Phone call

209 20 18
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.

                    *♡MANAR¸.•💥*
               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

                                05.

#Phone call..  
    
        Wani irin yammm yaji jikinsa yana yi,da sauri ya fizge hannunsa,ta sake kawo hannu za ta rik'esa ransa a b'ace yana mata wani kallo a kausashe yace "don't dare touch me!" Rau² idanunta suka yi da muryar kuka tace "Yaya!" Tsawa ya mata "be quite!" Jikinta har b'ari yake tsabar tsoron da maganarsa yasa taji,tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta juya da niyyar barin gurin yayi saurin fizgota,k'ara ta fasa ta k'ank'ame jikinta she thought ko zai daketa ne,da sauri ya waiwaya yana kalle²,kafin tayi wani maganar tuni ya jata da sauri ya nufi backyard,a jikin apartment d'in Dadda ya tsayar da ita yana mata wani kallo ransa kamar a b'ace yace "me zan miki?" Sheshshek'ar kuka ta fara tak'i masa magana,sanda tayi mai isarta kafin tayi shiru,ya nad'e hannunsa a k'irjinsa ya zuba mata idanunsa da suka fara juyawa,sanda ta fara gajiya da tsayuwar a hankali ta zumb'uro baki still kuma bata da niyyar cewa wani abu,almost 15 minutes suna ta tsaye babu wanda yace da wani k'ala kafin Manar ta shawaran tafiya ba tare da ta yi masa magana ba ta fara k'ok'arin barin gurin,saurin rik'ota yayi ya dawo da ita,fuskarsa babu alamun wasa ya zuba mata idanunsa masu cike da kwarjini fuskarsan nan a daure still kuma har lokacin bai ji zai iya yi mata magana ba,idanunta ta d'aga tana kallonsa a shagwab'e tace "Yaya!" Yace "Uhn!" Ya d'aga mata girorinsa,ta k'ara narke murya tace "ina son tafiya" wani kallo ya mata yace "na ba-ki izini?" Ta dunga kallonsa kamar za tayi kuka tace "to ai na gaji da tsayuwa" kamar bai gane me take fad'a ba ya sake d'aga mata gira,kuka ta fara yi mara sauti sanda ta shammacesa tayi wuf za ta gudu,taji ya rik'o arm d'inta da k'arfi ya dawo da ita,fuskarsa a d'aure yace "u have nowhere to go girl!" Kuka ta fashe da shi bata gane me yace ba,da wani braking voice tace "to ni fa na gaji,kuma kak'i bari na tafi" wani murmushi yayi ya d'aga gira yace "hukuncinki kenan" saurin kallonsa tayi tana tsayar da kukan tace "ni me nayi maka to?" Yace "u have no idea?" Ta zuba masa idanu tak'i cewa komai,a d'an tsawace yace "ba dake nake ba?" Zumb'uro baki tayi tace "to ni na ji me kace ne?" Ya bud'a idanunsa yana kallonta yace "baki sani ba?" Ta gyad'a masa kai,gyad'a kai shima yayi kafin yace "wancan ranar me ya had'a ku fad'a,da zan aika a kiraki kik'i zuwa?" Squeezing fuskarta ta fara kafin ta b'ata rai tace "to ba su bane dai daga zuwa suka fara fad'a mana magana" idanunsa akanta yace "suka ce me?" Tayi shiru tak'i cewa komai sai da ya mata tsawa,a shagwab'e tace "kawai daga na tambayi Ameerah lokacin ba da su nake ba na ce har ta dawo? Ameerah tace kai sis mun dad'e fa a skul d'in tun 7am muka fita,na san time d'in ma ko juyin farko baki yi ba shi ne wannan Deejan ta tab'e baki tana mana kallon banza tace ya ma za'ayi ta sani tunda babu fuss! Ita kuma Diyanah tace dama tunda an fi ganewa a tafi wani duniyar karuwanci a b'ige da karb'an sabil ana cewa sana'a ake ai baza'a san komai ba,haka za azo a koma cikin duhun jahilci shi ne suka dunga mana dariya,sai ita Deejan ta sake cewa ai ko yanzu ma sis Diyanah kada ki fitar da tsammanin kamosu aka yi aka dawo da su,basu yi niyyar dawowa ba shi ne Diyanah ta dunga dariya har tana rik'e ciki tace wai kina nufin sun zama *TAKARI?* Shi ne dan Ameerah tace musu wannan ai ba yi bane,me yasa za kuna fad'an irin maganganun nan? Shi ne Diyanah tace an fad'a d'in ko akwai abunda za kiyi? Da Ameerah tace babu abunda zanyi zan dai fad'awa Abba muddin baku daina ba,shi ne Deejah tace ai dama dole Ameerah ta tare min,tunda an tab'a k'anwar uwarta,shi ne dan Ameerah tace mata a'a Deejah kada mu kai nan,duk abunda za ku fad'a ya tsaya iya kanmu,amma kada ki kuskura ki k'ara saka iyayen mu,shi ne ita Deejan a tsiwace tace idan an tab'a me za ki iya yi? Ameerah tace sai kin gwada zan nuna miki abunda zanyi suka yi dariya su biyun suka tafa Diyanah tace kin ji fa sis kamar za ta iya mana wani abu,duk fa kwad'ayi ne yasa ta shiga maganar itama Deejah tace ke rabu da su kwad'ayi dai mabud'in wahala,idan ma za ku hak'ura da abunda kuke da shi ku zauna ku rungumi rayuwarku zai fi muku,amma kuna biyewa waccan tsohuwar tana d'ora ku turba mara kyau,duk sai kun yi dana sani a lokacin da bazai muku amfani ba" kallon bakinta ya dunga yi sanda yaji ta yi shiru yayi ajiyar zuciya yace "uhn! Daga nan sai aka yi yaya?" Manar dai sai cika take kamar yanzun abun yake kan faruwa tace "shi ne ni kuma na cakumo wuyanta,muka kama kokawa,nace wa take cema waccan tsohuwar?" Wani kallo ya dunga binta da shi kafin yace "su kuma sauran me ya had'a su?" Tace "Diyanah ce take k'ok'arin shigarwa Deejah,shi ne Ameerah ta tareta tace baza su min taron dangi ba,itama tana da wanda za su shigar mata,sai ita Diyanan tace ta matsa kafin ta bigeta,shi ne dan Ameerah tace wa za ta bige? Ai sai dai su buge juna,shi ne sai Diyanah ta ture Ameerah da k'arfi saura k'iris ta fad'i k'asa,da ta d'ago shi ne ta fizgo Diyanah,ita kuma Diyanah tana juyawa sai ta kai mata mari,da bata sameta ba shi ne itama Ameerah ta kai mata marin ita sai ta sameta,daga nan sai suka fara kokawa" Waleed dake saurarenta jin ta yi shiru yace "Uhn! Daga nan sai mene ya faru?" Tace "shi ne sai ka fito za ka tafi masjeed,ka ganmu muna fad'a.." Gyad'a kai yayi yace "and by then nace kar na dawo ban ganku a gurin ba,da yake kunnen k'ashi gareki sai kika k'i zuwa,saboda kina da wanda za ta d'aure miki k'ugu ko?" B'ata rai tayi tace "a'a" yace "haka ne mana" girgiza kai tayi za tayi magana ya maka mata tsawa yace "am i lied,ba haka bane?" Duk da yadda jikinta yake b'ari bata fasa bashi amsa ba "to ni ai ba-ni na fad'a mata ba" wani kallo ya dunga mata yace "idan baki fad'a mata ba ya akayi ta sani?" Idanunta suna kawo k'walla tace "to ba Ameerah kasa ta kira ni ba,shi ne Dadda ta tambayeta da tace kai ne kace nazo,tace me zanyi maka? Shi ne ta fad'a mata komai" tab'e baki yayi yace "matsalar duk maganar ki sai da shi ne ya fi yawa,taya zan gasgata abunda kika fad'a?" Sabon kuka ta sakin masa da sauri ta fad'a jikinsa tace "ni fa ban maka k'arya ba,kuma ma idan baka yarda ba ka tambayi Ameerah ko su" tamkar ginannen dutsen da aka kafe haka ya daskare ya kasa cewa komai cikin y'an mintuna jikinsa ya yi wani irin mutuwa,jinta kwance a jikinsa da sautin kukanta dake ratsasa nan da nan jikinsa ya fara wani irin vibrating kamar wanda ake jijjigawa,da sauri ta d'ago kanta tana kallonsa,a tsorace ta dunga share hawaye tace "Yaya!" Runtse idanunsa yayi da wani irin shak'ak'k'en murya yace "jeki!" Tsayawa tayi ta kasa tafiya,da wani irin murya ta sake cewa "Yaya! Me yake damunka?" A tsawace yace "bar nan nace" kuka ta sake fashewa da shi za ta rik'esa ya bud'e idanunsa da sauri,a tsorace ta koma baya ganin yadda idanunsa suka yi ja,ya zuba mata su yana binta da wani kallo mai cike da warning,babu shiri ta juya da sauri tana waiwayensa ta fara tafiya,komawa yayi ya jingina bayansa da bango a hankali yana sauke wasu irin ajiyar zuciya,sanda ya tabbatar ta bar gurin kafin ya juya ya bar gurin shima,ta backyard ya bi sai da ya kai apartment d'insu sannan ya zagaya ya shige,ko mutum d'aya bai tarar a parlon k'asa ba,ya haura sama cikin sauri kamar wanda ake hankad'awa ya shige bedroom d'insa yayi locking k'ofar ta ciki yabar key d'in a jiki,direct ya nufi bathroom bai ko tsaya cire kayan da suke jikinsa ba ya sakarwa kansa ruwa cold one,yadda ruwan yake sauka jikinsa haka yake jin sanyinsa yana ratsa jikinsa,for about 10 minutes ruwan yana sauka jikinsa then ya matsa ya cire jik'ak'k'en kayan ya jefasu washing machine ya d'aura towel ya fita,ya zauna bakin bed da duka hannuwansa ya rufe fuskarsa ya dunga sauke wani irin ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka then ya kife ya zubawa roofing d'akin ido. Da safe sanda ya fito kafin ya bar gidan sai da ya fara nufar apartment d'in Dadda because bai manta warning da Abba ya masa ba,yayi sallama bai jira a amsa ba ya shiga fuskarsa a d'aure,as usual kwance kan kujera ya sameta ta k'ure TV da idanunta tana sanye da gantalallun kayanta,kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa ya zauna kan kujera yana lumshe idanuwansa,ta d'ago da sauri jin mutum ya shigo ganin shi ne ta masa murmushi tace "Yaya ina kwana?" Kadaham kadahan ya amsa yana sake d'aure fuskarsa gudun kada taga fuska tace za ta zo jikinsa,daga haka babu wanda ya sake magana ta koma ta kwanta guiwoyinta a sanyaye ta ci gaba da kallonta,shi ma yayi shiru sai wayarsa da ya ciro ya fara dannawa,Dadda ta fito kitchen rik'e da plate da aka cikasa da farfesun kayan ciki k'amshin garlic sai tashi yake kamar shi kad'ai akasa ciki,tun kafin ta k'araso ta hangosa ta washe baki hak'orin makkanta suka fito tace "a'a Mamman maraba" kwantar da kansa yayi yak'i cewa komai,ta k'araso tana kallonsa tace "to me kuma ya faru kana ji ina maka magana ka share ni?" Ya d'ago kansa ba tare da ya saki fuskarsa ba har sannan yace "ina kwana?" Da fara'a sosai a fuskarta tace "lafiya lau,ka tashi lafiya?" A can k'arshen throat ya amsa "alhamdulillah" tace "har anyi shirin fitar ne?" Yace "ehh" daga haka ya mik'e,Dadda tayi saurin kallonsa tace "ko a zuba maka farfesun kaima?" Kai ya girgiza mata ya juya ya nufi k'ofa,ta bisa da kallo baki sake,har ya kusa fita ya waigo yaga shi take kallo yayi squeezing fuskarsa kamar bai shirya fad'ar maganar ba yace "arhmm! Think ya kamata tunda ke kad'ai kike fad'a mata taji,ki hanata saka irin kayan nan tana zama da su" k'uri Dadda ta masa da ido tace "ko saboda me?" Yace "wanda suke shigowa" kama baki tayi tace "yau naji ikon mai mana ruwa da k'ank'ara,fisabilillahi su waye suke shigowa idan ba ku ba?" Kallonta yaci gaba da yi,Dadda ta fara mita "kuji dai wani magana kuma,wai na hanata sawa,akan me ni kuwa zan hanata,yarinya tana shan iska kawai sai nace ta kirb'a uban kaya a jikinta..? A'a wallahi bazan hanata sa abunda ranta yake so ba,kai wa yake hanaka saka wanda ranka yake so? Idan ba ka son ganinta a haka sai ka daina shigo min,babu lallai babu tilas" gyad'a kai yayi bayan ya gama saurarenta ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fita ya barta sai mita take,Manar da ta gaji da sauraren mitarta ta mik'e tana b'ata rai ta nufi hanyar fita,Dadda ta bita da kallo tace "ke kuma ina za kije?" bata ce mata komai ba har ta k'arasa bakin k'ofa,haushin shirun da ta mata yasa Dadda d'aga murya tace "kina ji ina maki magana kika share ni?" Still Manar bata kulata ba ta bud'e k'ofar,gyad'a kai Dadda tayi tayi k'wafa fuskarta kamar za tayi kuka ranta ya sosu da abunda Manar tayi mata ta zubawa farfesunta idanu ta kasa ci,Manar dai tuni ta sa kai ta fice daga gidan,a parking space ta hangosa yana shirin barin gidan tun daga nesa take kallonsa sanda ya kallo gurin da take da sauri ta d'auke kai tana zumb'ura baki ta tsaya balcony tana knocking k'ofar tana satar kallonsa,mother ta bud'e mata k'ofar kasancewar duka yaran gidan basa nan,a door way ta tsaya tana k'are mata kallo,fuskarta a d'aure babu alamun wasa ta watso mata tambaya tace "a haka kika ratso gidan kika taho nan?" Kallon jikinta Manar ta fara yi,ta dago a shagwab'e tana kallon mother tace "mother me nayi?" Wani kallo mother ta mata a d'an fusace tace "ni kike tambaya me kika yi?" Rau² idanunta suka yi ta kasa magana,wani tsawa mother ta mata da yasa ta sakin kuka da gudu ta juya ta nufi hanyar komawa apartment d'in Dadda,har lokacin Dadda ta tasa plate d'inta gaba da hannuwanta biyu ta rafka tagumi,sanin yadda suka rabu yasa ko da ta shiga bata tsaya parlor ba ta wuce bedroom da sauri tana matsar k'walla,Dadda ta d'ago ta bita da kallo bata ce mata komai ba,tana shigewa ta kwanta saman gado ta ci gaba da rera kukanta. Da dare lokacin Waleed ya shigo fuskarsa a d'aure ya tarar da su zaune a parlor su hud'u,direction d'in da Manar take ya fara kalla,wannan karon sanye take da 3quarter na jeans da sleeveless light blue kanta babu hula,ya kalli yadda suke hira da Amaar sai dariya take b'ab'b'akawa ita da Ameerah,wani k'wafa yayi a k'asan ransa ya juya zai koma,Dadda da tun shigowarsa ta hangosa tace "kai kuma fa?" Tsayawa yayi daga bakin k'ofa,tace "da kai nake fa Mamman ka min shiru" bai juyo ba yace "me zan miki?" Tace "amma dan wulak'anci kana ji nake maka magana,shi ne za kace me za ka min?" Saurin juyawa yayi yace "laifi ne dan na tambayi abunda zan miki? Think ke kika ce idan bazan iya ganin jikarki a yadda take ba na daina shigowa,right?" Kicin-kicin tayi a masife tace "ehh! Na fad'a d'in,daga yau ma kace ka daina zuwa ka gani idan wani abu zai dame ni" gyad'a kai yayi yace "Ok! That's good,daga yau zan daina shigowa kamar yadda kika ce,but kada kuma daga baya ki k'ara zuwa ki had'a ni da mahaifina,tunda bakya son a nuna maki gaskiya,kin fi son wanda za suyi miki shiru,shi kenan kuyi duk yadda kuka so.." Yana gama fad'a ya aikama Manar da ta kafesa da idanu wani kallo a tsawace yace "bar kallo na" then yasa kai ya fice,tafa hannuwa Dadda ta shiga yi baki sake ta kasa furta komai,Amaar sai k'unshe dariya yake shi da Ameerah,Manar ta d'auke kanta tana tab'e baki,can Amaar ya daure duk da dariyar dake cinsa yace "Dadda wai me ya faru ne?" Kamar yayi playing d'inta idanunta sun cicciko da k'walla ta fara mita "ina ce a gabanku mutumin nan ya gama farfad'a min maganganun duk da suka zo bakinsa? Fisabilillahi ko dai ban had'a alak'a da shi ba,ya dace ya kalleni ya gaya min wannan maganar? Ko dai bai girmama shekaruna ba ai ya girmama furfura ta,ko ba haka ba?" Amaar ya gyad'a mata kai yace "hak'k'un!" Ta fara share hawaye kafin tayi zaraf ta mik'e,Amaar yayi saurin kallonta yace "ina kuma za kije yanzun?" A fusace kamar shi yayi mata laifin tace "ya ma za'ayi bayan kana kallon abunda ya faru ka tambayeni inda za ni?" Wani murmushi yayi yace "Allah ba-ki hak'uri" tayi gaba tace "ameen" tana fita Ameerah ta fara dariya tace "wallahi ta tafi kai k'aransa gurin Abba" Manar ta b'ata rai tak'i cewa komai kamar ba ta parlon,sai da aka jima kafin Amaar ya kalleta yace "wai me ya faru?" Manar tayi saurin kallonsa,yace "i meant me ya had'a su?" Tab'e baki tayi kafin ta sanar masa abunda ya faru da safe,Amaar dake saurarenta ya gyad'a kai yana kallonta yace "My brother ya yi gaskiya,as he said bai kamata kina zama da irin kayan nan ba tunda kin san muna shigowa,dukan mu babu muharraminki,so kinga akwai aure tsakaninmu kenan,a shawarin da zan iya ba-ki matsayin k'anwata,duk lokacin da muke nan ki daina sawa kinji?" Shiru tayi ta kafesa da idanunta,yayi murmushi ganin yadda ta b'ata rai yace "Ba fa ina nufin ki daina sawa duka ba,i just mean idan mun shigo nan,kin gane?" Gyad'a masa kai tayi ba don ta so ba,yayi murmushi yace "yawwa k'anwata,na san ki da biyayya Allah sa za kiyi amfani da shawaran da na ba-ki" k'in cewa komai tayi har Amaar ya gaji da mata maganar,ya d'auki wayarsa yana sakin murmushi yace "ko dai na kira maki Mommella kuyi magana?" Tayi sauri ta kallesa,bai jira cewarta ba yayi murmushi ya fara making call,ba'a jima ba Mommella ta d'auka,yasa wayar a hands free suna jin maganarta suka fara rige²n mata magana,da sauri ya mayar da wayar yadda shi kad'ai zai ji ya kai wayar kunnensa,suka gaisa da Mommella,Manar ta zuba masa idanu ta b'ata rai,Ameerah ma ta koma gefe ta masa k'uri da idanu tana jira yace su zo su karb'a,yana kallonsu yayi murmushi ya mik'e tsaye kamar zai fita da sauri suka fara masa magiya "Yaah Amaar dan Allah.." Saurin juyowa yayi ya d'aga musu gira yace "what?" Manar dai kamar za tayi kuka tace "to kuma ya za ka fita baka bari mun gaisa ba?" Ya d'an matsar da wayar daga kunnensa yana musu wani kallo yace "thought bakwa buk'atar ku gaisa ne?" Da sauri Ameerah ta tari numfashinsa "a'a wallahi muna so" gyad'a kai yayi yace "ohoo!" Ya dawo ya zauna,a nutse suka gama magana da Mommella then yace "Mommella Azaan fa?" Mommella tace "baya nan ya fita" yace "alright! Na kirasa ban samesa ba" Mommella tace "think ya bar wayoyinsa a gida,nima tun d'azun nake kiransa ban samesa ba" kallon Manar yayi da take cika yace "ga kids d'inki suna hararata saboda ban basu waya kunyi magana ba" Mommella tayi tace "give them the phone kai kuwa mana.." Manar ya kalla yana d'aure fuska yace "ni kuke jira na kawo muku wayar?" A tare suka yi saurin tasowa ya mayar musu wayar hands free,suna kan magana da Mommella Azaan ya shigo,yayi sallama Mommella ta amsa masa,zaunawa yayi har suka gama magana,suka yi sallama lokacin Manar take tambayar Mommella "Mommella yaushe za ku zo?" Shiru Mommella tayi da farko then tace "i'm so sorry baby mun d'aga zuwan ne amma da yanzun haka muna 9ja" b'ata rai tayi kamar za tayi kuka tace "to kuma sai yaushe za ku zo?" Mommella tace "maybe sai end of the year" ba'a son ransu ba suka amsa "Allah kawo ku lfy" Mommella ta amsa "ameen" Azaan da tun zamansa baiyi magana ba Mommella ta kalla tace "Amaar ya kiraka bai sameka ba,ina ka bar wayoyinka?" Suna jin sanda yace "i'll call him" Manar tace "Yaah Azaan!" Yace "Mmm! Baby ya kike?" Tace "lafiya lao.. Kaifa?" Yace "alhamdulillah" kafin ta sake magana yace "kice da Amaar za muyi magana anjima kad'an" kallon Amaar da ya kulle idanuwa tayi tace "yana jinka ma" yace "alright! Later dear.." Suna yin sallama suka mik'awa Amaar wayarsa,ya tashi ya fita ya barsu su biyun suka ci gaba da hira suna dariya..

#Share pls.
#Asli Smasher.

MANARWhere stories live. Discover now