Cikin hanzari ta fito daga cikin keke napep din da ya kawo ta kofar gidan, ta juya kusan a guje ta shige cikin gidan ko sallama babu. Kai tsaye dakin su ta nufa a gurguje ta fiddo karamar jakarta ta tafiya wadda daman tun cikin daren jiya ta hada kayanta tsaf domin barin garin a yau. Sai da ta dauko jakar ne sannan ta nufi falon gidan in da mutanen gidan ke ta faman kallon TV. Daga bakin kofar ta tsaya tai sallama kana ta gaida aunt din tata wacce ke zaune a kujera rike da karamin littafin forty Rabbana a hannu, "Assalamu Alaikum! Ina wuni anty." "A' aha! Safeenah daman kin dawo?" Cewar aunt din tata " yanzu nake tambayar Nanah ko jarabawar taku ta yamma ce, naji shiru baki dawo ba gashi kin ce yau kike son komawa" Safeenah ta dan ja gajeran tsaki tace "wallahi dan matsala aka samu shi yasa sai wajen karfe biyu ma muka shiga" "lallai kam! Allah dai ya taimaka ya sa kun yi a sa'a." Safeenah ta amsa da amin.
Dake aunt din bata lura da jakar dake hannun safeenar ba sai ta cigaba da cewa "ai sai ki shiga ciki ki canza ki zo ki ci abinci ki huta. Ke Nanah tashi maza ki dauko mata abincin kafin ta fito, kin yi shiru gaban TV kina ji ana magana dan kin raina mutane. Ni shi yasa wannan kallace-kallacen banzan ban san shi..." Safeenah ce ta tare ta da cewa " a'a anty, dama kin kyaleta kawai dan yanzu haka ma sallama zamu yi in tafi dan ga jakata ma na dauko kuma ga mai napep na tsaida zai kaini park" "ban gane sallama ba; da wannan yamman kike son kama hanyar doguwar tafiya irin wannan? Ai ko baza ki tafi yau ba. Ke Nanah, ungo kudi je ki sallami mai kurkurar. Ke kuma ki maida jakar daki gobe in Allah ya kaimu da wuri sai ki tafi"
Safeenah ta bata rai, dan ita bata son ko kwana ta kara a garin bayan gama jarabawar ta. Ba wai garin bane ba dadi; a'a, kowa ya san Katsina akwai dadin zama kuma ita ma tana jin dadin garin amma qawazucin gida ne da ita sosai. Duk yanda gari yai mata dadi in dai ba abin da take to tafi kaunar ta ganta a gida gaban iyayen ta. In baka sani ba sai ka zaci bagidajiya ce domin bata san barin gida ko garinsu ko kadan amma abin ba haka yake ba domin Safeenah ta ziyarci garuruwa da dama; wasu lokutan dan makaranta wasu kuma don ziyara da sada zumunta kuma tana jin dadin tafiye- tafiye sai dai bata dadewa a gari take kewan gida hakan yasa da ta kammala abin da ya kaita take komawa.
"Kai anty, da dai kin barni na tafi, da yau da gobe ai duk daya ne?" "Ja'ira! Yo tunda kin san haka sai ki bari goben ki tafi ai duk daya ne." "To ai na riga da na fada masu cewan zan taho yau din." Aunt din ta fara harzuka " to in kin fada musu sai me? Nace baza ki tafin yau ba sai gobe saboda dare yayi, dubi yanzu karfe biyar; har yaushe kika je tashar kika samu mota har ta cika kuka tashi? Idan ma kin samu motar kenan domin sanin kanki ne cewa ba a samun motar Abuja in ba da safe ba. Ko su in suka san yanzu zaki tafi ai sa ce ki jira gobe, idan kuma ita Zainab din ce tace ki tafin sai in sani"
Nan idon Safeenah yai raurau da hawaye, ta dauki jakar tata ta koma daki dashi ta ajiye.
Bata sake fitowa ba sai bayan da aka yi maghrib sannan anty ta aika kiran ta " wato fushi kike dan na hana ki tafiyar dare? Ke baki san ran ki da lafiyar ki nake dubawa ba; a dai irin yanda kasar nan ta zama, to ai shi kenan" nan Safeenah tai maza ta zauna saitin kafar aunt din ta na dan matsawa tace " kai anty ni ba fushi nake ba, ai na hakura. Yau da goben duk daya ne in Allah ya bar mana rai ma awanni nawa suka rage. Kawai dai hutawa nake tun da goben da wuri nake son tafiya" "to ai kin ga hakan ya fi, ido na ganin ido sannan ki isa da wuri har ki samu ki huta ma"
Nan dai suka ci gaba da hirar gwanin dadi har Nanah ta ida sallah ta zo ta iske su aka ci gaba da yi da ita, dake ba wani tazaran shekaru tsakanin su. Dududu bai wuce shekara biyu ba Safeenar ta ba Nanah yasa ma zaman nasu yazo daya.
A nan ne Nanar ke cewa "yanzu goben in kin tafi yaushe zaki dawo?" Safeenah ta dan yi murmushi tace "Nanah kenan! Ni ma zan yi kewar ki ai amma kar ki damu, duka hutun namu sati biyu ne kawai so in Allah ya yarda ba zan wuce 3 weeks ba"
"Yo dama duk wannan zalamar sati biyu ne kawai hutun? Kai wannan 'yar da kawazuci kike. Maimakon kiyi zaman ki" cewar aunt din tata.
Tab! Yaushe zan iya, hutu ai ko na kwana daya ne sai na tafi in sha Allahu
Safeenah ta fadi a zuciyarta amma a fili sai cewa tayi "ai dake in muka dawo sabon semester za a fara kuma babu wani hutun nan kusa shi yasa" "tafi can! Kawai dai kulafuci ne kawai" inji aunt din. Ai ko Safeenah sai ta zumburi baki ita ko Nanah sai dariya take.
A haka mai gidan, Alh. Mu'azu ya iske su, bayan sun gaishe shi da aiki ne suka kawo mishi abincin shi ya ci har shima ya tofa albarkacin bakin shi na yadda jiran gobe da tayi shi yafi dacewa.
Allah dai ya kaimu wannan goben cewar Safeenah cikin ranta.
Daga nan suka cigaba da hirar har lokacin kwanciya bacci yayi kowannen su ya nufi makwancin shi.
That's it! The 1st chapter, I knw it's nt much bt I promise it'll get better nd I really hope u lyk it; so do vote, comments nd share.
See U guys on the next update
Thanks.
YOU ARE READING
Tarayyar Jini
RandomTun haduwar su ta farko bai manta ta ba don haka bai daina neman ta ba amma shin a ina zai ganta bayan ko fuskarta bai gani ba balle ya san sunan ta. Hasalima babu wani abu daya hadasu face jininta dake yawo a jikin shi.
