Saboda wulakancin da Alhaji Ghali yai mun a duniya yanzu lokacin daukar fansa nai, hakika kai hadimi ne na gaske komai ya tafi yadda nakeso, na sa shi a hanyar da ba zai iya bullewa ba, ina so ka wargaza duk wani aiki da kai musu."

"Hhhhhh! Ya sheke da dariya da muryarsa mara dadin amo, tabbas bukatar ka ta gama biya saura kadan ya girbi abun da ya shuka. Hhhhhh!"

Hhhhhhhhh! ya sheke da dariya "a yau burina ya gama cika a duniya, na dauki fansar jinin dana da matata da Alhaji Ghali yai silar salwantar su a duniya, sai kuma ya fashe da kuka ya mike ya sake komawa cikin bukkarsa yana hada kayansa.

_Waye wannan bokan wai?_

Ainihin sunansa Malam Habu, mutum ne mai ilimi sosai irin kararun kolawan nan na Maiduguri asalinsa dan Maiduguri ne, yakin Boko Haram ya sa suka gudo suka dawo Kano, suna wannan yawon Allah ya hadasu da Alhaji Ghali ya daukesu ya kai su gidan. Ya bawa Malam Habu aikin gadi ya basu boys quarters a gidan suke zaune, yaron Malam Habu sunan sa Khalil yaro ne fari kyakykyawa mai tsananin kyau, shekarunsa ba zasu wuce shekara goma sha biyu ba, zama suke cikin jin dadi dan Alhaji Ghali na wadatasu dama shi mutum nai mai tsananin kyauta, tun san da ya gamu dasu Allah ya dora masa kwadayin san Khalil duk da ba wani shi be masa ya ke ba, amma sai da Alhaji Ghali ya ja shi zuwa wajen sa har ta kai yana neman ya taya shi kwana, ana haka ya jashi don su kwana tare a daren yai masa fyade, wanda sanadin wannan fyaden Khalil ya rasa rayuwarsa abun da ya daga hankalin iyayensa musamman da suka ga gawarsa, anan suka shaida abun da ya faru, suka tuhume shi amma fafur yace baisan zancen ba, sunyi kokarin kai kara wajen yan sanda su kai musu bayanin yadda abun ya faru, tun da ficewa yai ya bar shi mahaifiyarsa taje taso shi taga gawarasa da danyen aikin da akaiwa Khalil, amma saboda kudi basu da wanda zai tsaya musu aka ce ba shi bane, kuma tabbas sunji ihunsa amma basu kawo shi bane a daren, kememe kudi su kai aiki aka rufe maganar,wannan bacin ran yasa Mahaifiyar Khalil ta hadiyi zuciya ta mutu, tashin hankalin daya shi ga ba kadan bane, a karshe ya rasa ta hanyar da zai dau fansa shi ne yai wannan tunanin, saboda yasan auren jisi kadai idan Alhaji Ghali yai shi zai tona masa asiri, wannan dalili yasa yai badda kama ya fara wuridi ya nemo aljani mulmuli, shi ne silar fara bokancin sa wanda ya samu kudi sosai daga garesu wannan shi ne silar bokancin sa kuma ya dau fansa wannan kena._



****************


Ba inda ya tsaya sai kofar gidan su Laila ya ai ka aka kirawo ta, sai da taja ajinta da kyar ta fito dan ta san jarabarsa ce ta motsa ya biyota, tana mota tana kallon ikon Allah ganin yadda ya ke lallabata wai ta shi ga mota ko wace yar iska ce wannan kuma?

Bakin ciki ya cika ta saboda sam bata gane Laila ba kishi ya rufe idon, "wallahi Lawan ba ka da mutunci na shi ga mota kai mun uban mai kuma? ka gama wulakantani a asibiti saboda ba ka sona kai mun sakin wulakanci yanzu kuma kazo ka daukeni kaje ka caccaka ko? to wallahi ba inda zanje inji ma da wahalar cikin da ke jikina da mai zanji?"

Habawa tana mota sam bata jin mai ta ke fada taga dai suna magana ana nuna mota, da zuciya ta debeta ta fito tana zuwa ba tai wata wata ba ta shake wuyan Laila ta gaura mata mari wanda sai da taga taurari, "dan uban ki wacece ke?"

Zata kuma magana ita ma taji saukar wani marin a kuncin ta, "uwar ki ce ita, matata ce ita mai yanci bake ba wawiya shashasha" ya kama Laila na ihu ya danna a mota ya sawa motar key.

Doctor Saudat duk ta haukace kamar ba wayayyi ba abun yai mata ciwo, bata san iskancin Lawan ya kai haka ba dole ta kara shiri, bakaken maganganu ta ke gaya masa bai ce mata uffan ba ya damkota har motar ta ya watsa, "ta kije zanzo na sameki wallahi sai kin raina kanki dan kan ki zaki tonawa asiri sakaryar banza kece kesan rufin asiri."

Idan kika kuma bibiyata da matata wallahi sai kin raina kanki, matatace Laila mutu ka raba tsakanina da ita ba mai jure halina sai Laila ita kadai tasan waye ni, kin gane?"

Wani hawaye nai ya gangaro mata mai kuna, dama wadda taga yana kusanta a asibiti ce amma sam bata gane taba kodan kishi ya rufe mata ido, Allah yasa bata gane ta ba ita gudun tonuwar asirinta dan Doctor dan fillo ya matsa mata yanzu kuma bata so yasan tai aure.

Tabbas ta biyewa san ranta ga shi tun ba'a je ko ina ba ta fara nadama, zata jure komai ban da duka daga namiji dan wallahi ta tsani namiji mai duka, duk da tasan yana duka amma bata san abun ya kai haka ba, duk da ta aure shi dan san ranta da kuma niyyar daukar fansa, dan haka dole tai kokari ta dawo da shi hanya, dole shi ma tasa a tara masa gajiya dan bai mari banza ba, tana hawayen nadamar auren Lawan taja motar ta dan shi har ya bar wajen.

Kuka Laila ta ke yana rarrashin ta da ke yasan lagonta nan da nan ya shawo kanta, lafiya kalau suka isa Taheer dan yayi kewar ta anan suka wuni dan ya maida ta dakin ta, amma tai rantsuwa bazata koma gidan ba sai dai ya kama mata gida.

Ya ce bai da kudi shi sam, "to shi ke nan zan kama da kaina" farin ciki ya lullube shi ya samu inda zai sa Hajiyan sa hankali kwance, "shi ke nan Laila ta shi ya sa nake kara kaunarki tayaya zan rayu ba ke, na amince kiyi yadda kike so ai ni naki nai, sai dare ya maida ta gida ta sanarwa kawunta ya maida ta dakin ta cike da tsananin murna da zakwadi, dan gaba daya jinta ta ke kamar akan kaya wannan zaman.

Ransa bai so ba sam amma ba shi da yadda zai saboda an riga an kwashe albarkar auren tun a titi, dole aure yaki dadi ba ganin mutuncin juna baya san wannan auren ko kadan, musamman yadda yaron ya zauna ya kalli tsabar idonsa ya din ga gaya masa maganganu saboda bai dauke shi da mutunci ba, yanzu kuma ya sake ta ba biko ba komai kuma wai ya dawo ya ce ya maida ta.

Duk da ya fuskanci laifin na Laila nai, dan ita ta ba shi dama duk abun da yake, shi ya sa ba'asan kabar yarinya har ta wuce minzalin aure ba kai mata ba karshe sai kayi nadama mara amfani, gashi saboda san ranta da tausayinta na rashin iyaye ya bar ta tayi karatu mai zurfi har ta fara aiki, wanda shi nai silar lalacewar ta da haduwar ta da wanda baya ganin mutuncin kowa baya jin kunyar kowa a hankali ya ce.

"Wato Laila na fuskanci ke kike bawa Lawan damar wulakantamu a duk san da yaso, duk diban albarkar da kuke wallahi idon mutane na kan ku duk abun da kuke ana kallonku idon mutane na kan ku, tun da aka fara wannan auren naku ba kwanciyar hankali a cikinsa ba albarka sam.

Ta fashe da kuka "wallahi kawu ka tsani Lawan ni nasan baka kaunarsa ko kadan, dan anga iyayena sun rasu shi ya sa ba'asan farin ciki na, yanzu mai yai kuma? ya ce ya maidani ai abun farin ciki nai" kuka take duk jikin kawu yai sanyi da tsananin mamaki ya ke kallonta yanda lokaci daya ta ke furta masa haka saboda san namiji.

"Shi ke nan Laila kiyi shiru ke amanace a wajena, bazan ci amanar dan uwana ba shi ya sa nake kulawa da lamarinki, amma ina so ki sani wallahi sai kin yi nadamar auren Lawan ko da a gaba ne wallahi!" Ransa ya sosu ya mike ya fice ya bar gidan.



*To fans mu hadu a next page insha Allah ni ce taku a kullum a koda yaushe.*

                *Feedyn Bash*



Pls
Share
Comments
Vote

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now