tana shafa kanta,suka k'arasa bakin gado tana rik'e da hannunta suka zauna,Amaar dake zaune yana danna waya ya d'ago ya kallesu,kafin yayi magana aka turo k'ofar,duka suka juya suka kalli gurin,Dadda ta tsaya gurin fuskarta babu fara'a tana kallon Manar tace "yanzu idan ba iya shege ba,daga zuwa har kin taho gantali,ni kike nufin zan gyara miki gidan?" Tsuke fuska Manar tayi ta d'auke kai tak'i cewa komai,Aunty tayi murmushi tace "sannu da zuwa Hjy" wani kallo Dadda tayi mata kafin tace "yawwa" fuska babu wadataccen fara'a ta ci gaba da mita "ka ga yarinya kamar ba da ita nake magana ba ta manna min hauka.. To kin yiwa uwarki shiru.." Dariya Ameerah ta fara tace "sannu da zuwa Dadda" ko tankata bata yi ba,ta zubawa Manar ido da tak'i kallonta,a fusace tace "wai ba dake nake ba kika k'i kula ni?" Manar ta juyo ta kalleta tace "me zan miki tou?" Dadda tace "da kika taho kika barni ni baiwar uwarki ce ko ta ubanki?" Kicin-kicin Manar tayi ta tsuke fuska itama tana yiwa Dadda wani kallo ta gyad'a kai tak'i cewa komai,a fusace Dadda tace "wallahi tunda kika min haka sai dai ki tafi gurin uwarki dama,baza ki kwanar min a gida ba" murmushi Aunty tayi tace "kiyi hak'uri Hjy bari a tura maids su gyara" saurin washe baki Dadda tayi hakor'in makkan ta suka bayyana tace "to babu laifi,dan dai ni kam dama bazan iya wannan aiki ba daga zuwa na" Aunty tayi murmushi tace "ki shigo ciki Hjy kafin a gyara muku part d'in" saurin girgiza kai tayi tace "a'a a'a! Barni a nan ma tafiya zanyi nasa musu ido,na baro kaya uban dukiyarmu idan ba na gurin ai sai su samu damar sacewa" tagumi Amaar yayi ya zuba mata ido,Aunty tayi murmushi tace "baza su sace ba Hjy ki shigo har su gama" juyawa Dadda tayi fuska a tsuke tace "yau naji jaraba,mutane sai musun bala'i.. Ni dai na tafi bazan zauna ba aje a cuceni" dariya Ameerah ta fashe da,Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Aunty ta tashi da sauri ta fito,a parlon k'asa ta tarar da matar d'azu ta k'araso tana sakin murmushi tace "sannu da hutawa Hjy" wani kallo matar tayi mata kamar ana mata dole ta amsa "yawwa!" Daga haka ta d'auke kai,Aunty tace "kin san Hjy ta dawo?" Bata kalli direction d'in Aunty ba tace "ehh! Da wani abu ne kuma?" Aunty tace "thought ko bayan ta fita kika sakko" ta girgiza kai tace "not at all.." Gyad'a kai Auntyn tayi itama ta wuce hanyar kitchen da take jin motsi,a bakin k'ofa ta tsaya tayi sallama,maids uku dake ciki suna aiki suka amsa suna gaisar da ita,dattijuwa d'aya sai y'an mata biyu,ta amsa fuskarta a sake tace "idan aikin da kuke yi babu yawa Haulatu ke da Ruqayya kuje b'angaren Hjy ku gyara da sauri" amsawa suka yi suka fito,y'ar dattijuwar ta ci gaba da aikin,Aunty ta juya ta bar gurin matar dake zaune parlor ta bita da wani kallo ta tab'e baki,a k'asa Aunty ta tsaya ta rad'oma Ameerah kira,da sauri ta fito tana daga sama tace "ga ni Aunty" Aunty ta mata wani kallo tace "ni kike so na zo na same ki a nan?" Ta fara sakkowa da sassarfa tace "i'm sorry" Aunty tace "ina Manar d'in take?" Tace "tana sama" tace "maza kira min ita kuzo tare" komawa tayi saman,suka dawo tare da Manar,Aunty tace "maza wuce dining kici abinci" satar kallon matar dake zaune tayi,suna had'a ido ta sunkuyar da kanta da sauri ta girgiza kai tace "a'a na k'oshi" wani kallo Aunty tayi mata tace "na fara miki wasa kou?" Murmushi ta d'ago tana yi,aunty ta had'e rai tace "wuce kafin na sab'a miki" girgiza kai ta sake yi kamar za tayi kuka tace "Allah Aunty ba na jin yunwa,ni gida zanje wajen mother" kallonta Aunty ta dunga yi ta fahimci dalilin k'in cin abincin da bata son yi tace "baki je ba dama?" Ta gyad'a mata kai da sauri tace "nan na fara zuwa" Aunty ta gyad'a kai tace "alright Ameerah maza kuje ki rakata" Ameerah dake tsaye har sannan tace "Aunty kayan fa ban gama ba" tace "kuje zan k'arasa" amsawa suka yi suka juya za su tafi,matar dake zaune tun d'azu bata ce musu komai ba ta tab'e baki tace "son a sani.. Wai gaida uwar miji a kasuwa" tsaf Aunty ta fahimci magana ta yar mata,tayi murmushi ta juyo tana kallonta tace "ai ba wani abu bane dan ka gaisheta ko da a taron arfa ne ba a kasuwa kad'ai ba" tab'e baki Mama tayi tace "a'a ke dai kike ganin ba komai bane yin hakan,amma wannan ai dangin shishshigi ne" wani murmushi Aunty tayi tace "haka ne kam.. Sai dai shi kansa shishshigin ma iyawa ne,idan wani yayi an yaba wani idan yayi shegen duka zai ci.."

  
     _#Maa sha Allah! I'm back again by Allah's grace... Hope u guys will love the book. Don't missed it! Yanzun za'a fara._

      #2 be continue 1st/Jan,2021.

   
#Share pls.
#Asli Smasher.
#19/Dec,2020.A.D.

MANARWhere stories live. Discover now