Ji yai an turo kofar cike da sallama "temakon ka muke nema Doctor wani patient ne damu" ya tsine fuska yai "Doctor Zubair ku je kawai" "sorry Doctor abun yayi worst ne ina ga fannin kane na zuciya."

Nan ba dan ya so ba ya mike suka je dakin, likitoci uku ne akan sa yana zuwa ya ga shi ne abun ya dake shi sosai, tabbas shi ne wanda su kai sa'insa akan Maryam sunan da ya ji an kirata da shi.

Ransa a bace ya fara duba shi dan wani mahaukacin kishi yaji yazo masa, an masa duk wasu gwaje-gwaje zuciyarsa ce tai mugun bugawa lokaci daya, Allah ne yai da kwanan sa a gaba kawai.

Abba ne ya kalli Daddy "to Alhaji yanzu yaushe kake ganin asa lokacin bikin tun da komai yazo karshe" ya fada yana ta murna.

Daddy yai murmushi "ai Alhaji ko yaushe  ka tsayar yayi" Abba ya ce "ai idan nine sati me zuwa ma a daura, kawai matsalar kayan daki ne ina bin bassuka sai an biyani" ya fada yana satar kallon Daddy.

"Ai idan dan kayan daki ne ka kwantar da hankalin ka, bana bukatar a kai ta da komai komai a kwai a gidan kar ka damu." Jikin sa sai rawa yake nan Daddy yai masa alkawarin makudan kudi dan yai hidimar dasu amma asa wata biyu yayi.

Abba farin ciki kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan murna, suna wannan hirar Momy ta shi go tana kuka ta sanar musu halin da Arfan ke ciki, hankalin su yayi masifar ta shi na jin abun da ke faruwa, lokacin da suka je likitoci sun hanasu shi ga dakin suna kan aiki.

An gama duba shi Doctor Zubair ne yace Daddy ya bishi office, bayan sun je yai musu bayanin komai na bugawar zuciyarsa kuma tabbas yana da damuwa, bashi abun da yake so shi ne masalaha idan ba haka ba komai ze iya faruwa da shi.

Tun da Doctor Mahmud ya gano matsalar hankalinsa ya tashi ya koma office ya hada kai da gwiywa, tabbas ya ga tsagwaron soyayyar ta a idonsa mijin yayar ta, "ya ilahi" abun da kawai yake iya furtawa kenan.

Da hanzari ya mike ya fita ya nufi dakin da take ya tura kofar a hankali, Umma ce zaune a kujera ta kurawa ruwan dake shi ga jikin ta ido a hankali daidai lokacin ta farka ta bude idon ta.

"Wayyo Allah Umma! innalillahi wainna'ilaihir raji'un! Allah kasa mafarki nake, Daddy ne yake so na innalillahi wainna'ilaihir raji'un! wallahi Arfan ka cuceni ka gama da rayuwata ina zan sa kai na" kuka take sosai maganar ta daki Doctor Mahmud.

Umma tai kan ta Doctor Mahmud ya karasa shi go wa ya ce "ya isa haka baki da lafiya a yanzu kina bukatar nutsuwa ki nutsu please." Umma ta ce "bar ta ta fadi abun da ke ranta wannan wane butulci ne haka da zallar kwadayi da san zuciya.

Wanda ya rikeke shi da yayarki ki rasa wanda zaki aura sai mahaifinsa, ki kishi da uwarsa, to muddin kika amince a kai wannan cin amanar babu ni babu ke." Ta fashe da kuka da hanzari ta tsige karin ruwa yana riketa ta fisge ta diro kasa.

Rungume Umma tayi "wallahi Umma bana san sa ko Abba zeyi gunduwa gunduwa da nama na bazan aure shi ba, Umma ki bani ko waye na yarda na amince zan aure shi, zan miki biyayya na zauna da shi har karshen rayuwata na miki alkawari Umma."

Besan san da bakin sa ya subuce ba "idan kun amince na yarda zan aureta, dan ina san ta!" da sauri suka kalle shi wata muguwar kunya ce ta kamashi saboda ganin Umma sam ya manta da ita, besan san da maganar ta subuce masa bane.

Kunya ce ta kama shi amma ya kanne Umma ta maze duk da Allah yai mata kunya tace "zauna mi magana" suka zauna dukansu.

"Ina so ka gayan tsakanin ka da Allah zaka aure ta?" "eh Umma zan aureta har ga Allah" wani farin ciki ya cika zuciyarta ita ko Maryam tun da ya shi go take jin zuciyarta na tashi saboda warin turaren sa, kawai daurewa take kafin kace meye wannan ta fara sheka amai.

Abun da ya daga hankalinsu kenan kallo daya yai mata da kalar aman da take hankalinsa ya tashi ya fice da sauri.

***************


Nan da nan aka kai Maimuna emergency room aka bata temakon gaggawa, tashin hankali ne ya sa ta faduwa amma bata da komai an mata text har na ciki.

A haka suna cikin tashin hankalin rasuwar Inna me koko ya kira Malam ya sanar masa, nan da nan ya sanar da jama'ar unguwa ya taho asibitin kafin yazo har Maimuna ta farka kuka take kamar ran ta ze fita.

Sai da su kai cike-cike aka basu gawar suka tafi gida, a ranar akai mata sallah karfe hudu aka kai ta makwancin ta na gaskiya.

Haka aka din ga zaman makoki makota sun yi kokari sosai saboda Inna anyi zaman lafiya da ita mutum ce ta mutane 

Haka kawu kullum sai an kawo abinci daga gidan sirikan sa dan iyalansa suna gidan, abinci ne lafiyayye da kaji da naman rago da lemuna alhamdulillah anci an sha.

Bayan sadakar bakwai kowa ya watse sannan mutuwar ta dawo musu sabuwa danya sharaf, amma kullum cikin godiya ga Allah yake da Inna bata mutu ba sai da taga danginta, kullum addu'a suke mata ba dare ba rana,

Maimuna sam bata jin dadin zaman gidan yai mata kunci saboda rashin Inna, sun saba sabo me yawa sun shaku shakuwa me yawa, ita take mata wanka tai mata tsarki ta bata abinci ta kasa mantawa da ita.

Bayan kwana arba'in da rasuwar kawu yazo ya samu Malam tun da shi ne kamar mahaifin Bello, ya sheda masa komai na dukiyat sa amma yasan baze iya kula da kamfanonin sa ba saboda karancin ilimi, saboda haka ze kai shi waje shi da matarsa suyi karatu.

Farin ciki ya cika Malam na wannan cigaban daya zowa Bello, kullum fatansa ya samu ya koma makaranta ashe bama a kasar ze ba, Malam yayi farin ciki ya sawa abun albarka.

Aka kira Bello ya gaya masa komai yayi murna yayi farin ciki sosai, su kai addu'o'in nuna godiya ga Allah kuma ya ce sisi be tabawa a kudin Bello, za'a din ga juya masa har ya dawo, kuma karatun shi ze dau nauyin su har su dawo.

Haule kafa ta yi kyau ta warke yau ta shirya tsaf dan zuwa ta ciwa Indo mutunci, taci uwarta da ubanta ta rufe gida ta shi ga makota tayo gayyar makotan ta masu zugata suka shi ga gidan Indo.

Tana zaune dake cikin me laulayi ne tana ta shara amai suka sa kai gidan, ba sallama tana tsugune tana shara amai wani ashar da Haule ta saka tai kanta ta fara dukanta kamar Allah ya aikota, suko kawayen ta dariya suke suna kara zugata gashi Indo tayi weak bazata iya kwatar kan ta ba.

"Wallahi sai na kashe ki ban da cin amanar da ki kai mun kin rabani da mijina da bakin asirin ki, hakan be miki ba sai kin dau ciki a gidan mijina, karya kike wallahi tsinanniya."

Sam jikin Indo ba kwari bazata iya kwatar kanta ba, kawai cikin take hara Allah ya bata sa'a daidai lokacin da ta daki cikin, daidai lokacin Malam ya shi go, "innalillahi wainna'ilaihir raji'un!" Kawai ya iya furtawa ya karaso, yana zuwa ya wanka mata mari ya kara mata wani.

Ai da ta daka tsalle sai tai kan randunan ruwa ta sauka akan su ta fashe su ji kake tim, ta din ga hauka ta dakko ice ta ce sai ta fashe musu kai, kafin kace meye wannan Indo jini ya fara bin kafarta da sauri Malam ya kira me adaidaita sahu a waya.

Ya kalli ragowar matan da su kai fiki fiki sun rasa ya zasi da Haule dan kamar ta zauce, kunya ta gama isar su duk sun firgice ya kallesu "dukkan ku kun kyauta, amma muddin na rasa dana wallahi sai kun yi nadama dan sai nai kararku.

Ke kuma Haule ki gama fashe fashen ki wallahi sai na dakko na gidan ki na kawo mata duk abun da kika lalata, kuma zan dawo na sameki zaki girbi abun da kika shuka" sai sannan ta shi ga hankalinta saboda sanin halin malam din sarai musamman yai zancen kotu.

Ga matan da suka rakota suka zugota sunce masa sam ba haka sukai ba ca tai zata zo yi mata murna basu san haka ba, suka bada hakuri suka bar ta a gidan suka zuke, Malam ya rike Indo suka fitadaga gidan, da gudu ita ma ta fice hankalin ta a matukar tashe sun kai ta sun baro.

Sun gama jika mata aiki gida ta koma kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ai da sauri ta zari mayafi ta bazama gidan Malam dan kawo kawo karshen Indo ta kwato mijin ta fatan ta daya cikin ya zube gaba daya dan barazane ne ga zaman auren ta.

*To fans mu hadu a next page, ni ce taku a kullum a koda yaushe mesan ganin farin cikin ku da walwalar ku.*

              *Feedyn Bash*

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now