Wajen ya bari ya koma dakin da aka kwantar da Momy, ya hada kai da gwiywa ya din ga kuka kamar karamin yaro, a hankali a ka turo kofar aka shi go.

Momy ce ta zauna a gefen sa ta rungume shi, ta fashe da kuka ita ma, "wannan wace irin masifa ce ta shi go rayuwar gidana? ga babanka can rai a hannun Allah, saboda san da ya kewa wannan yarinyar, kuma likita ya tabbatar da cewa in dai be samu abuda yake so ba zuciyar sa zata iya bugawa."

Da wanne zan ji? kai kuma ga kalar taka masifar ta san kanwar matar ka, to na gama yanke hukunci wallahi ko yai wa kowa dadi ko a kasin haka, amma bazan zuba ido rayuwar gidana ta salwan ta ba." Ta rungume shi tana rarrashin sa suna kuka dukan su.

Duk maganar da suke a kunnen Umma tazo wajen Momy, saboda Abba na wajen Daddy ya farka yace a kirata, amma har yanzu jikin sai godiyar Allah, taji wannan batu fasa shi ga tai ta koma da baya tana rusa kuka.

Ji tai ance "kiyi hakuri Hajiya zata warke, mun shawo kan matsalar firgita tai, akwai abun da ya firgita ta saboda haka yanzu sai dai kuyi hakuri har ta farko, amma karku tuna mata da abun da ya faru, ze iya kara jefa ta cikin wani halin."

Ana haka taga Momy ta fito a fusace tayi dakin da aka kwantar da Daddy, da sauri ta rufa mata baya, tana shi ga ta bita ta zubawa Daddy ido cike da tausayi da zallar so, "Alhaji in dai saboda ni ce na yarda na amince da bukatar ka, saboda haka ni zan nemi wannan alfarmar da kai na."

Wani zafin nama ne ya zowa Umma ta toshe mata baki, "kiyi wa Allah kiyi hakuri ki rufa maganar nan," tana maganar tana hawaye, ta bambare hannun nata da karfi, a she kin ma san komai, to wallahi abun da baze yiwu bane ko a mafarki.

Kiyi hakuri nasan kece mahaifiyar Maryam ga mahaifinta, ina rokon alfarma ku temaka ku aurawa mijina, baban Arfan mijin yar ku Nafeesat auren kanwar Nafeesat, ga baban Arfan ma'ana mijina Alhaji Kamal.

Wata zabura Abba yayi ya mike, "me kika ce Hajiya?" "abun da na fada haka ne alhaji a rai na, ina so ka yarda ka amince da bukatar mu." Da gudu Umma ta fice tai dakin da Maryam ta ke, tana kuka kamar ranta ze fita.

"Maryam kin tarwatsa farin cikin mutane da dama, meyasa zaki mun haka ba kalar tarbiyyar dana baki ba kenan, dole akwai lauje cikin nadi game da zaman ki gidan Nafeesat, har ga Allah ba'a san rai na kike zaune ba, dan dai mahaifin ku yafi karfina ne ga kwadayi da san abun duniya da yai masa yawa."

"Hajiya kin san me kike cewa kuwa? "na sani Alhaji wannan shi ne dalilin daya kwantar da mijina a gadon asibiti da ni kai na, saboda haka muke rokon ka ni da shi akan wannan batun."

Yai shiru yana tunani "ka dena tunani Alhaji komai mun dauke ma a wannan auren, zaka samu manyan kyaututtuka daga wajen Alhaji ka kwantar da hankalin ka, kawai yardar ka muke nema kai ne mahaifin ta.

Jikin sa har rawa yake saboda san abun duniya, "Hajiya in dai ku kun amince ai ni me sauki ne a wajena, tun da ku kuka nema." wani kakkai fan abu ne kamar mashi ya soke Momy a zuciyarta, jin furucin Abba amma ta danne saboda tasan kishi ne.

"To mungode Alhaji sai a ta shi daga gado haka, na amince mahaifin yarinya ya amince, bukata ta biya sai ka mike." A hankali ya ta shi zaune fuskarsa cike da walwala, "nagode sosai Hajiya Allah ya biya ki jihadin da ki kai, ban da bakin godiya a agareki." "Ba komai" ta juya ta fice da sauri saboda hawayen da ya zubo mata.

Har yanzu kuka yake ta koma ta same shi a kwance lakadan yana hawaye, "dama ka hakura da kukan nan Arfan ka rungumi matar ka, saboda a halin yanzu an riga an bawa mahaifin ka Maryam." "What?" ya fada da karfi ji kake tim ya fadi.

 
       *********************


Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! shi ne abun da mutanen dake wajen suke fada, kafin kace meye wannan likitoci sun dauke shi zuwa emergency, iyalansa kuka suke suna cewa su Maimuna mayu ne, wallahi idan ya mutu sai sun yi shari'a dasu, suma sai sun kashe su sun bi hakkin babansu.

Tashin hankali ba irin wanda basu shi ga ba, saboda wannan sharrin da akai musu, kafin kace kwabo Yan sanda sun zagaye su da duk wanda ke dakin, dan sun ce binkicen ya shafi kowa.

Kuka Maimuna ta ke tana addu'a a ranta,  ta kalli Ustaz Bello "sai da nace ma ka bari na sai da keke na daya da fridge amma kaki, ga shi yanzu bamu ji ba bamu gani ba kaddara ta fada mana, da ace mun siyar da yanzu an mata aikin." ta kara rushewa da kuka me tsuma zuciya.

Kiyi hakuri matata, tabbas ke Yar aljanna ce, wannan kaddara ce ta bakin naki, amma ba komai Allah shi ne gatan mara gata, shi ze fitar mu daga wannan mummunan zargin.

Duk wanda ke wajen ya tausaya masu ainun, amma wasu mutanen sai tsine musu suke suna mayune su, Allah ne ya tonu asirin su dama wannan kyan nasa shi da mahaifiyar tasa ai daga gani mayu ne.

Kusan awa uku sannan wannan Alhajin ya farfado, yana farfado wa ya fara kiran 'Tata! Tata!" likitoci su kai kansa, ya tsai dasu "ku kai ni wajen yar uwa ta, ku kai ni naganta." Ya fashe da kuka kamar karamin yaro.

Nan da nan aka kira matarsa da yaransa, suka shi go suna kuka "Amina ki tayani yiwa Allah godiya, yau Allah ya nuna min Yar uwata Tata, wadda nake baki labari ita kadai ce ta rage mun a duniya."

"Wacce kake nufi Alhaji? kad dai  wadda ka yanke jiki ka fadi a wajen da suke?" "eh ita ce, ita ce ku kai ni naga yayata."

"Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! Alhaji rashin sani yafi dare duhu, ai mu mun dauka mayu ne, mun kai Yan sanda suna gadin su saboda kar su gudu, ganin lokaci daya daga ganin su ka suma haka."

"Yasalam muje dan Allah kar wani abu ya samu yayata, muje Amina." Da hanzari ya sakko daga gadon suka nufi dakin, daidai lokacin jikin yadan lafawa Inna me Koko, ta dan farfado tana ta bawa Maimuna baki, ta dauka saboda lalurar ta take kuka.

Suka karaso wajen kowa kallon su yake cike da mamaki, yana zuwa ya rungume Inna me Koko, abun da ya bawa kowa mamaki kenan! "Yaya Tata dama zan kara ganin ki a duniya baki rasu ba?" duk dakin mamaki su kai karma Bello da Maimuna suji labari, sun zama kamar gumaka.

A hankali ya daga ta murna fal fuskarta, "Ahmad maza daga ni zaune yau na ganka" da sauri Bello ya temaka masa suka dagata, ta kara rungume shi suka din ga kuka, "Ahmad ina su Addar mu? da Baffana? da Yan uwana?" ya share kwallar sa "Yaya kowa ya rasu a wannan lokacin, ni kadai nai saura da dukiyar mu, nida Baffa munzo garin nan neman ki bamu same ki ba.

Haka mu kai ta garari ga kadarorin mu na gwalagwalai da lu'u lu'u, mun neme ki mun rasa, har Allah ya hada mu da mahaifin Amina, shi ya temaka mana aka seda su suka zama kudade, wanda bansan adadin yawan su ba a lokacin, babanmu ya raba kaso biyu yace ni daya, daya na kine in ajiye har Allah ya hadamu, shi yasa nake yawo dasu duk inda zani, mu kadai muka rage ko bayan ransa.

Mahaifin Amina shi ya tsaya mun nai karatu na, ya bude mun kamfanoni wanda suke aiki a yanzu, Baffa ya rasu da dadewa yaso ya ganki Allah beba, amma Alhamdulillah! yau zan sauke nayin dake kai na, duk wata dukiya taki tana nan a hannuna sisi ban taba ci ba, kullum juyawa ake ana adana miki.

Amina ki zama sheda yau zan cika tsohon alkawarin mahaifina na bawa yaya ta dukiyar ta, dakkon jakata a mota." Ana kawowa ya zaro wani file ya mika mata, tana kuka tana bata so ita ta bar masa, ga dan ta nan ya kula mata dashi, amma dole suka sa ta karba.

Ta rungume yaransa da matarsa, ta damka file din ga Bello, na baka halak malak wannan naka ne dana me biyayya, Allah ya saka ma da gidan aljanna kai da matarka, burina ya gama cika naga ahalina ko yanzu na mutu Bello baka da matsala, kana da gata a duniya ga kanina nan shi ne a matsayin mahaifinka.

Ta rungume su dukkan su sannan ta kankame dan uwanta tana hawaye, kunsan minti biyar bata cika shi ba, ya zare jikinsa ya ga ta tafi ragwaf, ya taba ta ba wani bayani, nan da nan ya kira doctor yana zuwa ya dubata sosai, kawai yaja zani ya rufe ta ruf gaba daya dakin ya kaure da salati.

Wani kallo maimuna ke musu kamar almara, wai me kuke nufi ne bangane ba? yayana me hakan ke nufi naga an rufe Inna kowa na kuka?"

Alhaji Ahmad ne yai zaman Yan bori a kasa ya fashe da wani gurshekan kuka, Allah ya jikanki Tata, Allah yai miki rahma, jiri ne ya kwashe ta ya buga ta da kasa, da gudu su kai kanta anma taje kasa.

*To fans nagode sosai, ku kara hakuri dani sai mun hadu a next page, nice taku a kullum a koda yaushe, me san nishadin ku da farin cikin ku, nagode masu yi mun ta'aziyya.*



                 *Feedyn Bash*

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now