Seizure

238 26 36
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.

                    *♡MANAR¸.•💥*
               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

                                07.

#Seizure

        Da kallo Mama ta dunga bin Diyanah sanda ta zauna,tana squeezing fuskarta tace "Mama u know what?" Mama dake kallonta har sannan ta kasa kauda idanunta a kanta tace "sai kin fad'a" Diyanah tace "yanzu naga wancan yarinyar ta fito daga d'akin Yaya,ko uban me ya kaita,ohoo?" Still Mama tayi tana kallonta kafin tace "wace yarinya?" Diyanah tace "wancan Manar d'in mana" wani irin zaro idanu Mama tayi da k'arfi ta kwala cewa "kutumar uba! Uwar me ya kaita d'akinsa,me za ta masa?" Diyanah ta watsa hannuwa alamun bata sani ba,Mama ta dunga cika kamar za ta fashe a fusace tace "Deejah maza² je ki k'ira min Yayanku" da sauri Deejah tace "kaiii! Mama ni dai gaskiya ki aiki Diyanah Allah ba na son zuwa kusa da shi" wani kallo Diyanah ta aikama Deejah tace "Tabbb' d'i wallahi bazan je ba,naga dai ke Mama tace ki kirasa ba ni ba,salon naje ya haure ni da k'afa ko ya rankwashe ni? Wallahi idan baza ki ba sai dai a bari har ya dawo gidan" ganin sun tsaya jayayya yasa Mama nufar hanyar fita ba tare da ta sake bi ta kansu ba,ta tsaya dai² bedroom d'insa tana knocking,kusan mintuna biyar ta d'auka tsaye a gurin ta k'i hak'ura sai bubbuga k'ofar take a tunaninta yana jinta yak'i bud'ewa sanda taji shirun ya yi yawa babu alamun da mutum a ciki da sauri tayi k'asa tana tambayar maids Waleed,Haulatu dake goge² ta sanar mata ya fita babu jimawa,ta gyad'a kai bata ce komai ba ta koma sama. Yinin ranar gaba d'aya Manar bata zauna apartment d'in Dadda ba,haka a b'angaren Mama itama ta wuni neman Waleed motsi kad'an taji sai ta fito daga ta duba ko shi ne ya dawo but ranar har dare bai shigo ba. Da daren lokacin Amaar ya shigo ya samu Dadda zaune ita kad'ai ta hard'e k'afafu tana girgiza su,da sallama ya k'arasa Dadda ta d'aga kai ta bisa da kallo sanda ya isa inda take yace "Hjy barka da dare" idan ta amsa materials da suke parlon sun motsa,yadda tayi ba k'aramin dariya ta kusa basa ba ya danne yace "Hjy Manar fa?" Kamar wanda take jira a mata magana a fusace ta d'ago tana masa wani kallo tace "wace ce wata Manar kuma?" Yace "jikarki mana" tace "aka ce maka kuma a nan gidan take?" Shima da yake tsokana yake ji sai ya nemi guri ya zauna k'asa² yake dariya yace "to wai a ina take ne?" Dadda ta masa banza,yace "Hjy ki taimaka ki fad'a min inda zan sameta" banza da shi tayi,da yaga ba ta da niyyar masa magana ya tashi yace "shi kenan tunda baza ki fad'a min ba,auren ma daga yau na daina tunda kina jina baza ki min magana ba" wani kallo ta watsa masa da yasa shi fashewa da dariya,a fusace Dadda tace "ni dai yau ina ganin masifa k'uru² wani ya fad'a maka akwai wata mai sunan a nan gidan ne?" Murmushi yayi yace "alright! Dama sak'o aka ba-ni,ko na ba-ki ki ajiye mata?" Cikin fad'a tace "kada ka ba-ni dan wallahi bazan aje ba,ni da ita haihata²,daga yau ni da ita kowa yayi ta kansa.. Allah na tuba me ake da mutane irin ku,duka taron marasa amfani" juyawa yayi saurin yi yana dariya ya san idan ya tsaya ta dunga mita kenan,duk fushinta a kansa za ta saukesa,yana fita ya hangosu ita da Ameerah suna fitowa apartment d'in mother,da kallo ya bisu ya tsaya gurinyana murmushin fad'an Dadda sanda suka k'araso Manar tace "Yaah Amaar ina wuni?" Yace "lfy lou y'an matan Hjy Dadda,daga ina kuke?" Manar tace "munje gurin mother" ya gyad'a kai yana sakin murmushi yace "yaji kuka yiwa Dadda yau?" Dariya suka kalli juna suka yi,yayi murmushi yace "yanzun ina za ku?" Ameerah tace "abinci za muje kai mata" ya gyad'a kai yace "sai kun dawo ni bari na tafi.. Allah tsare ku da fad'anta" har ya yi gaba ya waigo ya kwaloma Manar kira,ta juya tana kallonsa,yace "idan kun dawo ku sameni d'akin Aunty akwai sak'on da zan ba-ku" amsawa suka yi suka nufi k'ofar apartment d'in kowa tana had'e rai suka yi sallama,Dadda bata ko d'aga kai ta kallesu ba,Ameerah dake d'auke da folded basket green colour ta k'arasa kusa da ita ta ajiye tace "ga shi inji Aunty Mammy" kamar ta kunno Dadda ta fara fad'a "d'auki abunta ki mayar mata bazan ci ba,ko an fad'a muku ni y'ar yunwa ce da za ku kawo min wani shegen shinkafar da babu dad'i babu dadad'awa" kallonta suka tsaya yi baki sake,a fusace ta tura basket d'in gefe tana mita,Manar tayi k'wafa suna had'a ido da Ameerah ta gyad'a kai ta k'araso gurin,ta kai hannu za ta d'auke basket d'in a fusace Dadda ta kai mata duka,fashewa da dariya suka yi,Ameerah dake kallon Dadda tana dariya tace "Ha'a! Kefa kika ce bakya so a mayar mata" cikin jin haushi Dadda tace "kuji wani masifar kuma! Ni yaushe kika ji na ce haka? Salon dai kar abar mutum ya zauna lafiya,yanzu idan Maryam taji fisabilillahi ba sai ku janyo ta k'ullace ni ba" Manar ta had'e rai tace "ke dai Dadda ki daina haka Allah,sai ki fad'i magana idan ance kin fad'a kice ba haka ba?" Dadda ta juya ta kalli Ameerah tace "yanzu y'ar nan tsakani da Allah kin ji na ce muku wani abu tun shigowarku?" Dariya Ameerah ta sake fashewa da ta girgiza ma Dadda kai,nan da nan Dadda ta k'ule saboda dariyar da Ameerah keyi tace "ke ni fa ban son haka,sai kuzo kusa mutum gaba kuna masa wani dariya kamar kwancen mahaukata" da sauri Ameerah ta juya ta kalli Manar tace "Sis muje Yaah Amaar yana jiran mu" Dadda ta tsuke fuska bata sake ce musu komai ba ta ja basket ta fara fito da warmers dake ciki,kusan tare suka shiga gidan da Waleed Manar ta dunga kallonsa ganin ya d'aure fuska ta kasa masa magana,Ameerah kad'ai ta gaishesa Manar kam tuni ta yi sama,ta gefen idanunsa ya bita da kallo yayi k'wafa,bai dai ce komai ba ya nufi saman shima Ameerah ta biyosa a baya,yana wucewa ta bud'e bedroom d'in Aunty ta shiga,ta tarar da Manar ita kad'ai a d'akin sai cika take k'iris take jira ta fashe,da kallo ta bita ta tsaya doorway bata k'arasa shiga ba tace "Ina Yaah Amaar d'in kuma?" Manar ta watsa hannuwa fuskarta a d'aure tace "nima ban samesa ba da na shigo" juyawa Ameerah tayi da niyyar zuwa ta kirasa taga ya fito daga d'akinsa d'auke da wata jakar kwali,yana zuwa yace "muje ko da bina za kiyi?" Tayi murmushi bata ce komai ba ta shiga ya biyo bayanta,kujeran gaban mirror ya janyo ya zauna,Ameerah ta matsa kusa da Manar ta zauna sai kallon jakar hannunsa take,ya mik'a ma Manar yace "take! Azaan ya bayar a kawo miki" kallon jakar ta dunga yi,mamaki k'arara a fuskarta tace "Yaya mene a ciki?" Ya d'age kafad'u yace "abun a hannunki kina tambayata,ki bud'e ki duba mana" Ameerah ce tayi saurin karb'a tace "kawo muga tunda kin kasa fitowa da su" tasa hannu ciki ta janyo kwali biyu dake ciki masu d'an girma,waya ne guda biyu k'iran samsung galaxy A70,Ameerah ta zaro ido tace "Yaya ai phones ne" yace "yeah! I knew" murmushi tayi kafin ta fara duba kwalin phones d'in,ya mik'e zai fita yace "akwai layi ciki,and akwai numbers d'in kowa sai ki duba abunda bai yi ba ki gyara" godiya ta dunga masa kamar shi ya ba-ta,Ameerah ta fito da su duka Manar ta kalli wayoyin taga iri d'aya babu bambanci sai na colour tayi dariya tace "Sis ki d'auki d'aya nima na d'auka d'aya" Ameerah ta girgiza mata kai tace "a'a ni bazan d'auka ba" saurin kallonta Manar tayi tace "saboda me baza ki d'auka ba?" Ameerah tace "ai duka ke yace a kawowa" Manar tace "to kuma iri d'aya? Ni me zanyi da waya biyu?" Ameerah tace "a'a ki rik'e duka kin san dalilin da yasa ya aiko miki su?" Manar tace "ko mene ne ni dai ba na so d'aya ya ishe ni" duk yadda Ameerah za tayi sai da tayi akan baza ta karb'a ba itama Manar ta dage,dole daga k'arshe ganin ranta ya b'aci ta d'auki d'ayan tana fara mata godiya ta katseta tana aika mata harara a fusace ta tashi ta fita. Yana shiga bedroom d'insa ya fara unbuttoning shirt d'in jikinsa Mama ta banko k'ofar kamar wanda aka cillota,ya juya da niyyar ganin waye ya shigo,ganin Mama yasa shi yin ajiyar zuciya,but kallon da take aika masa yasa jikinsa ya bashi akwai matsala,a nutse yana kallonta yace "Mama lafiya?" A fusace tace "uban me ya had'a ka da yarinyar can?" Zaro k'ananun idanunsa yayi cike da mamakin maganarta yace "wace yarinya?" Tace "yarinyar Maryam nake maka magana" tunani ya tsaya yi because bai fahimci akan wanda take magana ba,cikin fad'a tace "yarinyar da kakarku ta gama gurb'atawa ita kake shige ma Waleed? Shin ban hanaka mu'amala da duk abunda ya shafi Maryam ba?" Sai lokacin ya fahimci akan wa take maganarta,ya sauke wani heavy ajiyar zuciya ba tare da ya ce mata komai ba ya koma bakin bed d'insa ya zauna,fad'a sosai Mama ta rufe ido ta dunga masa har kamar za ta aro baki,yayi shiru bai ce mata komai ba sai da ta gama yace "Mama babu wani abu tsakanina da ita fa" wani kallo ta masa tace "ehh! Saboda ka d'auke ni sha³ ko? Shisa kake fad'a min babu komai tsakaninku,bayan an fad'a min an ganta d'akinka? Idan har babu komai tsakaninku me ta zo ta maka?" Still yayi yana kallonta fuskarsa d'auke da mamaki yace "waye ya fad'a miki Mama?" Wani kallo ta aika masa tace "me ka d'auke ni ne kam Waleed? Bazan san abunda kake aikatawa a bayan idanuna ba kake nufi?" Zai yi magana ta katsesa "ba na buk'atar jin ko wane irin magana daga bakinka,ka rufe min baki kafin raina ya b'aci" kamar yadda ta buk'ata haka yayi shiru,sai da ta gama masifar fad'an dan kanta tayi shiru,a hankali yace "i'm very sorry Mah,amma abunda kike tunani ba haka yake ba,Abba ya aikota ta karb'i sak'o" kallonsa ta dunga yi tace "sak'o?" Ya gyad'a mata kai yace "sure" a hankali ta sauke wani bayyanannen ajiyar zuciya jin ba abunda take tunani bane,but duk da haka bata fasa fad'in "ni dai na fad'a maka babu kai babu ita,kabi hanyarka itama tabi nata,bana son ko wane irin kusanci yana had'aku,kai idan da dama ma ko hanya ta bi kada ka kuskura ka bi,ka canja wani kawai shi ne abunda nake buk'ata,hakan shi zaisa nayi farin ciki kuma ya ba-ni nutsuwa" gyad'a mata kai yayi a hankali cike da wani irin mutuwar jiki yace "done!" Tayi masa murmushi tace "good" then ta juya za ta fita,da idanu ya bita yana jin gabansa yana tsananta fad'uwa saboda k'aryan da ya yanko mata,ya san halin fad'anta akan yar k'aramar magana sai ta masa babu dad'i,kome kuma zai fad'a mata ba yarda za tayi ba but yana had'awa da Abba sai gashi har ta fita,a hankali ya rufe idanunsa yana tunanin maganganunta,wani tambayar da yake yawan yiwa kansa game da alak'arsa da Manar da Mama ba-ta so,ba tun yanzun ba abun ya tsaya masa a rai,iya bincikensa kuma ya kasa gane gaskiyar dalilin Mama na son datse alak'ar nasu,shin me  yasa yake hango tsana mai girma a idanunta duk lokacin da aka ce mata wani abu ya had'asa da Manar? Wannan amsar ita ne ta gagaresa samu har yau,ya rasa kuma wanda zai tambaya ya bashi amsa. Tana fita d'akin fakam² take tafiya,underneath ta fara zana munanan kud'urinta towards Manar,ta bud'e bedroom d'inta ta shiga lokacin duka yaran basa nan already sun fita,ta mayar da k'ofar ta kulle,bakin gadonta ta k'arasa ta zauna,wani tunani ne ya fad'o mata a rai,da sauri ta d'auki waya ta fara kiran line aminiyarta Hjy Izzatu,bugu d'aya a na biyu ta d'auka da fad'in rai ta furta "k'awata ya gari?" Hjy Asama'u tace "lafiya,ba lafiya ba" da sauri Hjy Izzatu tace "tofa! Wani matsalar ya faru?" Mama tace "ina gudun ace haka ya faru Hjy" Hjy Izzatu tace "me yake faruwa?" Mama tace "ina ga gobe zan shigo,maganar ya fi k'arfin muyi shi a waya" amsawa Hjy Izzatu tayi da "alright! Allah kawo ki lfy,sai kin shigo d'in" suka yi sallama,ajiyar zuciya Mama tayi tana gyad'a kai,a fili ta furta "dole ne na tsaya a kanka Waleed,idan ma akwai abunda yake tsakaninku kake b'oyemin,tabbas zan shiga na rabasa.." Da safe lokacin Waleed ya shiga apartment d'in gaida Dadda ya tarar bata nan,da murnanta Manar ta d'auko wayarta ta nufesa tace "Yaya ina kwana" bai kalleta ba ya amsa,ya nemi guri ya zauna,ta k'arasa kusa da shi ta zauna tace "Yaya ka ga wayana da.." Bata k'arasa ba taga ya wani irin juyo ya kalleta sai da ta tsorata tayi baya,ya zuba mata idanunsa yace "waye ya baki damar rik'e waya?" Rau² idanunta suka yi tace "Yaya Azaan ya aikomin da shi" d'aure fuskarsa yayi yace "Azaan?" Ta gyad'a masa kai,gyad'a kai yayi yace "ba ni na gani" girgiza masa kai tayi,ya kafeta da idanunsa ganin da gaske baza ta bashi ba ya mata tsawa yace "ba ni nace" jikinta har b'ari yake ta mayar da hannuwanta baya ta b'oye ta ci gaba da girgiza masa kai,yace "baza ki bayar ba?" Da sauri ta gyad'a masa kai,murmushi yayi yana lumshe idanunsa yace "kada ki bari na kamaki baza kiji dad'i ba" zumb'uro masa baki tayi tace "to ba k'wacewa za kayi ba?" Yace "haka kika ji na ce miki?" Ta girgiza masa kai tace "to ai na san haka ne" gyad'a kai yayi bai sake mata magana ba ya kawar da kansa daga kanta,jan jikinta ta fara yi tana matsawa,ba tare da ya kalleta ba yace "ina za kije?" Da sauri ta mik'e hannayenta a bayanta tana b'oye su ta juya za ta gudu,yana sane yasa mata k'afa,saura kad'an ta fad'i k'asa yayi sauri ya fizgota ta fad'a jikinsa,a tare suka saki wani marayan ihu,k'amshin scent's d'insa da suka kaiwa hancinta ziyara da fad'uwan da tayi ba a k'asa ba yasa tayi saurin bud'e idanunta,idanunsa a kulle yana sauke numfashi a hankali,Manar dake jikinsa yadda taji yana kara cuddling d'inta yana wani k'ara kulle idanu yasa ta fara mutsu² tana son tashi,a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa ya saukesu kan kyakykyawar fuskarta,tura baki tayi a shagwab'e idanunta suna tara hawaye tace "Yaya ka sake ni" d'aure fuskarsa yayi yace "ni zan sake ki ko ke za ki d'aga ni?" A shagwab'e tace "to ba kai ka rik'e ni ba" wani kallo ya mata kafin yayi saurin janye hannayensa da ya zagayeta da su yana aika mata harara yace "sai ki tashi ai" da sauri ta mik'e daga jikinsa tana zumb'uro masa baki ta juya bayanta,ya harareta maimakon ya tashi kawai sai ya sake gyara kwanciyarsa ya lumshe idanunsa,juyawa tayi za ta bar gurin ta jiyo maganarsa "kuna da ruwan zafi?" Tace "ehh akwai a flask" ya gyad'a kai daga kwancen da yake yace "je ki had'a min tea" saurin juyawa tayi ta kallesa tace "Yaya yau alhamis fa" idanunsa a rufe yace "I knew" tayi still tana kallonsa tace "Yaya ba kana azumi ba yau?" Bai bud'e idanunsa ba yace "ina ruwanki?" Ta zumb'uro masa baki tace "to ba gani nayi duk litinin da alhamis kana yin azumi ba?" Yace "za kije kiyi abunda na saki ko sai jikinki yayi tsami?" Da sauri ta juya tace "Allah baka hak'uri" bai kulata ba ta juya ta shiga kitchen ko minti uku ba'a yi ba ta fito da mug cike da ruwan zafi,tana k'arasowa inda yake tace "Yaya" bud'e idanunsa da suka d'an birkice yayi ya kalleta,tace "ga shi" ya kalleta yana d'aure fuskarsa yace "mene ne wannan?" Tace "ruwan zafin daka tambaya" yace "haka nace kiyi min?" Ta tsaya kallonsa,ya sake d'aure fuskarsa yace "ba dake nake ba kika kafe ni da idanu?" Juyawa tayi tana k'unk'uni ya gyad'a kai yace "ina jinki ki gama zagina" saurin juyowa tayi tana kallonsa,fuskarta kamar za ta fasa kuka tace "nifa bance komai ba,yace "nayi miki k'arya" ta girgiza kanta da sauri tace "a'a.." Wani kallo yayi mata yace "me kika ce?" Kamar za tayi kuka tace "nifa ban ce komai ba" ya gyad'a kai yace "k'aryar dai kike nufin na yi miki,right" kafin ya sake magana tuni hawaye har sun wanke mata fuska,ya sake gyara zama ya zuba mata sexy idanunsa,cikin matuk'ar d'aure fuska yace "idan kika bari ruwan nan yayi sanyi za ki ji jiki" share hawayen tayi saurin yi ta koma kitchen sai b'ata rai take ta had'a masa lafiyayyen tea thick one,ta dawo ta kawo masa,ya karb'a yana kallon spoon data sa yace "waye yace miki ina shan tea da spoon" ba tare da ta ce komai ba ta d'auke,ta juya ta koma kitchen ta ajiye,tana fitowa ta tarar ya ajiye mug d'in yana danne² a wayarta data ajiye,ta dunga kallonsa gabanta sai fad'uwa yake,tana kallon mug d'in ta fara tunanin masa magana,a hankali tace "Yaya shayin zai huce baka sha ba fa" bai d'ago ba yace "wani yace miki ina shan abu da zafi?" Tayi still tana kallonsa,mamakinsa yasa ta kasa sake cewa komai,kusan mintuna biyar ya d'auka kafin ya kai hannu ya d'auki mug d'in ya kai bakinsa,idanunsa har lokacin akan wayar yace "me kike kallo?" Tayi saurin girgiza masa kai tace "babu komai" yace "idan akwai dai ki fad'a" sake girgiza masa kai tayi,daga haka bai sake tambayarta ba parlon yayi shiru,sanda ya kusa shanye tea d'in tace "na d'auko maka bread?" Ya girgiza mata kai alamun baya so,ta juya tayi shiru tana tunanin wayarta da ya d'auka,ba tare da ya kalleta ba yace "je ki kunna min TV" tashi tayi ta kunna,ta dawo ta zauna hankalinta akan TV amma zuciyarta ta yi nisa gurin tunani,tsaf ya gama dube²n da zaiyi ya ajiye wayar kusa da nasa,ko cikakken minti biyu ba'ayi ba aka fara kiranta,ya kalli screen d'in sunan wanda ya gani yana kira yasa shi d'aure fuskarsa,har kiran ya katse aka sake kira bai ce mata komai ba,ring d'in da taji yana sake tashi yasa ta d'aga idanunta ta kalleshi tana jira taji ko zai ce tazo ta karb'a but har kiran ya sake katsewa ko tari yak'i yi,for the third time ana sake kira yayi tsaki ya mayar da wayar silent,Manar da taji bai ce mata komai ba ta sunkuyar da kanta tana matsa fingers d'inta,ya jima sosai a gidan kafin ya tattara belonging d'insa ya nufi hanyar fita,ta d'aga kai ta bisa da kallo sanda ya kai k'ofa kamar ance ya juya,yana waigawa yaga shi take kallo ya tab'e baki ya k'arasa ficewa,kuka ne ya kwace mata da gudu ta tashi ta shige d'aki ta fad'a saman gado,bayan ta yi mai isarta bacci ya d'auke ta sai da Ameerah suka dawo skul ta shigo ta tasheta,tana bud'e idonta ta fara jan zuciya Ameerah ta zuba mata ido tace "me ya faru sis?" Wani kukan ta fashe da shi,hankalin Ameerah a tashe tace "tell me please! What happened? Me aka miki?" Da muryar kuka tace "ya k'wace min wayana" Ameerah ta zaro ido tace "waye?" Tace "Yaya" still tayi tana kallonta kafin tace "ya akayi yaga wayar?" Manar cikin kuka tace "nice na nuna masa" dafe forehead Ameerah tayi saurin yi tace "kema fa sai da nace miki kada ki bari ya gani zai kwace,shi ne baki jiba kika kai masa,ai ga shi nan kin janyo ya kwace" tana share hawaye tace "ara min naki na kira Yaa Azaan" Ameerah tayi shiru da farko then tace "sai dai idan baza ki fad'a masa ba" Manar tayi saurin kallonta tace "wa zan fad'awa?" Ameerah tace "shi Yayan" gyad'a mata kai tayi tace "bazan fad'a masa ba" Ameerah tace "promise?" Manar dake kallonta tayi squeezing fuskarta tace "me?" Ameerah tace "kinyi alk'awari?" Da sauri ta gyad'a mata kai tace "ana bu'udak" murmushi Ameerah tayi then ta mik'a mata wayar,da sauri ta karb'a da yake ta haddace number Azaan a kanta nan da nan tayi saurin sakawa ta fara kiransa,lokacin Azaan yana driven kamar bazai d'auka ba da farko ganin da number Nigeria ake kiransa yayi shiru yana tunani kafin yayi parking gefen hanya,ya d'auka yasa wayar hands free,muryar Manar ya ji ta ce "hello! Yaya" da sauri ya katse ya kirata back,hannunta har rawa yake ta d'auka da muryar kuka² tace "Yaa Azaan" tana jinsa yayi ajiyar zuciya yace "na'am baby" kuka ta fashe da shi,a rikice yace "Subhanallah! What happened? Waye ya tab'a min ke?" Toshe bakinta tayi saurin yi,hawaye wani na bin wani,Azaan sai magana yake mata ta kasa amsawa,da sauri ya katse kiran hankalinsa a mugun tashe ya kirata video,tana ganin kiran ta kasa d'auka,shi kuma ya kasa hak'ura sai kiranta yake sake yi,Ameerah dake kwance ta zubawa sarautar Allah ido ganin Manar ba ta da niyyar d'auka ta fizge wayar tayi answering,da wani breaking voice yana ganin an d'auka ko gama tantance fuskar waye akan wayar baiba ya fara tambayar "Baby tell me what happened,me aka miki,ke da waye?" Ameerah tace "Yaa Azaan ita da Yaya ne fa" da sauri Azaan yace "Ameerah! Ita da wane Yayan ne?" Tace "Yaya Waleed" idanu ya zuba mata yana maimaita "Waleed! Me ta masa? Can u explain me ya had'a su?" Ta gyad'a masa kai tace "wayarta ya kwace mata" Azaan yace "ya kwace,for what reason?" Girgiza kai tayi tace "nima ban sani ba,na dawo skul yanzun take fad'a min" gyad'a kai yayi yace "tun yaushe ya karb'a?" Tace "i don't know,amma ina jin tun safe ne" lumshe idanunsa yayi yace "alright! Ba ni ita muyi magana" mik'awa Manar wayar tayi,ta kasa karb'a sai kuka take,Ameerah tace "Yaa Azaan tak'i karb'a fa" da sauri Azaan yace "Baby!" Kina jina?" Ta gyad'a kai bata d'ago ba,yace "kukan ya isa haka,dan ya karb'i wayan kike damuwa?" Tayi sauri ta d'ago kanta wasu hawayen suna sauka cheeks d'inta tace "ni ba a kansa bane" yace "Uhn! Tell me akan mene ne to?" Da muryar kuka tace "kana ta kira ban d'auka ba,na san ka yi fushi" wani beautiful smirk ya sakar mata yace "banyi fushi ba dear,yanzun ba gashi na san dalilin k'in d'aukan kiran ba" saurin karb'ar wayar tayi daga hannun Ameerah tace "da gaske?" Ya gyad'a mata kai yace "absolutely sure dear" tayi murmushi ta share hawayen,ya sake yi mata murmushin da yake k'ara masa kyau,a hankali yace "ki daina kukan haka nan,anjima za'a kawo miki wani kinji?" Gyad'a masa kai tayi,ya sake yin murmushi yace "shi kenan?" Tace "Ehh!" Yace "ina Dadi?" A shagwab'e tace "bata nan" yace "ina ta tafi?" Tace "ta je gidan k'awarta" gyad'a kai yayi yace "sai ku kad'ai ta bari?" Tace "ehh!" Ya gyad'a kai yana lumshe idanunsa yace "alright! Later za muyi waya idan na k'arasa gida ina hanya kika kira" ajiyar zuciya tayi tace "to! Allah tsare hanya" yayi mata murmushi yace "ameen.. Thank u" tace "ina gaisar da Momellah" ya amsa mata,ita ta fara katse kiran,tana d'agowa ta saki ihu,da wani muryar shagwab'a tace "sai yayi ta karb'ewa,ai dai ga shi za'a k'ara kawo min wani" Ameerah tayi dariya tace "Iyeeeee! Y'ar gatan Yaa Azaan" Manar tayi murmushi had'e da yin fari da idanunta tace "ya son ranki?" Ameerah tace "Aahhh! Normal" saurin tashi manar tayi tace "ke ni banyi sallah ba" tayi sauri ta dira daga gadon,bayan ta idar hira sosai suka yi kafin yunwa tasa su tashi suka fita zuwa gidan mother..

#Share pls.
#Asli Smasher.

MANARWhere stories live. Discover now