11 & 12

2.9K 59 2
                                    

_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_



             _IN BETWEEN THE LOVE_
            ❤ _Lies another love_❤


            _✍🏿M Shakur_

                        1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣

_How to subscribe_

_*zaki tura 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watdsapp number na 07012181461. For those da basu da account you can also send MTN card ta watsapp number na saina saki a group din danake posting*_


_Free page_
Shigowa dakin Dady yayi sanye da jallabiya fuskarshi lema leman ruwa alamun kaman alwala yayi hada ido sukayi da Dady yana zaune kan kujera, bedroom dinshi Dady yawuce baiwani jima acikiba yafito dawani white iron jallabiya mai kyau namaka yafito daga dakin nashi yace "tashi kasa mutafi masallaci" turo baki yayi yana karasa shan yoghurt dinshi yace "ni banyi alwala ba" ajiye jallabiyan Dady yayi kan saman kujera yazo inda yake ya karbe cup din hanunshi yace "you and yogurt, give me the cup" ya karbe cup din ya ijiye akan center table yace "to tashi kashiga nan visitors toilet kadauro alwala Son, kaga anma fara kiran salla" gyadamai kai yayi yamike tsaye ahankali yana tafiya kaman baison yi ya shiga bayin Dady yabi bayanshi da kallo kafin yadau cup din yogurt din daya ijiye yawuce kitchen yaje ya ijiye a cikin sink, fitowa yayi daidai shima yafito daga bayin daure da alwala Jallabiyan Dady yadauka yamikamai karba yayi yasaka suka fita daga dakin sukai masallaci Dady nabashi labarin yanda yayi dasu Mama da Khamis dazu har mari saida yama Khamis lafiyayyu guda uku da yaso ya kulleshi ma da kyar yahakura bayan sunbabbashi hakuri, murmushi kawai yayi yanajin Dady harsuka shiga masallaci. Saida sukai isha'i sanan suka dawo gida zaiyi part dinshi Dady yace "let's go to side dina muyi dinner" girgixa kai yayi yanadan lumshe ido ahankali yace "am sleepy and am not hungry Dad, I love you gud night" tsayawa Dady yayi yana kallonshi kafin yadan numfasa yace "shikenan gud night kiddo I love you more" turo bakinshi yayi yace "Daddd kiddo kuma" hancinshi Dady yaja yace "kafito da mata namaka aure kaga idan nakara kiranka da Kiddo" dan dariya yayi yace "nay nay na" tallabe keyanshi Dady yayi yace "zakaci gidanku da nay nay na ne, motar waye a pake a gaban side dinka?" Dady yay maganan yana kallon gaban shashinshi dansai yanzu ya lura da motar, juyawa yayi ya kalli shashin dan murmushi yayi yace "is Abdul Dady, bye gud night bari naje" yafada da sauri yana tafiya, murmushi Dady yayi yace "su aboki anzo har ana sauri ko an manta dasu Dady" juyowa yayi da sauri jin maganan da Dady yayi da sauri yaje ya rungume Dady yay lamo a jikinshi ahankali yace "you know you are the best Dady in the whole world" shafa bayanshi Dady yayi yana washe baki yace "and you are the best son in the whole world Aliyu am a proud father to this yaro maijin magana just a lil stubborn and annoying atimes" dariya dukansu suka fashe dashi a tsakar gidan atare kafin sundanyi shiru yana jikinshi har lokacin, murya chan yace "Dad" anatse Dad dake rike dashi  yace "na'am Gadanga na" ahankali yace "you are my Dady and My Mummy, kamaye gurbin Ummi, baka taba bari naji kewanta ba, you feel that hole in my heart, you are my everything Dad, and happy Fathers day" rungume shi tight Dady yayi his heart is so swollen kalman Mum daya fada yasa yatuna da marigayiya matarshi the best wife daharyau yakasa samun kamanta shiru sukadanyi for a while kafin yasaki Aliyu yana share hawayen dasuka cikamai ido da sauri dan karya gani sanan yay murmushi yace "wuce katafi Abdul na jiranka, zan aiko muku da abinci" gyadamai kai yayi ahankali yace "bye Dady" "bye son" juyawa yayi yay part dinshi Dady ya tsaya yana kallonshi saida yaga shiganshi yawuce yay part dinshi shima.

Ahankali yabude door din part dinshi babu kowa a falon sai manyan jakunkunan kwali da aka rubuta Men by Robanni wears ajiki hakan yasa yagane kayan bikin dazasu sakan gobene Abdul ya karbo musu din, hanyar bedroom dinshi yayi, bude kofa yayi ya shiga babu kowa adakin sai car keys da waya dake kan gado karan ruwan dayaji yasa yagane yana bathroom, dan ajiyan zuciya ya sauke ya zare jallabiyan jikinshi yay hanging a hanger yasaka a wardrobe sanan yazo yafada kan gado.

ATSAKANIN SOYAYYA (In Between the Love) Where stories live. Discover now